Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 21

Sponsored Links

21…

 

_this novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binka bashi, pay anan or pay achan_

Related Articles

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting_

 

Saida tajishi shiru sanan ta dago kai idanunta sunyi jajir ta kalleshi, sosai taji wani irin tausayinshi yanda ya dukunkune kaman wani maraya, zanin lullubanta tajawo ta lullubeshi dashi sanan ta tashi tahau kan gadon ko minti biyu baya karaba wani bacci mai nauyin gaske yay awon gaba da ita.
Wuraren karfe biyar na asuba Kaka tazo tabuga kofarta. “Hamida, Hamida wai bazaki tashi kiyi salla ba iyye yarnan?” da kyar ta iya bude ido cikin bacci ta kalli inda take kafin ta kalleshi ganin har lokacin yana kasa bacci yakeyi sosai ya dukunkune kaman maijin sanyi yasa ahankali tace “natashi inakan dadduma ne Kaka” kwafa Kaka tayi ta wuce dakinta tana masifa tace “yau bazaki zo dakin nawa muyi tareba, kyaji dashi mai bakin hali” tahau kan dadduma takabbarta salla, yunkurin tashi tayi daga kan gadon takasa takara komawa ta kwanta wani banzan bacci ne yakara tafiya da ita dan tamugun gaji gashi batai baccin kirki da daddare ba sabida Aadil dinan.

Wuraren bakwai ta iya farkawa daga baccin da kyar, ahankali ta karanto addu’an tashi daga bacci tabude idanunta ahankali tana kallon window dakin yanda rana ya hasko har zuwa tsakar dakin ta tashi zaune tana dafa zanin katifar gadon abune taji ya soke mata hannu hakan yasa ta kalli gefenta da sauri ledan biscuit din data bashi jiyane tagani ya ninnike ya maida shi suffar flower da sauri tadau ledan biscuit din tana juyawa tana kallo tadanyi murmushi ta mika hannu zata ijiye idanunta suka sauka akan yar takarda akan gadon da sauri ta dauka tajuyo da paper, zanen fuskan mutum ne yana kuka saiya rubuta sorry my wife a gefe, dan murmushi tayi saikuma ta tabe baki ta juyo dakai da sauri danta kalli inda yake taga bashi awurin, da sauri ta mike tsaye tana kalle kallen dakin ganin bashi yasa tai kofar bayin ta tsaya tai knocking har sau biyu, jin ba’a amsaba yasa tabude kofan da sauri ta leka amma babu kowa cikin bayin, dawani irin sauri tai hanyar kofan ta tana karanto addu’a aranta ta kalli sakatan data saka ganin babu sakata ko daya yasa gabanta yawani irin mugun faduwa, juyowa tayi ta kalli tsakar dakin ganin har lokacin akwai sneakers dinshi akasa yasa taji cikinta yawani irin yamutse ya kulle sosai tsabagen tsoro, kaman daga sama taji Kaka taja wani dogon ihu tabuga uban salati. “innalillahi wa innailaihi raji’un jama’a, Sama’ila, Sama’ila” ta kwalama Abban su kira, arude ta dafa kirjinta dake neman tarwatsewa yadena aiki koina na jikinta na rawa “jama’a gardi a sasa na kufito, Sama’ila” karan bude kofan sasan Kaka taji saikuma taji muryan Abban su