Yanci da Rayuwa 19
Arewabooks;hafsatrano
Page 19
*****
“Wallahi Baba.”
Ammar yace cikin son kara nuna yadda abun yake. Murmushi Saddam yayi ya kara gyara airpod dinsa yadda zai ji komai sosai.
“Lafiya?” Rafeeq yace yana kallon sa.
“Lafiya lou Sir.” Yace yana maida kansa titi ya cigaba da driving din cikin farin ciki da annashuwa
“Tabbas na gamsu shi din mutumin kirki ne, sannan bani da haufi akan soyayyar sa ga diyata, irin mijin da nake mata fata kenan Ammaru, sai dai wani hanzari ba gudu ba, Fatima ita kadai ce ta rage min a halin yanzu, bani da kowa sai ita sai Allah, dangi na kaf suna wata nahiya me nisan gaske, ba kuma ni da niyyar waiwayar su nan kusa ko nesa, kana ganin iyaye irin nasa, babban gida irin nasu zasu amince da wannan al’amarin?”
“Duk wannan ba matsala bace Baba, in dai ka amince duk wannan zai zo da sauki.”
“Waye ni da zan ki amincewa? Zan tuntubi Noorun da maganar, duk da musulunci ya bawa iyaye damar zabawa yar su budurwa miji na gari.”
“Mun gode sosai Baba, Allah ya saka da Alkhairi.”
Da sauri Saddam ya bugi steering motar, cikin matukar farin ciki yace
“Yes!!!” Sake kallon sa Rafeeq yayi, sai yayi saurin waskewa yana maida kansa gaba kawai
“Kana da matsala ne?” Ya tambaya
“I’m sorry sir, ayi min afuwa.”
Shiru kawai Rafeeq din yayi be sake cewa komai ba, har suka karaso gida ya sauke shi ya shige shi kuma ya juya ya koma asibitin wajen Ammar dan su karasa tataunawa.
A falon ya tarar da Mummy tana magana da Aneesa,dan dukawa yayi ya gaishe ta sannan Aneesa ta gaishe shi a dan tsorace ya amsa ya nufi part dinsu
“Son zo mana.”
Mummy tace tana tsaida shi. Dawowa yayi da baya ya zauna a gefen Aneesan. Murmushin mugunta tayi sannan tace
“Maganar jiya da mukayi da AJI.”
Mikewa yayi da sauri sannan yace
“Duk abinda kuka yanke daidai ne.”
“Eh toh dama maganar dai daya ce, an samu mata uarinyar kirki me hankali kamar kai, zuwa zamuyi kawai a kai tambaya da komai, idan muka samu yadda muke so ma sati biyu ya isa ayi komai, dan na matsu naga wannan ranar dama.”
“Duk yadda kikayi yayi.”
Ya wuce kawai ransa na baci. Dariya ta saka aneesa ta kalle ta, ta marairaice fuska
“Mummy Laila fa?”
“Kanwar uwarki ce Lailan ko ta ubanki?”
“Kai Mum!”
“Toh Allah mana, ki daina shigar min magana abinda babu ruwanki, kuma wallahi naji wannan maganar a bakin Laila ko Ummitan sai naci ubanki.”
Hannu tasa ta kama bakin ta sannan ta mike tana buga kafa.
“Ni kowa ya tsane ni a gidan nan.”
“Shegen halin ki ne na rawar kai ya ja miki.”
Barin falon tayi da gudu tana sakin kuka. Tsaki Mummyn tayi ta tashi ta wuce part din AJI domin wasu mahaukatan kudi take so ta karba a wajen sa duk ta fake da auren Rafeeq din ta yagi rabon ta.
Asim na zaune a falon nasu suna magana da Noor a waya Rafeeq din ya shigo. A kishingide yake ganin Rafeeq din yasa shi mikewa ya zauna sannan yace
“Zan kira ki.”
Hannu Rafeeq din ya mika masa yana kokarin daidai damuwar sa sannan yace
“Ashe kana ciki.”
“Eh wallahi, tunda na dawo daga office ban fita ba ma.”
“Oh ok, ya Aikin?”
“Ban iya yin komai ba bayan tafiyar ka, I felt bad ganin yadda gaba daya baka da walwala. Please me yasa ka bawa su Mummy go ahead akan irin wannan case din, kai ne zaka zauna da ita basu ba, please kaje kace dasu su kara maka time.”
“Ni na fada maka bani da walwala? I’m very ok fa, kuma menene laifi dan na bama iyaye na zabi? Nasan ba zasu taba yin mun zabin abinda zai cutar dani ba.”
“Haka ne, but kasan zabin su ai, kasan irin taste din da suke dashi akan matan da zamu aura.”
“Ba komai duk yadda sukayi daidai ne.”
“Oh ya Allah, I know you are just pretending, please ka barni naje na samu Mummy nayi mata magana, zata yi ma AJI magana.”
“Kar ma ka fara, ranar kace zaka bani labari, yanzu ina jinka.”
