Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 33

Sponsored Links

Sheshekan kuka datake ji yasa ta farka cikin tsakiyar daren nan, ahankali ta mika hannu ta kunna wutar dakin hakan yasa baccin idonta ya washe sosai, wawwaigawa tayi bataga kowa akasa ba hakan yasa ta sakko daga gadon, Farida tagani ke kuka a kwance da sauri tahau matattakalan bonk din tahau kan gadon ta dago ta, ta zaunar da ita takai hannu arude ta taba wuyan ta tace “baki da lafiya ne?” girgiza kai Farida tayi tana goggoge hawayen dake zubowa kaman an bude famfo, komawa tayi zata kwanta Islam tariko hanunta tace “talk to me please, problem shared is problem solved” fadawa tayi jikin Islam tafashe dawani irin kuka harda shesheka hakan yakara ruda Islam ta kankameta tace “Faree konaje na taso Mum ne?” girgiza kai Farida tayi ahankali tace “wlh Islam ina mugun sonshi, son da bazan iya kwatanta miki ba, amma kwata kwata bama ya daukan wayana yanzu, baya kulani na rasa yanda zanyi da kaina” kama fuskarta Islam tayi tace “listen listen kidena kuka kinata wahala shi baimasan kinayi ba, ki manta dashi jor, kanme zakizo kina wahala, ki manta dashi” girgiza kai tayi tace “bazan iyaba, I tried but nakasa I love my superman so much Islam bazaki gane bane” shiru Islam tayi cike da tausayin ta ahankali tace “to kinfada mai kina sonshi?” girgiza kai tai alamun a’a, tace “to duk randa kika sake ganinshi kinfada mai am sure zaisoki back” murmushi tadanyi ahankali tace “thank you Islam” kwantar da ita Islam tayi sanan ta kwanta agefen ta sukaja bargo suka kashe wutan dakin.
Gabaki dayan su suka hadu suna aiki a kitchen sabida Abba yace zaiyi baki sha daya zasuzo, Farida ta rame har Abba saida ya tambaye ta meke damunta tace bakomi Wuraren goma suka gama aka zuzzuba abincin a hadaddun kuloli, sanan kowa yawuce daki danyin wanka.
Suna shiga daki Farida ta kulle kofar su hadda sa sakata sanan ta kalli Islam dake kokarin cire kaya tace “kinsan me mommy tacemin?” girgiza kai Islam tayi tace “cewa tayi wai aurenki fa za’a zo nema yau” sosai taji kirjinta yabuga dum! Farida tace “kinsan dama baki bani labarin yanda kuka karasa da Fahad ba dama kin yarda yaturo ne?” arude ta girgiza kai tace “cemai fa nayi sainayi magana da Mummy, baifadamin zai turo ba and kona kirashi baya picking fa rabona damagana dashi tun Ina hospital” dariya Farida tayi harda kama ciki tace “yamin daidai, gwarama daya turo kinadai ji Abba yace mungama school dinan zai xhanza mana wanine, to mezaki zauna kiyi har next year, wlh nima dazaran na sasanta da superman dina aure zamuyi abunmu na cigaba da school din a dakina” tsaki Islam tayi ta ijiye wayar tace “kinga yaki picking ko” gwalo Farida tayi tace “ke dalla chan ki kyaleshi idan aka samuku rana yau ai automatic soyayya ce zata wani kara kulluwa” harara ta wurgamata tasake dariya tareda yin wurin kofa tace “kinga bari naje na debo mana abincin mu a flask dan dazaran iyaye sunzo bamu sake sauka kasa ina zasuga Amarya kafin aure” takalmi ta dauka ta jefamata da sauri tafita daga dakin tana dariyan shakiyanci rabon datai dariya haka harta manta.
Wuraren sha daya da rabi suka iso Babban Khaleel da Baban Eesha sai Kuma Abba da wasu abokana yen shi biyu duk sunci manyan kaya, da kanshi baban Islam yamusu iso nan suka zazzauna afalo ana gaishe gaishe kafin Mum da Anty Hindu da Maman Miemie suka fito aka gaggaisa sanan aka gabatar musu da abinci sukaci suka sha sanan aka fara magana. Basu boyema Baban Islam komi akan Khaleel ba ba karamin tausayin shi yajiba, nan ya yarda ya amince yabasu Islam yace ai tun randa Anty Hindu tafada mai yatura a kamai binciken halin shi Alhamdulillah duk yan anguwa sunce mutumin kirki ne ga zuwa massallaci. Aka fara maganan sa rana wata biyu yace amma Abba ya roki alfarma abarshi wata daya sabida suna son Yaron yakoma bakin aiki ya dade rabonshi da aiki nan baban Islam ya yarda, Baban Eesha ne yafita ya shigo ga jakunkunan gorori mai gadi ya tayashi dauka da su sweet nan aka ijiye dubu dari kudin nagani Ina so Anty Hindu tawani saki guda. Bayan anyi finalizing everything aka rufe taron da addu’a sanan suka wuce massallaci danyin sallan azahar dagangan suna dawowa suka tafi murmushi akan fuskar kowa.
*JARABTA*
Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button