Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 45

Sponsored Links

XLV
<45>

*MunayaMaleek is Five hundred naira, pay to 3200689860 Haruna Rukayya first bank, then send evidence of payment to my WhatsApp number, 07082281566(don’t call me, chat only please)*

 

Related Articles

Tun karfe shida da rabi ya iso gidan doctor Aaban saboda yanda ya kwana da abinda ya faru jiya a ransa, amma sai ya kasa yin horn, domin gani yake kamar babu dacewa ya shiga tun Masu gidan basu tashi ba, amma da yake ganin gashi ga gidan hankalin sa yafi kwanciya.

Bakwai da yan mintuna kalilan ya danna horn, mai gadi ya leko, ya koma yana buɗe gate, domin ya dade da shaida Maleek.

Yana shigar da hancin motar sa cikin gidan ya ga fitowar Munaya tare da little Amnah, little sai surutu take zubawa Munayan duk da baya jin abinda take cewa, amma ya ji sanyi a ransa, domin bai taɓa expecting ganin ta cikin farin ciki haka ba bayan irin kukan ɗaya ji tana yi jiyan.

Ya dauke idanun sa daga kallon little, ya zuba wa Munaya, wacce take sanye da jilbab fari kal da canvass baki daya yiwa ƙaramar kafar ta masifar kyau, a yau bata saka siririn farin glass dinta ba, babban glass na ado ta kafa a saman kanta brown color, ta rataya wani mini bag a kafada, duk da cewa babu makeup a fuskar ta amma tayi masa wani masifar kyau, yayinda take looking so fresh, ya lumshe idanun sa yana sauraran bugun zuciyar sa.

Munaya ta zo daidai inda motar sa take sannan ta saki hannun little Amnah ta mika mata lunch box din ta kana ta yi gaba.

“Mummy ba zaki shiga motar Daddy ba?”

Munaya ta girgiza kanta tana yin gaba, wato yarinyar nan bazata daina haɗa ta da uban ta ba, ta fada a ranta, duk da akwai motoci a gidan, amma tafi son ta fita titi da kanta domin bata son ya Zamana cewa tana takurawa mutanen gidan, duk da cewa barrister Abrar ta hana ta fita titin kan tana bari a kai ta amma ta ki, ita a ranta sai tana ji kamar dawainiyar da suke da ita da little yayi yawa, duk da cewa they are not complaining Kuma babu alamun gajiya a tare da su.

Tana cikin tafiya taji ana mata sallama, ta waiwaya ta ga wani saurayi hadadde cikin motar sa yana driving slowly, haka kawai ta tsinci kanta da tsayawa ba dan tayi niyyar hakan ba, musamman ganin motar Maleek din ta kusan karaso inda suke, ta amsa sallamar fuskar ta a sake sosai.

Yace “yanmmata kina lafiya ina zaki?”

“Gwarinpa” ta amsa masa a takaice.

“Please shigo na ajiye ki idan babu damuwa”

Daidai lokacin da motar Maleek ta karaso wajen, wani irin cute smile Munaya ta sakar masa daya sanya Maleek kauda idanun sa yana kokarin controlling kansa domin ji yake kamar ya fita ya garwatsa wanna tsayuwar da suka yi yake ji, idanun sa ya sauya cikin kankanin lokaci, ya wani ja motar da mugun speed har kura ta na tashi, Munaya ta bi motar da kallo, ita kam Allah ya tsare yarta dai kar yaje ya watsa ta a titi shine addu’ar ta, shima saurayin ya bi motar da kallo kana ya dawo da kallon sa ga munaya yace “Please shigo”

“A’a na gode sosai bawan Allah” Munaya tace tana yin gaba.

Ya bita da kallon ban so hakan ba, domin da farko yayi tunanin ya samu nasara musamman ganin yanda take masa fara’a.

“Daddy Ina ta cewa ka tsaya ga mummy na ka…”

“Shut up angel!” Maleek ya buga wa little Amnah tsawa a karon farko tunda aka haife ta.

Sosai tsawar ya gigita ta, domin sabon abu ne a gare ta daga gare shi, sai ta fashe da kuka tana rufe bakin ta da hannu ta.

Zuciyar Maleek na tafasa, yayinda take kara hargitse wa, ya lumshe idanun sa kana ya bude su cikin sauri ganin ya kusan yin karo da wata mota.

