Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 32

Sponsored Links

BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KUƊI NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616

Ina godiya bisa ta’aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma ban san su ba, sun nuna mini kara ƙwarai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba🙏🏿🙏🏿32
Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo kafin ya ce “Baki da hankali?” Ta buɗe idanu wanda sukai jajir ta ce “Me na yi?” Da idanu ya dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buɗe, itama tayi saurin kallon kanta tana ɗan marairaice fuska zuciyarta duk babu daɗi ta kasa cewa komai sbd yadda ƙirjinta ke ɗagawa ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harɗe hannu a ƙirji shi ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can ƙasa ya ce “Kuma da gaske fita zaki haka? Tsirara?”
“…. Tsirara!?” Ta faɗa da sauri cike da tsoro, Alpha ya haɗe fuska ya ce “Mene marabar dambe da faɗa?” Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta Kaɗaita da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai ƙara magana ba ya bi ta gefenta ya shige ya zauna saman kujera yana harɗe ƙafafuwan. Majeederh ta shige part ɗinta not too long ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo baya can ta ce “Ina yini?”
“Lafiya” Ya bata amsa a taƙaice. Majeederh ta yi ƙasa da kanta cikin sanyin murya ta ce “Ance an maka ƙarin girma congratulations” Alpha ya ce “Uhm” Yana ɗan kaɗa ƙafa kafin babu wasa idanunsa ya kira sunanta ya ce “Majeederh!” Ta yi shiru.
“Zabiya?” Ta kwaɓe fuska tunda bata son sunan ya ɗan shafa kai daman He just wants to tease her. Ta miƙe zata bar parlourn ya ce
“No, please” Ta zauna kamar zatai kuka ta ce “Tun ina ƙarama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to”
“Stop it Majeederh!” Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a ƙahon zuciya, ya girgiza kai ya ce “Sorry”
Ta yi shiru speaking calmly ya ce “Sannu da dawowa ƙasa Nigeria, yanzu sai me?” Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce “Sai abin da Abbu ya ce” Alpha ya watsa hannu ya ce “Kina sane da problem ɗinki, komai zaki ki fara tuna aure first” Kunya ta kama Majeederh sai yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba ɗaya bane tuni Ubangiji ya ye mata “Kina ji?” Ta ce “Aiki zan nema” Da wani irin sauri ya ce “Aiki?” Ta ɗaga kai ya ce “Shi ma Abbu ne?” Tayi shiru cike da tausayawa ya ce “Am sorry, zan masa magana ya fara bari kiyi aure” Wani irin abu ne mai ɗaci ya tsayawa Majeederh a maƙoshi ta runtse Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi al’ƙawarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Idan ya amince nayi auren wa zai aureni?” Alpha ya zura mata manyan idanunsa ya ce “Kamarya? kina nufin tsayin shekarun da ki kai a Egypt baki saurayi ba?” A hankali Majeederh ta girgiza kai ta ce “Even friend ban ba, shekaruna ashirin da takwas 28 ban taɓa yin saurayi ba idan ka ɗauke Imran shi ma ya guje ni ba tare da sanin dalili ba, baƙin jini ne dani Yaya na zama mujiya a idanun mazan duniya, hatta soyayyar ƙuruciya ban san ya take ba, ban san daɗin soyayya da wahalar cikinta ba, ko saurayin da zai zo ya yaudareni ban taɓa yi ba, balle wanda zai ji muradin aurena a zuciyarsa….,”
Ta yi shiru sbd numfashinta dake fisga kaɗan kaɗan kafin ta ce “Duk son da maza suke wa farar mace, duguwa mai kyan fuska nawa ya tashi a banza, mummunar mace wada ta fini farin jini, to idan ban yi aiki ba me zan Yaya? Shi ma Abbu fahimtar hakan ce ta sanya ya zaɓa mini wannan rayuwar kuma ina farin ciki da ita” Duk rashin imanin Alpha kasancewar shi Soja, wanda yaga masifu da yawa ya kashe rayuka da yawa amma a yanzu a gaban Majeederh sai dai zuciyarsa ta karye ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana bugawa hannayensa waje guda kafin cikin sauri ya tsaya a gaban Majeederh ya ce “Majee ki minin wani al’ƙawari, do me a favor please” Ta kasa kallonsa ya kai hannu zai riƙe nata tayi saurin janye nata tana ɗan yi murmushi ta ce “Na maka”
Ya ja baya ganin bata son ya taɓa jikinta, numfashinsa na sauka ya ce “Kiyi accepting duk wani abu dana yanke miki muddin ba cutarwa bane, ki yarda ba zan cuceki ba Majee” Ta ce “Me zakai?” Ya bata amsa ya ce “Zaki ji, ki amince first” Ta jinjina kanta bai ƙara cewa komai ba, ya fice daga part ɗin ya shige part ɗin Abbu ita kuma ta nufi Kitchen ta fara haɗa dinner harta gama ta shige part ɗinta ba taga fitowar Alpha ba….

