Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 29

Sponsored Links

Husnah ce tayi zaman dirshan a kitchen din dake malale da ruwa, gaba daya ta jike jagab daga saman cikinta har xuwa ƙafafuwanta, ta wawwara hannu ta runtse ido cikin daga murya tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Wayyoo na shiga uku na lalace, gaba daya na kone a jiki… Don Allah a kawo min agajin gaggawa” daga gefenta tukunya ce dauke da ruwan zafi a ajiye, Khalil ya shiga kitchen din da sauri yace “Me ya faru haka?” Ta bude ido ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa tace “Don Allah ka taimakeni wallahi, ruwa me uban zafi ne ya kwaro min gaba daya tun daga cikina har kafa, taliya naje zan zuba ruwan ya kifo min, don Allah ka kawo min agaji kar jikina ya toye” Da mamaki Khalil ke kallonta, kuka kawai take tana jijjige kafarta da hannu tana cewa “Wayyo Allah na, wllh ruwan ya tafasa sosai, don Allah a taimakeni duk radadi jikina yake min” Khalil yayi ma kofar kitchen din kallon kasa kasa jin kamshin Nihad, ya ganta tsaye bakin kofar, bai yarda ya kalli fuskarta ba, ya kashe gas din ya karasa kusa da Husnah ya mika mata hannu yace “Taso” Karaf ta cafke hannunsa ya dagota ta mike tana kara sautin ihunta tana cewa “Wayyoo mamata, Wayyoo zafi, na shiga uku me za a shafa min ya daina min wannan radadin da nake ji..m” Hanyar kofar kitchen din ya nufa da ita still ya ki kallon Nihad, ita kanta Husnah bata kalli Nihad ba sai gunjin kuka take tana jijjiga kai tana yi tana runtse ido, ganin Nihad ta ki matsawa daga kofar kitchen din Khalil ya daga kai a karo na farko ya kalleta, rungume hannu tayi tana kallon su, yace “Matsa a hanya” Ta zabga masa wani ta juya da sauri ta bar wajen ta wuce dakinta, Husnah ta bi Nihad da kallon gefen ido tana cewa “Don Allah a taimakeni kar jikina ya kwaile in ma asibiti ne mu je” sai kuma ta zame hannunta daga nasa tayi dai dai a kasa ta kwanta tana birgima tana kuka, dakinsa ya nufa ta bi sa da kallo, sai ga shi ya fito da makullin mota yana kallonta yace “Mu tafi asibitin” tana girgiza kai cikin kuka tace “Wallahi baxan iya tashi ba” Yace “Toh kira kawarki” Daga haka ya fita ya je parking space ya tada mota, Mikewa Husnah tayi tana gunjin kuka ta tattale hannu ta bi bayansa, tuni ta isa gun motar tana cewa “Don girman Allah mu yi mu tafi asibitin kar na mutu, ko ina zugi yake min” Ya bude mata back seat ta shige ciki, Tun da ya tada motar Nihad ta fito parlor ta tsaya jikin window tana kallon su, sai da ya bude gate ta ga ya dawo zai shiga motar kawai ta fito ta nufi front seat ta shiga ta kulle, ya bude gefen mazaunin driver yana kallonta da kyau yace “Ina za ki?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Asibitin da za ku” Ya kalleta daga sama har kasa yace “Ohk, haka za ki je asibitin kenan” Fuska daure tace “Sai ka jira ni in dauko mayafina” Daga haka ta fice daga motar da Husnah ta cika da ihu kamar warce ake gunduwa gunduwa da namanta, tana ganin Nihad ta sauka tace “Don ya Rasulullahi ka ja motar mu tafi kar a rasa fatar jikina, wllh jin jikin nake kamar ba nawa ba, kar fatana ya karasa zagwanyewa” Bai ce mata komai ba ya shiga motar, amma bai ja motar ba, sai ga Nihad sanye da Hijab ta shige gaban motar, ya ja motar suka fita gidan ya sauka ya kulle gate. Wani