Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 31-32

Sponsored Links

BMGJY 31-32

_Haramun ne a juyamin wannan labarin ta kowacce siga ko a karantamin shi a YouTube channel_

_Don ci gaba da karanta wannan littafin ki biya ta 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank, ko hoton kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 idan a Niger kike zaki tura katin Airtel na 400CF ta wannan number +227 95 04 58 22 sai kiyi screenshot ki turomin nasaki a group._

★★★~~~★★★~~~★★★

Kallon kallo suka shiga yima juna kowa na jin tsoron sanar dashi asalin dalilin faduwar tata, tsawar daya daka musu ce tasa Khalisa saurin cewa “Bafa komai bane kawai kanta ne ke ciwo shine ta mike jiri y ɗebeta” ajiyar zuciya yayi ya miƙe da ita a jikinsa ya nufi ɗakinsu, ya ɓata lokaci wajen bata kulawa kafin daga bisani yaji taja ajiyar zuciya ya sauke numfashi tare da neman guri ya zauna yana me kallonta.
Ajiyar zuciya yaji tana saukewa yasa hannu ya ɗago fuskarta, hawaye yaga tana fitarwa yasa yatsansa yana share mata ya haɗa kalmominsa daƙyar yace “Meye kuma Wyf?” Bata ko kalleshi ba bare ta bashi amsa saima ƙoƙarin tashi da takeyi ya riƙota yace “Meye ne banason damuwa wlh Habeebah”
Hannunta tasa ta zame hannunsa tunaninsa ko bayi zata shiga maimakon haka sai yaga ta fice masa a ɗakin, nan ne zuciyarsa ta fara raya masa lallai da damuwa akwai abinda ya taɓa zuciyar Rayuwar tasa amma takaicin yanda ta watsar dashi yasashi kwanciya yasan dai itan bata da ɗabi’ar riƙe fushi.
A tunaninsa ya fita damuwa ya kamata daya rasa mafaka ya taho gareta ta danne ko mene yake damunta ta bashi lokaci da kulawar da zai samu nutsuwar da zata kwantar masa da hankali.

 

Da wannan tunanin yaji wayarsa tana ruri ya ɗagota ganin me kiran yasashi jan dogon tsaki a fili yace “Wannan halitta kwai mayya” a zahiri kuma ya kashe wayar saboda baisan wata kalma ɗaya da ta rage da Khausar zata sanar dashi da tayi saura a kwanciyar hankalinsa bayan tasa ƙafa tayi ƙoli da duk wani farin cikin da yake tanadawa rayuwarsa.
Kiran ɗaya kuma shigowa ne ya sashi gyara kwanciyarsa ya danna wayar ya ajiye ya sake jan bargo saboda sanyin zazzaɓin da damuwa ta saukar masa.
Cikin Murya me nuna alamun karaya da tsantsar damuwa Khausar tace “Prince Habeeb nasani a yanzu duk duniyar ka baka da wata matsala data wucce ni, nasani kanamin kallon wata halitta data addabi rayuwarka take neman zama katanga ga samuwar farin cikinka, A matsayina na damuwar da kakeji da kallon haɗa rayuwa da ita matsala ne a gareka ina mai baka hƙr bisa kasancewata a hakan, kayi sani bani na jarabci kaina da ƙaunarka ba kamar yanda Allah ya jarrabeka da son wani jinsi da kukasha bambam a addini da al’ada haka Nima ya jarabceni dakai, Habeeb nasan abubuwa da yawa da kake ɓoyewa a rayuwarka idan ka bani haɗin kai zanci gaba da rufa maka asiri harma na baka dama, barima kaji wani abu bayan aurenka da Habeebatullah da kayi ba tare da sanin kowa ba still a yanzu haka nasan tanada shigar cikinka na watannin da basu gaza biyu ba……”

 