yace “lafiy…” bai karasa ba taji yay shiru, muryan Mama taji itama bayan ta turo kofan sasan Kaka arude tace “Umma lafi…” jitayi gabaki daya jijiyoyin jikinta sun dena aiki tsabagen wani irin shegen tsoro da fargaba dasuka dirar ma zuciyarta, ahankali take matsawa tana jan kafarta dasuka mata wani irin nauyi sosai tana komawa baya, maganganun dataji afalo da tsabagen tsoro yasa tama kasa gane me’ake cewa yasa ta sanya hanunta akan bakinta tana kokarin taushe wani irin kukan dake shirin kufce mata, tura kofar dakinta akayi da karfi suka hada ido da Aadil, da gudu Aadil dake sanye da dogon wandonshi da farin singlet ya shigo dakin hanunshi duk ruwa kaman yay wasan ruwa, da gudu yayo wurinta kafin ma tai yunkurin matsawa ganin kanta yayo ya shige bayanta ya riketa gam gam ya sakin mata kuka awuya kirjinshi na bugawa sosai, daidai lokacin su Abba suka bude kofan dakin suka shigo, da sauri ya daga hanunshi yana rikiketa yanuna mata su Kaka yace “my wife see this people they’re scary, sunata kallona am sacred, hide me” yay maganan yana kara komawa bayanta hanunshi duka biyu akan cikinta ya riketa gam cikin tsananin tashin hankali ta fara kokarin turashi daga bayanta da kafadarta take amma ya riketa gam ta bayanta yana make mata kafada yasakin mata kuka ahankali yana kara kankameta, daga idanunta tayi dasukai jajir tahada ido dasu Kaka, Abba, Mama, dasu Zainab daduk sun kasa magana sunyi suman tsaye sun kasa gasgata abinda idanunsu ke gane musu, sai Ya Faruk dake sanye da kayan sojoji shigowanshi gidan kenan ganin yanda su Abba suka shigo dakin Kaka da gudu yasa yabiyo bayansu shima ya tsaya a gefen Zainab ya zubama Hamidan ido kirjinshi nawani irin tafarfasa, fashewa Hamida tayi dawani irin kuka ganin yanda yan gidansu ke kallonta ta fizge hanunshi daga kan cikinta da karfi tawani irin tureshi cikin tsananin fushi har yana buga bango tace “let go off me” da sauri tai wajen Abba ta kalli Abba cikin tsananin faduwan gaba tana kuka bakinta har rawa yake tace “A..bba wl…” cikin wani irin zuciya Abba ya dauketa dawani irin hadadden mari da baitaba mata shiba tunda ya haifeta jikake “pau!” tai wani irin tangal tangal tai baya zata fadi tsabagen yanda marin ya shigeta zaro ido Aadil yayi yazo wajen da mugun sauri yatare ta tafado jikinshi luuu kaman wacce ta suma, fashewa da kuka sosai Aadil yayi ya kalleta yanda take kokarin ta bude ido ma takasa, cikin wani irin tsananin fushi da zuciya yawani irin kalli Abba, fizge ta Abba yayi daga hannunshi cikin fushi yakara daga hannu zai sharara mata mari Aadil yawani irin fizgota da karfi ya rungumeta ajikinshi ya kankameta sosai kanshi na girgiza wa sosai jijiyoyin gaban goshinshi sun fito idanunshi sunyi jajir ya kalli Abba da jajayen idanunshi yay wani irin ihu ya nunamai hannu yace “stop beating her mugu”.