asibiti da babu nisa daga anguwansu ya kai ta, duk nurses suka tattaso da sauri saboda tun daga Gate ihun Husnah ya cika asibitin, Nurse daya na kallon Khalil tace “Me ya sameta?” Khalil da ya koma gefe ya tsaya yace “Wai konewa tayi” Nan aka shiga da ita emergency aka dau scissors za a fara barke riga da wandon jikinta, Nihad dai na reception din hospital din ta zauna, babu wanda zai ce tare suke, Khalil kuma na kofar shiga reception din ya jingina da bango ya rungume hannunsa, wani ihu Husnah ta sakar ma nurses da Dr din tace “Don Allah a kira min yayana ya zo kila mutuwa zan yi, a kirasa ya zo kusa da ni” Wata Nurse ta fita ta kira Khalil, yana kallonta yace “Me xan yi a can din?” Rai bace Nurse din tace “Haba bawan Allah ko da baka santa ba ta bukaci ka je ai ko don saboda condition da take ciki zaka je, wai ko ba matarka bace?” Daga haka ta juya ta koma emergency ward din, Khalil ya bi ta da kallo kafin ya shiga asibitin ya bi bayanta, Nihad ta bi sa da wani kallo, bai ma san tana yi ba, yana tsaye bakin kofar ward din Husnah ta hangosa ta dinga miko masa hannu wai ya zo ya ceceta kar ta mutu, likitan da Nurse dai sun gama 6arke kayanta da scissors suna neman inda ta kone, Can likitan ya kalli Khalil da ya ki karasawa ciki yace “Wani irin ruwa ne ya zubar mata?” Khalil ya buda ido yace “Ban sani ba fa, ko kafin na fito ruwan ya gama kwararewa a jikinta” Nurse din na kallonta tace “Ruwan zafi ne ko dai ruwan dumi” Husnah ta hade rai tace “Ban gane ruwan dumi ba, sharrin zan ma kaina ince ruwa zafi ya zubar min a jiki bai zuba ba, kawai dai dama fata iri iri ce, amma Allah kadai yasan zugi da radadi da nake ji yanxu haka, har cikin raina nake jin wannan axaban wallahi” Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, likitan ya cire safan hannunsa yace “Nurse ki basu magunguna” Yana kai wa nan ya fice daga ward din, nan nurse ta fito reception ta harhada magungunan ta dawo ta mika ma Khalil Bill din dubu sha biyar, amsa yayi ya fiddo Atm card dinsa ya mika ma nurse din, daga baya ta sake dawowa ta bukaci pin dinsa sannan ta juya, Husnah dai sai gunjin kuka take tana kallon wata nurse dake mayar da kayan aikinsu mazaunin su tace “Aunty Nurses babu wani abu da za a shafa min?” Nurse din tace “An rubuta maki magani da za ki sha, Allah ya sauwake” Daga haka ta fita, Nurse din ta kawo ma Khalil magungunan tana kallon Husnah tace “Allah ya kiyaye gaba, za ku iya tafiya yanxu ga magunguna da prescriptions a jiki” Daga haka ta juya ta bar wajen, Khalil ya daga kai ya kalli Husnah, share hawayenta tayi ta sauko daga kan gadon da take a hankali kamar me gudun kar ta fama wani ciwo a jikinta, duk sun yayyaga mata kayanta wandon ne kawai basu karasa ba, amma daga saman cikinta duk a bude yake, Khalil zai juya ya bar wajen cikin kuka tace “Wallahi baxan iya tafiya ba ko Nihad ce ka turo ta kama min hannu” Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo, da sauri ta karaso kusa da shi ta kama hannunsa, ya dake ya fara tafiya tana dingishi tana bin sa har suka fito reception din, har suka isa mota Husnah ta shiga baya ta zauna Nihad bata fito ba, Khalil na tsaye jikin motar for almost 5 mins ganin bata fito ba still ya koma reception din, hade rai yayi yace “Malama ke muke jira” Ko Kallonsa bata yi ba ta