Yanci da Rayuwa 14-15
Arewabooks; Hafsatrano
Page 14-15
*** Laila ce ta mika mata wayar, ta kira Hajiya Maryam din tana saka wayar a handsfree
“Allah ya taimaki hajjaju, yau an tuna dani kenan.”
“Barka dai Hajiya, ya gida ya kasuwa? Ya jamaa kuma?”
“Alhamdullillah wallahi, ana fama.”
“Haka ake so, da fatan dai ba zamu samu matsala ba ta bangaren nan.”
“Karki ji komai Hajjaju, tunda kina dani ai baki da matsala.”
“Haka nake son ji. Sai batun yarinyar da kika kawo mana.”
“Toh me ya faru? Ina fatan ba wani laifi ta aikata ba.”
“Eh toh, dama dai tunda kika kawota hakuri kawai muke ganin dai akwai alaka, kinsan yaran nan kana tausaya musu ne su basa tausaya ma kansu.”
“Haka ne.”
“Toh yau dai hakuri na ya kare Hajiya, duk abinda yaro zai yi ka shanye banda magana ta dauke dauke.”
“Dauke dauke kuma? Fatiman?”
“Wallahi.”
“Toh subhanallahi, kuma wallahi yarinya ce ta gari, ban zaci haka daga gareta ba. Shekara uku muna tare ban taba samun ta da irin wannan laifin ba.”
“Kamar baki san halin dan yau ba Hajiya? Ai mutum yana iya chanjawa a kowanne lokaci.”
“Haka ne, toh Allah ya kyauta. Ta bata wayon ta dai gaskia. Yanzu me kika shirya yi akai?”
“Tunda da sanayya ai dole ko nayi niyya ma nayi hakuri, sai dai dole ta tafi gida, ba zan iya ba.”
“Toh nagode sosai Hajiya, hakan ma yayi nagode.”
“Ba damuwa, ai kin fi haka ma a wajena.”
Godiya ta sake yi sannan suka ajiye wayar.
Fusge mata nikaf din fuskarta Laila tayi dan tun dazu take son ganin ainahin fuskar ta dan daga idanun ta kadai ta lura da kamannin ta. Sai da ta dan tsorota dan batayi tunanin haka zata ganta ba. Duk da kukan da take yi amma kyawun ta na nan daram sai ma wani irin ja da fuskar tata tayi.
“Tashi ki wuce kije ki tattara kayan ki, ki bar gidan nan tunda ba gidan ubanki bane ba, shegiya me zubin mayu.”
Hajiya tace cikin son lallai sai ta kushe hallitar ta, tun daga kan mahaifyar Rafeeq ta tsani mace me kyau duk in da tagan su sai tayi kokarin kaskantar dasu hakan ne kawai yake dan kwantar mata da hankali.
Kasa tashi tayi saboda yadda kukan yaci karfin ta, kuka take sosai kamar irin wanda tayi ranar da ta rasa mahaifyar ta, bata taba sanin zafi da ciwon kazafi ba sai yau, kazafi irin na sata yafi komai. Bayan haka kuma a bata ka a wajen mutanen da suke ganin kimar ka, wannan wacce irin rayuwa ce.”
“Dallah tashi ki fita malama.”
Suka yi mata cha a ka. Da kyar ta mike tana layi kamar zata fadi, ta nufi hanyar fita daga falon ido a rufe ko kallon gabanta bata yi. Karo taji tayi da mutum kawai kanta yayi wani irin juyawa jiri ya taso mata amma duk da haka sai ta cigaba da kokarin barin falon.
Finciko hannun ta, taji anyi da karfi, sannan taji an tunkudata gaba tayi kamar zata fadi amma sai taji ta tokare da wani abu, a hankali hannun sa ya sauka akan nata ya dakatar da ita daga karasa fita.
“Asim menene haka?”
Mummy tace tana zaro ido ganin ya rike ta sosai yana wa musu wani irin kallon tsana ransa a matukar baci.
“Saketa, ka cikata nace.”
Ko gezau be yi ba, sai kawai yaja hannun nata ya karasa ficewa da ita daga wajen. Binsa kawai take har ya kaita bayan sannan ya saki hannun ta ya juya da sauri ya koma ciki.
Suna tsaye yadda ya barsu, duk sunyi tsuru cike da mamakin abinda ya faru sai gashi ya shigo
“Ina take? Ina ka kaita?” Mummy ta tare shi da tambayar. Be amsa ba, sai saukar mari da ya sauka a fuskar Aneesa, ihu ta saka kamar wadda aka yanki naman jikin ta, ta zube kasa tana kuka wiwi.
