Hausa NovelsNi da Almajirina Hausa Novel

Ni da Almajirina 1

Sponsored Links

NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 1

_NOTED# WANNAN SHINE LITAFINA, NA FARKO WATAKILA SHINE NA KARSHE 🥹 IDAN KUN GA KUSKURE KUYI MIN AFUWAN 👏🏼_

Related Articles

*ALHAMDULILLAH*
*Dukkan yabo da Godiya sun tabbata ga ALLAH mai kowa mai komai, da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi mai suna “NI DA ALMAJIRINA” ina roƙon Allah ya bani ikon rubuta abin da al’umma zasu amfana da shi Amin. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammad SAW*.

_I dedicated the whole book to MissDmk my one and only Sister🫡Thank you for your endless love,support and for also believing in me ❤️❤‍🔥

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

“HajjahKaka in shaa Allah nine zan zama mijin Falmata.

Wacce aka kira da HajjahKaka akala zata haura shekaru sittin a duniya,ta saki baki da hanci tana kallon sa, kafin can tace, amma Baana dai kai Dodi minal Dodi ne ko? Ato in ba Dodi minal Dodi ba kana ALMAJIRINTA ina kai ina zama mijin ta?

Murmushi Baana yayi wanda shi kadai yasan fassarar Murmushi sa, can yace HajjahKaka to shi ALMAJIRI ba mutum bane?

Mutum ne man, amma ko wacce kwarya da uwar gurbin ta, kai tsaya kaji Falmata tafi karfin ka ta ko ina, bacin makirci da mugunta na shuwari(Gidan Sarauta)da kai baka issa ka bude wannan bakin ka mai wari kace kaine mijin ta ba,tana gama fadin haka taja wheelchair inta ta shige daki.

1pm
Karfe daya rana, wata fara, doguwa kyakkyawar yarinya wacce akala baza ta wuce shekaru sha biyar a duniya ba, ta shigo gidan da salama, Baana dake wanki ya dago da fara’arsa ya amsa salamar, kafin yace barka da dawowa Hajjahna.

Tamke fuska Falmata tayi kafin tace haven’t I warned you to stop using that awful word? Oops na manta baka jin yaren da nake yi, well in na sake jin kace Hajjahna sai na ci mutunci ka, rubbish. Tana fadin haka ta shige cikin gida..

Murmushi Baana yayi wanda ya bayyanar da fararan hakoransa masu kyau da ban sha’awa,”        Baana dai baki ne, hakoransa ne kadai fari a jikin sa, harta dasashin sa baki ne wanda hakan yake kara masa kyau duk lokacin da yayi murmushi, Baana dai Saurayine matashi mai jini a jika da kuma kiran jarumi, ga tsawo ga kwari, wanda akala zai wuce shekaru ashirin a duniya.

Falmata na shiga ciki, direct dakin HajjahKaka, ta nufa da salamar ta, HajjahKaka dake tasbh ta dago tana kallon ta kafin ta dauke kai ta cigaba da tasbh.

Cikin shagwaba Falmata tace HajjahKaka nifa inaso naje Bama idan ayi wannan hutun.

Cikin tsiwa HajjahKaka tace to maza tashi kije, ki ga yadda za ayi miki koran kare a wannan bakar masaurata, yanzu duk labarin da na baki akan irin cin kashi da akayi miki baki yarda ba? amma shine kika budemin wannan burmame bakin ki kike ce min zaki? Ah ban ga laifin ki ba? Laifi nane da nabar masaurata ta gado na zauna dake..

Turo baki Falmata tayi kafin tace to HajjahKaka shikenan haka zan ta zama ba tare da sannin dangi mahaifiya ta ba?

HajjahKaka tace to dan ubanki ni dangi ubanki ne? Inasha nice dai na haifa Shafaatu?

Falmata tace amma kinsa dalilin da yasa Abba yace nazo garin mahaifiya ta kenan dan na saba dasu.