Bayan sun iso makarantar ya tsayar da motar hadi da cire mata seat belt, sannan ya janyo ta kan cinyar sa ya na bubbuga bayan ta, cikin rarrashi yace “I’m sorry angle”

Sai yarinyar ta ƙara sautin kukan ta ya runtse idanun sa da karfe, yana nadamar wanna ihu da yayi mata, amma ya kasa sarrafa kansa ne, musamman da kwakwalwar sa ke cigaba da haska masa munaya na yin murmushi ga wani can, bai taba sanin cewa tana da dimples ba sai data yi wa wani can murmushi, tabbas Munaya na dab da hauka ta shi.

Abinka da Kuruciya tuni ta manta ihun da yayi mata, ta dawo da walwalar ta amma fuskar ta yayi mugun ja, ganin tana dariya ya saka masa dan nutsuwa.

Munaya na sanye da sky blue din uniform, yayinda ta saka medium hijab, tayi wani mugun kyau cikin uniform din, cikin kwarewa ta saka wani kayan aiki a baki mai suna *ultrasonic scaler* tana cire wa patient din ta *plaque da tartar* a haƙoran daya sauya kala daga fari zuwa brown, aikin take amma rabin hankalin ta na ga little Amnah, domin ba ƙaramin tsorata tayi da irin uban gudu yayi ba, kawai daure zuciyar ta tayi dazun, a ranta tana addu’a Allah ya sa ya kai mata yarinya makaranta lafiya.

Maleek kuwa na zaune a office dinsa, yana aiki yana kuma duba lokaci domin dauko little, hankalin sa a rabe yake, tunanin hanyar da zai ɓullo wa Munaya yake.

“She’s too stubborn” ya fada kamar mai rada yana shafa kansa hadi da furzar da iska mai Dumi daga bakin sa, wanda hakan ya saka ya shaki ƙamshin da bakin sa ke yi a hancinsa.

*Kano tumbin Giwa*

Doctor Abbas na zaune a falon mahaifiyar sa, yayinda yanmmata biyu na zaune a gefe da gefen sa suna hira cikin so da kaunar junan su, daga Irin kamanin da sukayi zai tabbatar wa mutum da cewa su din jini daya ne, babbar mai suna Amina tace “yaya dan Allah ka lallaba Hajiya ta barmu ayi DJ da bikin mu, kaji wai bazaa yi ba, wai ita bata son bidi’a, kuma wai baza mu gidan kwalliya ba, sai dai ayi mana light make up a gida ko muyi da kan mu” ta fada kamar zata yi kuka.

Abbas ya bude baki zai yi magana kenan
Dattijuwar mace doguwa ta shigo dakin bakin ta ɗauke da sallama, duk suka amsa, kana yanmmatan suka mike suka basu wuri, ta zauna kan kujera, kallo daya zaka mata kasan tsayayyar mace ce wacce bata wasa da ya’yan ta bare tarbiyyar su, doctor Abbas Yace

“Barka da shigo Hajiya”

“Yawwa babana, mun tashi lafiya, TOH Allah ya yi albarka, Allah ya tsare ka da sharrin masharran ta ya kuma kara budi, kuma dan Allah a a cigaba da riƙe gaskiya da amana sai kaga Allah yayi kara maka daukaka ta hanyar da baka taɓa zato ba”

“In sha Allah Hajiya ngd” yace cikin farin ciki da samun uwa ta.

 

“Madallah! Jiya na dawo daga makaranta a gajiye bamu samu mun yi maganar daka ce xamu yi ba”

Ya gyara zaman sa, kana yayi kasa da kansa yace “eh dama Hajiya mun daidai ta da yarinyar da nake so ne”

Cikin maɗaukakin farin ciki Hajiya ta washe bakin ta daya bayyana haƙorin Makkah’n ta, sannan tace “Masha Allahu, nayi farin ciki da jin wanna maganar, Allah ya nufa babana” ta karasa da dariya.

“Wallahi Hajiya…” Doctor Abbas ya amsa da murmushi cikin jin kunya yana tuno kyakkyawar fuskar munaya, yayi matukar kaguwa da son mallakar ta matsayin matar auren sa.

Hajiyar sa ta katse masa tunani da cewa “yar ina ce, a ina kuka haɗu babana?”

“Ammmm yar can Abuja ce”

“Masha Allah, iyayen ta ma yan can ne?”

“Ai Hajiya marainiya ce”

“Ayyah, Allah ya jikan Muslimi”

“Ameen Ameen”

 

“Toh gaya min wacce ita, gidan da take, inda ya so gobe sai na je can kawo gidan kawun ka sai a fara shirye-shiryen zuwa can Habujan nema maka auren ta”

A da ya yanke shawarar bazai bayyana cewar munaya na yarinya ba, tunda ba gari daya za su zauna ba Hajiyar ba so bazata sani ba.

