Mijin Malama Book 2 Page 1
For more updates
“Ka faɗa mini waye zai zama mijin Malama na gaske wacce tauraron ta da na shi yazo ɗaya, na sake faɗa maka ko da wasa kada Abuturab ya taɓa kusantar Majeederh, dan tsinannya ce yadda kasan ayo yanzu zaka ganta da ciki, ni kuma bana son hakan ya kasance, burina a rayuwa tai ta yin ƙasa ni kuma ina sama, ina baƙin ciki da duk wani samunta, kuma nayi al’ƙawarin yadda za a fini kyau ilimi ta fini arziƙi da nasaba, to ba zan taɓa yarda da a fini da gidan miji ba, ba zan yarda da a fini farin ciki da kwanciyar hankali ba, Turzum kayi duk yadda za ka yi kada His Excellency Abu-turab ya kusanci Majeederh ko da sau ɗaya ne”
Wani irin kallon Turzum yake mata, yaga mugwayen mutane kala-kala daban daban, yaga wanda suka haukata kishiyoyin su, naga wanda suka sabauta uwar miji, wasu ma faccaloli sbd kawai abin duniya,amma ya jima bai yi aikin akan wacce ke son ganin bayan aminiyyarta ba, makashinka na gidanka ta shiga rigar annabi Musa bayan zuciyar Fir’auna ne da ita. Turzum ya kwashe da mahaukaciyar dariya yana yi yana ɗaga ƙafa tare da sakin tosa, girman bakinsa kaɗai ya isa bawa mutum tsoro, balle daƙwa-daƙwan idanunsa ya gyara zama ya ce “An gama, yadda kike so haka nan za a yi azzalumar mugwayen wacce bata da rabon rabauta, zamu kwantar da kayan aikinsa zamu cire masa sha’awa” Latifa Omar da har lokacin take durƙoshe yafe da wani jan yadi ta ce “Da kyau uban bokaye Turzum, ka faɗa mini miliyan nawa kake so?” Ya buga mata tsawa ya ce “Kin jima da sanin mana amsar ko sisinki ni bana amsar kuɗi a aiki, wannan cikin dake mararki da zarar ya yi wata huɗu kawai ki zubar da shi, jinin ɓarin shi Aljanu suke buƙata zasu sha, matan da kike bi kuma a duk sanda kuke masha’a Aljanu na gefe suna kwashe ƙazantarku” Latifa ta miƙa hannu ta shafa mararta ɗumin na ratsa hannunta, wani irin so da ƙaunar cikin ya wanzu a zuciyarta, nan da nan kuma shaiɗan ya ƙawata mata muguwar niyya cikin sauri ta ce “Da zarar ya yi wata huɗun zan zubar, ina fatan dai aikin yanzu zaka mini ko?” Turzum ya ɗaga ƙafa ya ƙara sakin tosa ya ce “Lashakka yanzu zamu kammala komai, Aljanu kawai za kiwa al’ƙawari, bayan wannan ne kike buƙata?” Ta gyara zama ta ce “To ai matsalar kace asiri ba zai tasirin a jikinta ba, banda haka da ita Majeederh kawai naso a sabauta ta shiga duniya ko kuma ta kwanta jinya har ajalinta ya yi, kuma ko anyi aikin baya tasiri sosai tunda gashi dana saka ta zama mujiya a idanun maza anyi hakan, to daman kace mini duk sanda ta haihu asirin zai karye, to ni dai ta shammace ni ban ma san yaushe ta samu cikin ba, daga haihuwarta zuwa yanzu samari sai magana suke suna sonta daga ciki kuma har mijina Aliyu, kuma wallahi manyan mutane fa? Shi yasa kawai naso ta auri wannan kafurin yaron ya zama mijin malama tunda kaga ana zaton ma bashi da Iyaye shi ma shege ne gantali kawai yake, gashi burina bai samu cika ba, kace mini wata tayi mini shigar sauri ko?” Turzum dai kallonta kawai yake babu ƙiftawa ta ce “Wallahi wulaƙantacce miji naso Majeederh ta aura wanda zai dunga cin Ubanta yana gallazawa rayuwarta, amma idan babu damuwa shi kansa His Excellency Abu-turab ɗin kawai a saka masa hannu a arziƙin shi, komai ya saka hannu ya lalace yadda E.F.C C zasu garƙame shi a gidan yari” Turzum ya ce “Zan yi tunani sai na kammala wannan aikin, ki je sai ki dawo kuma kada ki matsanta akan sanin waye MIJIN MALAMA na har abada, kada ki matsanta kada ki matsanta kinji na faɗa miki baƙar muguwa” Latifa ta jinjina kanta ta ce “Shi kenan Turzum bari na je” Ta miƙe tana ajjiye masa ƙyallen wanda yake ta zuba wari ta shiga fita daga ƴar bukkar tana kaɗa masa mazaunai, Turzum ya bita da idanu yana dry.
