Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 74

Sponsored Links

Dagowa tayi ya sakar mata mayaudarin murmushinsa yace “muje inason ganawa dake” kawar da kanta tayi tace “kaje Ina zuwa” yanda tayi mgnr ba qaramin bata masa rai yayi ba amma tunda nema yakeyi sai kawai yayi gaba tabi bayansa da kallo tayi qwafa sukaci gaba da hirarsu da Nazir saida ta bata kusan awa guda sannan sukayi sallama ta nufi cikin gdan tun a qofa ta cire hijjab dinta tana cewa “gsky Hajiya weather din yau batada dadi ga zafi…”

 

Mgnr ce ta maqale a bakinta yanda taga ya zuba mata ido sun kada sunyi jawur ta kawar da kanta da sauri ta dauki Nawwarah ta nufi dakinta da sauri ta mayar ta kulle tana ajiyar zuciya koda yamma ma data fito yana zaune inda ta barshi da Nawwas a hannunsa Shuraif yanata zuba masa surutu amma hankalinsa baya kansu tazo ta giftashi sanye da wata riga fitted sheet iyakar qwaurinta ta hada gashinta ta daure gashin goshinta da yake gaf da hadewa da girarta ya kwanta luf cikakken qirjinta ya tsaya qam kamar bata taba shayarwa ba rigar ta kamata sosai ta fitar da qirarta da sheps dinta.

Related Articles

 

Allah ya sani badonshi tayi shigarba saboda yanayin zafin da ake cikine kawai ya raya mata tayi hakan kuma tanajin sha’awar sanya qananan kayan saboda rabonta dasu tun ana gobe Sulaiman zai rasu kitchen ta shiga domin dauko cake yabita da wani wahalallan kallo numfashinsa na shirin barin jikinsa yace “Tabarakallahu ahsanal kaliqin” yanajin wani irin yarr a jikinsa tsigar jikinsa tana tashi ya rasa meyasa yake mugun sha’awar Umaimah tunda yake baitabajin yanayin da yakeji akanta akan wata mace ba yana hasaso irin dadin dake qasanta har wani yawu ya hadiya ya miqe zaune tare da matse qafafunsa ya tashi da sauri ya shiga dakinsa ya riqe gabansa da hanunsa da qarfi yanajin wani feeling na bijiro masa ya dauki wani qwayar magani ya hadiya ya kora da ruwa saboda yanzu itace ta zame masa taimako gareshi donma shi kansa yasan a cikin lalurarsa kashi dari yanzu babu talatin tunda yakanyi sati gudama baiji sha’awar jima’i ta bijiro masa ba.

 

Ranar bai sake fitowa ba saida safe ya fito ya zauna a dinning ya fara break yana raba idon ganinta amma shiru can yaji murda handle dinta ya zubawa qofar ido ta fito cikin shigarta ta alfarma data qara fito da asalin kyawunta sanye take da wata yaluwar atamfa dinkin doguwar riga data baje sosai a ciki ta yafa blue din mayafi takalmi da jakarta duk blue sai wata siririyar sarqa data sanya a wuyanta ta gold wadda kyautar Sulaiman ta haihuwar twins kudin sarqar ya haura million biyu amma Idan ka ganta a ido zaka dauka batafi dari biyar ba saboda sirantarta ta zauna dass a wuyan Umaimah da zobunan sarqar suma sirara guda biyu sai agogonta shima gold kai iya haduwa ta hadu Hameed kusan qwarewa yayi saboda kallonta ta zuba masa ido ta cikin siririn glass din dake idonta shima ita yake kallo ta rungume Daddy tace “morning lovely” yayi kissing dinta yace “morning lovely daughter” ta sakeshi ta sake rungume Hajiya tace “ina fatan uwata abar faharina ta tashi lfy” dariya Hajiya tayi tace “qlau yar albarka yau sai skull kenan?”

