Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 32

Sponsored Links

Cikin tsananin damuwa ta kira Mama saida tayi ring uku sannan ta ɗaga tana kuka ta zayyane mata komai maimakon hankalin Mama ya tashi kawai sai taji tayi tsaki tace “To ai kece kikaci amana ba itaba dama itace zaɓinsa bake ba ke matar cushe ce wadda bata daraja saboda haka zaifi miki ki kawar dakai Hasina dai bazata baro garinnan ba saita gama karatunta kuma idan mijinta ya zaga bazance karta bashi ba ta bashi ya lasa abinsa ne”
Cikin kuka da sallamawa tace “Mama Abdul-Ahad mijina ne fah kuma kece da bakinki kike cewa bazaki hana yayata taci gaba da bibiyarsa ba Mama wannan shine irin naki hukuncin wannan shine adalcin da zakiyi tsakaninmu?”

 

Murmushi Mama tayi tace “sai kuma kiyi Aneey Ni nariga na sallamawa duniya ke” ƙit ta kashe wayarta Aneey ta rungume wayarta tanajin wani sabon kuka ya kwace mata a fili tace “Ni wacce irin uwa ce damu?” Kuka takeyi sosai tun ranar har zuwa dare bata daina ba tanata kukanta taji an safa kanta taja ajiyar zuciya da sauri ta ɗago ganin surukarta saida gabanta ya faɗi tsoro ya shigeta Mother ta durƙusa tace “akwai abinda kuke ɓoyewa dagake har mijinki Aneey Please meye yake faruwa ne da yake neman haifar muku da matsala”
Wani kukane me ciwo ya kufce mata karon farko a rayuwarta da wani cikakken mutum ya tsaya domin jin damuwarta har ya roƙeta sanin dalili bayan mahaifinsu kwantar da kanta tayi jikin Mother nan hankalinta ya ƙara tashi hƙrn matar ɗannata yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke ƙara mata ƙima a gurinta ta shafa kanta tace “Idan har kin ɗaukeni uwa ki faɗa min meye matsalarku Prince yanacan tunda yaji labarin barinki gdan ya faɗi sai yanzu da akace anganki a ɓangaren bayi sannan ya samu nutsuwa don Allah meye ya faru shi yaki faɗamana komai”

Related Articles

 

Cikin muryar kuka tace “Babu komai Mom nidai don Allah Hasina tabar gdannan wlh idan bata barshi ba Ni zan barshi bazan iya zama ina kallonta matsayin kishiyata ba” zaro ido Mom tayi tace “kishiya kuma ta yaya?” Shiru tayi taci gaba da kukanta ganin alamun bazata magantu ba yasa Mom janta Suka tafi ta nufi sashinsu da ita saida ta kaita har kan gadonta sannan tace “duk da kunƙi faɗa mana abinda ke gaskiya bazanƙi baki hƙr ba tabbas nasan ke akayiwa laifi Aneesah kiyi hƙr kowacce mace da take zaune da mijinta hƙr takeyi kiyi hƙr don Allah” kafin Mom ta fita ya shigo ganinta zaune tanata sharar hawaye yaja wata gwauruwar ajiyar zuciya ya zubanta idanu itakuma ta ɗauke nata akansa Mom tayi musu sallama ta fice sun jima babu wanda yace da wani komai saida ya gaji yaja jiki da sanyin gwiwa ya matsa gabanta ya zauna a gefenta ya zuba mata idanu ya rasa da wacce kalma zaiyi mata mgn daƙyar ya aro juriya yasawa kansa yace “Aneesah wlh bansan ya akayi hakan take faruwa ba ina roƙonki ki tayani da addu’a ko na samu na samu kaina Aneey Ni kaina zuciyata baƙi takeyi da wannan abin da yake faruwa na ɗauki kusan wata uku bana iya yima Hasina musu komai tace binta nakeyi ban samu kaina ba sai cikin satinnan shine na janye mata ita kuma taci alwashin rabani dake…..”

 

Daga masa hannu tayi tace “don Allah na roƙeka kayi shiru bazan taɓa ganewa me kake cewa ba bare na fahimceka Abdu kabarni kawai na yarda da duk abinda ƙaddara zata zaɓamin wlh ji nake kamar na kasheka Abdu bana ƙaunarka a yau naji na tsanarka bantaɓa jin tsanar wani abu kamark….. Rufe mata baki yayi da sauri jikinsa na rawa yace “wlh Aneey bantaɓa jin kunyar wani kamar yanda nakejin kunyarki ba ki taimakeni ki rufamin asiri” bige masa hannu tayi ta haye gadon ta ƙudunduna zuciyarta naci gaba da ƙuncin da takeyi haka suka kwana kowa da sako a zucci.
Washegari da safe ta fice daga ɗakin ta shirya break ta koma ta zauna a parlourn ya fito ya tsugunna a gabanta yasa hannu ya ɗago fuskarta ya ɗora bakinsa a kuncinta hakanan taji kamar ya ɗora mata garwashi wani baƙin ciki ya disashe mata hasken zuciya daƙyar tace masa “ina kwana”

 