Washegari ya kama weekend ne, Aaliyah na zaune a parlour watching Ds t.v lokacin 10:10 na safiyar Saturday jin ana sallama ya sanya Aaliyah ɗago kanta tana amsawa da faɗin “Wasalamu Alaiki, Anti Latifa” Latifa ta zauna tana cewa “Ashe fa yau weekend da tuni kina school” Aaliyah ta yi murmushi ta ce “Ina kwana?” Ta amsa da “Lafiya lou” Sukai shiru can Latifa ta ce “A level nawa kike ne yanzu?”
“… 200″ Aaliyah Said, tana ɗan buɗe Idanunta akan series ɗin _My heart knows_ da take kallo a zee wrld. “All The best little sister, ina Malama?” Aaliyah ta nuna mata hanyar kitchen da hannu ta ce “She’s in the kitchen” Lura da hankalin Aaliyah nakan series ya sanya Latifa miƙewa ta nufi hanyar kitchen ɗin tana zuwa ta samu Majeederh tsaye gaban sink tana wanke hannunta tayi dariya ta ce “Sannu da aiki Madam koko” Majeederh ta ɗan yi murmushi ta ce
“Uhm” Latifa ta ce “Gasky am lucky na samu abinda nake so”
“… Kike so? Ko ya ke so?”
Latifa ta ce “Shi wa?”
Majeederh ta watsa mata harara tana ɗauke plate ɗin data wanke ta ce “Nasan ciki ne dake”
Latifa ta ce “A’a ba ciki ba, baya ne dani” Ta faɗa tana tofar da yawo a bakin kitchen ɗin har sai dai Majeederh ta runtse idanu a ɓoye.
“Ni dai zuba mini breakfast yunwa na ke ji” Da mamaki Majeederh ta ce “Idan na baki mijinki fa?” Latifa ta jima tana kallon Majeederh can ta ce “Na yi fa, idan ni nayi bana iya ci sai na kwaɗayi” Bata ce mata komai ba, ta haɗa mata breakfast fal cikin warmer hadda kunun gyaɗa mai kyau, tana bata tayi godiya ta fita a hanya taci karo da Raihan tana shigowa cikin compound ɗin a haɗaɗɗiyar motar ta, bata kulata ba ta fita tare da shigewa nata gate gidan… Lokacin da Raihana ta shiga gidan duk suna parlour suna breakfast ta cire mayafinta tare da ajjiye hand bag ɗinta tana zama saman dining ta ce “Ki ce nazo a daidai” Aaliyah bata ce komai ba haka ma Majeederh, sai da Raihana ta kai abinci bakinta ta ce “Majeederh ba gaisuwa?” Da sauri Aaliyah ta ce “Wakike so ta gaisheki Anti Raihana?” Kai tsaye ta ce “Majeederh?” Baki buɗe Aaliyah ta juya ta kalli Majeederh kana ta kalli Raihana ta ce “Anti Jeederh ce zata gaisheki? Bama ke ki gaidata ba?” Raihana ta ce “Ai ni ya dace ta gaisar” Aaliyah da ranta ya fara ɓaci ta ce “A sbd kin haifeta? Shekaru nawa Anti Jeederh ta baki?” Raihana ta saki dariya hadda buga dining ɗin dake gabanta ta ce “Ji banza wake ta ƙama da shekaru? Ai tunda nayi aure to yanzu ni ce gaba da ita, bayan nayi aure haihuwa zan yi Kinga durƙosawa wada ba gajiyawa bane ko? Ai aure shi ne martabar ko wacce mace, kiyi ƙoƙari ki aure sai mu iya haɗa kafaɗa dake”
