Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 72

Sponsored Links

Karan dataji yasa ta bude ido ahankali tana karema falon kallo, a kitchen ta ganshi tsaye yana kokarin daukan heater kettle yana sanye da farar singlet dayar 3 quarter kafarshi cikin slippers, tashi tayi daga kujeran tazo wajen kitchen din yanajin ta amma yaki kallonta hanunta yaji ta daura kan nashi cikin sanyin murya tana kokarin karban kettle din tace “kawo nasama, mekake so nama?” batare daya kalli fuskarta ba yasa dayar hanunshi yacire hanunta dake kan nashi ya bude tap yatara kettle din yana diban ruwan, saida ya dibi daidai wanda yakeso sanan ya kashe tap din yarufe kettle din yajona shi da igiyar shi, dan juyowa yay ya kalleta yace “i can manage” ta gefenta yazo zai wuce tariko hanunshi da sauri muryan ta har rawa yake tace “am sorry, dan Allah kayakuri idan kaji haushin abinda nace jiya ne, babu yanda zanyi ne Farida yar uwata ce, my only sister kaji” takarashe tana wani rera sabon kukan dan juyowa yay ya kalleta hakan yasa tadan tsagaita kukan datake yi, hanunshi ya fizge daga nata yakara mata wani kallo sanan yace “nasani i know she’s ur only sister” ya maimaita mata maganar da tamai na karshe yawuce wurin kettle din ganin yana tafasa ya kashe ya dauko mug zai juye ruwan aciki da sauri ta tsayar da kukan datake yi tazo wurin tace “kawo natayaka” daukar kettle din yayi ya tsiya ya ruwan aciki batare daya kalleta ba yace “zan iya da kaina” ajiye kettle din yayi ya dauko nescafe ya zuba aruwan da honey sanan yadau spoon yafita daga kitchen din yawuce falo ya barta anan, yana gamasha anan falo yabar cup din ya shiga ciki ya chanzo kaya zuwa Jean da t-shirt daya daura jacket akai yazo yafita daga gidan, wani irin abu taji ya tsaya mata arai hawaye kawai taji yana fita ta dinga goge wa ranan hartai bacci bata ganshi ba, da safe ma data tashi bata ganshi ba tadai ga note a gefenta kan gado daya rubutu ta hada kaya yau zasu tafi wani dadi ne taji ya lullube ta zataje taga Farida, bayan sallan Isha ya shigo gidan afalo ya sameta zaune da doguwar riga ja ajikinta ga akwatin su babba data hada kaya ta fito dashi falo, baiko kalleta ba ya shigo yaja jakar yafita da ita waje sanan ya dawo duk tana tsaye, tashi jakar yafito dashi batare daya kalleta a yace “muje” bayanshi tabi jikinta duk asalube suka fito ya kulle gidan yabama Raymond dake waje key da wasu kudi Yaron yarakasu har wajen mota suka shiga yana daga musu hannu suka wuce airport. Bayan sunyi checking in suka zazzauna suna jiran afara boarding, goma dayan kai aka fara boarding suka shiga jirgin nan jirgin ya tashi jarida yake ta karanatawa abinshi chan yaji kanta akan kafadar shi Jaridar yarufe yadan kalli fuskarta bacci yaga tanayi hakan yasa yadan gyara mata kwanciya tareda sauke ajiyar zuciya shima ya lumshe ido.
