Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 31

Sponsored Links

Gyaran murya Baffa yayi zai fara magana, Mami takasa daurewa ahankali ta zamo daga kan kujera ta saukar da gwuiwanta kasa ta hade hannayenta biyu alamun roko tana kallon matar da kamanin ta da Hamida yasa tagane itace mahaifiyar Hamidan tace “dan Allah, dan Allah ba danniba, ku dauki Aadil a matsayin danku kunsan duk abinda zaisa yaron nan farin ciki ya taimaki rayuwan shi, kome yakeso zaku iyayimai koma menene abin dan samun lafiyan shi” da sauri ta share hawayen daya zubo mata, zatai magana saikuma wani irin kuka yazo mata tafashe da kuka sosai tsabagen yanda zuciyarta kemata wani irin rawa, da sauri Mama da Anty Lami sukace “subhanallahi, hajiya dan Allah kidena kuka” cikin wani irin kuka Mami ta girgiza musu kai ta kalli Abban Ra’is da Abba ta kalli Kaka data kafeta da ido sanan tasake kallon Mama har lokacin hannayenta ahade tace “dan girman Allah badanni ba bakuma dan halina ba, alfarma nake nema dudda nasan mai girma ne, mai kuma wuya babu wanda zai dauki yarshi yabama mai kwakwalwan yara, amma dudda haka da Allah nake hadaku Maman Hamida da baban Hamida, ku dubi girman Allah, ku taimakama d’ana kubama d’ana Aadil auren Hamida karya rasa ranshi dan darajan All…Allah” tafashe da kuka sosai kowa na dakin saida kukanta yataba ranshi har Kaka, da sauri Mama ta dagata tama kasa magana Baffa yace “ku shiga ciki mu maza zamuyi maganan mu anan” tashi Big Mum tayi da Anty Lami da Mama suka wuce da Mami dake wani irin kuka sosai ciki tana sambatu bama tasan metake cewaba.
_🌹 IN BANI 🌹_

 

Maman Abd Shakur

Related Articles

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button