Aaliyah ta miƙe tsaye itama tana sakin dariya ta ce “hehehe, matar na tuba bata rasa miji aure, ai dake da Anti Jeederh da ke kwaryar sama ce take dokan ta ƙasa, mene marabarki da ita? Sunan kinyi aure amma kullum kina hanyar barbaɗa na zuwa gida ana ƙarar da albarkar aure akan titi, Anti Jeederh da izinin Ubangiji ba zatai auren barbaɗa irin naki ba, zata auri miji wanda yake kishinta yake sonta wanda zai jure duk wani ƙalubale nata wanda zai sota fiye da yadda take son shi zatai aure inda aka san darajarta, ba zata taɓa auren wanda zai sallamawa duniya matarsa ba” Aaliyah ta riƙe ƙugu ta ce “Mema kika ce haihuwa? Ai sai dai kici ki haifi kashi ba dai ɗan mutum ba, domin juma’ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta….,”
Hannu Raihana takai zata kifawa Aaliyah mari tayi saurin ja baya, Raihana na huci ta ce “Zan yi maganinki dan uwarki idan ni sa’arki ce” Aaliyah ta zare idanu ta ce “Ni na isa na haɗa kaina da uwar mata mai aure? Wlh wani ya kalleki sai ya ɗauka kin yi shekaru 20 da aure duk kin rakwaɓe kamar tsohuwar mota” Wani baƙin ciki ya turnike Raihana ta ce “Ni kike faɗawa haka?” Sai a lokacin Majeederh ta tashi ta zabgawa Aaliyah mari ta ce “Ya zama ƙarshe” Aaliyah saka kuka sosai ta ce “Na gaji Anti Jeederh na gaji da abinda suke miki, su basu da aiki sai gorin aure? Kamar ke zaki aurar da kanki sun manta komai lokaci ne? Ita Anti Raihana da take yin ɓari ta taɓa zama ta tambayi kanta me yasa cikin baya zama? Da aure da haihuwa da arziƙi duka na Allah ne, wani jinkirin alheri ne kuma da aure irin nasu wallahi gwara mutum bai aure ba, mata nawa suke aure amma baya zuwa ko’ina auren ke mutuwa” Majeederh na ƙoƙarin yin magana suka ji gyaran murya a tare suka juya Alpha ne tsaye hannunsa harɗe a ƙirji fuskar nan kamar an aika masa da saƙon mutuwa, yana sanye cikin wani jeans da Racing jersey ya saka p.cap a kansa sai ƙamshi yake. Gabaɗaya sukai shiru jikin Aaliyah da Raihana ya ɗauki rawa musamman Aaliyah domin tasan Alpha baya son raini da rashin kunya ga babba bakinta na rawa ta ce “Ya…yaya A.b don Allah….,”
Hannu ya ɗaga mata, idanunsa akan Raihana ya ce “Ke dan kan uwarki Majeederh sa’arki ce?” Raihana ta yi shiru ya ƙara sakar mata tsawa ya ce “Shegiya munafuk za kici ubanki daga ke har mijin da kike tunanin kin aura wanda yasa kikewa wata gori akan haka, duk sanda na ƙara ganin ƙafarki a gidan nan without any reason wlh sai na kusa karya ki” Ya nuna mata ƙofa ya ce “Bar nan wajan kafin na karyaki na karya banza, shi ma mijin naki bashi da tunani bai san ciwonki bane” Ganin ta juya zata shige part ɗin Mami yasa ya nufeta ta kwasa a guje tana kurma ihu ta faɗa part ɗin Mami, tsayawa ya yi yana shirin komawa kan Aaliyah yaga wayam babu ita sai Majeederh dake tsaye. Bai ce mata komai ba ya juya zuwa part ɗin Abbu. Mami ta kalli Raihana dake haki duk tayi wujiga-wujiga ta ce “To shi haka ake bai ji ta bakin kowa ba sai ya hau faɗa?” Raihana ta ce “Shi daman baya son mu ai, ya fi son Anti Jeederh da Aaliyah he’s so selfish” Mami ta ce “To ai shi ba Allah bane, kuma ke matar aure ce yana dokanki Shari’a ba zata barsa ba, yabar ganin shi soja ne wlh garƙame shi za ai a bayan canter” Raihana tayi shiru Mami ta kalleta ta ce “Kema bana son rashin ta