Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 56

Sponsored Links

56

Cikin satin kafin tafiyarsu umara wani irin sabo da shaquwa mai qarfi ya shiga tsakaninsu,qaunar khalipha babu inda bata jinta cikin jiki da jininta,bata taba sanin tayi nisa a qaunarshi ba sai yanzu,haka ta nashi fannin ya gama sallamawa gaba daya,hakanan ya gama tafiya,dukkan wasu hakaye na aysha wadanda baisan dasu ba a yanzu ya karancesu,komai nata yayi masa,komai nata yadda yakeso ne,irin matar da yake mafarki da fata gami da burin aure a yanzu ya samu,wani lokaci yakanji kanshi kamar bashi ba,ayshan ta sauya dukkan wanin tunani nasa,burinta ya zama nashi nashi ya zama nata,qiris yake jira su zama abu guda,sai yanzu yake jinsa cikin wata sabuwar duniya,jinsa yake kamar an sauyashi,kamar ba shine khalipha ba na ainihi,ta wanke masa duk wani burbushin bacin rai da yayi saura a rayuwarshi,shi yasa yake da fata da kuma burin ya zama silar wankewar duk wata damuwa tata da tayi saura a zuciyarta.

Ana ya gobe zasu tafi da daddare ya sanyata ta shirya don ya kaita suyi sallama da daddy,tsaf ta shirya tayi adonta kamar yadda ta saba ya kuma zame mata jiki dai dai misali mai sanyi ba hayaniya,shi kansa khaliphan yayi kyau cikin shaddar daya buga,ya kawo hularshi gaban goshi shigar cikakken bakano abun sai wanda ya gani ??.

Tare suka jero shida ita,duk wanda ya gansu a lokacin saiya juya ya sake dubansu,cikakkun masoyan da sukayi nutso duniyar soyayya suka dandana zaqinta,masoyan da tun a siffa da kama suka dace da juna zuwa ga halaye,bude mishi motar akayi saiya matsa mata ita ta shiga,shi kuma ya bude da kanshi sannan suka rufe suka tada motocin suka fice.

Itace a gaba kai tsaye zuwa sashen daddyn,saboda tun a harabar gidan mai gadin ya shaida mata mummyn na can sashen,dawowa tayi ta shaidawa khalipha saiya gyada kai
“Ki fara shiga ki sanar mishi shigowata ko?,kaman hakan yafi tsari”
“To” ta amsa mishi tana juyawa saiya bita da kallo
“Uwaishahh…” Ya kirata,ta waiwayo tana murmushi can qasan ranta,don idan da sabo ta saba,don khalipha saiya kirata sau nawa kafin taje waje musamman idan tayi kwalliya,kawai sai yace tafiyarta yakeson kalla,ko kuma kai kawonta yakeson gani,hakan kawai ya isheshi abun farinciki,saitinshi ta ranqwafo,saiya miqa hannunashi saitin bakinta
“Ciromin sweet dita,yanzu yaci ace kinsha rabi aiko?” Murmushi ta saki,cikin motarshi ta dauka,suna nan sunfi talatin,amma kawai bazai sha ba sai wadda tasha ta rage
“Kayi haquri ka barmin wannan ka dauki wata mana ya khalipha”ta fada tana langabe kai
“aifa bazaiyiwu ba,amma.idan kina so zan.barmikin,saidai da sharadi” sai yayi qasa da muryarshi yadda ita dashi ne kawai zasuji abinda yace mata,kunya ta tilastata rufe fuskarta da hannayenta tana son tashi a wajen amma ya danne mayafinta
“If kin yarda nima nafison hakan,saboda wannan bakin yafi sweet din dadi nesa ba kusa ba” da sauri ta ciro alewar daga bakinta tana miqa mishi,saiya turbune fuska kadan yana kallonta bayan ya narke kamar qaramin yaro
“Rowa ko?,tona fasa shan sweet dinma”
“Am sorry ba haka bane,yi haquri ka amsa kasha” hannu ya sanya ya karba alewar ya saka a bakinsa,sai ya lumshe ido yana cewa
“Nifa ban taba sanin haka alewar nan keda dadi ba saida kema kika soma sha,duk sanda ta taba miyan bakinki kamar yana qara mata dadi ne” dariya ta saki sosai tana ficewa a wajen,indai khalipha ne yanzu zai shagaltar da ita,tana murmushi gami da miqa godiyarta ga sarki Allah daya mata baiwa da miji irin khalipha har ta isa sashen daddy.