tsura ma Tvn dake aiki a reception din ido, yace “Ohk ga kudin mota duk sanda kika zaman sai ki dawo gida” Ya ciro dari biyar ya mika mata, zuwa lkcn nurses din sun fara kuskus ko kishiya da kishiya ne, can ta mike ta fice daga reception din fuskarta a daure, juyawa yayi ya bi bayanta sai yaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga motar shi ma suka bar asibitin, suna hawa saman titi Nihad tace “Hostel za a kai ki ko ina?” Husnah tace “Wallahi kin bani mamaki Nihad har in kone a gidanki amma ki kasa budan baki ki min sannu? Sai yanxu ki wani bude baki kice hostel xa a kai ni ko ina?” Nihad tace “Saboda ai sai da nace ki bari in dafa kika ki, Yanzu idan wani abu da yafi wannan ya sameki su Mumy da Abba suka ji bayan sun hana in kawo kowa gidan fa? What did u want me to tell my parent? Ni yanzu dai hostel za a kai ki ko ina, kin dai ga dare yayi” Khalil yace “Kinsan dare yayi kike kira mata hostel yanzu? Ba kwana ta zo maki ba dama?” Nihad ta wani jefa masa kallo tace “Ni bata ce min zata kwana ba, salon mu koma gida wani abu da yafi wannan ya sameta in shiga uku? Kawai ta koma hostel ko gobe sai in kai mata jakarta can din” Kallon Nihad kawai Khalil ke yi, Husnah tace “To baxan wani je hostel ba jakana na gidanki kuma ID card dina na ciki, kuma ai soyayya ce tasa na zo gidanki ba wani abu ba, me yasa su Naf da Zully basu zo ba, amma ba komai Nagode da walakancin da kika min Nihad” Khalil dai ya nufi hanyar gida, bayan ya shiga ciki yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta wuce ciki, Husnah ta sauka ita ma ta shiga gidan Khalil ya bi su da kallo, jingina yayi da motar ta ta6e baki. Husnah na shiga dakin Nihad ta fashe da kuka sosai tace “I never expect this from you, in wani yace min zaki min haka wallahi baxan yarda ba, saboda wannan mere Drivern ya taimakeni ya kai ni hospital kike jin haushi Nihad?” Nihad tace “Ya baxan ji haushi ba mutumin da ko magana bana yi masa za ki ja min raini a wajensa ya zata ya mana alfarma, ko kadan i am not happy with what happened da kawai kirawoni kika yi na fita waje na nemo mana taimako akan wannan yaron da kika kula, yaron da ya tsaneni nima na tsanesa shine har zaki yarda ya wani kai ki asibiti?” Husnah tace “Tohh idan mutum na cikin azaba ai baya ma tunanin komai, kawai burinsa a fitar da shi daga axaban da yake ciki, to situation din da na tsinci kaina kenan, amma ni kaina ina ni ina wani driver can” Nihad bata sake cewa komai ba, Husnah tace “Shikenan, tunda har kika koreni bari in yi tafiyata ko hotel ne in kwana don a hostel na riga nace masu baxan dawo yau ba” Nihad tace “Ni fa bance kar ki kwana ba, kawai haushin yaron can ne yasa nace mu kai ki hostel” Tana kai wa nan ta mike ta cire Hijab din jikinta tace “Bari in mana boiling din spaghetti din yanzu, daga can xan gyara kitchen din” Tana fadin haka ta fita parlor ta wuce kitchen tsaye taga Khalil yana kokarin mopping din kitchen din, ta wani hade rai, yana ganinta ya ajiye mop din ya fice daga kitchen din ya shiga dakinsa, bayan few minutes da fitar Nihad Husnah ta leko daga dakin tana lekan parlor amma bata ga Khalil a ciki ba, komawa dakin tayi ta cire yagaggen wandon jikinta da riga ya rage daga ita sai bra da skin tide ta dau after dress dinta ta saka tayi buttoning dinsa