ido, ina ke ina zabgawa Majeederh wannan maganganun? Kar na kuma ji balle ki ja mini zagi” Raihana ta tura baki Mami ta ƙara cewa “Yau kuma me ya kawo ki?” Ta ce “Jiya da daddare ya dawo, ya kuma da asubar fari a haɗa kayansa wai wani aiki ke ya taso masa” Mami ta zabga tagumi ta ce “Shi kuma ƙaddararsa kenan tafiye-tafiye? Wai aikin me yake ne?” Raihana ta ce “Ni ban sani ba” Ta ce “To Allah ya kyauta”…… Kwana biyar kullum sai Alpha ya zo wajan Abbu ba tare da sanin meke kawosa ba, da yamma liƙis Anti ta shigo gidan ƴarta Sona bayan sun gaisa da Mami ta ce “Ina Majeederh?” Mami ta ce “Ta leƙa gidan Latifa daga nan ance sun fita” Kafin Anti tayi magana Majeederh ta shigo bakinta ɗauke da sallama Anti ta amsa “Daga ina kike?” Majeederh ta ce “Mami gidan Latifa” Cikin faɗa Mami ta ce “Ji munafukar ƙarya ba ance kun fita ba?” Majeederh ta ce “Oh na rakata asibiti na sameta tana ta amai ne ashe ɓari za tai” Mami ta ce “Au ciki ne da ita?” A hankali ta ce “Eh” Mami ta ƙara cewa “Yanzu ya ɓare cikin?” Nan ma Majeederh ta ce “Eh” Mami ta jinjina kai ta ce “Ikon Allah, wannan ɓarinta na uku kenan, mahaifarta ce bata da ƙauri ina zato” Babu wanda ya yi magana tsakanin Anti da Majeederh, Mami ta gyara zama ta ce “To me Likitoci suka ce kuma” sai a lokacin Anti ta ce “Haba Asabe wannan tambayoyi kashi da kashi ita yanzu Majeederh me zata ce?” Mami ta ɗan yi murmushi, Anti ta ce “Daman abin alheri ya same mu” Mami ta ce “Ma sha Allah” Anti ta kalli Majeederh kana ta ce “Alpha ne yake son Majeederh yana son ya aureta” Da wani irin Shock mai kama da mamaki Mami ta ce “Shi Alpha ɗin? Kuma Abbu ya amince?” Anti ta ce “Shi ne ma ya saka ranar auren ai” Da wani irin Scorned expression Mami ta ce “Ikon Allah bani da labari Allah ya sanya albarka” Majeederh ta yi shiru She couldn’t say a word sai bin Anti da idanu take. “Majeederh kin amincewa da yayanki kuma ɗan-uwanki Alpha? Kin aminci ya zama mijinki?” Buri Majeederh ta auri wanda ya san kima darajar ta, wannan yasa take yawan kallon Alpha matsayin crush ɗinta take jin inama ya aureta? Ganin bashi da interested akanta yasa bata taɓa sanyawa ranta ba, Majeederh ta tsinci kanta cikin tashin hankali sbd babban burinta ta zama matar A.b Alpha Bello, It’s her dream tun sanda ta buɗe idanu ta gansa yana kula da ita, She can’t afford to lose him, her life will be incomplete without him, She’s felling scared and restless me yasa take jin tsoro?… “Majeederh”
Anti ta kira sunanta. Ta ɗan kalleta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce “Kina son auren Alpha?” Majeederh ta ce “Anti ai zaɓi ba nawa bane kamar taimakona ya yi” Anti tayi shiru sai kuma ta ce “Shikenan jeki Allah yasa haka ne alheri a rayuwarki” Miƙewa tayi ta shige bedroom amma deep down na zuwarta mamaki take anya shi yace zai aureta? Mai yasa bai fara neman Soyayyarta ba? “Ke da za a taimakawa ina ruwanki da neman soyayya?” zuciyarta ta bata amsa.