“Baka da hankali Asim? Dama mahaukaci ne kai ban sani ba? Akan banza yar aikin zaka daki kanwar ka?”
“Mummy please.” Ya fada a zafafe sannan ya nunawa Laila da Ummita hanya rai a bace yace
“Kowacce ta wuce gidan ubanta.”
Da sauri Ummita tayi waje Laila kuma ta tsaya dan be isa yace zai ci mata mutunci haka ba. Be kula ta ba ya sake juyawa kawai yabi bayan Ummitan sai da ya rakata har mota yaga ta shiga sannan ya juya ya koma bayan. Dakin a bude babu kowa da alamun ta tattare kayan ta, har ta fice daga gidan. Gate ya nufa ya samu gateman ya tambaye shi ko ta wuce yace masa eh yanzu ta fita. Da sauri ya koma wajen da akayi parking motocin gidan ya karbi key a fice daga gidan.
Tana tafe tana kuka har ya iso in da take, yayi parking da sauri a gaban ta sannan ya fito ya bude mata gaban motar. Bata da zabi da ya wuce ta shiga kawai dan yadda take tafiya bata san inda take saka kafarta ba bin nasa shine saukin ta. Tuki yake amma zuciyar na tafarfasa, ba dan babu kyau dukan mace ba da babu abinda zai hanashi yi musu duka saboda yadda ransa ya baci. Wai kuma ace mahaifiyar sa, itace zata aikata wannan danyan aikin.
“Me yasa kika boye min?”
Bata amsa ba, sai ya cigaba da driving din kawai har suka fita daga unguwar tasu suka hau titi sosai.
“Bani address din.”
Yace yana kallon titi kawai. A hankali cikin muryar kuka ta fada masa, kansa ya kara kullewa ya cigaba da tukin kawai. Suna cikin tafiya wayar sa tayi kara, dubawa yayi yaga Rafeeq din sai ya daga.
“Ka dawo?” Ya tambaya yana daga kwance tun dazun.
“Na dawo but na fita, wani uzuri ya fitar dani but ba zan dade ba.”
“Ok, idan ka dawo ka kirani.”
“In sha Allah.”
Ya jefar da wayar kawai ya cigaba da tukin sa. Har ya kawota unguwar be ce komai ba, ta kalle shi taga yanayin yadda fuskar sa take cike da fushi ya juya yana kallon waje yana jiran ta fita kawai. Jiki a sanyaye ta bude motar ta fita, tana rufewa yaja motar a fizge ya bar wajen ba tare da yace mata komai ba. Kukan ta cigaba da yi har ta karasa gidan nasu amma ga mamakin ta sai taga kofar a rufe. Wayar ta, ta laluba da nufin ta kira baban sai ta tuna bata saka ta chargy ba tun jiya. Gefen kofar ta samu ta ajiye kayan sannan ta karasa gidan Malam Hamza tayi sallama. Yana a zauren gidan yana alwala saboda an soma kiran magriba lokacin.
“Noorun Baba, kece da magribar nan haka?”
“Ina wuni?” Ta gaishe shi ya amsa sannan yace
“Shiga ciki ku gaisa da Salamatu sai kizo ki karbi mukullin gidan, babanki yace idan kinzo na baki.”
“Ina ya tafi Baban? Be fada min ba.”
“Baya so ki ce zaki taho ki bar aikin ki, wata kungiya ce irin masu taimakon marasa karfin nan tazo suka kaishi asibiti za’a duba kafar sa sannan ayi masa aikin kyauta, yanzu haka ma an gama komai ranar aikin kawai Ake jira.”
Wasu hawayen ne masu zafi da dumi suka sake sauko mata, hawayen bakin ciki hade da na farin ciki suka hadu suka hade mata har ta rasa wanne zatayi a ciki. Duk abinda ya faru ta sanar dashi ya jajanta sannan yace taje ciki. Shiga tayi suka gaisa da Salamatun sannan ta fito ya bata mukullin yace ta kai kayanta tazo ta karbi abinci.
Zuwa tayi ta ajiye kayan sannan ta koma gidan anan tayi magriba da isha ta sake komawa ta dauko wayarta lokacin an kawo wuta ta jona chargy.
***Tunda Asim ya fita Mummy ta kasa zaune ta kasa tsaye, tsoron ta kar abinda take gudu ya kasance dan bata taba ganin irin haka a tare da Asim din ba, yadda ya rufe idon sa ya manta kowa da komai akan yarinyar yayi matukar daga mata hankali. Tana ta kaiwa da komowa ta kasa yin komai har aka kira magriba, da kyar ta lallaba tayi sallah tana idarwa sai gashi ya shigo kamar tsohon kumurci zai wuce ta babu magana
“Asim.”