Wata zabura yayi ya miƙe zaune yana shirin yin magana tace “Dakata Habeebullah banason kace komai kasan nasani cikin abinda na faɗa babu wanda nayi maka ƙarya saboda haka kabini a sannu kawai…..”
Kashe wayarta tayi ya ajiye tasa cike da kidima ya miƙe cikin tashin hankali ya fara haɗa kayansa tabbas alama ta nuna masa akwai abinda ke faruwa yau dole ko ta wacce hanya su isa Nigeria.
Wayarsa ya ɗauka ya kira layin Beebah kiran sa yakai biyar taƙi ɗagawa ya canza layi ya kira na Hudah ta ɗaga ya basu umarnin shirya kayansu cikin gaggawa babu wanda ya tambayeshi kasancewar sunsan sarai raine zai ɓaci haka suka shiga rarrashin Beebah da har zuwa yanzun take kukan tausayin kanta daƙyar suka samu ta shirya suka zauna zaman jiransa, ya ɓata lkc kafin ya dawo suka fito suka shiga Mota suka nufi airport duk yanda Habeebah taso raba mazauni dashi ƙin amincewa yayi hakanan ranta baiso sukayi tafiyar nan har kuwa suka isa 9ja bayan bacci daya ɗauke ta ta kwanta a jikinsa babu wata kalma data shiga tsakaninsu.

 

Motar Gidan sarautar ce tazo ta ɗebe su a Kano abinda ya sake dukan zuciyar Beebah harda Khausar a zuwa tarar tasu, da gaske ranta suya yakeyi zuciyatta tafasa takeyi na yadda taga Khausar na shigewa mijinta har tana wani kama hannunsa shi kuma sai zuƙewa yakeyi yana harararta yana bin Beebah data lafe a jikin Kilishi da kallo.
Ko wajen shiga motar maƙalewa Kilishi tayi wannan takaicin yasashi baisan sanda ya dannawa Khausar ashar ba saboda takurawarta garesa yasan duk tanayin hakan ne don ta kuntata zuciyarsa data Beebah kuma tayi nasara saboda kallon da Beebah take binsa dashi kaɗai ya ishe shi hisabi.
Aikam duk nacinta bai bari sun shiga Mota daya ba haka ta ta shiga tasu Khalisa gwiwa a sage Hudah nayi mata dariya can ƙasan maƙoshi kasancewarta dama abokiyar dabinta ce duk da ta girme mata itan sa’ar Khalisa ce.
Iya jarabar nacinsa na son yasan halin da Beebah ke ciki abin ya faskara da yake Sallah ce gidan sarautar a cike yake da baƙi yasa bai takura ba haka ya hƙr ya shige sashinsa yayi wanka yayi Sallah ya miƙe a gado yana saƙawa da warwarewa, baiji shigowar Najeeb ba sai ji yayi an zauna kusa dashi ya buɗe idanunsa suka zubawa juna idanu na tsayin lkc can Najeeb ya kawar da shirun da cewa “Meyesa Khalisa bata sona ne?”

 

Yunƙurawa yayi ya tashi zaune yace “Dalilin da nake ta tambayar kaina kenan Najeeb kowa ya kasa ganewa bazan iya koyawa kaina soyayyar Khausar ba zatafi rayuwar farin ciki idan ta auri wani ba ni ba amma taƙi fahimta kowama yaƙi fahimta Najeeb zanyi wani abu da zai tada hankalin kowa domin da wata damuwar gara wata…..”
“Zuciyarka tana faɗa maka ka saketa ne?” Da sauri ya ɗago yace “Ya akayi ka san abinda ke raina?” Fasali Najeeb yaja yace “nasanka tun bamusan kanmu ba nasan irin tunaninka a koda yaushe Prince kuskure ne babba zaka tafka da zai tone duk wani ɓoyayyen sirrinka, kayi saurin kawar da tunanin sakinta, tana sonka kai kuma kanason Habeebatullah zakayi amfani da soyayyar da take yi maka ka bawa Beebah guri a gidan da zaku rayu ka bata ƴancin mace itama, duk lkcn da tayi yunƙurin fitar da mgnr kai kuma kayi mata barazanar saki kuyita tafiya a haka har lkcn da gsky zatayi halinta don kasani na sani ramin ƙarya kurarre ne”