sannan ta fito, ta fi second goma tana kallon kofar da take tunanin dakinsa ne sai kuma ta murda, dago kai yayi suna hada ido ta sunkuyar da kai ta shiga dakin ta tura kofar tana tsaye bakin kofar tace “Dama nace bari in maka godiyan dawainiyar da kayi da ni, Allah ya saka da Alkhairi…. kuma don Allah abinda ya faru kwanaki ina sake neman yafiyarka don wancan ranan baka ce min komai ba da na baka hakuri” Kallonta kawai Khalil yake, can ya ajiye lemon kwalin dake hannunsa yace “Ohk, kawarki ki ce ta aikoki ki bani hakuri kenan?” Husnah ta zaro ido tace “Waaa?? Ai inda muka bambanta da ita kenan, da ita ce baxa ta ta6a baka hakuri ba, kasanta da taurin kai da kafiya, yanzun ma bata san na shigo nan ba da baxata bari ba, amma ka sani wllh tunda muka maka wannan rashin kirkin bana samun nutsuwa saboda ba halina bane” Yace “Ohk ai na zata duk ku ke sa ta a hanyar walakanta mu talakawa” Husnah ta dafe kirji ta karasa cikin dakin tace “Waa?? Halin kishiyar mamarta ne ta dauko, kasan duk abinda ta sata tayi shi take yi, amma basu san da talaka da mai kudi duk Allah ne yayi su ba, ka gan ni nan babana yalo yake siyarwa a kawo kaduna, ni ba er kowa bace shi yasa nasan mutuncin ɗan adam” Khalil yace “Ohk, ai ina ce er kano ce” Husnah tayi wani dariya tana jujjuya ido tace “Wallah er kaduna ce ni gaba da baya, Zully da Naf ne yan kano” Yace “Toh naga makarantar taki ta masu kudi ce” Husnah tace “Ehh wallahi wani saurayina ne ya biyamin tun daga level one har karshe, wata kawar mu zully ma saurayinta ke biya mata, Naf ce dai iyayenta ke biya mata don su ma masu kudi ne” Khalil ya gyada kai yace “Allah sarki” Husnah ta zauna gefen gadon tace “Amma ina jiye maka zama gida daya da Nihad, yanda bata kaunarka ta tsaneka kullum a makaranta cikin tsine maka take wai kana matsayin driver kana nuna mata isa, bayan anyi auren nan har ikirari tayi wai zata kasheka, nan kuwa kai jahadi kayi, halan baka hawa social media? Ina nufin baka da babban waya?” Ya girgiza kai yace “Bani da” Husnah ta gyada kai tace “Allah sarki, kawai dai ka saka ido sosai kada kiyayya yaje ya kaita ga aikata abinda ba shi kenan ba, in sha Allah in xan sake dawowa nayi maka alkawarin babban waya” Khalil yace “Toh Nagode, amma kawar taki bata da saurayi ne?” Husnah ta rike ha6a tace “Ita kuwa take da saurayi wanda ita ta makale masa ba shi ba, kana jin janaral jikamshi?” Khalil yace “Eh nasan shi, ko ba wani babban soja ba?” Husnah ta dafa kafarsa cike da kissa tace “Yauwaaa, Toh shi fa…. ɗan sa kwaya daya take so kamar ta kashe kanta, tun yana basar da ita har dai ban san sanda suka dinke ba, mu dai mun fi zargin bashi kanta tayi, don kawai lkci daya muka ga ya fara kiranta ba kakkautawa a maimakon ita da ke yawan kiransa” Khalil ya sauke idonsa kasa daga kallon da yake ma Husnah, Husnah tace “Kuma fa duk wannan abun sau daya ya zo wajenta a nan kano suka hadu a wani waje, kamar dai kar su hadu shkkn ya makale mata, kasan mu mata idan muna son abu babu abinda baxa mu yi kan abun ba, to tun dai daga sannan ya fara kulata sosai, kuma kar kace fa yana zuwa gidansu, aa sam… duk xuwan da yake yi wajenta nan kano sai dai su hadu a wani waje su yini sannan yayi tafiyarsa, toh kwanaki can ban san ya aka yi ba yaje gidansu wai xai tura iyayensa, mu dai ko gaya mana