Bamagujiya 45-46
Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_
Tunda Kilishi ta fara mgnr jikin Habeeb ya ɗauki wata rawa ya miƙe tsaye da nufin ya fice jiri ya fara ɗaukarsa dole ya koma ya zauna yana tare da dafe kansa dake sara masa da ƙarfi jikinsa na ƙara ɗaukar tsuma ya furta “Innanillahi wa inna ilaihirraji’un Allahumma ajirni fih musibati wa’akalifni khairin minha” yayi wannan furuci yafi sau ashirin kafin ya aro juriya ya dago idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya zubasu akan Kilishi yace “Yanzu ina ta tafi?” Cikin sarewar murya Kilishi tace “Inda nasan inda ta tafi da bazakaji meye ma ya faru ba Habeeb”
Sake dafe kansa yayi yana ayyana abubuwa da yawa tabbas ya tabbata wannan tsabar sharrine da makirci aka ƙullawa Habeebah ko kaɗan baiga laifinta ba domin Hausawa sunce in wani yaƙika da yini wani da shekara yake neman ka kuma ƙasar Allah me yalwa ce in aka ƙyamace ka anan idan kayi gaba murna za’ayi dakai, Amma shima Yakamata kafin ta tafi ta dubashi meye ma yasa bata kirashi ba ya nema masu mafita domin ya haƙiƙance ko Shari’a bata isa rabashi da matarsa ba matuƙar yana numfashi a doran duniya bare kuma ma akan karya da son zuciya.
Miƙewa yayi ya nufi ƙofar fita yana haɗa hanya kamar ɗan ƙwaya sukaci karo da Mai Martaba a hanya ko kallonsa baiyi ba yayi gaba abinsa Najeeb yace “Habeeb Mai Martaba na magana” batare daya juyo ba yace “Me zanyi masa to son rayuwata yakeyi da zaimin magana ya barni na mutu ma mana tunda burinsa kenan.
Yana faɗin haka yana shiga Mota dake Najeeb bai cire key ɗin ba ya kunna ta da mugun gudu ya fice daga gidan sarautar yanda yake tuƙin ya tsorata kowa don tabbas ba cikin hayyaci yake ba.
Shikuwa kamar yanda zuciyarsa ke gudu wajen ganin ya isa inda zaiga Beebah haka yake keta mugun gudu a hanyar ya nufi ƙauyen su Beebah karo na biyu tun bayan aurensu da yazo ƙauyen ya tsaya yana ƙare wa gdansu Beebah kallo yasha gyara kamar baa ƙauye ba yananan tsaye Baba Jimo ya fito ya tsaya turus ganin Habeeb ɗin a tsaye jikin mota.
Cikin hassalar bala’i ya nufoshi yana nunashi da yatsa yace “Wato kai kunnen ƙashi ne dakai ko nace karka ƙara takowa gareni shine ka sake dawowa halan ajali ne ke ɗawainiya dakai…..”
Cikin karayar zuciya Habeeb yayi ƙasa hawaye ya zubo masa yace “Wlh Baba ba laifina bane ko a mafarki bantaɓa jin a raina akwai ranar da zan iya rabuwa da Beebah ba Bana Beebah rayuwata ce ka taimakeni ka bani matata……
Kallon bakada hankali ya rinƙa bin Habeeb dashi can yace “Kai yaro fice cikin ƙwayar idanuna kaga nayi kala da wasanka? Zakazo kana cewa na baka matarka wacce matar ke gareka a gurina?” Miƙewa Habeeb yayi cikin nunkuwar tashin hankali yace “Wai Beebah banan tazo ba Baba?” Duk da Baba Jimo yana cikin halin tsananin fushi Saida gabansa ya faɗi yace “batazo ba ina tayi cemaka tayi zatazo nan?”
Hannu Habeeb ya zuba a kansa yace “Na shiga uku Ni Habibu Habeebah ina kike…..”
Cakumarsa Baba Jimo yayi yace “Na rantse da abar dogarona kamar yanda ka ɓatar min da Bibo kaima labarinka saiya shafe saina ɓatar dakai….” Shi baima damu da riƙon da yayi masa ba hawaye kawai yake shara yana cewa “Mai Martaba ka cuceni ka wargatsamin gda ka tafi da farin cikina, yanzu ina Beebah tashiga ita ba cikakkiyar lafiya ba?”