Karfe tara da minti arba’in jirgin su ya sauka a airpot din Abuja, ahankali take bude ido harta bude su duka hada ido sukayi hakan yasa ya dauke kai da sauri, daga kanta tayi daga kafadar shi tana zare ido, fara fita akayi daga jirgin hakan yasa yatashi itama ta tashi sauka sukayi wata mota tazo ta dauke su ta ijiye su a gaban luggage claim nan suka jira akwatinan su suna zuwa ya kwasan musu ya gungura tana bishi abaya suka fita daga arrival din wani driver sune da Ammi ta turo musu yazo ya karbi akwatinan daga hanun shi yana gaidasu cikin fara’a, Khaleel ne ya amsa suka shiga motar sukabar airport din. A wuse gaban wani babban gida driver yay horn aka bude musu suka shiga ahankali tafito daga motar mai gadi yazo ya cicciro akwatinan daga bot shikuma driver yakoma cikin mota yamusu sallama yabar gidan, kofa ya bude ya shiga haka yasa tabi bayanshi duk agajiye wani hadadden duplex ne, falon anmai fentin brown da milk, furniture din cikima kalan su kenan, upstairs dataga yayi yasa tabi bayanshi dadan sauri wani falon tasake gani a upstairs din sanan ga dakuna uku, wani daki taga ya shiga kasa binshi tayi tabude dayar dakin akwatin ta da tagani adakin yasa ta gane nanne natama, karasa shiga dakin tayi tana karema dakin kallo anma dakin fentin baby pink ga akwatin ta da aka jera asaman wardrobe kaya tacire ta shiga bayi tai wanka Koda tafito abinci tagani lafiyayyen white rice da stew ga farfesu agefe duk anjera mata a tray, salla tafara yi sanan tazo ta zauna taci iya cinta ta ijiye sauran akan drawer gefen gado ta kwanta sabida ta mugun gaji within 2min bacci yay gaba da ita.
Koda tatashi da asuba tai salla tai karatun al Qur’ani sake komawa bacci tayi sai wuraren 7: 30 ta farka bayi ta shiga tadan kuskura bakinta tafito tasaka hijabi, ahankali tabude kofa tafito daidai shima yafito sanye da uniform dinshi na navy bakaramin kyau yayiba, dauke kai yayi da sauri daga kallonta, harda dan saurin ta takarasa gaban shi ahankali tace “good morning” batare daya kalleta ba yace “morning” juyawa yay zaibar wajen ta bishi da saurin ta ahankali tace “uhmm dan Allah kadan kiramin Abba inaso inyi magana da Farida ne” batare daya kalleta ba ya cigaba da sauka daga kan stairs din sanan yace “bazan kiraba” da kyar ahankali tace “to yaushe zamuje yolan?” baiko kalli fuskarta ba yace “babu inda zaki” wani irin kuka ne taji yazo mata, fita daga gidan yayi da sauri, ta dade tsaye a wurin tana hawaye sanan takoma dakint.
Saida taji yunwa na neman mata illa sanan ta sauko kasa tana neman kitchen sallama dataji yasa ta amsa wata ma tace da zatai 29 haka tanadan murmushin ta tashigo tace “sunana kande nice mai tayaki aiki mai gidan ne ya turo ni, ai tunda akazo akai jere nike zuwa kullum Ina gyara gidan, yau da safe ya kirani yacemini kun dawo nazo natayaki aiki” dan murmushi tai ta gaishe da Matar, tare suka shiga kitchen suka dafa abinci mai rai da lafiya sai kallon yar torch light phone din matar take ahankali tace “indan ari wayar ki?” da sauri Kande tace “eh gatanan” ta dauka ta mika mata karban wayar tayi tafita daga dakin taje parlor ta zauna number Abba tasaka tai dailing ringing biyu Abba ya daga da sallama da sauri tace “Abba Ummi ce” murmushi Abba yayi yace “Ummi dazuko nake tambayan mijin ki ke yake sanar dani yana wajen aiki toya kuke ya karfin jikin naki” ahankali tace “Alhamdulillah Abba ya Farida” ajiyar zuciya ya sauke yace “ga Farida nan sai addu’a batama San wanda ke kanta ba” wani kuka ne taji yazo mata hakan yasa ta taushe bakinta “amma muna ta addu’a in sha Allah zata sami lpy so karki damu kanki ki kula da kanki kinji kinsan kema baki dade da samin lpy ba, Allah muku albarka duka” kasa amsawa tayi ta katse wayar tafashe da kuka sosai, kande tafito daga kitchen din da gudu tana lpy, kasa amsawa Islam tayi saima kukan datake yi da kyar tai shiru ganin yanda Kande dukta damu ta mika mata wayarta dadan murmushi tace “Ya tace batada lpy” Kande tace “to ai addu’a zaki mata ba kukaba Allah bata lpy” ahankali tace “Ameen nagode” share idonta tayi tace “dan Allah tayani diban abinci kibama su mai gadin, kema ki diba” murmushin dadi kande tayi sanan tace “to” diba tayi ta kaima su mai gadi Sanna itama tazo tadiba a yar kula tamata sallama ta tafi.

