Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 3

Sponsored Links

Tafi takeyi batare da tasan inda ta dosa ba idanunta da ƙafafunta sunyi mata nauyi daƙyar suke ɗaukar ta jiri na ɗaukar ta tana neman faɗuwa a dole ta nemi guri ta zauna rungume da bahon Shinkafarta tanata shassheƙar kuka me dukan zuciya jin ruwan ya fara dawowa ne yasata dafa ƙasa ta miƙe daƙyar taci gaba da tafiya jiri na ɗibanta ga ruwan saman sai ƙara ƙarfi yakeyi tunanin tare ɗan sahu ma ya kasa zuwar mata.
Tayi tafiya me tsayi cikin gushewar hayyaci da ƙunar zucci taji anayi mata horn bata juya ba taci gaba da tafiyarta ta kumajin anyi mata horn ganin batada niyyar tsayawa yasashi fitowa a motar ya nufeta da sauri yasha gabanta yace “Am bakiji Ba Hanisa meye yasa kikayi dare haka har ƴar’uwarki ta koma gda”
Kawar da kanta tayi ta sake ɗaukar hanya tana shirin barin gurin ya riƙo hijjab ɗinta yace “dare yayi Hanisa kizo na kaiki gda kinga hadarin nan ƙara haɗowa yakeyi fah” sabon hawaye ne ya wanke mata fuska tace “Na gode Abdul-Ahad kaje kayi harka gabanka” juyawa tayi ta tafi yabi tafiyarta da kallo faɗuwar gaba ta dirar masa yace “Innanillahi wa Innah Ilaihirraji’un Hanisa meye ya faru dake haka?” Durƙushewa tayi a gurin ta rushe da kuka tana girgiza masa kai.

 

Matsowa yayi gabanta yace “Tashi muje akwai matsala fah Anisa alamu sun nuna yau kin shiga sabon yanayi don Allah ya akayi haka ta faru dake garin yaya Anisa?” Kukanta ta ƙarawa ƙarfi tace “Na rantse da Allah bantaɓa jin a raina zan sarayar da budurcina don neman duniya ba tsoron faɗan Mama ne yasani zama har hadarin nan ya riskeni ashe cikinsa littafin ƙaddarata zai fara buɗewa Abdul-Ahad na rasa budurcin dana daɗe ina tanadi domin mijina na rasa ƙimar da take kankarowa duk wata mace ƙima sanadin tallah Na yarda da Lawwali yau ga ranar da yardar tayimin yayi reaping ɗina yayimin fyaɗe kuma banida ikon neman haƙƙina kawai don na kasance mara galihu wayyoh Allah wayyoh Babana Allah dama mota ce ta takeni na mutu nasan nayi shahada”
Wani mugun matsanancin tausayin yarinyar ya ɗarsu a ransa yinin yau sur da ita ya yini a ransa duk da ya ɗauki yar uwarta Hasina sun fita shan minti ya kasa hassala mata komai lissafinsa ya goce daga lkcn da idanunsa ya sauka akan Anisa ashe ita tananan wata mummunar ƙaddarar na shirin faɗa mata.

Related Articles

 

Wani tuƙuƙin baƙin ciki da baisan daga inda ya taso ba ya cika masa zuciya ya miƙe yace “Ok tashi akwai wani asibiti anan baya muje su baki magani sai na kaiki gda yau yaron nan bazai kwana a ɗakinsa ba wlh sai nasa an ɗauke……. Saurin rufe masa baki tayi da hannunta daketa rawa tace “Aa Abdu idan ka taɓashi asirina zai tonu don Allah ka barshi wannan ba komai bane ƙaddararmu ce ƴan talla ba shine da laifi ba Mama itace me laifi tunda itace ta ɗora min tallan da bata ɗoramin ba aida hakan bata faru dani ba”
Bawai don ya bari ba yace mata ok muje a dubaki dare na ƙara yi shiga motar tayi yaja suka nufi wata hanya ya shiga cikin wani asibiti yayi parking suka fita yanata kallonta kyakkyawar yarinya itama rayuwarta ta gurɓata.
Office na likitan suka shiga yayi musu bayanin komai dake asibitin kuɗine nandanan suka dubata suka bata magunguna yayi musu gdy suka fito suka nufi unguwarsu ya sauketa tare da bata kuɗi masu kauri yace “Gobe zanje Lagos ki kula da kanki ki kuma kula da shan magani zaki samu ƙarfi kada kije tallannan gobe don Allah kinji”

 

Ɗaga masa kai tayi ta buɗe bakinta cikin sanyinta na halitta tace “na gde” gdan ta shige babu kowa a tsakar gdan saboda ruwan da akayi ta ajiye kwanukan ta nufi ɗakinsu ta kwanta saman tabarmasu ita kaɗai tasan azabar da takeji a ƙasanta wani tunani ne ya faɗo mata na ta tashi taje Madafi ta haɗa wuta ta samu ruwan ɗumi ta gasa ƙasanta ko ta samu sassauci.
Miƙewa tayi daidai lkcn da Mama ta bankaɗo labulen tayi saurin komawa ta zauna harara Mama ta zabga mata tace “Duk uwar daɗewar nan da kikayi don lalacewa baki iya siyar da abincin nan ba kekam na rasa baƙin jininki a rayuwa talla ma idan kika ɗauka kwantai kikeyi” sosai kalaman Mama suna dukan zuciyarta saidai bata iya mayar mata kamar yanda Yaya Hasina take mayar mata saidai tayi kukanta ta cinye a ranta, jakarta ta duba ta zaro dubu huɗu ta miƙa mata tayi saurin karba ta ƙirga nandanan ta saki ranta ta fara rawa tana juyi tana cewa “Masha Allah masha Allah itama ta dau hannu Hanisatu wannan kyalla kyallan kuɗaɗen hala juye akayi miki?” Kawar da kanta tayi wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata, nan Mama ta kira Hasina ta fara raba musu cefanen gobe Hanisa cikin kuka tace “Wayyoh Allah Mama wlh bazan iya tashi ba marata ciwo takeyi ƙafafuna zasu karye”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button