Fir Baba Jimo yaƙi sakin Habeeb kawai sai huci yakeyi yau ga ranar yayansa Uda gashi mutuwa tayi gaggawa, daƙyar mutane suka raba hannun Baba Jimo da kwalar rigar Habeeb rigima ta sarƙe shi Habeeb na roƙonsa ya bashi matarsa idan yasan tazo shi kuma yana rantsuwar saiya fito masa da yarsa rigima har gidan Dagaci koda Dagaci yaji abinda ke faruwa a bakin Habeeb hankalinsa yayi mugun tashi shima tabbas abin akwai tashin hankali gashi babbar damuwar baasan inda za’a nemi Beebah ba.
Duk yanda Dagaci yaso Baba Jimo yabar Habeeb ya tafi yaji da damuwarsa hanawa yayi Saida Dagacin yasa aka kira irin bokayensu na tsubbu suka tabbatarwa da Jimo Habeebah tananan cikin aminci kuma zata dawo saidai basusan inda take ba, to sannan ne fah hankalinsa ya kwanta yabar Habeeb ya tafi amma da sharaɗin duk inda Habeebah take ya nemo masa ita tunda ubansa bayason zamansa da ita to ta gama aurensa har abada.
Shidai bai bawa mgnrsu muhimmanci ba burinsa kawai sanin inda Beebah take, hakanan ya ɗauki hanyar Dutse ikon Allah ne kawai ya kaisa gida kai tsaye ɓangaren Khausar ya shiga ya tarar da ita taci wanka sai faman taunar cingam takeyi kamar karuwa.
Babu furuci ba komai ya ajiye mata takarda a cinyarta ya fice daga ɗakin da sauri ya nufi ɗakin Beebah ya faɗa gadonta yaja rigarta ya rungume a ƙirjinsa numfashinsa na ɗaukewa yana janyoshi da ƙyar yanda zuciyarsa ke masa zafi a yanzu
Haka baya buƙatar kowa a tare dashi ji yake yi ma kamar ya tashi yabar garin, zuciyace ta bashi shawarar dole ma ya bar garin da daren ya tattare komansa washegari daga masallaci ya ɗauki mota sai Abuja Saida ya shiga cikin garin Abuja ya kira babban amininsa da sukayi karatu dashi a Oxford cikin murna engineer Wali yazo ya taroshi daga yanayi ya fahimci Habeeb na cikin damuwa haka dai suka ƙarasa gdansa zama Habeeb yayi ya dafe kansa da yakeyi masa wani mugun ciwo, dafashi Wali yayi yace “Nayi mamakin ziyararka ta bazata haka duk da dai yanayinka ya nunamin baka cikin nutsuwa shin ko zan iya sanin meye ke faruwa?”
Iska ya furzar ya miƙe ya nufi wani ɗaki ya buɗe ya shiga bathroom ya watsa ruwa yana fitowa ya kwanta zazzaɓi na sauko masa me zafi.
Shigowar Wali ce ta sashi sake jan bargo Wali ya janye yace “wai meye yake faruwa ne Habeeb ina matanka ko wani abu ya faru ne?”
Numfashi ya sauke me huci yace “Ka kiramin likita” baiyi masa jayayya ba ya dauki wayarsa ya latsa wayar cousins dinsa Dr Al’Amin yayi masa bayani yace masa ok yanzun yanakan wata petiant ne amma yana gamawa zaizo. Haka sukayi sallama ya aje wayar sukaci gaba da zaman kurame Wali ya gaji yace “Don Allah ka faɗamin meke faruwa ina Hudais da mamansa?” Zubawa Wali ido yayi can yace “Bansan inda Habeebah take ba tafiyar da nace maka nayi zuwa Lagos wasu abubuwa suka faru har yasanya Mai Martaba yanke hukuncin sakarmin mata da bakinsa bada nawa ba kuma ya ƙwace mata ɗanta ɗaya data ɗauki so ƙauna da burin duniya ta ɗora masa ɗan da takejin zata iya rabuwa da komai dominsa Zubair Habeebah na sona amma na tabbatar da a yanda take da haƙuri da kawaici kuma a lkc guda idan hƙrnta ya kare take da kafiya Wallahi ba zata nemeni ba koda kuwa sona zai zama silar yankewar numfashinta, meye yasa Mai Martaba zai rabani da zuciyata Zubairu Habeebah rayuwata ce inajin yanda zuciyata take zafi da zugin ciwo tsaf zata iya daina aiki indai babu Wyf a kusa dani Wanne taimako zaka bani ta dawo gareni Zubair don Allah Please help me…..”
[5/20, 9:07 PM] AM OUM HAIRAN: _*