Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 60

Sponsored Links

Haushi da takaici ne suka hanata dariya kullum Hameed qaro wulaqanci yakeyi wai be qoshi ba amma ya hqr qala batace masa ba ta miqa masa Shurafah ya karbeta ta haura sama ta dauko hijjab da safa ta saka ta dauki jaka da takaimi me dan tudu saboda idan tasa flat hijjab dinta jan qasa zaikeyi safar ta zauna tasa ta dauki niqaf din ta daura ta sanya baqin glass ta kalli kanta a madubi tayi ajiyar zuciya fitinar Hameed yawa gareta tunda take bata taba ganin tsohuwar matarsa Sadiya tasa hijjab ba amma ita harda niqaf saboda rainin wayo.

 

Fita tayi saboda lecturer safe ce dasu daidai lkcn shima ya miqe ya zuba mata ido tare da jan numfashi yace “koma ya kikayi ke me kyau ce kuma bazan fasajin kishinki ba Allah bloody ji nake kamar nace a hqr da karatunnan” bude idonta tayi tayi raurau da ido tace “don Allah kayi hqr kar kace a fasa Allah inason karatu a rayuwata bloody” kama hanun Shurafah yayi yana cewa “ya zanyi to tunda kinaso amma kinsani wlh ko duniya zata taru a kaina bazakiyi aiki ba”

Related Articles

 

Daga masa kai tayi suka jera suka fito yace da me wankin motar ya shiga motarta ya biyosu sukuma suka shiga tasa yaja suka fita har sukaje baice mata qala ba saboda shidai baisan meye yasa ba zuciyarsa tana kishin Umaimansa taje tayi cudanya da maza a university shiyasa tun farko yaqi nema mata admission suna shiga skull din yayi parking a faculty dinsu ta dauki waya ta kira layin Saudat Alfah bugu biyu ta daga tace.

 

“Hello Shuwa’arab kin shigone?” Murmushi tayi tace “banason sunan nan kuna ina a wanne venue din muke?” Kwatanta mata tayi tace “ok ganinan” kashe wayar tayi ta juya gareshi ya hada kansa da sitiyarin motar ta sanya hanunta ta dafashi hawaye suka zubo mata tace “ In kana ganin da matsala bloody mu koma ka saukeni a gda” dagowa yayi ya zuba mata lulu eyes dinsa yayi murmushin yaqe yace “ zan sadaukar da farin ciki daya dominki bloody bazai yuwu ace kowacce sadaukarwa kece kikeyimin ba yakamata nima nayi miki koda dayace tak Umaimah iyakar rayuwarki farin cikina kike fifitawa fiye da naki bakin farin ciki ba sai nawa bakisan dadi ba sai wanda nace shine dadi kuma bakisan kyau ba sai abinda na nuna nace shine me kyau kazalika bakisan so ba sai abinda nace inaso saboda haka sau daya tak na sallama miki na baki qwarin gwiwa akan karatunki ki mayar da hankali kiyishi bil haqqi da gsky amma ban yarda ko group disquetions kiyi da wani da namiji ba duk abinda baki gane ba indai kun kasa ganoshi keda qawarki to ki bari kizo gda na koya miki na roqeki kiyimin wannan alfarmar wlh duk ranar da naji wani namiji ya kiraki da sunan abokin karatu ko naji lbrn kuna friendship da wani namiji tsaf zan mutu nabar miki filin duniyar Umaimah nayi karatu nasan ya rayuwar jami’o’i take daga 9ja har England na fita nayi karatu kin sani saboda haka ki taimaki mijinki dan’uwanki kinji”

 

