Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 44

Sponsored Links

Likitan ne ya dubi Daddy sukayi larabcinsu ya miqawa Hameed hanu sukayi musabiha suka juya suka fita Daddy ya dubesu yace “zuwa sati idan ka qara warwarewa saimu tafi gda ko babana?” Lumshe idonsa yayi ya bude Daddy yayi murmushi yace “gadai Umaimah tazo ta kawo maka Shurafah nima hankalina ya kwanta yanzu zamu iya tafiya”

 

Daddy ne ya taimaka masa ya miqe kasancewar komai a asibitin ake masa babu abinda suka dauka sai kayansa yana rungume da Shurafah Daddy yana riqe dashi haka suka fita motar asibitin ta daukesu zuwa masaukinsu dakin da Daddy ya kamawa Umaimah nan yakaiwa Hameed kayansa ya juya ya fita ya barsu su biyu zama yayi a gefen gadon yana binta da shu’umin kallonsa me kashe mata jiki bata iya ce masa komai ba sai neman guri da tayi ta zauna a saman resting chair din dake gefen gadon ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kansa daga kanta yace.

Related Articles

 

“Ina buqatar zan kwanta na huta” da sauri ta dubeshi ya sake kawar dakai yace “ina nufin Ina buqatar privacy zaki iya fita kice da Daddy ya kama maki wani dakin” dagowa tayi zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace “banason surutu kuma banason takura kitashi kije ki kwanta dare yayi”

 

Jikinta a mugun sanyaye ta miqe ta nufi gadon idanunta ya ciko da hawaye ta sunkuya zata dauki Shurafah ya daka mata wata tsawa data sata saurin yin baya yace “get out for my room” da sauri ta juya ta nufi qofar dakin ta bude a tsorace ta fice daga dakin.

 

Miqewa yayi ya kwantar da Shurafah dake bacci yasha magungunansa ya kwanta tare da janyo yartasa a jikinsa da haka bacci ya daukesa.
Umaimah kam a tsayawa tayi jikin qofar dakin zuciyarta nayi mata wani zafi da ciwon irin korar da yayi mata takeji wai ta fice masa daga dakin wasu hawaye ne masu zafi suka ziraro mata ta zauna a parlourn saman carpet zuciyarta nayi mata suya wannan ko wanne sabon wulaqancin rashin lfyr tasa tazo masa da ita oho.

 

Da wannan tunanin ta kwanta saman carpet din bacci ya dauketa da asuba ya farka yayi alwala yayi sallah yana zaune saman sallaya ta bude qofar ta shigo ta saida gabanta ya fadi data ganshi zaune yana lazumi kamar wacce qwai ya fashewa a ciki ta nufi bathroom din ta dauro alwala ta juya ta fita zuwa parlourn ta tayar da sallah tana idarwa yana fitowa yana cilla Shurafah sama yana cafewa ya zauna saman kujerar yana yima yarinyar wasa cikin faduwar gaba tace masa.

 

“Ina kwana” kallonta yayi kallo irin na rainin wayo yaci gaba da yima yarsa wasa shiru tayi masa taci gaba da azkar dinta kamar daga sama taji muryarsa yana cewa “wato da nace kije ki fadawa Daddy bana buqatarki a kusa dani ya nema miki dakin da zaki zauna kafin mu koma gda shine saboda ban isa ba kika kwana anan ko? To bazan hanaki kwana anan ba tunda haka kika zaba amma kisani kada ki kuskura ki shigomin daki da dare ranki baci zaiyi”

 

Harya gama mgnr batace masa qala ba sai hawayen da take zubarwa a rayuwarta babu abinda yake mata ciwo irin jizgi da wulaqanci bata jurewa hakan ko kadan.
Bai sake bi ta kanta ba ya tashi ya miqa mata Shurafah yace “yarinyata me hqr ya kamata a bata abincinta taci” yana fadin haka yasa hanunsa ya zare hijjab din jikinta ya zuge zif din ya sanya hanunsa ya dago qosasshen breast din nata yayi ajiyar zuciya tare da hadiye wani yawu ya saita bakin Shurafah yasa mata ta kuwa kama da sauri harda sanya hanunta ta dafe.