Related Articles

Da daddare bayan Majeederh ta gama dinner tayi sallar Magriba tana zaune tana azkar wayarta ya yi ringing ganin sunan Alpha yasa gabanta faɗuwa har kiran ya katse bata ɗauka ba, wani kiran ya sake shigowa ta yi bismillah ta ɗauka a hankali ta ji ya sauke ajjiyar zuciya ya ce “Me kike?” A hankali ta ce “Azkar” Ya yi jim ya ce “Shi ne baki picking kiran farko?” Ta ɗan marairaice ta ce “Kayi haƙuri” Ya share maganar ya ce “Majeederh” Ya kira sunanta ta kasa amsawa ya ce “Wannan shi ne hukuncin dana yanke mana, ina fatan banwa rayuwarki Shisshigi ba, idan kuma baki so na baki son aure let me know first” Ta yi shiru Ya ce “Kina son Aurena? Majee?” Da sauri ta kashe wayar tana rufe Idanunta kamar yana gabanta, daga can ɓangaren murmushi Alpha ya yi kana ya kashe wayar ya shiga Parlourn Mahaifiyarsa zaune ya sameta ya ce “Sannu da dare Mama” ta ɗaga masa hannu ta ce “Ya isa” Tana faɗin hakan ta miƙe tare da ficewa daga parlourn…… Ciki sati gudu wata muguwar shaƙuwa ta wanzu tsakanin General Alpha Bello da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Tana jinsa har cikin zuciyarta gashi da masifaffen kishi, Anti ta kira mai gyara aka shiga yiwa Amarya Majeederh wani mahaukacin gyara, sosai Alpha yake kashe kuɗi har kawo lokacin ko hannu Majeederh ta hana ya riƙe mata….. Ana saura kwana ɗaya ɗaurin aure tun safe aka haɗa Family meeting gidan Uncle Isma’il an cika sosai yara da manya maza da mata, Alpha ne kawai babu a wajan can Uncle Bello ya ɗakko wayarsa ya kira shi yana ɗagawa ya ce “Wanne irin iskanci ne haka? Mu zamu zauna zaman jiranka?” Muryarsa can ƙasa Ya ce “Am sorry” Uncle Bello ya kashe kiran babu jimawa ya shigo kansa a ƙasa ya zauna can kujera, aka buɗe taro da addu’a Uncle Isma’il ya ce “Ma sha Allah, a gobe In sha Allah muna da ɗaurin auren da zai kafa tarihi a Khan family” Cikin sauri Alpha ya ce “Auren wa za’a ɗaura Uncle?” Gabaɗaya aka kallesa cike da mamaki Uncle Isma’il ya kasa bashi amsa, Alpha ya ce “Me ya sa kowa ke kallona? Why are you staring at the?” Anti ta ce “Gidanku General Aurenka mana” Ya ware idanu ya ce “Aurena kuma Anti? Dawa?” Ta ce “Da Majeederh” Ya ƙara waro idanu ya ce “Wacce Majeederh? Ni zan yi aure kuma Majeederh zan aura?” Innati ta ce “Ji wawa dilla kuyi abinda ya kawo ku” Uncle Isma’il ya kwaso katin ɗaurin auren ya ce “Gashi nan It’s too late ka bawa friends ɗinka” Alpha ya kwashi katin da Shock ya dinga bin sunansa da idanu da kuma na Majeederh ya ɗago kansa ya ce “Ke ni na ce zan aureki? Wai meke faruwa ne?” Uncle Bello ya miƙe ya zabgawa Alpha ya ƙara zabga masa ya ce “Bana son hauka, lokacin da kazo da maganar aurenta kwana bakwai daga shige uban waye ya yi maganar ba kai ba?” Alpha ya girgiza kai ya ce “Wallahi Abba ni ban taɓa cewa ina sonta ba, ni me zai saka na aureta ƙanwata ce fa?” Innati ta ce “To da sauƙi tunda ba nono ɗaya kuka sha ba” Alpha ya ce “Uncle,Abba this is misunderstanding wlh ni bance zan auri Majeederh ba infact ina da wacce nake so kuma gobe zan kawota ku ganta don Allah kada ku aura mini Majeederh…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button