 

Ta gyada kai ta dagawa Hameed hanun tace “Hi brother” tana fadin haka ta juya ta fara tafiya da sauri tace “nayi let Hajiya bazan samu karyawa a gdannan ba Allah yasa ma Hassan ya wankemin motar ji tayi yace “jirani nazo na kaiki” tayi kamar batajishi ba Daddy ne yace “bakiji ba yayanki yana miki mgn uwata” tsayawa tayi cike da takaici ya miqe ya nufi dakinsa ya dauko mukullin da wayoyinsa ya fito suka jera suka fito abin gwanin sha’awa ya bude mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fita daga gdan suka dauki hanya a hankali yake tafiya cike da nishadi ya sanya waqar R-kelly yana sauraro zuciyarsa na raya masa yayi mata mgn amma girman kai da izzah irin tasa ya hanashi waishi jira yake tayi masa mgn haka har suka isa harabar mkrntar yayi parking a wani guri me yalwar bishiyoyi da furanni ya kalleta sosai yace “qarfe nawa zaku fito?” Batare da tunanin komai ba tace masa “hudu” tana bude qofar ya ruqo hanunta yace “ki kula da kanki zan dawo na daukeki” bata bashi amsa ba sai fita da tayi ta nufi Hall din nasu yabi bayanta da kallo tun kafin ta ida shiga suka hadu da Prof Khair wani balaraban Qatar ne da yazo Reasech a skul din kusan tare tasanshi da D.S yana ganinta ya tsaya yanayi mata murmushi itama murmushin tayi ta qarasa suka gaisa sosai ya tambayeta yara tace suna qlau yaci gaba da janta da hira har suka isa Hall din ta shiga shikuma ya wucce apartment din da yake duk wannan abun akan idon Hameed ya hadiya sosai “wato har larabawa take kulawa” ya fada yana bawa motar tasa wuta ya juya ya fice ya nufi sabon gdan da yake ginawa a Ribadu road Hameed kwai dan wawuya duk gdajansa hudu ya siyar idan baku manta ba yana da gda a Nassarawa G.R.A inda Sadiya ta zauna sannan yanada wanda ya ginawa Umaimah a Zingeru road sannan wanda ya siya Mata a Farawa layout sukayi zaman daduro still wanda ya gina na qarshe me part biyu da suka zauna ita da Salma amma duka ya tattara ya siyar ya zuba kudin a gidan gonarsa sai yanzu da akace masa mijinta ya rasu yazo yasai wani katafaran floot a Ribadu road ya wawaki gini na uban ubansun ya fara batare da iyayensa ma sun sani ba saidai ya turowa Yusuf kudin shikuma ya bawa yan kwangila aikuwa aikin yana tafiya sosai duk da bashi da burin idan sunyi aure su zauna anan California zai tafi da ita tayi master da PhD dinta acan in yaso idan wani Abu ya tashi sunzo sake sauka anan.

 

Yaje ya yini sur a gurin aikin ginin qarshe uku da rabi ya koma makarantarsu yana zuwa ya kirata tana ganin kiran taqi dagawa Saudat Alfah ta kalleta tace “ba wayarki ake kiraba” tabe baki tayi tace “itace mana niyyar dagawa ne banyi ba” daukar wayar Saudat tayi har yanzu sunan sa haka yake “Bloody” tayi murmushi tace “Allah sarki masoyan asali Umaimah jinki kawai nakeyi wlh bazaki taba iya rabuwa da Hameed ba kada ki wahalar da shari’a ki bada kai kawai bori ya hau dama rabon twins ne ya rabaku kuma rabon wasu da bamusan adadinsu ba ya kashe D.S saboda haka kiyi hqr kawai ki rungumi qaddara wlh a duk duniya baki da masoyi saman Hameed”

 