 

Miqewa yayi ya shige dakin saboda wani yar da yakeji a jikinsa ya fada bathroom da sauri ya sakarwa kansa ruwa ya fito ya dauki wani magani da Dr Maheelr ya bashi wanda yake taimaka masa wajan control din feelings dinsa sosai yasha ya koma ya kwanta tare da jan blanket sanyi Umaimah takeji sosai saboda weather din sanyin Saudi akwai shiga jiki amma tsoron ta tashi ta shiga dakin take ta dauko rigar sanyinta saboda ta lura ya qaro rashin mutunci sosai hakanan ta zauna data gaji ta dauki pillows din kujerar ta kwantar da Shurafah itama ta kwanta.

 

Ta jima tana baccin kafin ta tashi yana zaune a parlourn yana kallo miqewa tayi ta nufi dakin ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta tsaya jikin mirrow tana gyara jikinta daidai lkcn ya shigo dakin da Shurafah a hanunsa ya cire mata kayanta saurin dauke idonsa yayi daga kan Umaimah ya nufi bathroom ya fara yima yarinyar wanka lkcn daya fito itama ta gama har tasa kayanta ta koma parlourn ta soma hada tea bai fitoba saida ya shafama yarsa mai ya bude jakar kayansu ya dauki kayanta yasa mata ya shafa mata powder tare da taje mata sumarta baqa sidik mai yawa da tsayi yayi kissing lips dinta ya dauketa yace “ehhhh beautiful daughter kinfi kowacce ya kyau a duniya”

 

Suna fitowa Daddy yana nocking door din qarasawa yayi ya bude Daddy ya shigo ya dubi Shurafah da taketa hanqoron zuwa gurinsa yayi murmushi tare da daukanta ya cillata sama ya cafe yace “kin tashi lfy ayar Allah” kallonshi dukkansu sukayi yayi murmushi irin nasu na manya yace “sunanta kenan iznah ce Zulaiha” share zancen yayi da cewa.

 

Naso na bari sai nan da kwanaki shidda mu tafi so amma wani uzuri ya tasomin na gaggawa saboda haka yau da yamma nakesa ran zan tafi…” da sauri Umaimah ta tari numfashin sa da cewa “yawwa Daddy dama inason ce maka nima zan bika mu tafi saboda saura kwanaki uku hutunmu ya qare” wani malolon kishine ya tasowa Hameed yayi saurin kallon Daddy yace “hutun me Daddy?” Murmushi Daddy yayi yace “hutun makaranta ta fara degree dinta a Skyline University har sunyi semester guda”

 

Daure fuska yayi ya zabga mata wata uwar harara ya juyo ya kalli Daddy yace “kayi tafiyarka kawai Daddy idan na qarajin qwarin jikina zamu taho” dagowa tayi cikin tsoro saboda ita tunda taganshi jiya yayi Mata wani kwarjini sannan tsawar daya daka mata jiyan tasata jin wani mugun tsoronsa ya darsu a zuciyarta tace “amma don Allah Uncl….” hanunsa ya dora a lips dinsa alamun tayi masa shiru yace “ba dake nake mgn ba malama banason rashin kunya”

 

Kallonsa Daddy yayi da mamaki yaga yanda ya wani tsare gda shi a dole me iko yasan tabbas idan ya barta bazaa shuka abin arziqi ba ya miqe yace “debo kayanki kizo mu tafi Jidda mu jira lkc mu tafi” miqewa tayi zuciyarta fari tas ta shiga dakin ta fara hada shirginta saboda Allah ma ya sani bazata iya zama inuwa daya da wannan sabon Hameed din mara mutunci ba.
Baiyi mata mgn ba har saida ta gama hada kan kayanta ta goya yarta tabi bayan Daddy har Daddy yakai bakin qofa ya zai fita suka tsinkayo muryar Hameed yana cewa “nine mijinki ba Daddy ba idan kika taka qafar wajen dakin nan a bakin igiyoyin aurenki”……..

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/24, 9:32 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *G.U*

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button