bata yi ba gaskiya sai daga baya, ai ko muna ta murna xa mu hade da ‘ya yan manya mu ma a dama damu tunda abokanansa duk ‘ya yan manyan kasar nan ne kawai wai sai ga videon tsaraicinta ya bazu a duniya, ni takaicina daya da ba a bari sai da muka hadu da abokansa ba, har yau mun rasa ta ina video din nan ya fita, muna dai tunanin garin yawace yawacenta ne aka mata video din nan” Khalil bai kuma cewa komai ba, lkci daya kuma duk mood dinsa ya canza, Husnah ta shafa kafarsa a hankali tana kallon kwayar idonsa tace “Sai kaji babu dadi ace videon tsaraicin warce aka aura maka na ta yawo a duniya ko? A ranka kana tunanin an cuceka ko?” Kallonta Khalil yayi, tana Murmushi ta janye hannunta a hankali tace “Toh Nagode bari in je inyi wanka” Daga haka ta mike tana juya manyan mazaunanta ta nufi kofa, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai har ta fita dakin, karo ta kusa ci da Nihad, Nihad ta tsaya tana kallonta daga sama har kasaasa, Husnah tace “Ke yace min maganin na wajenki kuma ni ban gansa a dakinki ba” can kasa kasa Nihad tace “Ba ya wajena” Daga haka ta shige dakinta, Husnah ta tafi parlor ta dau magungunan nata ta dawo dakin Nihad. Nihad dai na ta zaune gefen gado, Husnah tace “Wai taliyar bata yi bane Nihad?” Sai a sannan Nihad ta kalleta tace “Mu je mu duba” Husnah tace “Ohk” Daga haka ta mike ta fita Nihad ta tashi ta bi bayanta, tana tsaye parlor har Husnah ta shiga kitchen, a hankali ta bude kofar dakinsa ta leka taga baya ciki, ta kalli kofar bandaki sai kuma ta kulle kofar dakin, entrance din fita ta kalla bata ga takalminsa ba, ta karasa jikin window ta tsaya ta bude labulen a hankali tana lekan waje, yana tsaye balcony ya rungume hannunsa, can ta ga ya nufi dakalin da yake son zama ya zauna kana ganinsa kasan he is moody, Husnah ta fito daga kitchen tace “Me kike nema a waje” Nihad tace “Ba komai, kin zubo taliyar?” Husnah tace “Ehh na zuba, ashe har kin sauke” Nihad tace “Toh dauko mu je daki” Husnah ta koma ta dauko suka wuce dakin, bayan sun gama cin abincin Nihad ta fitar da kwanukan ta sake leka waje taga har sannan khalil na zaune inda yake staring into space, kafin Nihad ta dawo Husnah ta jawo jakarta ta fito da kayan mayenta ta sha sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta kwanta, Nihad na dawowa dakin ta zauna gefen gado, tana son shiga bandaki tayi wanka amma ta kasa tashi, Wajen karfe sha daya da rabi Husnah ta mike Nihad na kallonta tace “Ina za ki?” Husnah tace “Ruwa zan dauko kitchen” Nihad ta dauko wani bottle water dake daya side din gadon ta mika mata, Husnah ta amsa ta koma ta zauna tana sauke numfashi a hankali, ita fa dama kwana biyu duk samarin nata basa Kano gaba daya a takure take dama, daga karshe dai Husnah ta kwanta ta kulle ido duk da ba bacci tayi ba, Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad ta mike daga kwancen da take ta nufi kofa ta sa makulli sannan ta ciro, Da mamaki Husnah ta mike zaune tana kallonta tace “Me yasa zaki kulle mu har da cire makulli Nihad?” Nihad tace “Saboda duk dare haka nake yi dama” Husnah bata kuma cewa komai ba ta kyabe baki ta koma ta kwanta, Nihad ta saka makullin cikin pillow ta kwanta kai. Washegari da sassafe bayan sun yi sallan asuba sun koma bacci kiran Umma ya tashe su, Bayan Husnah ta daga jin