Asma’u dake tsaye can gefen wasu shukoki tana ganin abinda ke faruwa ta saki ajiyar zuciya,wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar tunkarar khaliphan,komai nashi yayi mata,dukkan wani abu da take bida ta ganshi tattare da shi,matuqar zai amince mata kashe aurenta ba wani abu bane mai wahala a wajenta,bare a yanzu da take jin auren tamkar ana dorata saman qaya ne,ko qawaye yanzu ta yanke alaqa da kowa,don kada ma wani ya rabeta ya fahimci halin da take ciki,kayan da daddy ya mata order tuni sun taru sunci uwar kayan da kudin ita da qawaye tun suna wancan gidan nasu,bata iya adani ba,bata iya tattali ba,batasan ta juya biyar ta koma goma ba,ta riga ta saba tun agida saidai ta bid’a a bata,takowa ta dinga yi har zuwa inda khalipha ke zaune cikin motar tayi knocking,ya tsammaci aysha ce saiya sauke gilashin yana murmushi,idanu biyu sukayi da asma’u,take yayi gaggawar gimtse fuskarshi yana dubanta
“Ranka ya dade yau kaine a gidan namu da kanka?”
“Eh…yaron oga ne da ‘yar aikin gidan sukazo gaida mai gidan” saita danyi dum saboda tasan magana dai yake gaya mata,cikin barikanci tace
“Banda dai tuna baya,abinda ya wuce ya riga daya wuce,na baka haquri amma na fuskanci har yau baka haqura ba” tsaki yaja yana shirin daga gilasanshi saboda sauraton tama sam baida amfani saita dafe cikin karyewar zuciya
“Don Allah khalipha kayi haquri,ka taimaka ka karbeni kamar yadda ka amshi aysha,ba sonta kake ba tun asali nice wadda kakeso,qaddara ita takawo faruwar komai,kai kadai kai zaka cikamin burina”
“Burinki na kudi ko?,baki da matsala waisaita kudi ne?,a duniya babu wani abu mai daraja bayan kudi?,inasom in miki gargadi na qarshe kar bakinki ya sake kuskuren cewa bana son aysha na aureta,har abada aysha itace zabina,tun kafin nasanta nake qaunarta,tin kafin nasan zatazo cikin qaddarata nakesonta,kin fahimta?”
“Kamar yaya?” Ta yiwa kanta tambayar,saidai bai tsaya bata amsa ba yadaga gilasanshi yana jan tsaki ranshi yana baci,wato a rayuwa ma ka aikatawa mutum ba dai dai ba kazo daga bisani kana jin kunyarshi ka rahama ne?,wannan kenan na nuna zuciyarka akwai ragowar danshi,idanunka basu qarasa qeqashewa ba.

Kallo daya tayi masa tasan yauma baida lpy,hankalinta ya tashi sosai,tunda yayi wancan rashin lafiyar kullum saita kirashi amma ko sau daya bai taba nuna mata yana kwance ba,amma saboda qarfin hali irin na daddy nuna mata yake ba komai,ta sanar mishi tarr da khalipha suke,yace
“maza shigo dashi mana indo,yaron kirki dan albarka”.

Tana juyawa daga wajen motar sukaci karo da aysha,kallon data jefa mata shi ya sanya jikin ayshan ya bata akwai wata a qasa,me take jikin motar khalipha?,tasan halin asma’u sarai shekarun da suka diba gida daya ba wasa bane,saita gifta ayshan ba tare data ce mata komai ba,itama ganin haka yasa ta kama kanta tunda tasan ba wani abu data yi mata.