Murmushi yayi yace “me zanyi ki yarda dani….?” Bai rufe bakinsa ba yaga ta miƙe ya saki baki yana binta da kallo yaja fasali yaje shima ya zauna a dinning ɗin ta haɗa masa break ta miƙa masa itama ta haɗa takai bakinta taji kamar ta zuba ruwan dalbejiya dole ta aje ta rinƙa juya cokalin zuciyarta na karyewa hawaye nabin kurmin idonta.
Hannu yasa ya ɗago fuskartata ya zuba idanunsa cikin nata ta kawar dakai tare da lumshe idonta jikinsa duk yayi sanyi baya ƙaunar ganinta cikin damuwa yace “kiyi hƙr” daga haka ya juya ya fice a kasalce tausayin kansa yakeyi Allah ya jarabceshi da tsananin ƙaunar Aneey bayason damuwarta bare kuma damuwar da yasan shine sanadinta a wahalce ya yini ranar yana ganin kiran Hasina yaƙi ɗagawa ƙarshe ma ya watsata a blacklist shikuma yayita Kiran ta Aneey taƙi ɗagawa baya ƙaunar ya kira waya aƙi ɗaga masa musamman nata da yasan da gayya taƙi ɗagawa, gashi aiki yayi masa yawa baisan ta inda zai fara ba bare ya samu dama ya fice ya koma gdan.

 

******

Tunda ya fice take kwance a parlourn kallo take amma idanunta abinda tagani jiya kawai yake hasko mata kashe tv ɗin tayi ta tashi ta koma ɗakinta ta kwanta tanajin yanda ɗan cikinta yaketa motsi daga lkc zuwa lkc tana share hawaye tashi tayi zaune cikin kuka tace “Allah kafini kafi uwata kafi ubana sanin daidai ɗin rayuwata Allah ka kawomin mafita ka yassarewa zuciyata yafiya ka azurtani da iya rintse idanu akan abinda yafi ƙarfina Allah na roƙeka ka shiryamin mijina ka cire masa ciwon zina a zuciyarsa Allah ka ɗaukemin wannan jarabtar ka musanyamin da wata wadda tafita sauƙi”
Ji tayi an turo ɗakinta ta kwantar da kanta tunaninta Abdu ne jin baayi mgn ba shine yasata buɗe idanunta ta saukesu akan Hasina zuwa yanzu bata ƙaunar ganinta wata dariya Hassy tayi tace “baki tsammaci ganina ba ko musamman dake kinsan kin haɗani da masoyina ya nemi illatani hhhhh Hanisa kenan kada ki ɗauka kinci bulus wlh kamar yanda kikasa ya dakeni ke naki hukuncin sai yafi nawa zafi mijinki ne kina taƙama da abar wandonsa nima da ita nake taƙama muddin ina raye baki isa na barki ki kwashi daɗinsa ke kaɗai ba banza shashasha dake kin yarda saboda ƙauna nazo gurinki, ai ƙauna ta kare tun lkcn da kika shirya cin amanata”………..

 

*SANARWA DAGA ALƘALAMIN OUM HAIRAN*

 

_Assalamu alaikum_
_Barkanmu da sfy da fatan kuna lfy_

 

_Alhmdllh Dukkan shirye-shirye sun kammala online class ɗin mu na *DOMINKI ƳAR GATA* zai fara a ranar Litinin 15/12/2021 ajin na wata ɗaya ne akan Naira 500 idan ta PC kikeso kuma 1000k ne kada ku bari a baku lbr._
_Zamuke koyar daku abubuwa da dama kamar Haka👇🏼_
_1- Sirrin gadonki domin siye zuciyar mijinki ba boka ba malam_

_2- Kishiya ƴar’uwa_

_3- Yanda zaki gamsar da mijinki koda bakwa tare_

_4-Tarairaya_

_5- filin sama ruwa_

_6- yanda zaki haɗa magungunan da zasu dawwamar miki da ni’ima batare da kin kashe manyan kuɗaɗe wajen haɗawar ba._

_7- Zamu koyar daku yanda ake gamsar da master ta hanyar wasanni batare daya shigeki ba_

_Zamu koyar daku yanda ake dafa ƴan shila na masu jego, da gumbar yar gata, da wasu fitinannun haɗe² na manyan mata._

_8- Akwai filinmu na tsafta wato ado da kwalliya_
_Hhhh kada fah kuce oum hairan zata koya muku kwalliya wlh Ni yar aƙidar zero make-up ce🤗_

 

_Akwai filin ƙamshi inda zamuke koyar daku turaruka farar humrah baƙar humra brow humrah kulacca dadai sauransu._

ga me buƙatar shiga zai biya ta wannan account ɗin 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank
Idan baki da account zaki iya tuntuɓata ta whattsAp number 09013718241 pls only WhatsApp ne wannan bana amsa kira dashi.

Don kira domin samun ƙarin bayani zaku tuntuɓeni ta wannan number 09031307566.

 

Taku a Kullum me burin ganin kowanne aure an zauna lfy da son ganin kowacce mace ta zama ƴar lelen mijinta.

 

*Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkin san siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya ,Mungode*

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/17, 4:54 PM] Oum Hairan&Affan:

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button