Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 5

Sponsored Links

“Abdul-Ahad! Abdul-Ahad!!” Ta Kira sunansa tare da cire wayar a kunnenta ta zuba mata idanu ashe ihun banza takeyi ma ya jima da kashe wayarsa, aje wayar tayi ta dafe kanta dake sara mata ta koma ta kwanta Hasina tazo ta zauna kusa da ita ta dafata tace “Nasan fargabarki Babane Hanisa insha Allahu bazai san wannan abun ya faru ba kiyi hƙr shima Abdu zanyi masa mgn zai hƙr yabar mgnr amma kisani kema dole ki saki ranki ki daina nuna damuwa Hanisa shi zanen ƙaddara wuyar goguwa gareshi idan kika cika takurawa ma saiki faɗa komar ubangiji.
Sauke ajiyar zuciya tayi taja zani ta rufe jikinta baccin wahala ya ɗauketa Hasina ta matsa kusa da ita ta kwanta itama baccin ya ɗauketa. Washegari tashi tayi da zazzaɓi sosai nan fah Mama ta hau masifar ai tana sane saboda baƙin cikin kada ta ɗaukar mata talla ne ta bari ruwa ya daketa gashinan ciwonta ya tashi batasan cewa ba wannan ne asalin sanadin ciwon ba.

 

Hasina data riga tasan matsalar ƴar uwarta ta miƙe ta rufe Mama da faɗan ita batada tausayi ta fiye son kanta tana ganin yanda Hanisa take kwance amma ita ba damuwarta bane lfyrta damuwarta kawai a ɗaukar mata talla jaka Hanisa ta dauka ta zaro kudin da Abdu yabata jiya ta miƙawa Hasina tace “Banason hayaniyar da kike tsayawa kunayi da Mama Yaya duk fa lalacewar Mama ta haifemu dole akwai haƙƙin biyayyarta akanmu ya zamuyi hakan shine ƙaddararmu muyi ƙoƙarin cinyewa shine kawai aikin dake gabanmu”
Ɗaga mata hannu tayi tace “Don Allah ki ƙyaleni da wannan matar Allah halinta ya fara ƙular dani Hanisa itace fa silar faruwar duk abinda ya faru damu ace ita kullum burinta a ɗaukar mata talla to nidai yau bazan ɗauka ba tayi duk abinda zatayi….” Rufe mata baki tayi tana girgiza mata kai tace “don Allah ki daina wannan mgnr batada amfani kinga Ni bazan ɗauka ba ki ƙirga kuɗinnan kigani idan sunkai ki ɗauki abinda kike tunanin yakai na abincinta ki bata tabarmu mu huta” karɓar kuɗin tayi ta ƙirga tare da zaro idanu tace “dubu Arba’in da shidda ne fah Hanisa wannan duk Abdun ne yabaki?” Ɗaga mata kai tayi ta jinjina lamarin tace “amma yabaki da yawa Hanisa koni Abdu baitaɓa bani sama da dubu Ashirin ba”

 

Shiru Hanisa tayi Hasina ta fita ta zari dubu biyar ta zubewa Mama a gabanta ta juya tayi tafiyarta a wannan ranar babu wanda ya fita tallan a gida suka yini sai yammaci Hanisa ta samu sassaucin zazzaɓin dake addabarta Hasina tayi mata shimfida a gindin bishiyar darbejiyar dake tsakiyar gdan ta fito ta zauna daga jiya zuwa yau duk ta zabge Hasina keyi mata komai ta dauki kuɗi ta siyo mata kayan ciye² ta kawo mata suka baje sukaci Mama tsoron tujarar Hasina ta hanata yi musu magana.
Bayan sun gama suna hirarsu wayar hannun Hasina ta shiga ruri ta zarota a aljihunta tayi murmushi tace “Allah sarki Abdu kana raina” karawa tayi a kunnenta tace “Hello Abdu” gaisawa sukayi yace “ya Aneey?” Kallon Hanisa tayi tace “Jiya dai da zazzaɓi ta kwana har zuwa rana amma yanzu ya sauka” cikin tausayawa yace “ayyah bata mu gaisa” miƙa mata tayi yace “Aneey ya jikinki” Amsawa tayi da cewa “Naji sauƙi Abdul-Ahad ya kk ya Lagos ɗin” ajiyar zuciya yayi Muryar yarinyar tana mugun yi masa daɗi da kashe masa jiki cikin muryarsa me cike da kasala yace “lfy alhmdllh Aneey kinji sabuwar rayuwa ko? Kiyi hƙr ita dama duniya haka take abinda kake ƙi da yawan lokaci shine yake samunka koda yake kema ai nasan zakiji daɗin harkar wuyarta ki saba kinga Hasina data saba ai tasan daɗin abin” kawar da wayar tayi daga kunnenta ta miƙawa Hasina, Hasina ta kara a kunnenta yace “Am Aneey mubar wannan mgnr me kikeso na taho muku dashi gobe da wuri zan dawo inaso nazo naga yanayin jikinki”