Tare suka jero har cikin parlour din,a sannan mummy na zaune tana hada magunganan daddy daya gama sha,idanunta kan khalipha sanda yake gaisheta,banbanci muraran ta ganshi,qyashi ya cika ranta,saita kasa zama tabar musu falon ta koma sashenta,wanda hakan ya basu damar hira sosai duka su ukun harda khalipha,irin hirar da zata ce ma bata tabayinta da daddy ba,har tayi mamakin dadewarsu sanda suka tashi zasu tafi suna mishi sallama kan gobe zasu wuce umara,dai dai sanda asma’u ta shigo falon,sai ta samu waje ta zauna tana jinsu,cikin farinciki daddy yayiwa ayshan murna,saboda yasa yunqurin kaita sai mummy ta sako wasu qorafe qorafe da zai sanya a dage zuwan da ita koda daddyn bai shiryawa hakan ba
“Uhmmm,ba sabanba,su umara manya,kai bawa da baka taba zuwa ba daka shiga uku” asma’u ta fada qasa qasa yadda ayshan zata jiyota,murmushi tayi sannan itama ta mayar matan ta yadda zata jita da kyau
“Mun godewa Allah da bai banbanta saudiyyan masu kudi da talakawa ba,duka dai gurin daya ne inda kaje nima can zani,Allah ya kirani babu damar dakatarwa” saita miqe ta isa gaban daddy tana masa sallama bayan fitar khalipha wanda yadan basu waje ne suyi sallama
“Allah ya qara maka lafiya daddy,bansan wanne irin abu zan saka maka dashi ba a rayuwarta,don Allah daddy ka tambayi koda abu daya ne a wajena wanda kake buqata daga gareni” murmushi ya saki
“Aysha indo har kullum kedin ta dabance,haka Allah yake tsarinsa cikin halittunsa saiya fifita wani kan wani,dukkan abinda nayi miki nayi miki ne Saboda Allah,na miki saboda a lokacin kina cancanci kuma kina da buqatar ayi mikin,abu guda daya da zan nema a gareki shine,ko bayan raina karki manta dani kici gaba da yimin addu’a”zuciyarta ce taji ta karye da kalamanshi,wani rauni ya kamata,take hawaye ya balle mata,asma’u dake zaune gefe ta tabe baki
“Kalen dangin masifa,kamar ta fimu sonshi,sai kace ita ya haifa bamu ba” ta fada a zuciyarta
“Indai xan manta dakai daddy to lallai zan manta da kaina,baka cikin jerin mutanen da zan iya mancewa dasu har numfashina yabar gangar jikina,ubangiji yayi maka jagora a dukka lamuranka duniya da lahira”
“Amin ya Allah ayshatu,idan na taba yi miki wani abu naba daidai ba tsahon zamanki a gidan nan ina neman afuwarki” kuka ta saki sosai harda sheshsheqa
“Daddy niya cancanci na nema afuwarka da zanyi tafiya,ba zaka taba laifi ba awajena daddy koda naman jikina kake yanka kullum”
“Daina kuka ayshatu,ubangiji yayi miki albarka duniya da lahira,idan kinje kimin dawafi na musamman kiyimin addu’a sosai”
“Zan maka addu’a daddy in sha Allahu fiye da yadda zan yiwa kaina”da haka sukayi sallama,haka kawai taji zuciyarta ta karye qwarai,hakanan taji kamar karta tafi,kukan da take yaqi tsayawa har a cikin mota,tun khalipa na daurewa har ya gaza
“uwaishah,ki taimakeni kiyi shuru,har cikin qirjina nakejin ciwon kukan da kikeyi” bata son bata masa rai ko qanqani,hakan ya sanya dole tayi shuru gami da yin luf a qirjinsa,kusan ranar wuni tayi a sanyaye,tunanin daddy fal zuciyarta.

????????????????

