Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 12

Sponsored Links

12…
Da kyar ta tseremai ta labe awani lungu tana haki sosai da tari, tunda take batajin ta tabayin irin gudun nan datayi yauba, dafe kirjinta tayi dan jitayi kaman zai fito sabida yanda yake bugawa, jin kaman motsi yasa tafice daga lungun da sauri ta bullo wani anguwa dat is very quiet mai kyau, da dan gudu gudu takara sa gaban wani katoton gida dakeda brown gate, bude gate din tayi ta shiga ciki da sauri, katoton gidane dakeda flowers a tsakar gidan sai motoci kusan biyar a compound din, ahankali take tafiya dan ta bala’in gaji kaman zata fadi sai zufa take kofa ta bude ta shiga babban sitting room din da aka rabashi bangare biyu bangare daya ansanya kujera Kiran royal brown sai dayan Kuma asha ga wani makeken tv bango daketa aiki shi kadai danba kowa adakin, maida kofar tayi tarufe sanan tadaura kanta akan kofar tareda da lumshe ido ta dafe kirjinta tana sauke ajiyar zuciya, wata matace mai aikin su da akalla zatai 30 tafito daga kitchen dauke da katon food flask tazo dining ta ajiye zata juyane ta hango ta tsaye a jikin kofa, dan murmushi tayi ta karaso cikin falon cike da fara’a tace “a’a su Anty Islam har an dawo ne” ahankali ta bude ido murmushi ta kakalo ware ido Matar tayi tana kallonta ganin yanda idanuwan ta sukai ja tace “Islam badai ahaka zaki koyi rainon bako yanzu Miemie ne tasa kika galabaita haka harda kuka” hannu takai dan ta kwanto kyakyawar baby da tunda ta ganta take tsalle a baya dan ta dauketa, kwanto ta Islam tayi ta mika mata murmushi matar tayi tace “oyoyo an babyn mamanta, iyye andawo daga anguwa ne da Anty Islam” dariya yarinyar takeyi sosai kaman ba ita ke shegen kukan nan ba, zanin goyon Islam ta mika mata sanan tawuce wajen stairs hawa tayi ta tafi sama, dogon corridor ne da dakuna kusan shida a wurin, wani kofa ta bude ta shiga dakine dake dauke da gadon yan boarding house saidai shi wanan na katako ne da akamai fenti pink, bunk biyu ne kadai adakin sai center carpet shima pink, da study inda uban littatafai kekai, gaban wardrobe taje ta tsaya tana kallon mirron dake jikin kofan wardrobe din ahankali takai hannu ta warware rolling din gyalen dake kanta dogon gashinta ne ya warware ya zubo har kirjinta dan tsaki tayi ta ciro ribon din daya hade da gyalen ta kama gashin, doguwar rigan jikinta tacire tabar shimi da sket ajikinta kan gado taje ta kwanta tareda sauke ajiyar zuciya dan har yanzu kirjinta bugawa yake.

Harwajen motansu Mallam isya ya rako Yusuf yana karamai godiya ganin marfin mota abude yasa Yusuf ya bude bangaren shi da sauri ganin ba Khaleel aciki yasa ya fara waige waige adan arude, Malam Isya ne yace “lpy Yusuf” arude yace “nabar Khaleel a mota bangan shibane” ganin yanda ya rude yasa yace “karka damu bari mudan tambaya” samarin dake gaban shagon Adamu yatambaya dan Allah kunga wani matashi bako nane” da sauri Yusuf yace “yanada gashi sosai akai” da sauri mai shago yace “to kodai wanan wanda ya rike yar mutanen ne yace yasanta? Dan naga gashi rututu akanshi” da sauri Yusuf yace “shine a ina ka ganshi?” “anan gaban shago na ya rike wata yarinya datasai ma wata yar baby ruwa yanace mata Eesha wai sutafi gida” ahankali Yusuf yace “Eesha kace?” “eh haka naji yanata kiranta nidai” “to yanzu ina suke” “Naga tagudu yabita chan sukayi” Ya nunamai hanyar dasuka bi da gudu Yusuf yabi hanyar da aka nunamai hankalinshi atashe.
Akarshen layin Yusuf yaganshi ya zauna akan wani dakali ya rike kanshi, karasawa wajen Yusuf yayi ya daura hanunshi akan kafadar shi, dago kai yay ya kalli Yusuf da idanunshi dasukai jajir, zama Yusuf yay kusa dashi ahankali yace “Khaleel wat is d matter?” murmushi yay mai ciwo yace “yau naga wata da ta tunamin da Eesha, for a second I tot she was my Eesha, yanda Eesha ke tafiya haka yarinyar ke tafiya” shiru yadanyi kafin yafuzar da iska yace “I think am loosing my mind” hanunshi Yusuf yarike gam ya girgizamai kai Yace “Khaleel Eesha tariga ta rasu bazata taba dawowa ba, and inhar son dakake mata is real kamata yayi kadawo normal kai kaman yanda kake da, kazaci inda Aisha na nan she will be happy da yanda kadawo ne? Bakama mutane magana, bakacin abinci kullum kana daki Ammin ka kullum saita kira Umma kusan 5 times tana tambayan jikin ka, duk ka rikita gabaki dayan family mu is that fair do you think Aisha zatai murna dajin labarin nan?” shiru yayi kawai yana kallon Yusuf, tashi Yusuf yayi daga dakalin yace” mutafi “ahankali ya sauko daga dakalin waigawa yasake yi kafin yajuya sutafi.

“Islam, Islam” ahankali ta bude ido, wata yar budurwa ce wacce suke kai daya da Islam tana sanye da doguwar rigar atampa ja take tashin ta, yatsine fuska tayi cikin muryan bacci tace “uhnnn wat Farida” yaye bargon data lulube dashi Farida tayi tace “kitashi” juyawa tayi ta kife cikin muryan bacci tace “leave me aloneeee” tsaki Farida tayi tahau up bonk dinta ta kwanta abinta, tsaki tasakeyi tace “Islam” shiru tamata bata amsaba, hakan yasa tai kwafa tace “okay o dama Anty Hindu ne tazo kinsan ta very well” zabura tayi ta tashi ta zauna ware manyan idanunta tayi, leko dakai Farida tayi daga sama ganin ta tashi ta zauna yasa tai dariya, juyo dakai tayi ta kalli Farida hannu tasa ta dafe goshinta tace “Faree please da gaske tazo?” gyada mata kai Farida tayi, da sauri ta tashi gaban wardrobe taje zaro wani abayan ta baki tadaura akan dan singlet din dake jikinta ta wuce tafita daga dakin.
[6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Related Articles

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button