Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 25-26

Sponsored Links

*25-26*_

Tana shiga part din nata ta dauki wayarta tana latse latsenta tana murmushi hirar manyan mata na bata nishadi a group din DOMINKI YAR GATA na Oum Hairan wanda Aunty Hajar ta biya mata tasata a ciki tunda ta shiga batace komai ba saidai murmushi da takeyi wata matace a group din tace _“wato Jiya naji dadin lectures din da Malama Ummi tayi mana a gidannan nabawa kafura kuka kwana sukayi suna bala’i inajinsu dake baa dakina yake ba na kulle qofata”_ stikers wata ta turo ta dariya Asmah ta sauke ajiyar zuciya kafin tayi mgn taji wata tace _“ ai koni da nake ni kadai jiya Munji Happy nida Abban Salim har kyautar kudi yayimin unguwar da na dade ina tambayarsa sai gashi ya daukeni ya kaini, Mukam sai gdy Oum Hairan group din dominki yar gata 2 yana taimaka mana wajen samawa kanmu yanci gurin riqaqqun mazajen nan na zamani babu boka babu mallam”_

 

Related Articles

Suna taka da wannan tattaunawa taga ansawa group din mukulli bayan kamar mintuna biyar alamun rubutu suka bayyana a saman group din sallama ce ta fara shigowa kafin me rubutun ta fara da cewa _”kamar yanda kuka sani yau Oum Hairan ke gabatar da shirin zuciyar masoyi ba Aunty Mamee ce saboda haka zan koma gefe Nima nayi sauraro aunty mamee bismillah dalubanki na sauraronki💃🏻”_
Tasa alamun rawa tayi dif abinta shudewar yan mintuna aka fara gabatar da lecturer me taken *ZUCIYAR MASOYI* matan sunji nayi duk sunyi zukudun suna saurare” jinjina kai kawai Asmah takeyi taji manyan wada wadai tuni ta shiga hankalinta wani abin idan Aunty mamee ta fada har daukewa numfashinta yakeyi saboda kunya, ta jima a zaune ko sallah ta kasa tashi tayi bayan an gama lectures ne kuma aka tafi bangaren gyara Hajjiya mandiya hamshaqiya Oum Hairan ce ta karbi filin da cewa _“Da yawan iyayenmu mata suna damun kansu Idan zasu auradda yayansu da nemo musu maganin mata wanda a zahiri ba abinda ya kamata ba kenan abu mafi muhimmaci shine dauki yarki ki kaita asibiti ayi mata gwajin sanyi ayi mata hoton maranta idan ta tsallake batada sanyi fine idan kuma akwai sanyi to aiki ya sameki ke uwa dole ne kiyi aiki da hikima wajen nemawa yarki lfy domin kuwa indai da sanyi a jikinta ba namiji ba macema yar uwarta bazatayi qima a gurinta ba”_

Numfashi Asmah taja cikin tsoro tace “munshiga uku sanyi kuma? Tab to muda ko ararrabi baa jiqa manaba ya kenan?” Wawurar wayar tagumi
a kashe datar ta kira number Aunty Hajar ta daga tace “Aunty ki hau online oum hairan nayi lecture akan ciwon sanyi a group din DOMINKI YAR GATA nifa kaina ya kulle” kashewa tayi ta sake kunna datar ta rinqa bin bayanan a hankali tana nazarinsu tunawa tayi batayi sallah ba ta miqe ta dauro alwala tayi sallah bata qara hawa ba saida tayi wanka tasa kayan baccinta ta kulle part dinta ta haye gado taja bargo sannan ta kunna tanabin bayanan wanda bata ganeba tana tambayar Aunty Hajar saboda anriga angama lectures din taji bayanai sosai har ta dauki na aikatawa gobe da safe.