Washegarin ranar jirginsu ya daga sai saudiyya,a garin makka suma soma sauka,suna sauka a masaukinsu dukkansu sukayi wanka suka dauki harama,saboda tsabar murna da zumudi ma ta rigashi kammalawa,ji take kaman tayi tsuntsuwa ta ganta bakin ka’aba,tana da abubuwa da yawa da zata roqa,tana da mutanen da takeso ta yiwa addu’a sosai,idanunta a kanshi sanda ya kammala daura hiraminshi,idanu suka hada sai suka sakarwa juna murmushi a kusan tare,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi.

Sati guda sukayi a garin makka,iya ibada kam sunyita saidai fatansu Allah ya amsa,bata taba sanin khaliphan ta fannin ibada jarumi bane sai a wannan karon,duk nacinta da son ibada sai taga ashe ya kere mata,sau tari idan ta gaji tayi kaman zata huta sai taga shi a sannan ya saka qaimi,sai ya sake zaburar da ita,tabbas ta yarda ta kuma amince cewa kowacce mace halayenta idan zama yayi zama na kamanceceniya dana mijinta,kota debi wasu dabi’u nashi koshi ya debi nata,idan akayi katari na gari ne sai nagartarta ta ninku,idan kuma akasin haka ne walau ya rinjayeta ta ko ta koyi kaso mafi yawa daga cikin halayensa,shi yasa akeson ko aboki zakayi ka aboci na qwarai,don annabi ya kwantata aboki na qwarai da misalin mai saida turare ne ko.baka siya ba idan ka zauna dashi dole wataran zai san maka,kaima zakayi qamshi,hakanan nara gurbin aboki tamkar abota da maqeri ne,kana zaune feshin wutar zai dinga sauka atufafinka yana bata maka sutura,hakan shike nuna auren miji na gari shine babbar sa’a hakanan abu mafi muhimmanci da gata da mace zata yiwa kanta da zuriyar da zata samu a nan gaba.

Randa suka cika sati guda a garin makka suka wuce madina don suyi ziyara,musamman ya samu motar da zata zagaya dasu duk wani wajen da tarihi yazo dashi a addinin musulunci,farincikin data dinga ji ya zarce wanda taji a garin makka,jinta take fes,zuciyarta qal,kamar babu wani abu daya taba samunta a rayuwa na bacin rai,kullum tana maqale da masallacin ma’aiki tana yiwa kanta khalipha daddy da anni addu’a,dama duk wanda ya ratsa rayuwarta,idan na neman shiriya ne ta nema masa,idan na fatan alkhairi ne tayi masa.

Randa suka cika kwanaki hudu a garin madinan,da wata safiya sun fito zuwa masallaci ita da khalipha,irin wannan yanayin yana mata dadi qwarai,takan jita wata ta daban ta musamman,zuciyarta da ruhinta kan cika da farinciki,tabbas garin madina dabanne,hatta da yanayinsa ma daban yake,tayo bangaren mata shi yayi bangaren maza taji sabuwar wayarta daya siya mata tana ruri,tana dubawa taga sunanshi ne,cikin mamaki ta kara a kunnenta
“Ta wacce qofa zaki shiga?” Ya tambayeta,gaya mishi tayi sai yace ta sauya ta shiga ta daya qofar,bata kawo komai ranta ba ta amsa mishi ta kashe wayar sannan taci gaba da takawa donta wuce zuwa cikin masallacin.

A hankali take takawa cikin zuciyarta tana ta istigfari kamar yadda ta saba tunda suka zo,bata minti daya cikakke bakinta babu ambaton Allah,tana son ta ribaci lokacinta da dimbin falalar da garin yake dashi,dukkan aikin da kayi cikin garin walau na alkhairi kona sharri kana da ninkin lada ko zunubi.