 

Zubawa Hanisa Ido Hasina tayi yace “kinyi shiru ko mgnr da nayi miki ce ta ɓata miki rai don Hassy tasha cemin abin dake ɓata miki rai bashi da yawa” dariya Hasina tayi tace “Aikam da alamar ka ɓata mata ɗin don tuni ta aje wayarka” basarwa yayi yace “Ƙanwar nan tamu tanada matsala koda yake maza sunyi mata laifi yanzu haushin kowa takeji” satar kallon inda Mama take Hasina tayi tace “kai kuwa anji sabon yanayi dole a samu canjin yanayi” dariya sukayi itakuwa ta haɗe rai tama miƙe zatabar gurin Hasina ta riƙe hannunta tace “Ayi hƙr don Allah” kwace hannunta tayi ta nufi bayi ta shiga wanka ta fito tasa kayanta ta kuma yin kwanciyarta iya mgn Hasina tayi mata taƙi sauraronta dole sai rabuwa tayi da ita har saida ta sauko da kanta sannan sukaci gaba da hirarsu.
Washegari taji sauƙi sosai Mama tayi musu abinci suka ɗauka suka fita tare suka tafi tana zuwa Hasina ta sauke musu abincin kowacce a gurinta sun fara ciniki kusan Hasina ce take siyar da abincin kasancewar Hanisa har yanzun batada kuzari ji sukayi an tsaya akansu suka ɗago a tare Hasina tace “Lahhh Bala dama kananan” idanunsa akan Hanisa yace “Jiya na shigo gari nazo na tarar da wani case ashe haka abu ya faru?” Kallon juna sukayi da sauri daidai lkcn da Abdul-Ahad ke isowa gurin idanunsa nakan Aneey Hasina tace “Meye ya faru?” Cikin faɗuwar gaba tayi tambayar.

 

Bala ya shafa sumarsa yace “Au dama baki sani ba ai Lawwali ne sukayi meeting da Me Abincin yan gayu har Sun gana shine kawai wani yazo a daren yasa aka kamashi har yau baasan inda yake ba”
Da sauri Hanisa takai dubanta ga Abdu shima itan yake kallo ya zuba mata ƙananun idanunsa kamar wanda yake nazarta wani abu, miƙewa tayi da sauri tabar gurin tana harhaɗa hanya Abdul-Ahad yabita da sauri yana mata mgn taƙi tsayawa itama Hasina biyosu tayi tana kiranta fir taƙi tsayawa saida ta taka da gudu sannan ta samu ta riƙota Ya ƙaraso da sauri ya riƙeta ta faɗa jikinsa ya haɗeta ya rungume yaja wata ajiyar zuciya me ƙarfi ya dubi Hasina yace “Am kinga Hasina jeki kiji da kayan abincin bari nabar da ita gurin nan” bai jira cewar Hasina ba yajata yasata a motarsa ya shiga yaja yabar gurin har zuwa lkcn kuka takeyi kanta kife cikin cinyarta kanta na wata sarawa me ƙarfi.
Batasan ya tsaya ba saida taji ya ɗora hannunsa akanta ta ɗago idanunta da suka ƙanƙance saboda kukan daya zame mata ɗabi’a a kwana biyun nan, murmushi ya sakar mata yace “taso muje ki huta idan Hasina ta gama zata iso nan sauku tafi tare” Binsa tayi da kallo zuciyarta nayi mata rawa akan shigarta gdan, ya fahimci inda ta dosa yayi murmushi yace “ba abinda kike tunani ne yasa na kawoki nan ba wlh banji a raina zan iya wannan rayuwar dake ba Aneey ki yarda dani da zuciya ɗaya nakeson taimakonki da jin tausayinki” ……….

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button