 

 

Yay maganan yana kara kankameta ajikinshi sosai da kyau yana kuka shima kaman yanda take kukan tana neman fizge jikinta daga nashi dan wani bala’in yake kara jefata, a zuciye Faruk yazo zai wuce Abba ya damko Aadil Abba yarike mai hannu cikin tsananin bacin rai batare dayace komiba, daidai lokacin Hamida ta fizge jikinta daga na Aadil dake kuka sosai da karfi ta tureshi tana kuka tace “stop touching me” tajuyo cikin tsananin tashin hankali da sauri ta tsugunna tasa guwiwanta akasa ta hada hannayenta, cikin kuka bakinta har rawa yake tace “Ab…ba dan Allah, Mama” takira sunan Mama da jikinta yay wani irin mugun sanyi idanunta sunyi jajir tana kallon Hamidan tace “Mama p..pl..” tama kasa magana tsabagen yanda zuciyar ta ke bugawa tajuya ta kalli Kaka dage mata wani irin mugun kallo tace “Kaka dan Allah kiyakuri wlh, wlh bansan yabiyo ni….” cikin tsananin fushi Mama ta fizgota tsaye tawani irin watsa mata mari, zatakai mata na biyun Aadil yajawota da karfi har Mama ne neman faduwa, yaboyeta abayanshi dudda yanda take fada dashi akan yasaketa yaki ya rike mata hannu gam yana make mata kafada Mama ta saki baki tana kallon ikon Allah yanda yarike Hamidan dayafi karfinta yana boye ta abayanshi kaman wani mijinta, cikin tsananin fushi Faruk yay kan Aadil Abba yawani irin dakamai tsawa yace “karka sake kataba dan mutane Umar karkai kisa agidana, yarmu itata nunamai gidan nan, ita ta shigo dashi, ita ta…” cikin fushi da kunan rai Kaka da tuntuni batai magana ba ta nuna Hamida dake kuka sosai a tsugunne Aadil shima a tsugunne a gefenta yana kuka yana leka fuskarta kaman wani yaro dan yaye tace “Hamida wlh kincuci kanki bamu kika cutaba, inda kinsan aure kikeso dakin fada anhada bikin ki dana Ayush tuni, kullum sai munafinci kina sussunar dakai ke adole mai tsoron mutane, ke adole ustaziya, hijabin nan biya biya har kasa yake sharewa ashe iskanci kikeyi, Sama’ila” takira sunan Abba cikin wata irin kakkausar murya tana share hawaye da bayan zanin ta tace “wlh Sama’il, kaji na rantse maka da Allah, tun jiya da Hamida tadawo bata bari nasata a idanunaba, bayan magriba yarinyar nan ta shigo gidan nan Sama’ila, yarinyar da kullum kofarta a bude yake kwana wlh tana shigowa jiya ta garkame kofan da sakata bam, ni dama nadinga jin motsi a dakinta harda ihu dasu barambarama kaman ana kaukawa..” tasake goge hawaye tana kallon Hamidan dake kuka sosai tace “babu yanda banyi da itaba tabude na dubata taki wai bacci zatayi, nai nai tafito to tazo taci abinci tadau tuwonta dake falo nan ma taki ashe tanada babban abinci ne acikin dakin, koda asuban nan danazo kin budemin tayi dudda mun saba sallan azuba tare a dakina ashe da kwarto tazo, yanzu Hamida har gida, har Sasa na, har gidan mahaifin ki zaki taho da namiji ki kawoshi shashina dankin rika, kin balaga, kinajin kanki sa’ar uwarki gaki kema kin tasako abinda uwarki kedashi kema kinada shi, to wlh bari kuji nafada muku dukan ku” tai maganan tana gyara tsayuwa tadawo gaban Abba ta tsaya ta nunamai Hamida da yatsa tace “nice uwarka daiko Sama’ila, nice kuma uwar mai gidan nan, sanan nidai bantaba iskanci ba dana auri ubanka ba, ubanka ma baitaba iskanci ba, sanan kaima baka taba iskanci ba dan haka bazan taba yarda dawata yar iska a matsayin jikata ba wlh, ni dama batun yauba nasha cewa Hamida ba jini na bace dan komi nata daban ne agidan nan bakaga kyan ta ba” tunda tafara maganan Mama ta kafeta da ido, hararanta Kaka tayi tace “kinsan menake fadi ai, dan haka Sama’il wlh dole ka zaba koni ko yarka, Hamida ta tattara tabar min gidana ga uwarta nan tafadi mata waye mahaifinta taje chan tasame shi, dagayau itaba yarka bace dan bama tayo komi nakaba, da uwarta take kama kaman tai kaki kanajina ko” wani irin runtse ido Faruk yayi zuciyarshi na tafarfasa dan sosai yaga haukan Kaka yatashi yau tafara maganganun banza, ahankali Abba cikin kwantar da murya yace “Umma kibari an….” “kamin shiru nace mara mutunci rubabben yaro kawai to wlh bazan bari kazama zanin daurawan mace ba” Kaka ta dakamai tsawa tace “tunda bazaka iya koranta ba nizan koreta kuma wlh inga wanda ya isa yadawo da ita gidan nan, na rantse da Allah saina tsine masa” ta kalli Hamida dake kuka sosai a tsugunnen tace “dau kwarton ki gashinan ya tasaki agaba yana kallo yana kuka kaman sabon maye, ki tashi kibar gidan nan yar iska, wato har cemai kikayi yadinga abu kaman dolo ko makira mai kama da uwarta, dau kwarton nan kibar gidan nan kafin nabar Faruku ya kaishi lahiran”

 