Daga masa kai tayi tare da kissing tonger dinsa tace “zan kiyaye insha Allahu bazaka sameni da dayan biyun daka lissafa ba” murmushi yayi yace “yawwa bloody Allah yayi miki albarka fita yayi ya karbo key din motarta a gurin drivensu ya dawo ya bata ya hada da hannunta yayi kissing ya bude dashboard dinsa kudi dashi kansa baisan adadinsu ba ya zuge jakarta ya zuba mata yace “gashinan koda zaa buqaci wani abu” gdy tayi masa ya sakar mata niqaf din fuskarta yayi murmushi ta miqe ta fita shima ya fito ya miqa mata Shurafah ya sake matso da bakinsa daidai kunnenta yace “ki kulamin da kanki da babys dina banason zama da yunwa zai iya taba lfyr babyna kinji” sake daga masa kai tayi duk da haka baiyi masa ba saida ya kama hanunta suka nufi hall din saida ya kaita har qofar hall din ya saki hanunta ta daga masa shima ya daga mata sunayiwa juna bye bye kamar bazasu sake haduwa ba itama Shurafah bye bye din tayiwa Abbanta yayi murmushi ya juya da sauri ya nufi motarsa bata shigaba saida taga tashin motar tasa sannan ta juya sukayi karo da S Alfah tayi ajiyar zuciya tace “masoyan asali Wlh U A Shuwa soyayyarki da mijinki tana matuqar qawatar dani tunda kuka shigo nake leqenku harda Zuhura Moddibo itace taje ma kirani tace nazo naga wasu masoya ina zuwa sai naga mijinki nace kece taketa mamaki” murmushi tayi ta daga fuskarta suka shiga ciki suka zauna ta kuma cewa.

 

“U.A Shuwa ina kishiyarki kuwa anya zataji dadin zama a tsakanin masoya irinku wlh tunda naje gdanku ranar bikin nan naga yanda mijinki yake manne miki nace wannan Mata data shigo gdannan zata hadiyi baqin ciki saboda na lura idon Abu Shurafah rufewa yakeyi a kanki U.A Shuwa a gabanmu fa ya daukeki yayi sama dake kunfi awa biyu kafin ku sauko downstairs Aunty Zarah tayita mita tana cewa harijin banza naga yanda zakayi ai idan ka tafi gurin waccen guzumar daka daukowa kanka” nayita mamaki shine Sa’ud tabani lbrn aurenku da soyayyarku shiyasa nace nasan Aunty Murjanatun mu da Muhd dinta nasan tarihin soyayyarsu amma bantaba tunanin zaa samu masoyan da suke sadaukarwa juna farin ciki kamarsu ba sai gashi banje ko inaba na hadu da wadanda suka fisu”

 

Kallonta Umaimah tayi tace “na shirya bayar da rayuwata fansa akanta bloodyna S Alfah wlh inason Uncle Hameed fiye da yanda nakeson Shurafah” kallonta S Alfah tayi zatayi mgn tayi saurin daga mata hanu tace “karki tambayeni dalili S Alfah wlh bansan dalili ba nidai kawai Allah ya halicci zuciyata da so da tausayin Abu Shurafah ina gasqatashi a dukkan furucinsa da aikinsa saboda na yarda dashi tun bansan kaina ba wannan tausayin shine rauni na bana iya yiwa bloodyna musu kuma bana iya bijirewa umarninsa amma wace Aunty Murjanatu S Alfah?”

 

Kawar dakai S Alfah tayi tace banason tuna wani abu daya shafi Aunty Murjanatu saboda kuka nakeyi har hawayena ya qare abu daya dazan iya fada miki shine Murjanatu da Muhammad masoyan junane wadanda zaa iya sanyasu a tarihin masoyan duniya saboda hatta ajalinsu tare ya riskesu ranar da Muhammad yayi hatsari ya rasu Aunty Murjanatu tanajin lbrn mutuwarsa ta yanke jiki ta fadi tashin da itama ba tayiba har yanzu zuciyarta ta buga tabi mijinta ga kabarinsa ga nata U.A Shuwa bafa basa fada bane sunayi amma ko sunyi wani bayaji tsakaninsu suke sasanta kansu idan kuwa har yayi tsamari to koda ta tafi gda yana zuwa zakaga sun fara tsotse²nsu daga haka saidai ka nemesu ka rasa sun gudu gdansu wlh baa taba shiga tsakanin Murjanatu da Muhammad ba wannan shine abinda zan iya fada miki”

 