muryar Umma tace “Auu Umma ce, ina kwana?” Umma tace “Lafiya lau Husnah baki yi saving number na har yanzu ba ko?” Husnah tace “Yanzu xan yi Umma, ya gida?” Umma tace “Alhamdulillah, ina Nihad din?” Husnah ta mika ma Nihad waya ta koma ta kwanta, Bayan Nihad ta gaidata, Umma tace “Ya, kin gano sunan iyayen nasa kuwa Nihad?” Nihad tace “Aa Umma, dama sai yau” Umma tace “Kin ji irin shiriritar taki ko? Ke da tun jiya nace kisan yanda kika yi ya gaya maki amma sbda shashanci baki yi ba? Ko dai kin fi son kiyi ta zama da dreban nan ne Nihad?” Da sauri Nihad tace “A’a Umma, in sha Allahu yau xan gaya maki” Umma tace “Toh kar ki bari Husnah ta bar gidan nan sai kin gano kin sanar min ta wayarta tukunna” Nihad tace “Toh Umma” Umma tace “A handsfree wayar yake ne naji maganata na dawo min?” Nihad tace “Aa” Umma tayi kasa da murya tace “To dai ki xama me rike sirrinki a ciki, ciki da kike gani ba don tuwo kadai aka yi sa ba, ko da mun gana waya kawarki ta tambayeki me muka ce kice mata ba komai kawai daddawa da kuka nace xan bada a kawo maki, don ba komai ake sanar ma k’awa ba, wa ya sani ko da hadin bakinsu aka saki video dinki a duniya” Nihad tace “Aa Umma ba haka bane gaskiya” Umma tace “Toh shikenan, ina sauraronki zuwa anjima” Nihad tace “Toh” Daga haka ta katse wayar, Husnah na kallonta tace “Wai me ya faru?” Nihad tace “Aa ba komai, abubuwan da zata kawo min ne take tambayata” Husnah tace “Ohk” Komawa tayi ta kwanta, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta ta daura kan kayan baccinta ta nufi kofa Husnah ta bi ta da kallo har ta fita, Nihad na murda kofar dakin Khalil taji an sa makulli, ta fi minti daya tsaye bakin kofar, can ta juya ta tafi parlor ta zauna, tana fitowa da minti biyar sai ga Husnah ma ta fito ta zauna parlon, jan Nihad ta dinga yi da hira, daga karshe wajen karfe tara Khalil ya fito daga dakinsa, babu warce ya kalla a cikinsu ya fita daga gidan, Husnah na ji ya fita da mota ta kalli Nihad tace “Lallai ke me hakuri ce da har kika kai warhaka da mutumin nan a gidan nan, Dubi fa yanda ya wani zo ya wuce mu ko gaisuwa babu, kai kana talaka da kai kayi ta yin abu isa isa?” Nihad ta kyabe baki tace “Ke ma kika lura da mutum ya zo ya wuce ta nan, ai ni ban ga kowa ba” Husnah ta kyalkyale da dariya tace “Ahh lallai kam” Nihad tace “Tashe mu je ko irish ne mu soya da kwai, ni dai na fara jin yunwa” Husnah ta mike suka wuce kitchen din, har kusan la’asar Khalil bai dawo gidan ba, kiran Umma uku duk sai Nihad tace mata ai bai dawo ba, kiran karshe da Umma tayi mata da ta kara sanar mata har sannan bai dawo ba, Umma tace “To kar ki yarda ki bari Husnah ta bar gidan, don tana tafiya babu ta inda xa mu yi communicate” Nihad ta kalli Husnah da ita dama bata ga alamar xata tafi ba tace “Toh Umma” Labari har da na kauyensu Khalil sai da Nihad ta ba Husnah dake ta kyalkyalewa da dariya har da faduwa kasa, tace “Kice ke kika ga asalin dreba ganin idonki?” Nihad tace “Hmm… I wish xaki ga kauyen nan Husnah, wllh with millons baxa ki yarda kiyi minti sha biyar a garin nan ba, it’s hell on earth” Husnah dai sai dariya take, sai ga Naf ta kira Husnah, Nihad da wayar ke kusa da ita tayi saurin dagawa ta kai kunne, Naf na jin muryar Nihad tace “Amma Husnah munafuka ce shine bata gaya mana ba tayi