Kaka ta daka mata tsawa. “tashi kibar gidan nan nace” cikin fushi Faruk yace “wai ina zatane Kaka? Ga wanda yabiyota bazaku ce komiba kuna cewa tabar gidan mahaifinta ina kikeso taje eh, kunki tsayawa ku saurari yarinya, ina kukeso taje?” “gidan uwarka zata” Kaka tabashi amsa cikin tsananin bacin rai tace “nace gidan uwarka zata, wlh ka kara magana anan wajen saina maka shegen duka na rantse da Allah, Sama’il kama Faruku magana ya maidani sa’arshi yauzan nunamai na isa da kowa a gidan nan dan ubanshi” ta kalli Hamida tace “tashi kibar gidan nan, wlh inhar batabar gidan nanba saina fada rijiyar sasan ku na rantse da Allah” kin tashi Hamida tayi sai kuka take tama kasa magana, kanta Kaka tayo hakan yasa ta tashi da gudu tafada jikin Mama tana kuka tana haki da kyar tace “Mama wlh shiya biyoni, mahaukaci ne, shine shine ya taimakeni a…” wani irin ingizata Kaka tayi har saida tabuge su Zainab tafita daga dakin tafadi akasa timm, da sauri Aadil yatashi yana kuka sosai ya bangaje Kaka da saura kiris ta fadi ta rike kofa yafita yadago Hamidan da sauri yana kuka sosai yasa hannu ya share mata hawayen yace “stop crying i will call police to come and arrest them, they’re beating u, they’re very wicked people” hanunta ya kalla data gurje yana dan jini yarike hanun da sauri yana zaro manyan eyes dinshi yakai hanun bakinshi da sauri yana lashe jinin yana kuka sosai, sosai take kuka tana kallonshi yanda duk hankalin shi yatashi dukya rude, ya cire hanun daga bakinshi yakai hannun bakinshi yana hurawa yana kuka. “fo, fo, fo” Cikin tsananin fushi Kaka tace “kagani ko Sama’ila Hamida tadawo karuwa, kutashi ku fitarmin daga gida” tadau tsintsiyar kwakwa dake gaban dakin Hamida tayo kansu, da sauri Aadil yasaki hanunta yaja Hamidan yasata ajikinshi yamata rumfa yana kuka sosai cikin turenshi dayafi kwarewa akai yace “stop beating my wife, stop, stop, mugu, mugu” rufeshi da duka sosai Kaka tayi da tsintsiyar tana haki yana ihu, tako ina take kaimai dukan yaki sakin Hamidan, Hamidan itama tana kuka dan yanda Kaka ke dukanshi yana kuka har cikin zuciyarta takeji, cikin fushi sosai Kaka tasaki dan ragowan tsintsinyan daya rage a hanunta dan dukya katse a jikinshi tace “kubarmin gidana, kutashi kubarmin gidana, kubarmin gidana” Kaka ta hankadashi, da kyar ya mike tsaye yana rike da Hamidan har lokacin yana kuka ba’a taba dukanshi haka a duniyan nan ba, Kaka tawani irin tura keyanshi tana dukan bayanshi tarakasu da duka har wajen gate suka fita daga gidan.

 

Binsu da kallo yan mutanen anguwan dake waje sukayi sabida yanda Kaka ke dukansu sanan tajuya takoma cikin gida ta rufe gate taciro wani karamin makulli daga lalitar ta ta kulle gate din tana masifa tana haki tace “inga mai fita daga gidan nan yau” taja kujera ta zauna anan gaban gate din tana karkada kafa tana kokarin ballan namijin goron data ciro daga lalita saikuma tafashe da kuka tana nuna kanta tace “Hamida, Hamida” tai kwafa tace “kinma kanki, uwarki kika cima mutunci bani ba”.

 

Ahankali tazare jikinta daga nashi cikin kuka sosai tawarware dan kwalin kanta dakeda girma sosai ta yafa ajikinta, hanunta yakara rikewa yana kallo yasa dayan hanunshi yagoge hawayen dayake yi dayaki dena tsiyaya yace “you are hurt, u are bleeding, those people are wicked” ahankali ta share idonta ta kallai yanda yake kuka sosai gashi sai kallonsu ake, ahankali cikeda jarumta tace “stop crying, am fine” kallonta yayi da jajayen idanunshi itama shitake kallo asanyaye, lumshe ido yayi wasu hawayen suka sake xubowa yace “i will tell Mami and Bid saisun rama miki” yasake kai hanunshi kan idanunshi yana kuka sosai, murmushi tamai taji wani irin tausayinshi tace “stop crying people are looking at u, let’s go” gyada mata kai yayi ahankali miyau na xubowa, sosai yawani irin bata tausayi ga wuyanshi da kafadarshi duk shatin tsintsiya, ahankali tasa bakin gyalenta takai saitin bakinshi ta share mai miyan bakin, lumshe ido yayi hawaye suka zubomai, asanyaye tazare dan kwalin daga wuyanshi tace “i said you should stop crying” gyada mata kai yayi yabude idanun dake cike da kwalla ya daurasu akanta da sauri ta dauke kai sabida yanda taji idanunshi sunsa gabanta yafadi sosai ta daga kafa zatai gaba yariko hanunta gam da sauri ta juyo ta kallai suka sake hada ido yasakin mata wani irin kuka mai tsuma rai, da sauri tace “menene why are you crying?” kallonta yayi cikin kuka sosai kanshi da kirjinshi namai zafi sosai baimasan meyake jiba yakasa magana, dan matso wa tai kusadashi tace “menene? Tell me” kafeta da ido yayi yana kuka batare dayah magana ba, cike da damuwa idanunta sun ciko sosai da kwalla tace “tell me Aadil menene?” ahankali yana kallonta da idanunshi dasukai ja suna kyallin hawaye yace “I love you Hamida my wife”.
_🌹IN BANI 🌹_

 

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button