Ajiyar zuciya Umaimah tayi tace “ina tunanin nima idan bloodyna ya mutu wlh mutuwa zanyi saboda da second daya banason naga yayi nesa dani ke shekaran jiya wlh ban iya bacci ba amma jiya baccina nayi me dadi tare da mijina” mamaki ne ya cika S Alfah tace “amma ai jiyama a gurinta yake ko?” Kawar dakai tayi tace “yace bazai iya kwana uku ba daya ta samu shima din a daddafe ina tunanin kwana daidai zaikeyi mana”

 

Da wannan zancen suka fara lecturer suka tashi ta shiga motarta ta nufi gda kafin taje gdan ya kirata yakai sau biyar saida tace masa tana gda sannan ya qyaleta.
Haka rayuwata taci gaba da tafiya shidai bangaran Hameed abin yanayi masa yadda yakeso amma bangaren Umaimah da Salma baa cewa komai ita Umaimah damuwar jarabarsa ga cikinta ya fara girma shima qaqqarfa irin ubansa sai damunta yake da naushi har ya shiga wata na takwas sannan ga hidimar karatu da ta dauki zafi sun gama level 100 sunyi hutu har sun koma suna 200 level.

 

Ita kuwa Salma kullum sake daura dammara takeyi ta ganin ta kori Umaimah daga gdan badon komai ba saboda an sake jaddada mata matuqar Umaimah tana gdannan to bazata tabajin dadin zama a gdan ba saboda itace zuciyarsu jininsu da komai nasu dayane bazai taba kulata ba balle tasa ran zaiyi wata mu’amala da ita zama takeyi kawai nacin abinci dukiyar da take hange gatanan amma tafi qarfinta saidai kullum idan zai fita zai bawa me gadi 3k ya bata inda ita kuma Umaimah yake bata 6k yace uku na hidimar gda uku na kula da baby’s dinsa a cikin wannan lkcn ne babar Salma taje mata Togo gurin amintaccen bokansu shine ya hado mata wani surkulle yace tasan yanda zatayi ta zuba masa a abinci yaci sannan ya hada mata turaren tsafi yace tayi amfani dashi a jikinta Hameed zai kusanceta idan ya kusanceta to mgn ta qare a ranar saiya saki Umaimah tunda ya fahimci sparm din bazai samu ba amma fah asirin bazai dade a jikinsa ba daga lkcn daya saki Umaimah zuwa kowanne lkc zai warware to daganan ita kuma tasan yanda zatayi saboda akwai yuwuwar uku babu zasuyi ya saki Umaimah ya saketa kowa ya huta.

 

Amma saboda toshewar basira haka Salma ta karbi aikin ta fara tunanin yanda zata aiwatar dashi saboda Hameed ko ruwa bayasha a bangarenta dabara ce ta fado mata ranar wata talata Umaimah bataje mkrnta ba saboda cikinta yayi nauyi sosai hakan yaba Salma nasarar shiga part dinta tayi sallama harda fara’arta abinka da mai tsarkakkakiyar zuciya Umaimah bata kawo komai ba ta yunqura zata miqe tayi saurin qarasowa ta kamota tace “wayyoh sannu Ummuh Shurafah wlh banyi tunanin haka Babyn nan yake wahalar dakeba da na rinqa zuwa Ina tayaki aiki to tsoro nakeji kada nazo kiyi tunanin wani abu” tsugunawa tayi a gabanta tace “don Allah kiyi hqr ke ki fahimceni tunda mijinki yaqi fahimtata wlh banida niyyar cutawa a gareku ban shigo gdanku domin na shiga tsakaninku ba ki yarda dani ba Salman da kuka sani a baya bace na canza sosai fiye da tunaninku”

 

Ajiyar zuciya Umaimah tayi zuciyarta da cikakken tsarki tace “ babu komai ni dama ban taba daukan ki a matsayin wacce zata rabani da mijina ba kawai na daukeki a matsayin qaddararmu kuma ni nasan babu abinda zai samemu face sai Allah ya qadarta faruwarsa ki saki jiki dani Aunty Salma banida matsala wlh da zuciya daya nake zaune da duk wanda Allah ya hadani dashi” Murmushin mugunta Salma tayi ta miqe ta zauna a kujera sukaci gaba da hirarsu tanata bawa Umaimah lbr suna dariya tana yima Shurafah wasa……….

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/30, 1:54 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *GU*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button