Sosa kansa yayi yana murmur
“Issue din nan ne akan househelp din nan da kace a sallameta, ban sani ba ashe itace new girlfriend din nan tawa da nake baka labari.”
“Oh really!”
“Wallahi, ban sani ba sai a die minute, nazo na samu yan iskan yaran nan sun tarar mata daga me zagi sai me dungurin ta.”
“Su Laila ko?”
“Eh su, hadda Aneesa da Mummy fa.” Yace yana dafe kansa.
“Gaba daya nayi loosing control dina na yi musu rashin mutunci, sannan naje na kaita gida.”
“Good, kayi abinda ya dace.” Yace yana mikewa
“Yanzu muna magana da ita ka shigo ma, inaso idan har muka fahimci juna sai aje ayi magana tunda naga Mummy ma tayi supporting abun a wajen Aji, nasan zata shige min gaba duk da bata son yarinyar.”
“Yayi, try your best ka samu amincewar ta, I will support you too .”
“I know, thank you bro.”
Yace yana murmushi, murmushi ya maida masa shima ya wuce dakin sa ya barshi cike da farin ciki.
***Sati daya tsakani da aikin aka sallami Baban, mota Rafeeq ya bayar aka kaisu har gida sannan aka sauke musu kayan abinci masu yawan gaske, kasa magana Baban yayi kawai saboda dawainiyar tayi yawa gashi babu damar yayi masa godiya dan tun ranar da yazo asibitin be sake komowa ba sai dai aiki tsakanin su da Ammar, ba zai iya kiyasta kudin da suka kashe masa ba a dan zaman nasa dan ba karamin kudade bane ba, asibiti a Abuja irin wannan sannan ayi maka aiki kasan dole an ci kudi me yawan gaske.
Har la’asar suna zaune da Noor bayan ta gama gyara musu gidan ta tsaftace ko ina yaga bata da shirin tafiya sai yace mata
“Ya labarin aikin naki?”
“Na daina aikin nan Baba.”
Tace tana marairaice fuska, dama abinda yake so tace kenan yake ta tunani dan in dai dan gidan yana sonta gwara ta hakura da aikin kar azo a samu matsala. Ta dauka zai ce ta tafi amma sai taji yace
“Allah sa haka ne mafi alkhairi.”
“Amin.”
“Tashi dauko min magunguna na nasha.” Tashi tayi ta dauko masa ta dawo ta kawo masa da ruwa yasha sannan ta zauna a gefen sa suna dan taba hira. Suna cikin hirar akayi sallama, Hajiya Maryam ce. Da sauri Noor ta tashi ta tare ta, ta karbi jakarta tana jin dadin ganin ta
“Yau dai nayi sa’a, kwana biyu kenan ina zuwa ajere bakwa nan.”
“Sannu da zuwa Hajiya.” Baban yace yana dariya
“Yawwa, aikin akayi kenan Baban Fatima.”
“Wallahi Hajiya, anyi aikin kafa Alhamdullillah, shiyasa ma bakya samu na kwana biyu.”
“Toh Masha Allah, Allah yasa anyi a sa’a.”
“Amin.”
“Hajiya Ina wuni?” Noor ta gaishe ta
“Lafiya lou yata, ya gida ya jikin Baban naki?”
“Da sauki.”
“Alhamdullillah toh, Allah ya bashi lafiya.”
“Amin.”
“Kawo ruwa Noor.”
“A ah a koshe nake, magana nazo muyi me muhimmanci, ke Fatima jeki ko gidan Malam Hamza ne ki jira mu.”
Tashi Noor tayi ta dauko Hijab dinta ta zura ta fita.
“Toh dama magana ce ta kawo ni, akan gidan da Fatima tayi aiki, kasan dai dama mutane na ne, dalili na ma suka karbi Fatima.”
“Eh tabbas haka ne.”
“Toh sune suka zo min da magana akan Fatima, matar gidan da kanta tazo takanas tace tana nemar wa danta auren Fatima, da fari nayi tunanin wasa suke ma ganin yanayin su da arzkikin da suke dashi, toh daga baya da sukayi min bayani sai na gamsu, har nayi musu alkawarin zan shige musu gaba, idan har ka amince toh zasu turo maza azo ayi magana ta fahimta, dan su basa so aja lokaci ma.”
“iKon Allah, kenan dai maganar akwai ta, tunda har manyan sun samu shiga.” Yace cike da mamaki
“Akwai àbinda ya faru ne?”
“Eh toh, na samu makamanciyar maganar daga bakin abokin shi yaron nasu, tun ranar nake jinjina maganar na zata dai magana ce kawai ta yara, ashe da gaske ne.”
“Gaske ne kuwa gaskia, kuma dai basu da wata matsala tunda nayi mu’amula dasu, yaran nasu akwai hankali da nutsuwa musamman shi wannan din, ina ganin dama ce tazo na samarwa Fatima rayuwa me inganci, rayuwar da kake mata shaawa da fata. Zata je tayi rayuwa me YANCI, rayuwa me cike da farin ciki in sha Allahu. Burin ta na karatu zai karasa ciki, daga nan har PhD idan tana da raayi zatayi.”