Daga mata hanu tayi ta miqe tace “inma kwangila ya baki to kice masa nafi qarfinsa yanzu idona yayi budewar da bazan iya hqr da mulkin kama karyarsa da son kansa ba nariga na shaqi iskar yanci D.S ya nunamin yancina ya bayyana min cewa zaman aure ba zaman bauta bane zamane na yanci kuma rayuwace me dadi a cikinsa inason Hameed nasani shidin wani bangare ne na rayuwata amma bazan iya sake rayuwar aure dashi ba keni auren ma gaba daya ya ficemin a kaina bana sha’awar sake aure a rayuwata wlh” miqewa Saudat tayi suka jero suka fito tana tafe tana rangaji kamar bishiyar gamji harta qaraso inda ta hangi motarsa sukayi sallama da Saudat ya bude mata ta shiga yaja suka tafi yanajin kishinta a ransa baisan sanda yace.

 

“Waye wanda kuka jera dashi dazu kuka shiga ciki dashi” batare da damuwar komai ba tace “abokin mijina ne” ya kalleta da sauri yace “abokin mijinki ince dai ba mijin naki bane?” Tabe baki tayi tace “ba abin mamaki bane idan kaji cewa ya zama mijin nawa ma…” wani uban birki daya taka shine yasata saurin dagowa tayi baya tayi gaba kawai saita fada jikinsa ya sauke wata ajiyar zuciya me qarfi yasa hanunsa ya maqaleta daga ita har shi sunajin wani irin yanayi a jikinsu janyewa tayi da sauri ta koma ta zauna ya sauke numfashi ya bude idanunsa akanta yace.

 

“Don Allah kiyi hqr da wasannan da kikeso muyi wahala zansha ki bani dama ta qarshe bloody idan har nayi wasa da ita kiyimin duk hukuncin da kikaga ya dace kada ki tausayamin amma yanzu ni abin tausayi ne a gurinki saboda zuciyata takasa hqr dake nayi iyakar qoqarina naga na cireki a raina amma na kasa nayiwa Daddy mgnr aurena dake tun jiya yace bazai miki dole ba sai abinda kikeso zaiyi miki har yana gargadina kada na takura miki”

 

Kallonsa tayi da wani irin salo na baka da wayo tace “aure kuma” dagowa yayi yace “Eh haka nace” dariya tayi sosai tace “tab kana ruwa iya wuya kuwa” daga haka bata kuma cewa komai ba shima baice ba yaja motar suka tafi gdan gonarsa yakaita yayi horn megadin ya bude ya shiga gurin ya girma sosai ya qawatu bangaren kaji daban na kifaye daban na gigs daban na shanun madara daban da bangaren tsuntsaye irinsu talo² dawisu da jimina abun dai baa cewa komai.
Wata qofa ya bude ya shiga ya tsaya yana jiranta amma sai yaga ta cake a waje ta tsuke fuska sosai ta yanda saida yaji gabansa ya fadi ta motsa dan qaramin bakinta tace “bance da Hajiya zan biyoka muzo nan ba saboda haka kazo ka mayar dani gda ko na fita na nemi abin hawa”

 

Murmushi yayi ya fito ya janyo qofar ya rufe ya qarasa kusa da ita yace “kina tsoron kada nayi miki fyade ko? Hmn” itadai batace komai ba suka koma suka shiga motar suka tafi gda suna zuwa ta bude zata fita ya ruqo hanunta ta juyo idonsu ya hadu tayi saurin janye nata yace “ki daina jamin aji Umaimah ni ba wanda zaki jawa aji bane ko yau kika amince min gobe zaa daura aurenmu so nakema naje nayi miki VISA saboda nagaji da zaman kadaici wlh kuma duk saboda kene bloody bazan iya zama da wata mace ba bayan ke idan har na rasaki to na hqr da aure har abada balle ma bazan rasaki ba wannan karon wancan ma qaddara ce ta rabamu” kalaman nasa mugun qonanta zuciya sukeyi saboda haka ta fizge hanunta ta shiga cikin gdan a fusace………

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…* ✍🏻
[2/4, 9:05 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *_GU_*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button