Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 16

Sponsored Links

Arewabooks; hafsatrano

Page 16

#Thelovetriangle💓

Related Articles

***Kamar ya karbi driving din haka yake ji, ya matsu ya ganshi a gabanta ya san babu yadda za’a yi ta gujewa bukatar shi musamman idan ya zo mata da abu mafi muhimmanci a gareta. Ko parking din kirki be jira Saddam ya gama ba ya balle murfin motar ya fito ya wuce cikin gidan da sassarfa, sashen su ya wuce kai tsaye ya shiga bedroom dinsa ya birkito kaya ya ciro wasu papers da yayi musu ajiya ta musamman ya bude yana dubawa. Duk abinda zata bukata yana a tattare a takardun ya kwaso su kawai ya fito ya nufi part dinta cike da kwarin guiwar abinda zai aikata din. Ya riga yasan babu yadda za’a yi ta gujewa tayin plazar da kason sa a ccompany din tunda ya san da cewa tun asali sune burin ta. Idan ya mallaka mata su yasan zata shiga masa gaba wajen samun cikar burin sa daga nan sai ya tattara ya bar musu gidan gaba daya da kasar ma sai sanda kuma ya sake waiwayo su. A bude ya samu kofar hallway din sai ya kutsa kansa kawai yana jin yau shine karo na farko tun dawowar sa da ya tako nan din iyakarsa living room shima main one din amma baya wuce nan.

“Karka ce min son ta kake Asim?”

Ta tambaye shi tana adduar Allah yasa ba hakan bane ba, tunda ya shigo take masa mita da fadan abinda ya aikata a dazun amma ko gezau kamar ma ya shiryawa hakan.

“Tambayar ka nake, for the last time ka fada min gaskiya, son yarinyar nan me aiki kake ko a ah?”

Daga mata kai yayi alamar eh, a daidai lokacin Rafeeq ya karaso kofar kuma yaji tambayar karshen da kuma amsar da Asim din ya bayar.

“Na shiga uku, yanzu Asim ka rasa yarinyar da zaka so sai me aikin gidan ku?”

“Mum please, tambaya ta kikayi fa na bada amsa. What’s so bad about it?”

“Wallahi wallahi kaji na rantse ko? Sai dai idsn bana numfashi. Ba zaka wulakanta ni ka tozarta ni ba, kai ko hankali ba zakayi ka lura da taku da moves din Rafeeq ba. Ya riga yasan abinda ya kamace shi hankalin sa gaba daya yana kan business din nan ba irin wannan shirmen ba,sai sanda ya gama tattare komai ya koma karkashin ikon sa sannan zakayi hankali. Bayan haka ma wai ka rasa wadda zaka ce kana so sai yar aikin gidan ku? Yaushe lalacewar har ta kai haka?”

“Please dan Allah Mummy, karki kawo maganar Feeqq. Be yi laifin komai ba, he is just trying his best, nasan ba zai taba cutar dani ba, so please Mummy let him be.”

“Ai na sani dama, nasan abinda zaka ce kenan,na rasa wannan jaraba wallahi.”

Duk yadda yaso ya danne zuciyar sa sai dai ka kasa, wani irin fushi ke taso masa da bacin rai. Ya dade da sanin bata kaunar sa amma jin hakan yau ya kara tabbatar masa da duk abinda zai yi sai ta zarge shi, me yasa zai zauna yana danne zuciyar sa akan ta? Me yasa zai cigaba da daukar komai bayan yasan shi din be yi mata wani laifi ba idan ka cire kasancewar shi daya daga cikin ahalin gidan ta tsatson matar da taki jini a rayuwar ta, laifin shi daya da ya kasance babba yasa take ganin kamar yayi hijacking komai bayan a zahiri ne kawai hakan amma a badini ba haka bane ba. Sai da ya zauna a motar ya daidai ta sannan ya soma tunanin yadda akayi har Asim ya fara son ta da har zai iya tsayawa a gaban Mummy kansa tsaye ya amsa tuhumar ta. Yaushe ma ya san ta har haka da har zai iya daukar wannan risk din? Ya riga yafi kowa sanin kyama da tsanar dake tsakanin iyayen su da talauci, abinda ya aikata daidai yake da tunzura AJI ya soma daukar mataki me karfi akansa.