Ya tuno irin yadda little Amnah bata rabuwa da mahaifiyar ta, idan yan’uwansa suka gani fa, ya kuma tuna cewa Yan uwan baban sa zasu je nema masa auren kuma dole zasu yi bincike, ya san Hajiyar sa ta tsani karya, is better ya gaya mata gaskiya tunda Allah ya sa mace ce mai zurfin kan ilimin addini ya san zata fahimce shi.

“Kayi shiru babana” Hajiya tace tana kallon sa.

“Eh Hajiya… ita yarinyar tana da, tana da y’a”

Hajiyar ta gyara zaman ta jin yayi maganar da bata yi zato ba.

“Ban gane ba, ita yar taka ce? Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, kar dai ka sauya hali babana, wanna ba tarbiyya ta bace”

Cikin sauri yace “a’a Hajiya ba yata bace”

Hajiya ta sauke numfashi, sannan tace “kenan bazawara ce, kuma har kake tunanin aurenta, yanzu Abbas duk matan garin nan da can Habujan ka rasa budurwa sai wacce ta haihu?”

“Hajiya ba abinda kike tunani bane, nutsatsiyyar yarinyar ce, kaddara ce ta fada…”

Ta katse shi da cewa “Allah ya bata ikon cinye jarrabawar ta, amma kai kam ka hakura da ita ka samo wata, idan kuma ka bani zabi kuma toh shikenan”.

“Hajiya kiyi hakuri wallahi ina son ta”

Cikin ɓacin rai Hajiya ta fara yi masa fada domin har idanun Hajiyar kifkiftawa suke wanda hakan al’adar ta ne, matukar tana cikin ɓacin rai haka take yi, ta ɗora da cewa “ina magana kana jayayya da ni saboda baka da tarbiyya ko soyyayya hauka ne, tun yanxu ina fada kana fada ina ga ka aure ta? Toh yi maza ka cire ta a ranka ka musanya ta da wata, domin matukar nice na dauki cikin ka wata tara da kwana takwasss na haramta maka auren yarinyar can, idan kuma ban isa da kai ba, ka je kayi duk abinda ranka ke so, amma ka sani bani ba kai”

Abbas ya ji tamkar ya ruza ihu, hankalin sa yayi mummunar tashi, yanda Hajiyar sa ke da ilimin addini bai taba tunanin zata ki ba, ya san ita ɗin kaifi daya ce, macece mai zafi da kuma sanyi, duk da haka bai yi tunanin zata fahimci maganar da wata fuska ba, ya mike kamar wanda kwai ya fashe wa a ciki ya fita, kannen sa dake madaidaicin haraban gidan su a zaune suka bishi da kallon tausayi kamar su mai kuka.

Abbas ya samu wani kofar gida nesa da na su ya zauna, ya yi ƙasa da kansa cikin tunanin mafita, a irin son da yake wa Munaya baya jin zai iya hakura da ita, domin tun kafin ta haifi little Amnah yake kaunar ta, ace lokaci daya ya hakura da dakon da yayi na soyyayyar ta, bayan ya samu nasarar datsa soyayyar sa a zuciyar Munaya.

A wanna rana gaba-daya bai da walwala har dare, bai kuma kara shiga inda Hajiyar sa take ba, itama bata neme shi ba domin kada ya dauka da wasa take, sai abincin sa ta shirya a cooler ta ce kannen su kai masa, suka tarar da shi a kwance kamar mara lafiya, ya mike zaune ganin su, karamar ta ajiye abincin tana cewa

“yaya gashi in ji Hajiya”

ya jinjina kansa kawai, babbar tace “yaya ko zaka yiwa baaba sabuwa magana? Na ga tana iya tausar hajiyar idan ta dauki zafi kuma tana jin maganar ta”

Cikin sauri ya cire hannun sa ɗaya dafe kansa da shi saboda ciwo da yake masa, murmushi ya wanzu a fuskar sa yace “Meyasa ban yi tunanin hakan ba tun dazu? in Sha Allah zan shirya zuwa wajen ta gobe, ngd kanne na”

Da wannan ya samu karfin guiwar cin abinci har ya kira Munaya suka sha soyayyar su, baiwar Allah munaya har da cewa ya gaida mata Hajiya.

 

_Hajiyar doctor Abbas fa boss ce, amma Meye kuke tunani zai faru? Ni dai gwara ayi auren doctor Abbas din da Munaya kila Maleek ya kara shiga hankalin sa_😂🙌

#MunayaMaleek
#NoorEemaan
#Paid book
#destiny
#love
#betrayal
#selfishness
#earttouching

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button