Kallon hadarin kaza HajjahKaka ta tsaya tana mata kafin can tace karya kike yi, ya turo ki nan ne sabida matsiyaciyar Matar sa dake daura ki a hanyar banza, ke tsaya kiji tunda har uwarki Shafaatu ta rasu Shuwari basu so ta ba akan auren bare da tayi to banga dalilin da yasa zasu karbe ki ba. Idan ma zaki cire wannan tunanin ki cire shi, nan ma sai da nayi da gaske kafin aka yarda na zauna dake.ato duk dangi mu ba fari sai ke, to ina ma aka taba ganin Kanuri mutum fari in banda kaddara da yasa uwarki ta bijire wa kakanta wato Sarki na uku mahaifi na kenan, ta auri wannan bahago uban naki Doctor yake ko waye ma?

Cikin bacin rai Falmata ta mike tana kunkune ta nufi dakin ta, jefa jakar makaranta tayi kafin ta dauki wayar tayi dialing number Abban ta, bugu daya yayi picking da Hello Ummi?

Abba when are you coming to see me? I really missed you Abba. Falmata tayi maganar kamar za tayi kuka..

Ummi? Abba ya kira ta dashi, sai da ta dauki seconds kafin ta amsa da na’am Abba?
Abba yace kinsa yanayin aiki na amma na miki alkwarin cewa karshen shekara zan zo na ganki, da fatan dai kina mayar da hankalin ki kan karatu?

Saida ta dauki time kafin ta amsa da eh Abba.
Abba yace to Allah miki albarka, yanzu zan tura miki da $500 ok?

Thank you Abba,please extends my greetings to Aunt and the twins.

Abba yace in shaa Allah Ummi na, bye.

“Waye Abba?
Abba dai sunan sa Alhaji Musa Buzu, wanda shine mahaifin Falmata, Alhaji Musa likita ne kuma haifafar dan agadez wanda ke jamhoriya Nijar,  Alhaji Musa ya hadu da Shafaatu Bulama wato mahaifiyar Falmata, wacce ta kasance jika a masaurata Bama, a aikin sa ta NGO da aka turo su garin Bama suka hadu da ita,bayan gwagwarmaya na auren su da akayi, har Allah ya sa ya aureta ya tafi can UK da ita, daman can yake da aiki a matsayin UN Doctor.
Tun daga wannan lokaci shuwari suka cire Shafaatu daga cikin su, sabida ta bijire wa Al’adar su ta masaurata.
Wannan kenan.

9pm
Baana ne zaune a parlorn HajjahKaka ya gama cin tuwon dare, can yace HajjahKaka yau idan mun tafi training za muyi sati Biyu kafin mu dawo, shiyasa na dage nayi duk wanki da sauran aikacen gidan, idan na dawo daga training sai aure..

Wanni irin mugun kallo HajjahKaka ta bisa da shi kafin tace, to ina ruwana da kai? Ni uwarka ce ko ubanka? Sai ka tafi can Damasak kaje ka gaya masu bani ba.

Murmushi Baana yayi kafin yace ai daman daga can, can nayi sai a taho ayi maganar Aurena da Falmata.

A hassale HajjahKaka tace wai kai Baana mai ka taka ne ?da kake irin wannan maganar? Yanzu kana ALMAJIRINTA kake bude bakin nan naka mai doyi kake cewa zaka aure ta? Kai karfa ka ga Falmata a haka? Ni nan da kake gani na, yar sarki Bama ce Kuma mahaifiyar Falmata jikace a masaurata sannan mahaifin ta mayen bature ne, dan haka ka rufa wa kanka asiri kar Falmata taji wannan zance, Ato nide na gaya maka.

Falmata da fitowar ta kenan daga daki tace Wanne zance kenan HajjahKaka?

Mikewa Baana yayi, yana kallon ta ido cikin ido kafin yace nan da sati uku mai zuwa zaki zama mallakina.

Falmata was loss for a word, can tace ban fahimce ka ba?

HajjahKaka tace yanzu dai Baana ba zaka bar wannan zance ba ko? Da alama so kake ka rasa yan canji ka.

Baana yace nan da sati uku mai zuwa zaki zama Matata Falma…bai karasa ba yaji saukar lafiyayyun Mari har biyu a fuskar sa.
How dare you talk me that way?
Ni sa’ar kace? Kalle wannan bakin kazamin ni zaka bude baki kake gayawa wannan zance?