“Allahumma Ajirni Fi musibati.”

Ya furta a hankali. Idan har ya tabbatar da abinda Asim din ya fada toh tabbas zai hakura, ko da hakan na nufin katsewar numfashin sa.
Da ace shi yake driving da kansa da kuwa tabbas zai iya samun accident saboda yadda gaba daya ya daina gane komai, duk da hakan yana tattare da calmness din nan nasa da Mummy ta tsana a tattare dashi. Duk yadda ta kai da son kona masa rai baya taba nuna mata ma yasan tanayi bare har taga sauyi a yanayin sa.
Bashi da niyyar zuwa gidansa a yanzu dan yana da bukatar nutsuwa sosai daga shock din da ya shiga, dan haka ya ce su wuce transcorp Hilton ya kama business suite ya ce suje sai ya neme su, duk jikin su a sanyaye yake musamman Saddam da ya riga ya san damuwar ogan nasu, gashi yaki yarda yayi maganin damuwar abunda yake da yakinin be fi karfin sa amma ya bari kullum yana kara taazzara matsalar sa. Sai da suka dan zauna kadan a lounge ko zai neme su ganin shiru yasa suka yi deciding tafiya kawai.
Tunda ya shiga ya zube a kasan lallausan carpet din dake tsakiyar falon ya rike kirjinshi da yake masa wani irin masifar zafi. Tun a Scotland da yayi masa karshe be sake masa ba sai yau din da yake jin gaba daya duniyar na juya masa da wani irin tashin hankali da tsoron rasata rashi iirn na har abadah, domin daga ranar da ta zama mallakin Asim daga ranar yayi sallama da duk wani abu da ya shafe ta ko ya dangance ta domin ita din ta haramta a gareshi. Da farko ya dauka abun me sauki ne amma the more yake tunanin yiwuwar hakan da more yake kara zama cikin tashin hankali.
Yadda chest din nasa yake dagawa da wani irin ciwo yasa ya cire hannu ya lalubo wayarsa ya kira Dr Mas’ud yace yazo ya same shi a Hilton. Ba dau wani lokaci ba yazo ya same shi a yanayin da yake, ya taimaka masa har ya samu daidaito a yadda yake ji din ya kwanta saman gado kawai ba tare da ya iya amsawa Dr Mas’ud din tambayar da yake masa ba.

“Wannan ne second to the last stage Feeqq, you have endured enough ya kamata kayi letting go na duk wani abu da ya zama zai kawo cikas ga samun sauki da lafiyar ka.”

“It wasn’t easy, but I will try wannan lokacin. Na gaji ni kaina.”

“It’s better kam, a yadda kuke da kudi na dauka ba zaka taba samun wata matsala ba feeqq, I always envy you sanda muna secondary school thinking ku baku da wata matsala, ashe ba haaka bane ba, kowa da tasa kaddarar kuma kowa da kalar jarrabawar sa.”

“The rich also cry Dr, ba komai ne kudi yake iya siya ba,sai dai yana kawo sauki sosai a rayuwa.”

“Na yarda da kai.”

“But Alhamdullillah ala kulli halin.”

“Yes alhamdullillah.”

“Kasha magungunan nan, sannan ka samu enough rest at least for good 2days, in sha Allah by then komai zai yi sauki. But gaskiya sai ka hakura da duk abinda yake saka tunani, and lastly, marriage…”

“Kayi aure, at least zaka samu company. You won’t be alone all the time, kuma you can share your problems with your wife, wannan ma kadai sauki ne. And believe me, akwai tarin abubuwa masu yawa a aure da sai kayi zaka gane.”