Kamar a mafarki kamar wasa sukayi kacibus da umminta tana shirin fita daga masallacin itama,kallon kallo suka fara yuwa junansu tamkar wasu baqin juna,dukkan wani tashin hankali da fargaba da aysha takeji a sanda suka hadu a yanzu fes take jinta,zuciyarta a taaye take kyam,idanunta cikin na umminta
“Assalamu alaikum”aysha ta furtawa ummin tana dubanta
“wa’alaikumussalam”ta amsa mata itama tana dubanta,idan batayi kuskure ba qwalla take gani cikin idanuwan ummin fal,saitadan gotata kamar zata shige,da sauri aysha ta riqe tsintsiyar hannunta,tsahon minti daya suna a haka kowa ya kasa motsawa,sai ta jiyo sheshsheqar kukan ummin nata,abinda yayi masifar tayar mata da hankali,da hanzari ta sakar mata hannu tasha gabanta,batayi auneba taji ummin ta rungumeta tsam tana sakin kuka sosai
“bazan iya ba,bazan iya ci gana ba”
“Kiyi shuru ummi don Allah” saiga ayshan dake bata bakin tayi shuru itama ta saki kukan,duk yadda taso daurewa ta kasa,kuka suke sosai,ganin masu wucewa zuwa cikin masallacin na kallonsu ya sanya ayshan janye ummi gefe.

“Naja’atu” dukkaninsu suka waiwaya jin an ambaci sunan ummin,wani mutumine wanda aqalla zaikai shekara hamsin da biyar,gefanshi kuma khalipha ne tsaye suna dubansu,kuka ummin ta sake saki tana kauda kanta daga garesu baki daya,takawa mutumin yayi har zuwa inda take tsaye ya riqe hannayenta
“Idan kowa bai isa alfarnar garin nan,da wanda kabarinsa ke cikin wannan waje mai albarka sun isa su sanya ki amshi diyarki”
“Abban basma…..bana so….” Sai maganar tata ta harqe
“Bana son maganar da suka fada ta tabbata akan aisha,banason ta silata wani abu ya sameta” ta fada tana sake barkewa da kuka
“Dukkaninmu ba zamu fahimci abinda kike magana akai ba idan ba bayani kika yi mana ba”
“Ammm….abba,me zai hana mu samu wani waje su zauna a can” cewar khalipha,kai abban ya gyada masa sannan ya riqe hannun ummi naja’atu dake ta kuka.

Shuru kowannensu yayi kafin abba ya daga kai ya dubi aysha
“Khalipha ya cancanci zama yaji kowanne irin abu da naja’atu xata fada,fita kice ya shigo” a sanyaye aysha ta miqe don zuwa kiranshi,saidai duka hankalinta nakan ummin,gani take kaman kafin taje ta dawo xata rasa ummin,kamar kafin taje ta dawo ummin xata sauya ra’ayi,zata fasa fada mata komai,zata fasa karbarta,itama ummin nata idanun nakan ayshan,ita kadai tasan me take hadiyewa a haka harta dawo tare da khalipha,kujerar dake daura da aysha abba ya nuna masa yace ya zauna,da fari baiso zaman ba,saboda yana ganinnkamar wani sirri ne da bai shafi yaji ba,amma abba yace ko daya,miji shine babban sirri na farko wajen matarsa,haka ya zauna kanshi da idanuwanshi a qasa yana harhada cukurkudaddiyar rayuwarsu shida ayshan waje daya
“A ranar dana bar gidan baffale a daren ba’a kwana ba akace ana sallama da baffana,yana fita baifi minti biyar ba muka jiyo hayaniya cikin zauren gidanmu,sai gashi ya dawo yace na fito ana son magana dani,ban musa ba na miqe na fito,saidai wadanda na gani a wajen inda ya gaya min su sukazo tabbas bazan fito ba,gefe daya na samu na tsaya ina dubansu,dukkan yayye da qannem baffale ne mazan sai inna yelwa
“halaa ma dai bakasan abinda ya faru ba?”cewar saya daga cikin yayyen baffale yana gayawa baffana,kai ya jinjina yace kai nake sauraro
” to mudai muna da tantamar indo diyar baffale ce gaba dayanmu,tunda cikinta bai tashi bullowa ba sai da yabar garin nan gaba daya”nan fa ran baffanmu ya baci sosai,duk haqurinshi kuwa,saidai ya hadiye yana dubansu kawai
“Me kukeson ku gayamin,nafi ku sanin wace naja”
“Ai ka tsaya malam duka na wannan ba,abu daya shine zai tabbatar mana da aisha jinin baffale ce kuma jininku” shuru kowa yayi nida baffa gaba daya muna sauraronsu,inna yelwa ce ciki izgili nuna isa da taqama tace
“Daga nan har shekaru goma dai dai da rana daya idan naja ta koda kalli indo kota sake ta nemeta toba jininmu bace,ba baffale ne mahaifinta ba,matuqar jininmu ce to babu ita babu ita,ba ruwanta da ita jininta zasu kula da ita…” Ban tsaya na qarasa saurarenta ba kawai na juya cikin gida na barsu nan da baffa na,maganar ta inna yelwa ta yimin ciwo qwarai,sharrin zina ba abinda ya kaishi muni,na shiga bacin rai sosai a sannan,na sake tsanar inna yelwa da ahalin gidanta gaba daya.