Murmushi mai wiyar fassara Baana yayi kafin yace sai mun sake haduwa Amarya ta! Yana fadin haka ya fice daga parlor, zubewa kasa Falmata tayi tana kuka mai cin rai,
“wai yanzu har yakai ace ALMAJIRINA ya budi baki ya fadamin haka? Lalle dole Abba yaji wannan zance..”

HajjahKaka tace to ke miye abin kuka? Kema dai kincika wauta..

HajjahKaka baki ji yadda yayi maganar da audacity ba?

To sai akayi yaya? Maganar shine zai sa a aura miki shi? Ke manta da wannan Dodi minal Dodi tunda ya shiga wannan training yake jin kansa wanni shege, sai ki ga yana wanni magana da issa amma karki wani damu yanzu nan zanyi maganin abin ba sai kin gaya ma Musa ba, HajjahKaka tayi maganar tana matsowa kusa da ita, Amma haryanzu Falmata kukan take yi.

Bayan Wata Daya

Falmata ne tsaye tana kokarin zira hijabin makaranta, dan tunda Baana ya tafi training take lattin zuwa school, gashi yar aikin da aka kawo bata da kuzari sam,

Jin alamu wayar ta na kara, alamar shigowar kira yasa tayi saurin duba mai kira, ta ga sunan ALMAJIRINA radau a screen, jan tsaki tayi ta yanke kiran kafin ta dauki jakar makaranta ta nufa dakin HajjahKaka da salama.

HajjahKaka dake lazami samar wheelchair ta dago da ido tana kallon ta,
Falmata tace HajjahKaka ni zan wuce school sai na dawo, gyaran murya HajjahKaka tayi alamar ta tsaya. Zunburo baki Falmata tayi cikin tsiwa da shagwaba tace shikenan kulum mutum sai yayi latti,

Mugun kallo HajjahKaka ta bita dashi kafin tace yau ba zaki bokon ba, cike da mamaki Falmata take kallon ta kafin can tace ko miyesa bazan je ba?

Baana yace…Falmata bata jira ta karasa ba ta fice daga dakin, ta nufi hanyar fita gidan, mai machine inta na baki kofa yana jiran ta, gaishe ta yayi kafin ta hau machine suka wuce school,
Mai Machine na sauke ta, ta shiga school daide lokacin da za a shiga aji, itama tayi saurin shiga.

HajjahKaka na zaune Ta’bawa ta mika mata wayar ta dake kukan kira, amsa kiran tayi ta kara a kunnen ta,
Baana yace HajjahKaka ina Falmata?
A hassale HajjahKaka ta amsa da ta tafi boko,

Cikin damuwa Baana yace HajjahKaka na gaya miki da matsala midin taje makaranta amma kika bari taje?

To sannu Baana ,kafa gareni da zan tare ta? Wai kai Baana ina kake samo wannan muyagun labarai, har cewa kayi mubar gari wai an sayar da Garin, dazun kuma da sanyiyar asuba ka kira kace kar Falmata taje boko, to abinda ban gane ba shine gidan uban wa kake samu….kit HajjahKaka taji a kunnen ta ya yanke kiran.

1pm
Falmata na aji aka aiko da taje tayi bako,da mamaki tabi teacher su a baya har suka nufa inda bakon yake, taji cikin harshen Barbanci Malamin makaranta su yana cewa yau za ayi ruwan jini ga hadari ya hadu, mun kosa mu issar da sakon mu, Murmushi bakon yayi kafin yace itace wannan? Malamin yace itace amma ko zo in kashe ka bata ji da yare… Tabe baki bakon yayi kafin yace daga masaurata aka aikoni,ana bukatar ganin ki yanzu.

Falmata was dumbfounded and loss for a word, saida ya sake magana kafin tace ina da lesson sai 3 zan koma gida tana fadin haka ta juya ta nufi aji da sauri, gaba daya jikin ta rawa yake, Batula dake kusa da ita tace mai haka kika shigo aji a razane?