 

Sun jima suna tattaunawa kafin su miƙe su fice a gidan kai tsaye gidan Prince Habeeb suka nufa wato ya kashe dukiya bata wasa ba wajen tsara gidan cikin watanni bakwai akayishi aka gama rayuwa da buri komai don Habeebansa yayishi idan ya tuna wata akeso tazo ta rayu cikinsa ba Habeebah ba sai yaji ransa ya bakanta komai yana neman kwace masa amma da shawarar Najeeb yaji ya samu nutsuwa ya yarda da abinda ya faɗa masa a yau yakeson yayima Habeebansa albashir na samuwar ƴancinsu amma taƙi sauraronsa ya lura zasu rina da Habeebah domin dukkan alamu sun nuna irin matan nan ne masu masifar kishi bata ƙaunar taga an raɓeshi ko kaɗan to shima baso yake yaga wata mace ta raɓeshi ba itanba saidai yanzu da dole take neman kamasu.
Washegari tun safe yakeson ganinta taƙi ganuwa har ya gaji dayi mata aike da kiranta a waya, gashi Kilishi tanada baƙi a bangaren bakuma son yawan magana ya cika ba shine kawai ya hanashi zuwa ya nemota da kansa.
Har dare yana jiran tsammanin ganinta amma abu ya faskara dole ya hƙr ransa na suya haka aka kuma kwana aka yini tafi-tafi har kwana biyar ranar dai ya muttsike kunyarsa ya nufi sashin Kilishi yayi Sa’a kuwa duk sun tafi kallon hawan ƙarshe ya haura saman ya buɗe ɗakinta bai ganta ba ya janyo ya rufe ya buɗe ɗakin Kilishi ya ishe ta kwance a ƙasan carpet sai juyi takeyi riƙe da ciki Kilishi nayi mata sannu.
Tsayawa yayi ya zuba musu idanu ƙasa ƙasa, Kilishi ta ɗago ta kalleshi tace “Akai yarinyar nan asibiti Habeeb wannan fetus ɗin na wahalar da ita…..” Ƙasa yayi da kansa cike da kunya yace “Kilishi fushi takeyi dani fah ko wayata ta daina ɗagawa rabona da sanyata a ido tun a airport”

 

Murmushi Kilishi tayi tace “meye kuma na damuwa akan abinda kariga kasan zai faru Ni tayimin kyan kai ma daya kasance kaiɗin take fushi dakai bani ba Habeebah tanada kawaici kuma kishi halal ne dole tayishi”
“Amma Kilishi…..” “Amma me Habeeb ka ɗauko mota akaita asibiti nace ba dogon surutu ba” juyawa yayi ya fita bai jima ba ya dawo ya ɗauki Beebah da take cikin mawuyacin hali ya fice yasata a mota Kilishi ta fito ta shiga duk akan idon Hajiyan ƙofa tayi murmushi ta juya ciki su kuma suka fice daga gidan suka nufi Emirates Hospital ɗin aka bata gado suka fara bata kulawa.
Haka ta kwashe kwanaki biyu a asibitin anata shagalin ɗaurin auren ƴaƴan gdan sarautar itakam ta kanta kawai takeyi ranar da aka daura wannan aure Habeeb kamar mace haka ya rinƙa kukan baƙin ciki itako Khausar har kyautar mota tayi saboda farin ciki burinta ya cika ta samu muradin zuciyarta itakam Beebah baiwar Allah tanacan a kwance a gadon asibiti Kilishi da ƴaƴanta da uban gayyar na bata kulawa, ji yake kamar ya cire ciwon ya dawo dashi kansa duk ya susuce.
Duk da damuwar dake damun Najeeb ta watsin da Khalisa takeyi dashi amma yafi tausayin abokin nasa saboda yasan yafishi shiga jarabawar rayuwa wacce ya kwallawa rai gata a kwance cikin halin jinya ga kuma aure an ɗaura masa da halitta mafi bakin jini a duniyarsa.

_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/10, 8:33 PM] AM OUM HAIRAN:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button