Lumshe idon sa yayi yana hasaso yadda ya tsara rayuwar sa da ita, rayuwa me cike da jin dadi, sassaukar rayuwa ba irin rayuwar gidan su mara kan gado ba, rayuwar karya da dorawa kai. Asim ne ya fado masa, sai ya tuna kalubalen dake gaban sa, da sauri ya janye tunanin yana bude idon sa da suka kara kadawa sukayi jawur sannan ya gida ma Mas’ud din kai yace

“Duk zan bi shawarar ka, nagode sosai.”

“Nima nagode, bari naje kar madam ta fara kira.”

Murmushi kawai Rafeeq yayi, ya raaka shi da ido har ya fice sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Dukkannin su bacci ya kauracewa idonsu. Kallon celling din dakin tayi tunanin Asim na cigaba da dawo mata, yadda ya tsaya yayi protecting nata a gaban family dinsa, da kuma yadda ya rike hannun ta cikin nasa sannan ya dawo da ita har gida. maganar da yaki yi mata ba karamin damun ta, tayi ba. Yayi fushi sosai hakan ya sa ta kasa sukuni. Wayar ta dake gefen ta, ta kalla taga karfe sha biyu har da kwata. Samun kanta tayi da dialing din number sa gabanta na faduwa. Yana kwance ya dora wayar a saman kirjinsa, bacci yake son yi ko ya samu saukin tunanin amma shiru, gashi Rafeeq ya kashe wayar sa kuma be dawo gida ba tunda ya fita, sau biyu yana leko shi har ya gaji ya hakura. Vibration din wayar yaji ya daga ta yana kallon me kiran sa a wannan lokacin, sai da ya kalli wayar sosai ya tabbatar da ita din ke kiran sa. Da sauri ya mike zaune, ya daga be jira maganar ta ba yace

“Bari na kiraki.” Ya katse ya kirata da sauri. Dagawa tayi sai ta kasa cewa komai, shi din ma shirun yayi dan bashi da abinda zai ce mata.

“Kayi hakuri.”

Ta fada tana share hawayen da taji yazo mata ta sama ta ka.

“Are you ok? Babu abinda yake damunki?”

“Babu komai.”

“Can I see you tomorrow?”

“Eh.” Ta gid’a kai kamar yana ganin ta

“Ok, zanzo na ganki.”

“Tom.” Tace a sanyaye duk da tasan akwai tarin kalubale a taraiyar su amma ya zatayi? Ba zata iya ce masa a ah ba.

“Ki kwanta kiyi bacci, I will call you da safe.”

“Ok, sai da safe.”

“Bye.” Ya kashe wayar ya kwanta gaba daya, Yana kwanciya bacci ya dauke shi da karfi.

***Da dan kwarin jiki ya tashi yayi sallah sannan ya tura wa Asim message ba zai shiga office ba zai je kaduna ya dawo. Be jira reply dinsa ba ya kashe wayar dan baya so ma Aji ya kirashi. Dayar wayar ya dauka ya kira Ammar lokacin karfe tara da rabi. Maganar Baban sukayi sannan yace masa idan Noor tazo asibitin ya sanar dashi. Daga nan ya kira Saddam yace ya koma unguwar tasu ya sake duba masa sannan ya zo ya sameshi idan ya dawo.
Murza gefen kansa yayi yana lissafin kwanakin da suka rage a waadin da AJIn ya diba masa, bashi da wani plan yanxu kuma musamman da abun nan ya faru zai zubawa sarautar Allah ido yaga abinda zai faru Amma tabbas ba zai taba hada nema da Asim ba, dole ya hakura ya bar masa ko da kuwa shi ma ba zai same ta ba.
Bayan kamar minti talatin da wayar su Ammar ya kirashi ya sanar dashi zuwan ta asibitin a daidai lokacin tare da Malam Hamza da suka hadu dashi ranar. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, a kalla hankalin sa zai kwanta yanzu yasan tana hannu na gari kuma ta kwana gida a jiyan bayan barin ta gidan nasu. Labarin da ya samu yasa ya dan samu sauki sai kawai ya sake mikewa a saman sofa yana jiran karasowar Saddam din su dan duba wasu ayyuka zuwa azahar.

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button