Yanzu naji Malam Modu yana cewa yau za ayi “Ruwan jini” tunda hadari ya hadu cikin yare.

Dariya Batula ta kwashe dashi kafin tace wani yare kenan? Falmata tace yaren ku man.
Batula tace a yaushe kika fara jin yaren namu ban sannin ba? Ke da ko gaisuwa ma baki iya balle kuma har kice kin gane zance da suke yi, ehen kina bani labarin mara kunya ALMAJIRINKI.

Falmata was dumbstruck and curious at the time, ko da Malamin su ya shigo hankalin ta sam baya gun,ganin garin na kara hadewa,yasa teacher rounding up da wuri, sabida a yadda garin kai kace dare ne, kafin kace mai ruwa ya sauko,suna aji suka ji wanni razananne kara da basu taba jin sa ba,a tsorace Batula ta rugumo ta,karan karuwa ya keyi kuma wannan karan bana tsawa bane,a zabure Falmata ta mike ta leka window,malaman sune kwance a kasa,ga wasu mutane rike da bindigogi suna harbin malamai ta ko ina ajikin su, sakin kara Batula tayi tace Falmata mutuwa za muyi ashe..bata karasa magana ba mutane suka shigo ajin suka cewa kowa ya fito, Batula da hannun ta ke cikin na Falmata sai karanto adu’a take.

Falmata ganin bakon dazun na tunkaro ta a tsorace taja da baya tana kare mai kallo,ganin yana kokarin raba hannun su da Batula sunki rabawa yasa bindiga zai harbe Batula, tayi saurin cire hannun ta, cikin yare yace ma yan’uwa nasa su tara yammata a mota daya, shi zai tafi da wannan, Falmata naji ta na gani aka tattara su Batula aka wuce dasu cikin wani bakin Van. shi kuma Gambo ya fizge hannun ta yayi wani motor da ita,

Falmata dai sai bin ko ina da kallo take, gaba daya tana ganin abin kamar a mafarki, bata kara tabbatar da zahirin abin ba,saida taga ko ina suka bi ruwan jini kawai kake gani da gawaki,ga shi ruwa akeyi kamar da bakin kwarya, har suka issa gida abinda take ganin kenan, pincikan ta yayi zai shigar da ita cikin gidan daya daga cikin su dake layin yayi magana cikin yaren nasu, yace ina zaka kai ta Gambo? Gaba daya wannan yanki jinin su ya hallata.

Gambo yace umurni ne daga Amir, jin ance Amir yasa suka bashi hanya ya shigar da ita ciki,

HajjahKaka da sumar ta yafi a kirga, tana ganin Falmata ta fashe da kuka tace Alhamdulillah nagode wa Allah ba harbe min ke ba, ko ta ina harbi kake ji papapappa kamar a pim

Falmata da haryanzu ba eh babu uhmuhm kawai gata nan dai, haryanzu kawai jira take a tashe ta daga barci ace mata mafarki ta keyi.
HajjahKaka tace satin can da ya gabata Baana ya kirani yake cewa mu tattara mubar garin an sayar, ni kuma na manshe shi Dodi minal Dodi ashe dai nice Dodin? Yanzu shikenan mutuwa za muyi?

Gambo yace sai abin da Amir ya fada amma gabadaya mazajen garin sun zama mushe jinin su ya hallata, yana gama fadin haka yayi kabbara, HajjahKaka tace wai wa ya aiko ku?

Dariya mai razanarwa Gambo yayi kafin yace idan Amir ya bayyana kansa zaku ji, indai kuna son kan ku a raye karda ku sake ku fito. yana fadin haka ya bar gun. Yana fita Falmata ta zube a kasa, haryanzu ganin take yi mafarki ne ba gaske ba.

Falmata wasu mutane wannnan?
Wa ya aiko su, su kashe mu?
Ya akayi Baana yasan da cewa za a farmake wannan garin?
HajjahKaka ta jero wa Falmata wannan tambayoyin kamar Falmata na da amsar da take nema.

”’NOTED# THIS BOOK IS BASED ON TRUE LIFE EVENT”’

THANKS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button