Ta kira shi ganin da gaske yake wucewar zai yi bayan ya ganta a zaune. Tsayawa yayi da tafiyar ya dawo ya tsaya daga gefe.
“Menene tsakanin ka da yarinyar nan?”
“Please dan Allah Mummy, kar ayi maganar nan yanzu. I can’t take it.”
“But dole ka fada min kuma karka sake kace min son ta kake yi, dan ba zan taba amince maka ka aure ta ba, sai dai idan bana numfashi.”
“Me yasa? Menene laifin ta? Ba mutum bace ba?”
“Asim? Ni kake ma wannan tambayar?”
“I’m sorry.” Sai ya wuce kawai dan idan ya cigaba da magana zai iya jawo ma kansa fushin ubangiji domin duk lalacewa ita din mahaifiyar sa ce. Sakar baki tayi tana kallon sa har ya shige sashen nasu.
“Akwai matsala.” Ta furta
“Banga ta zama ba.” Sai ta mike ta nufi bedroom dinta, ta shirya ta fito ta fice daga gidan.
A rufe Rafeeq ya dawo ya samu dakin Asim din, wayarsa da takalmin sa da ya gani a falon nasu yasa ya gane yana gidan, zama yayi a falon yana jiran ya fito jin shiru sai ya tashi ya fito ya nufi main living room din gidan. Aneesa na zaune ita kadai Laila ta tafi bayan da Asim din ya tafi. Tun lokacin sai yanzu ta fito daga dakin ta bayan ta gama cin kukan ta, ta koshi.
“Mummy fa?” Ya tambaye ta yana nazarin fuskarta da ta daga
“Ta fita.” Tace muryar ta a dashe.
“What’s wrong with you?”
“Ya Asim.”
“Ehen?”
“Marina yayi dazu.”
“Mari? Me yasa?”
“Akan wai dan Mummy tace mu duba dakin cook din nan ina neman bracelet dina, shine muka je muka duba kuma muka gansu a cikin kayanta har da watch din ka duk ta hada zata gudu dasu, shine fa muke ta mata fada ni ban dake ta ba amma Laila…”
“Ya Isa!!!” Ya daka mata tsawa me matukar gigitarwa, tashi tayi a zabure zata gudu ya fizgota ya wurgata saman kujerar sannan yasa kafa ya tare ta.
“Wallahi Allah Ya Rafeeq ban mata komai ba, kawai nace mata munafuka Laila ce da Ummita suka dungure mata kai sai Mummy Amma wallahi ni ban mata komai ba.”
“Ya salam.” Ya furta yana matsawa da sauri. Tana ganin ya matsa ta mike da sauri zata gudu ya sake rukota
“Idan kika sake kika fadawa Mum abinda ya faru yanzu sai kin gane baki da wayo.”
“Ba zan fada ba Allah.” Sakin ta yayi ta karasa arcewa.
Da sauri yayi hanyar fita yana ciro wayar sa, Saddam ya kira yace masa zasu fita, ya jawo motar ya fada da sauri.
_”Akwai matsala ne sir?”
“Yes akwai, muje gidan su.”
“Gidan su Nour?”
Gida masa kai yayi, sai yaja motar. Gidan a rufe suka tarar dashi da padlock dan bata dawo daga gidan Malam Hamzan ba Salamatu tace tayi kwanciyar ta kawai kafin gobe taje asibitin. Dunkule hannun sa yayi ya bigi ginin cikin tsananin fushi.
“Please call Ammar kaji ko taje asibitin.”
“Ok sir.” Saddam yace yayi dialing number Ammar shi kuma ya kira wanda yake kula da baban ya tambaye shi.
_”Bata zo ba.”_ abinda yaji kenan yayi gaba ya soma tafiya a titin yana jin ya sake failing a karo na ba adadi. Me yasa ya gaza nuna mata soyayyar da yake mata tun shekaru masu yawan gaske? Har yaushe zai cigaaba da farantawa wasu shi yana kuntace kansa? Tabbas lokaci yazo da ya kamata yayi wani abu da rayuwar sa shima, ko da hakan na nufin sacrificing duk wani abu da ya mallaka ne.
“Take me back.”
Yace kawai suka bar unguwar.
🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥
*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!
Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,
Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶
YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano
AMATULMALEEK
Mamuhgee
Guda biyun 1k
Guda Daya 500
Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902