“Tabbas Allah ne ya amsa addua ta, ya kawo mana dauki a lokacin da nake cike da tunanin mafarkin Nooru ta, zanyi istikhara akai, zan kuma barwa Allah zabin sa. Babu matsala in sha Allahu, duk sanda suka shirya sai su turo, sai a sanar dani kafin ranar domin na sanar da mutane na ma.”
“In sha Allahu, nasan da sun samu labari zasu turo dan basa son a bata lokaci ma, amma me zai hana ka sanar da dangi da yan uwanka Baban Fatima?”
“Da sauran lokaci, duk da zan so hakan domin asan ita din ma yar dangi ce gaba da baya, yanayi na rayuwa ne ya kawo mu nan, amma dai ba yanzu ba, akwai lokaci.”
Ya kara maimaitawa yana jijjiga kai.
“Babu matsala ai, in sha Allahu duk abinda ake bukata na dangi zan yi wa Fatima.”
“Nagode sosai Hajiya, Allah ya saka da Alkhairi.”
“Amin amin, bari na koma, duk yadda ake ciki zaka ji ni, sai mu tsara abinda ya kamata a kalla ita ma Fatima mu siya mata mutunci a idon dangin mijin ta.”
“In sha Allahu, zamuyi abinda ya dace.”
“Toh shikenan, sai anjima Allah ya kara lafiya.”
“Amin, ku gaida gida nagode.”
Fita tayi sai ya zauna jugum yana tunanin abinda ya kamata yayi din domin ya kankaro mutuncin yar tasa a idon irin wannan dangin da zata shiga wanda da dukkan alamu manyan mutane ne a kasar, abu daya zai yi shine, ya sauke abinda yake ji a zuciyar sa ya kira Alhaji Isma’il ya sanar dashi za’a zo neman auren Fatima a matsayin shi na walliyin ta, duk da yasan yin hakan tamkar ya karya alkawarin da yayi ma kansa ne na rabuwa da su da duk wani abu da ya dangance su amma ya zaiyi, zai yi komai ne saboda farin cikin diyar sa wadda bashi da kamar ta a duk fadin duniyar nan.
Yadda Noor ta fita haka tazo ta sameshi ta zauna tana kallon yanayin sa dake nuna yana cikin tunani.
“Baba lafiya?”
“Kalou Uwata, tunani nake ne kuma ina so muyi wata magana me muhimmanci, ina fatan zaki bani hadin kai domin magana ce da ta shafi rayuwar ki.”
“In sha Allahu Baba.”
“Akwai wata alaka da yaron gidan da kikayi aiki ne?”. Kallon shi tayi da sauri, ya girgiza mata Kai
“Karki ji komai, fada min kinji diyata.”
“Eh akwai Baba.”
“Toh Masha Allah, haka nake son ji dama, zasu turo tambayar musu auren ki, idan sun zo zan karbi tambayar su dan na yaba da hankali da tarbiyyar sa, ina fatan hakan yayi miki.”
Shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta fada kogin tunani maganar Baban da tazo mata a bazata, aure ita? Yaushe Asim din ya santa haka da har zai taka dokar iyayen sa takin talaka yazo ya nemi auren ta? Kenan Hajiya ta amince ko kuma gaban kansa zai yi? Be taba furtawa yana sonta ba sai dai dukkan alamun sa sun nuna hakan, ya dai ce mata yana jiran lokaci ne zaizo mata da maganar wadda a kullum take kasa ido da kunne tana jira dan ta yarda dari bisa dari shi din masoyinta ne na hakika zata kuma karbi tayin soyayyar sa duk da tana hango kalubale a tattare da hakan amma zata dauka idan har ya furta matan dan da gaske take jin sa har zuciyar ta.
“Baki ce komai ba Noorun Baba.”
“Bani da zabi fiye da abinda ka zaba min Babana, duk wanda kaga ya dace dani Baba ka zaba min shi zan karbe shi hannu bibiyu.”
“Tabbas nasan ke din ‘ya ce ta gari, wadda take kokarin faran tawa iyayen ta tun kina yar kankanuwar ki, a yanzu ba zan miki dole ba, idan har kina da wani abu a zuciyar ki sanar dani, sai na basu hakuri.”
“A ah Baba, na amince Allah yasa haka ne mafi alkhairi.”
“Amin nagode, Allah yayi miki albarka ya baki zaman lafiya ya cika miki burin ki.”
“Amin Baba.” Tace wasu hawaye masu dan dama suka shiga sakko mata, hawayen da bata san takamaimai dalilin saukar su ba, ba zata iya misalta yadda take ji a lokacin ba,tasan dai kawai dole akwai kalubale a gabanta da bata ma san ta ina zata fara ba.