Ana tsaka da wannan saiga inna sailuba,qawar inna yelwa ce sosai,saidai ikon Allah Allah ya hada jinina da ita tana qaunata qwarai,batasan aurena ya mutu ba saboda ba’a garin take auren ba,saidaga bisani tazo ta biyo ta yimin jaje tare da nuna rashin jin dadinta akan aninda inna yelwa tayi,ranar sai gata hankalinta a tashe,ban taba ganinta cikin tashin hankali ba irin ranar,ita take gayan maganar data sake sakawa na janye jikina da.aysha,na nuna mata qyama,na farko ta gayamin inna yelwa ashe ta rabani da baffale tasa aka sanya qiyayyar juna atsakaninmu,har ya mutu yana ambatona yana neman gafarata,sannan yanzu kuma sunyi wani shiri saboda basa son hada jini dani,duk ranar dana yiwa aysha wani kallo na tausayi ko jin qai a ranar ba zata sake kwana a duniya ba,saboda suna da yaqinin babu uwar da zata daurewar azabar da suka shirya suna gana mata iri iri,banso na rasa aisha diyar dana fara samu a duniya,tilas na koyawa kaina kyararta da tsangwarta,duk da a sannan na shaidawa baffa na kafin rasuwarshi yayi addu’a sosai da rubutu,idan baki manta ba mero na baki wani rubutu kisha waina tsari,shike aikawa meron ya bata yace ta baki,koya manta wani lokaci da kaina nake dauka na aika a zuwan baffa ne ya bayar,duk halin da kike ciki aysha ina sane labari yana zuwarmin,na hana ‘yan uwana su daukoki kosu karboki ne gudun kada wannan abun da suja qulla har a lokacin yana nan ya zama silar barinki duniya,silar barina qauyenmu bazan iya zama ina nuna miki qiyayya sauran jama’a na nuna miki ba,sai naga gwara nayi aure a nesa,gwara nayi nesa dake,wataqila idan bakya ganina zaki haqura dani,wataqila abinda kike ji cikin zuciyarki zai ragu,kullum ta Allah sai nayi kuka akanki aysha,sai nayi kuka saboda tausayinki,kullum addu’a nake Allah yasanya duk randa zamu hadu wannan mugun abun ya warware,haduwarmu a nan zuciyata ta bani yaqinin duk wani mugun abu bai isa yayi tasiri a waje mai tsarki irin wanna ba,ki yafemin aysha….dukkan abinda ya faru ya farune bawai don ina sane ba ko inajin dadin faruwar hakan…..”sai kuka ya qwace mata(a nan ina nemawa wadda ke cikin halin tsana da kyarar mahaifiyarta kamar aysha addu’a,ku sanyata a addu’a Allah yaye mata ya karkato mata da hankalin mahaifiyarta).

Rungumeta aysha tayi itama ummin ta rungumeta tsam suna kuka,sai khalipha ya kasa dauka ya miqe a hankali ya fice daga wajen,ganin haka ya sanya abba miqewa shima ya basu waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button