tafiyarta ita kadai” Nihad tace “Wallahi nima ban ji dadin da baku zo gaba daya ba, gashi throughout today I wasn’t lonely, muna ta hira da Husnah” Husnah ta fixge wayar tace “Toh ai naga xaku fita ne shi yasa bance maku mu taho ba Naf, amma meye a ciki next time idan xan zo ai sai mu taho gaba daya, ba wani tashin hankali bane” Naf tace “No but like seriously kinsan indai kince mana wajen Nihad xa ki babu abinda xai hanamu binki, kuma banji dadin abinda kika mana ba, yanzu ma kawai xa mu iya tahowa da zully tunda babu abinda muke” Husnah ta dinga cewa Hello hello, daga haka ta katse wayar tace “Ji shegen network din ya dauke” Hirar da take ma Nihad ta ci gaba da yi mata, Nihad tace “Kinga lokaci na wucewa me xa mu ci da daddare Husnah?” Husnah tace “Ni yanzu xan fita in amso wani sako na, ko indomie ce ma ci da daddaren, Hijabi kawai xan sa in je in dawo” Nihad na kallonta tace “Kar fa ki ki dawowa Husnah” Husnah ta zaro ido tace “Me xai hanani dawowa kuwa, cabb ai kamar na dawo kinsan yanda nayi kewar ki kuwa, to a nan ma xan bar wayata, amma kar ki cire min a flight mode har in dawo” Nihad tace “Toh” daga haka Husnah ta sa hijab ta dau handbag dinta ta bar gidan, ko da ta dawo bayan kusan awa daya Nihad ta dinga kallon hannunta ganin ba leda tace “Ina sakon?” Husnah ta ja tsaki tace “Wai ashe sai gobe, shine suka bari naje nayi asaran kudin motata na dawo” Daga haka ta shiga dakin Nihad. Sai after Magrib Khalil ya dawo gidan, Husnah da fitowarta daga wanka kenan ta dauki mai zata shafa ta rike ha6a tace “Dama haka yake yi ya fita tun safe sai dare kamar me siye da siyarwa a kasuwa” Nihad ta kyabe baki tace “Ohk ya dawo ne” Dariya kawai Husnah tayi bayan ta gama shafa cream dinta tace “Ke baxa ki yi wankan bane” Nihad ta mike tace “Zan yi” Daga haka ta shiga bandaki, mikewa Husnah tayi da sauri ta bude kofar dakin tana leka parlor, ba kowa parlon sai leda da ta gani a ajiye na eatry, ta dawo daki ta dau handbag dinta sannan ta fice tana waige waige kamar munafuka ta shiga kitchen ta bude handbag dinta ta dau allura me cike da wani liquid a ciki ta bude murfin syringe din, ta dawo parlor har tana tuntube ta tafi gun ledan ta bude ta ciro drink din kwali da ta gani ta tsira masa alluran ta sama ta juye duk content din ciki sannan ta mayar da shi ledan hannunta na rawa, sbda rudewa maimakon ta koma daki sai ta shige kitchen, ta fi second talatin a kitchen din kafin ta leko parlon a hankali still taga ba kowa da sauri ta wuce dakin Nihad ta kulle kofa ta zura doguwar rigarta ta dau wayarta ta kwanta saman gado tana danne danne tana ɗan murmushi…..

 

*Few mutanen da suka sameni jiya for discount wai basu da halin dari biyar, bayan message dina na jiya, sorry i didn’t acknowledge u guys yesterday, after all ni din ce dai zan yi loose still😏, don haka na amince nayi discount daga yanzu xuwa gobe in sha Allah*

Related Articles

 

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via👇🏻

07087865788

 

 

Assalamu alaikum manyan mata!!

For your Egyptian Abaya’s, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries… Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰

Ping me on WhatsApp to view our catalogue 👇🏻

https://wa.me/c/2349090591769

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button