Hariji Book 2 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 2 Page 71-72

Sponsored Links

71&72
*Alheri writers asso.*

Wani rudewa taji tayi,da fari yanda yayi kamar ya Santa ,but y pretend?

Wata zuciyar ce ta gargadeta,haba ummi kamar bakisan mafarki ba gaskiya bane? Karfa shaidan ya kaiki ya baroki ,wannan handsome din ma koda a budurwa kike ,me zaiyi dake bare kuma yanzu,much more kina kallon ko a qasashen larabawan en gidan sarauta ne kaman duba da yanayin shigarsu”

Related Articles

“Dady ba girmanka bane sanya sawayenka,a qasa bayan ga matsayin ka” ya fada yina masa nuni da shimfidaddiyar carpet din

Qur yayiwa Adnan da Ido
“Adnan me zaisa in hau,aini tun ranarda er uwata ta kasance ,ta bar wannan matsayin nima Na barshi” ya fada cikin tsananin damuwa

To ya zakaji in ya kasance er uwan taka komai ya wanye,ta kuma dawo tayi retaining position dinta,kamar da ,da can Dady”

“karka hasalani,son muqaddam suna kallon mu ,muje kurum”

Cikeda izzah Adnan ya murza yatsun hannun sa guri guda ,a take zobban zinaren da aka sassargafa masa a hannu da wasu kamar a warwaro fankata fankata suka girgiza suka bada wani irin sauti

Da fitar qarar ,kawai wainnan matan da suka rufe bayan Adnan suka kwaye tsakan kaninsu

Duk sukayi gefe ,saiga wata kyakyawar balarabiya a tsaye,sanye cikin wani irin doguwar riga yina sharar qasa mai ruwan fresh green ko taina tana walwali da hasken zinarai,Da lu’u lu’u

Ruf ta rufe fuskarta da hannayenta masu dauke da adon Jan lalle ga zobban zinaren kaida kai a Zara zaran yatsunta

Tsam quliya yayi da ransa,yina kallon Zara zaran yatsun hannun ta ,masu tsananin kama da nashi ,wannan ko shakka Babu ,Itace ,don mukadai ne Allah ya haliccemu da siffan yatsu masu kamanceceniya da juna

Kasa yarda da zancen zuciyarsa yayi,Kurum a qagauce ya finciki kansa yaje gabanta ya kwaye hannun ta akan fuskarta.

Dum!! dararam!!!

Gabansa ya yanke ya fad’i

“Sophyyyy?” Ya Kira sunanta with a trembled voice

Suuu ,tayi qasa akan gwuiwoyinta ,sannan ta dago idonunta ta kafe akan fuskar quliya

“Labbaik ya Akhyyy”

Wasu qwarzafaffun hawayene suka fara tsiyaya akan dakalin kuncinsa ,layi bayan layi

“Tammat ya Rab,ujjubta du’ai ,mashaallah”
(Komai ya cika,Allah ka kar6i adduata,mashaallah)

Kurum sai shima ya ranqwafa,ya kamota ya rungume ,suka hau kan darduman suka fara tafiya ,wainnan matan Wanda suka kasance hadimai a garesu suka rufa masu baya zuwa gaban tawagan motocin

Ummi kam tsuru tsuru tayi da Ido ,hannun ta sagale ,”Hmm da alama dai wannan dangin Basu maraba Dani” ta raya hakan cikin ranta

“Ahlan wa sahlan,ila Ahlan musannah ,Al’akramiy,Almaj’muud dduwailatul Arab..”

(Barka da zuwa ahlan musannah family ,abun karramawa ,Wanda ya ke juya nahiyoyi da dama Na daular larabawa)

Adnan ya matso kusa da ita,yina mata magana cikin hadadden larabcinsa da ya gama kwanciya a halshensa

Tsoro ne ya kama ummi,wai ya haka ?,nazo ina bahaushiya da bahaushen mijina lokaci daya sun rikide mun zuwa riqaqqun larabawa?

Ganewa yayi kamar ummi batajin yarensu,kurum sai ya murmusa yayi mata nuni da hannu ,alamar ta biyosa suje

Qyar tayi masa da ido kamar Na 2 seconds kafin ta janye eye ball dinta da sauri cikin nasa

Shikam Adnan suman tsaye yayi yina Jin wasu tartsatsin abubuwa suna shiga cikin idonsa ,cikin gaggawa suna kaima qwalwarsa saqon gaggawa

Layi ya farayi yina hada hanya
“Gaskiya wannan yarinyar shu’umace,lokaci daya ina neman makancewa a soyayya ta?”

“Akul dinka Adnan ,manage with your daters (khady da beelah) wannan fa matar dadyn kane…”
Wani sashe Na zuciyarsa yayi saurin kwa6arsa

“Hmm wajen tarayyar soyayya ba ruwan dangantakan jini mafita shine a baiwa zuciya abunda takeso,amma ta Yaya da auren ta? Wannan shine fassarar mafarkin da na dade inayi akan matashiyar nan,tabbas bazan haqura ba in barwa Dady…don rabon yarana a jikinta suke”

Kowa da saqe saqen zuciyarsa barinma Adnan da ummi ,da suka kasance a mota guda ,don quliya shaf ya manta da wai ya taho da amaryar sa takan Sophy kawai yikeyi,don haka mota daya suka shiga da Sophy shi kuma Adnan ya shiga wata motar ,ummi ma ta shiga dayan bangaren aka kullesu
Sannan rankatakaf din Motocin suka fara karakainan barin filin jirgin zuwa qayataccen destinations dinsu.

Tunda aka fara tafiya zufa ke tsatsafo ma ummi ,saboda yanda ta takure a inda take,wani irin fitinannen qamshin jikinsa yina haddasar mata da kasala ,gamida tashuwar feelings din da bata ta6a jiba a gurin kowa ni da namiji ba,ciki kuwa harda quliya…

Adnan ma kusan zamu Iya cewa hakan take a garesa,don duk in ya kalleta tamkar debo ruwan dalmar sonta akeyi ana masa izayar dalala masa a cikin qirjinsa

A wahalce yike furzo numfashi da saurin da sauri

Kansa ya dage saman majinginin kujeran motar,yana bude bututun hancinsa ,saboda yasamu saukin shaqan iska ,idonsa suna a lumshe, yanajin tsohuwar ciwon jarabansa ,da Saida aka kaisa Cairo ya samu maganinta tsawon shekaru uku da suka wuce yina qoqarin tashuwa masa a yanzun nan

“Anya baza ayi abun kunya ba kuwa? Tabbas in wannan baqon Al’amarin nan ya cigaba da qaruwa mun akanta to tabbas zan haiqe mata,don na Lura wannan itace matata tabbas! Wanda akace daga karkataccen haqarqarina aka halicceta…

##Tompha waye Adnan?
##Quliya??
##Sophy ???

** *Flash Back💫***

Da fari wanene Quliya?
Ni sunana…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button