Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 15-16

Sponsored Links

_Last Free page_*

 

Sosai hawaye kibin kuncinta tana qara saita injin idonta akan Aseem kallo takeyi masa da yake bayyana tsantsar tsana dajin haushi da kuma tausayin kai tasan duk duniya ba kowane yaja mata wannan wulaqancin ba face Mal, numfashi ta sauke kawai ganin wankin hula na neman kaita dare ta juya ta canza hanya ta tafi tabarsa tsaye yana bin bayanta da kallo yana murmushin mugunta shikadai tasan abinda yake saqawa a zuciyarsa yarinyar ta gama lalacewa idan ta zama mallakinsa zai nuna mata iyakarta zai nuna mata duniya da bambamci.
Komawa yayi yatada motarsa ya tafi sai lkcn Jiddarh ta lura da cewa ashe Asmah ta jima dayi mata nisa tabita da sauri tana qwala mata kira bata tsaya ta saurareta ba sai a cikin makaranta suka hadu bayan an gama assembly suka tafi ajinsu Jiddarh ta dubi asmah tace “wato Allah idan yana sonka da arziqi sai ka zagi sarki a gaban fadawa yace gaisheshi kayi wlh Asmah a rayuwata na dade banga kyakkyawan namiji irin Aseem Ba kayy gsky kin dace, amma fah da alamun dan izzar masifa ne zakisha fama….”

Related Articles

 

Wani naushi da Asmah ta kaiwa Jiddarh a baki yasata gocewa tare da cewa “daga fadar gsky kuma Allah mijinki dan kyakkyawa dashi” malaminsu ne ya shigo hakan ya tilastawa Jiddah yin shiru ita dama Asmah bakinta ya kulle kalaman Aseem ne kawai sukeyi mata yawo a kwanya iyayenta matsiyata idan ta tuna wannan kalmar sai taji hawaye ya zubo mata to amma komai ya samu shamuwa watan bakwai yaja mata da mahaifinta baibi son zuciya ba da yanzu tana tare da masoyinta, da taji haka a ranta saita tuna yace da quarter million ya siye Sadiqunta.
Gabadaya duniya tayi mata zafi ji takeyi kamar tayita rusa kuka hakadai a dafe aka tashi suka tafi gda daqyar takai gidan saboda azabar masifar zazzabi da yake dirar mata tana zuwa ko uniform bata cire ba ta fara kwara amai bayan ta gama ta shige dakin innah ta kwanta tana mayar da numfashi

 

A kwance take amma duniyar juya mata takeyi itadai bata qara sanin komai da yake faruwa ba sai farkawa tayi ta ganta daure da robar ruwa a hannunta ta rinqa bin dakin da kallo daya da daya tanason tunano ko a ina take a hakan taji an turo qofar an shigo ta juyo da kanta idanunsa na kanta yana wani lumshesu kamar me jin bacci.
Guri ya samu ya zauna ya bude takardar hannunsa yayi rubuce rubucensa ya rufe ya sake dagowa yanzun kanta yana saman silling fasali yaja ya miqe daidai lkcn da Inna Azeezah qanwar Innah take shigowa suka gaisa har yana wani rusunawa tace “ya me jikin?” Kallon Asmah yayi yace “gatanan da sauqi yanzu ta farka da alamun jikin dakyau insha Allahu gobe ma zamu koma gida yasu Innah?”

 

“Alhmdllh” ta furta koma ta zauna tana hade kaya shikuma ya fice bai jima ba ya dawo da tarkacen ciye ciye ya ajiye Innah Azeeza nata godiya yayi murmushi yace “babu komai Innah yiwa kaine fatanmu dai ta samu lfy ai taji jiki sati biyu a kwance ga hidimar biki sai matsowa takeyi yanzu fah saura sati biyar” jinjina kai tayi tace “Allah yasadai ayi lfy a gama lfy”

 

Amsawa yayi da amin sannan yasa kai ya fice zuciyarsa najin haske yanajin nishadi yasan yagama saita saarsa Asmah zata gane kurenta tabbas zatasan ta shigo gonarsa da wannan tunanin ya tashi mota ya nufi gdansa yajima a mota kafin yayi qarfin halin fitowa yana ayyana ta yanda zai tunkari Mime da mgnr auren nasa bayan shi da kansa yayi mata alqawarin bazai taba hada matsayinta da wata ba balle aje ga batun aure.
Shahada yayi daya haura ya tunkari saman a kwance a parlourn saman ya isheta tana duba jarida ya nemi guri ya zauna ta ajiye jaridar tare da dagowa ta dubeshi sukayiwa juna murmushi ya shafa kansa yace “ya gda?” Miqewa tayi zaune tana yatsina tace “gashinan babu dadi kadaici ya dameni kaikuma ka daina samun lkc na na rasa meye yake daukenka hankali gareni” kawar dakai yayi ya shafa sumarsa yace “abubuwa ne sukayimin yawa 2 days dinnan inason samun zama dakema nakasa samun lkc” shiru tadan ratsa na dogon lkc can ya dago yace “Maryam Aure zanyi…..” Wata zabura tayi ta miqe da sauri tace “me….me kace Aseem”…….

[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*

 

*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*

 

 

Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya 200 ta _account dina_
__0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTBank_ _ko kati MTN ta whattsAp a wannan number 09013718241 ko VTU ta wannan number 09031307566._

_Gareku yan’uwanmu na Niger kuma fah kuna da damar samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button