Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 26

Sponsored Links

Yau Monday bata da lectures amma sabida Farida data kirata tamanta da presentation dinta dake cikin file akan table Kuma yau zasuyi yasa ta tashi ta shirya tana tsaki.
Sauka falo tayi tadau presentation din akan table tafito Bala ne ya dauketa suka fito daidai yay parking motar shi a kusa da gidan su batama lura dashi ba suka wuce, ajiyar zuciya ya sauke sanan ya kunna motar ya bisu har AUN. Parking Bala yayi a parking lot tafito hanunta rike da file dakuma waya data kara a kunne, kasa dauke kanshi yay daga kanta bata lura dashiba sabida glass din motar shi tinted ce. Maida wayar tai cikin jaka tadan jingina da wata mota tasa kumbanta abaki tanaci dan taga yadanyi tsayi, Farida data hango tadan taho da gudu gudu, yasa ta karasa wajenta file din tabata ta karba ta bude tagani murmushi tayi sanan ta mikama Islam hannu suka tafa tace “bari nai sauri an fara amma ba’akai group dinmu ba” tana fadin haka tama Islam bye ta wuce ta tafi dadan sauri dawowa motar Islam tayi ta shiga Bala ya kunna sukabar wajen. ba karamin mamaki yayiba dayaganta da Farida, wayar shi yaciro da sauri neman number ta yafara dan baitaba kiranta ba, da kyar yagane number yay dailing, Farida data kusan class dinsu tanajin ringing ta duba wayarta ganin superman ne wani farin ciki ya rufeta da sauri tai picking, “Hello Mk” ahankali yace “how you” murmushi tayi tareda yin wani fari ta cigaba da tafiya tace “fine, yasu Ihsan” shiru yadanyi kafin yace “inaso nadan tambaye ki wani abu” baki tawani washe tace “ok” yace “ina parking lot din school dinku..” “school dinmu?” ta katse shi yace “yeah, naganki da wata, I think kaman tabaki wani folder ne, who is she?” “Farida Maikano” taji ana kiranta is time for her presentation kenan da sauri tace “Mk I will call you later, zanyi presentation ne bye”.

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button