Har dare haka ta wuni tana kuka, bayan tai sallan Isha tashiga bayi tai wanka tafito daure da towel, yunwar dataji tana addabar cikin ta yasa tafito daga dakin ta sauko kasa, kitchen ta shiga ta bude warmer ta dibi dan rice a bowl karami tadau spoon tafito daga kitchen din tareda kulle kofar, karan anbude kofar sitting room yasa ta daga kai hada ido sukayi yana sanye da uniform da sauri ya dauke kai yazo yafara hawa stairs da sauri ta ijiye abincin akan dining tabishi sama harya bude dakinshi ya shiga itama tabude dakin ta shiga wani kamshi ya bugi hancinta, dakin tsaf tsaf komi fari, ko kallonta baiyiba saima kokarin bude boturan rigar shi dayake yi, ahankali tace “Ya Khaleel dan Allah yaushe zamuje duba Faridan?” ko kallonta baiyiba saima karasa cire rigarshi yayi ya ijiye agefe ya tsugunna yana kokarin kwance igiyar takalmin kafarshi, duka ya kwance ya ijiye agefe yatashi tsaye yana kokarin cire dogon wandon uniform din jikinshi, tadan matso kusa dashi jikinta nadan rawa tana gyara towel din jikinta adan tsorace tace “eh yaushe zamuje” bai kalleta ba saima zame wandon dayayi yace “babu inda zaki” sosai tafashe mai da kuka hakan yasa yabude bayi ya shiga abinshi kuka take sosai tasa hannu tanata murza idanu tace “dazu dana kira Abba yacemin batasan wake kanta ba, Farida is suffering, tun ina yarinya mu biyu Mummy ta raine mu tare, Farida ita ke tare min fada a school, ita ke bani snacks din break, itake rikemin hannu, she is my best friend, so kake karaba mu yanzu?” tacigaba da kuka sosai kaman yanda yara suke suna kuka suna magana, da kyar tai shiru tana sauke ajiyar zuciya tace “tun ranan da ka karbo mata jakanta Farida take sonka, Farida loved u so much, Allah ne ya jarabce ta da wanan son and ni take fadama komi, yanzu she is seriously sick bazaka sakeni ka aure ta ba, wlh idan wani abu yasa meta bazan taba iya yafema kaina ba” takara fashewa da kuka harda shesheka, cikin kukan tace “kaki kiramin su nai magana da ita, sanan kuma bazaka barni naje naduba taba rabamu kake so kayiko hmmm” tacigaba da rera kukan sabida yanda abun ke mata ciwo, ya dade tsaye abakin kofar bayin daure da towel yana kallonta sabida ta juyama kofar baya, wani irin cije lips dinshi yayi sanan ya fuzar da iska sabida yanda ranshi ya mugun baci, rufo kofar bayin yayi da karfi har saida tai kara hakan yasa ta juyo a firgice ta kallai, ganin idonshi yasa ta tuna marin da tasha ranan da sauri tai hanyar kofa zata bar dakin ya fizgo hanunta ihu mara kara tayi, jijjigata yay rai abace yace “bazaki yolan ba, and saki kikeso ko baza’a sakekin ba, barima kiga” towel din jikinta ya fizgo ya yar arude tafara kokarin tsugunnawa tace “na shiga uku dan Allah ka yakuri Ya Khaleel, wlh bazan karaba” jefata yayi kan gado.
[7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button