Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 70

Sponsored Links

Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin ma’auratan cikin so kulawa da tattalin juna D.S ya shardantawa kansa kullum zai kira Daddy a waya ya tambayeshi jikin Hameed itama tana kiran Daddy sosai ta tambayeshi yakanyi mata nasiha da riqe mijinta amana yakan nuna mata sa’ar mijin da tayi nutsuwa hankali da dattako so tari yakance “uwata yanzu kikayi auren da hankalina ya kwanta Umaimah Hameed danane amma zuciyata taqi nutsuwa da aurenki dashi saboda nasani yafi qarfinki cutar dake yake a mu’amala irinta aure amma ke kinkasa gani kiyi hqr ki cireshi a ranki ki zauna da mijinki lfy kuma kiyi hqr”

 

Idan ya fada mata haka takan yini tana kuka amma takanyi iyakar qoqarinta ta boye damuwarta a gurin d.s saboda tasani idan yaganta cikin damuwa yakan fita shiga damuwar haka rayuwar taci gaba da tafiya cikin so da tattalin farin cikin juna.

Related Articles

 

*************************

 

A bangaren Hameed kuwa saida yayi wata biyar a asibitin yana karbar magani sannan ya farfado Daddy ba qaramin farin ciki yayi ba da samuwar lfyr dan nasa haka yaci gaba da samun kulawa har saida ya warware sosai a wannan lkcn ne kuma suke hira da Dr Ammar likitan dake kula dashi yake fada masa matsalarsa ta sex abuse ya tausaya masa sosai yace masa dama ana samun haka idan mutum mabuqaci ne kuma ya kasa samun kulawa tun farko ya rasa macen da zata iya daukansa akwai wani sinadari da yake sauka cikin jininsu ya rinqa bawa jijiyar mazakutarsu matsalar da zasuke fita daga hayyacinsu idan suka buqaci mace wasu sukan rasa rayuwarsu saboda ciwon cikin da zasu rinqa fuskanta ko wanne lkc wasu kuma hakanne yake sanyasu su kasa control din kansu idan sukaga mace kawai su afka mata wannan dalilin yana haifar da afkuwar fyade sosai a cikin al’ummah masu dama dama kuma sukan fada neman matan banza baji ba gani saboda kiyaye kansu daga hallaka.

 

Dafashi yayi yace “kayi hqr Abdulhameed kuskure ne na rashin fahimta da kuma qaddara yasa komai yaita faruwa a rashin sani amma komai ya kusan zuwa qarshe zakayi aure ka sadu da iyalinka kaji dadi ba wahala ba don s baya ba dadin sex kasani ba wahalarsa ka sani tunda zaka kwana kana kusantar mace batare da tana tayaka ba tama fita daga hayyacinta zan doraka akan wasu magunguna kuma zan hadaka da wani kakana likitan gargajiya ne akwai wani mutum da yataba zuwa da irin wannan matsalar shekaru uku da suka wucce yayi masa magani ya samu sauqi amma zaka zauna a gurinsa harsai komai ya zama normal”

 

Baiyi musu ba saboda a yanda yakeji jiyake dama zaa iya kashe masa sha’awar gaba daya ya huta idan ya tuna bloody dinsa tanacan tana rayuwa da wani namijin kawai sai yaji zuciyarsa tana tafasa hawaye nabin kuncinsa damma ya dage wajan addu’a da neman zabi da sauqi gurin ubangiji yana kuwa samun sauqin sosai duk da yasani son Umaimah bazai taba barin jininsa ba domin dashi aka halicceshi.
Hakan kuwa akayi ana sallamarsa daga asibiti yayima Daddy bayanin komai ya bashi goyan baya har dashi suka tafi qauyen Ghabriel garin da kakan Dr Ammar yake suka samu karamci sosai sukayi masa bayani ya cajeshi tsaf sannan ya dorashi akan magani ya fada masa zaiyi wata biyu anan baija ba saboda bama ya buqatar zaman 9ja din kwata² yana karbar maganinsa yana warwarewa sosai.

 

Watan auren Umaimah da D.S bakwai lkcn tanada cikin wata biyar sosai d.s ya dauki so da qaunar duniya ya dorawa cikin jikinta bashi da mgn sai tasa a lkcn kuma tana 300 level a jami’a tare suke fitowa kullum kowa yana yabawa soyayyarsu da kulawar da yake bata a lkcn ne kuma wata qaddarar ta fado rayuwar Ahlin Hameed Shuwa ranar wata juma’a Hajiya tana kitchen tana girki Nihal da Shurafah suna kitchen din suna wasansu saboda Maliha da Shuraif suna gdan Aunty Zarah kawai sai aka kira Hajiya a waya bisa tsautsayi ta fita tabar yaran a kitchen fitarta keda wuya Gas din yayi wata bindaga gobara ta tashi ta kama wani bangare na gdan ihu Hajiya ta rinqayi tana salati daqyar yan kwanakwana suka kashe gobarar amma abubuwa da yawa sun qone a gdan harda asarar rayuka biyu Nihal da Shurafah.

 

Wannan mutuwa ta girgiza mutane sosai Daddy ne ya hana a fadawa Hameed ita kuwa Umaimah sai Mijinta aka fadawa shine yaje ya daukota ya kawota gdan tun daga qofar gdan tasan wani abu ya faru gabanta ya yanke ya fadi tayi baya luuuuuu zata fadi yayi saurin tarota amma ta suma nan fa hankali ya dawo kanta ya dauketa shida Hajiyansa da aunty Zarah suka tafi Asibiti bayan wani dan lkc ta farfado tana tashi ta riqe hanunsa ta fashe da kuka tace “don Allah Sulaiman kada kacemin Abdulhameed ya mutu zuciyata bugawa zatayi…” Rufe mata baki yayi yace “ai dama na sani nasan tunaninki kenan to ki kwantar da hankalinki bashine ya mutu ba…” katseshi tayi da cewa “to waye waye ya mutu D.S?” Share hawayen idonsa yayi yace “Nihal ce da…” Saikuma yayi shiru daya tuna irin son da takewa Shurafah kullum burinta akan Shurafah ya qare katse masa tunanin tayi da cewa “dawa kuma D. S?”

 

Janye hanunsa yayi daga nata ya fice daga dakin da sauri Aunty Jameelah tace “kunyi Mata shuru ai dolene ta sani Umaimah hqr zamuyi Allah ya karbi rayuwar Nihal da Shurafah jiya da magaruba sakamakon gobara da sukayi a kitchen kiyi hqr Allah zai mayar miki da wadda tafita” ajiyar zuciya tayi tana kallon Aunty Jameelah tana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji’un” iyakar abinda take furtawa kenan har zuwa yamma da D.S ya dawo likitan ya sallameta suka tafi gdan rasuwar ta wucce akayi zaman uku da ita taso tayi kwana bakwai amma ya hanata yace ta dawo ana gobe bakwai din.

 

Haka kuwa akayi ana gobe bakwai da kansa ya kawota tunda ta shigo unguwar taji gabanta yana faduwa hakadai ta daure ta rinqa yi masa yaqe suka fito yana riqe da hanunta saboda cikinta yayi nauyi da girma sosai kamar yakai wata tara bayan yanzu ne ya shiga na takwas tana daga qafarta daqyar suka shiga parlourn yanata zuba mata sannu yana riqe da jakarta dagowa sukayi a tare idonsu ya sarqe da juna taja baya da sauri ta shige jikin D.S inda shikuma ya miqe da sauri yana nunata da yatsa yana kallon cikinta yace “Blo… bloody ciki…….”

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[2/2, 8:49 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *_GU_*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button