 

 

Washegari tun asuba data tashi bata koma ba ta gama gyaran part dinta ta sanya wasu yan iskan riga da wando rigar airmles ce wandon three quarter ta bude cikin akwatunanta ta dauki takalmi sawu ciki tasa ta hade gashinta tayi donnut dashi ta sauko daga saman da dan gudu gudunta ta bude qofar ta fice ta nufi gurin training din gdan tana yan guje²nta da tsalle tsallenta Aseem da ya dawo daga masallaci ya zauna a wani bangare na gurin ya zuba mata ido yana kallon yanda take sarrafa jikinta kamar babu qashi abin yayi bala’in burgeshi baisan sanda ya aje jaridar ya zubanta ido yana sauke ajiyar zuciya, dakatawa tayi tana duba agogonta tana share gumi.
Bakwai saura juyawa tayi ta nufi part dinta ta sake wanka ta sake kaya ta dauko wayarta ta nufi bangaren nasu bata tarar da kowa a parlour ba ta tabe baki ta fara hade kayan dake parloun bayan ta gama ta dafansu tea ta zubansu a flast ta soyansu doya da qwai ta jere musu tayi ficewarta tana fita suka fito qamshi ya cika gdan suka sauke ajiyar zuciya Mimee tace “wannan yarinyar ta shigo ne?”
Kallon falon yayi yace “idan haka kikabar parlounki to qila bata shigo ba” tabe baki tayi ta zauna a dinning din ta bude kayan abincin ta fara zubawa yayi murmushi yasakai ya fice a ya nufi inda yake parking motarsa har ya bude zai shiga yaji kamar ana kallonsa ya dagakai sama Asmah ya hango tsaye a corridor din samanta tana cilla teddy sama tana cafewa.

 

 

Jingina yayi jikin motar ya zubanta ido a fili yace “komanta shirme ne ita” qwafa yayi ya juya ya shige motarsa ya tayar ya fice daga gdan tayi murmushi ta koma ciki tace “ nagama wannan aikin” ita kanta ta gaji tana shiga bajewa tayi a gado ta kama bacci sai biyu ta tashi bata wani damu ba ta miqe tayi wanka ta sanya rigarta iya gwiwa ta daure gashinta ta sakeshi tasa hular rigar ta fito ta nufi part din na Mimee tana tafe da Bluetooth a kunnenta lkcn hudu harta gota tana rangaji kamar itaciyar mangoro ta shiga part din na mimee tana jibge a kujera daganta hannu tayi tace “Hi baby how per” bata jira amsar ba tace “sai hqr yau mijina yace na kwanta na huta zai shigo da abinda zaaci…..” Mgnr ce ta maqale lkcn da yake shigowa ta hadiye yawun tsoro lkcn da suka hada ido qasa tayi da kanta tace “your are wlcm My qalb…..” Kallon mimee yayi da sauri itama shi take kallo Matsawa Asmah tayi kusa dashi ta karbi kayan hannunsa ta Dora a center table tana tafe ne tana wani kadansa jiki ta sake juyowa ta wani kashe masa ido cikin matsiyaciyar kwarkwasarta ta qarasa gabansa ta shige jikinsa tayi dage ta sauke masa kiss a kuncinsa da yasashi rintse idonsa zuciyarsa na bugawa da qarfi.

 

Matsawa tayi ta fara bude ledojin kamar yasata yaja wata ajiyar zuciya ya zube a kujera wani tsalle ta saki ta fada jikinsa ta sake saukensa hot kiss a lips dinsa harda wani zura harshenta gabadaya yar banzar yarinyar ta kashe masa jiki ya kasa hassalawa kansa komai Mimee ta hadiya har wuya kadan take jira ta fashe ta tsinkayo muryar Asmah tana cewa “ni nasani mijina shine gwarzon mazan duniya bayamin alqawari ya saba inasonka har cikin ruhina…….”

 

_Wannan group shine group din zarrah pls idan kinsan kina daya daga cikin groups dina kada ki shiga ina post a kowanne group sannan idan kinsan bazaki comments ba kema karki shigo yawwa don Allah yasani ban buqatar yan labe da yan tanks_

 

 

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

 

_*Oum Hairan*_

_*Zarrah*_

 

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

 

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button