After Issha prayer, around eight and forty minutes, Majeederh ce durƙoshe gaban matan wan mahaifinta da Uncle’s ɗin sai Innati da Yaya Bilkisu, faɗa suke mata sosai Uncle Isma’il ya ce “Duk abin da zan faɗa alrdy an faɗa miki, Majeederh idan aka ce aure to ana nufin haƙuri, haƙurin gidan miji yafi daɗin yawa, kina da hankali shekaru 35 ya isa ki fahimci rayuwa, ki kwantar da hankalinki kima mijinki biyayya da ƴan uwansa da uwar mijinki, Majeederh yadda Ubangiji ya rufa mana asiri kika samu miji kamar Abuturab kada ki bamu kunya plx, kiyi zamanki lafiya, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri aure haƙuri ne, ka auri mai kuɗi ka yi haƙuri, ka auri talaka ka yi haƙuri shi ne” ɗaya bayan ɗaya suka shiga yi mata faɗa kusan kowa zai ce mata ta yi haƙuri, aure ɗan haƙuri ne. Ita dai kanta na ƙasa ta saka wani tsadadden lace black colour da feshin dutsun jaa ya zauna daram a fatar jikinta ya ƙara fidda haskenta ainun a fili. Sai wani vail babba white colour data ɗora akanta wanda Sona ta ɗaura mata ta fito a babbar mace idanunta ne kawai ya faɗa amma haihuwar da tayi ya sanya jikinta buɗewa irin na masu ɗanyen jego. Suna zaune Jawaad ya shigo yana ɗan murmushi ya ce “Finally he’s here” Gaban Majeederh ya faɗi ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa, Uncle Bello ya ce “To ya kai ɗaya?” Ya ce “Oh! Ya ce ba zai shigo ba, maybe kunyar surukan shi yake” Maman Alpha ta yi murmushi tana kallon Jawaad matsayin Alpha har yanayinsu ɗaya da ɗaga shoulder’s da suke. “To ai babu damuwa, ku bata ɗanta sai su shige” Da sauri Yaya Bilkisu ta ce “Wani ɗan ni ƴar nan? Kawai sai ta tafi gidan miji da ɗan mutane kuma jariri? Ai nan zamu riƙe shi in sha Allah taje kawai Allah ya bata sa a” Da sauri Majeederh ta ce “Plx zan je da shi” Yaya Bilkisu ta riƙe haɓa ta ce “Naga abinda ya Isheni ni Bilkisu, gidanku Hawwa’u ashe baki da kara? Ai kamata ya yi ki tsani ɗan kamar yadda kika tsani ubansa” Ita dai ta yi shiru, anyi ba ai ba, taya zatai farin ciki babu baby Khalil wajanta? Idanun yaron kawai idan ta kalla nutsuwa take samu.
“Gaskiya ban goyi bayan ta tafi da shi ba ni ma, ni zan riƙe shi In sha Allah daman ba nono yake sha ba madara ce idan ya yi kamar shekara ɗaya sai a kawo miki shi, kafin nan za a dinga kawo shi kina gani” Maman Alpha ta faɗa tana amsar Little dake ta bacci abinsa cike da kwanciyar hankali yana yi yana tsotsar lip’s. “I go for your idea Maman Alpha, amma mene amfanin kai mata shi ɗin? Nan da wata tara za kiji wani babyn yazo ita da mijinta sa raini abin su” Cewar Yaya Bilkisu. Uncle Bello mamakin mata da halinsu ya cika shi magana ɗaya amma sai wannan ya ce wannan ya ce? Ya miƙe tsaye ya ce “Nan da ba gidan biki bane da ake ta gutsira magana” Ya dubi Majeederh ya ce “Ke Hawwa’u ta shi kuje Allah ya tsare ya baki sa a” Sai a lokacin ta ce “Uncle kamar mara gata ni kaɗai zan je haba…” Sai kuma ta saki kuka wanda kana ganinsa za kaga da biyu tayi shi, da kukan barin Baby Khalil dana tafiya ita ɗaya. Uncle Isma’il bai tsaya jiran mai bata haƙuri ba ya damƙi hannunta sukai waje yana zuwa ya samu P.a Hammad da Jawaad suna hira hadda tafawa kamar wasu sa’anni. His Excellency yana zaune a bayan mota tun zuwan su bai fito ba, ya sanya wani haɗaɗɗen brown ɗin Yadi mai kyau da tsada ɗinkin Half body da gajeren hannu babu babbar riga, yanayin yadda fuskarsa ke fitar da annuri zaka san cewa shi ne angon,Happiness lies on his face,He feels himself like a new man, calmness descends on him in his whole body. Maimakon ya buɗe Ƙofar ya fito sai ya danna number Hammad tana fara ringing ya katse, Hammad dake tsaye shi da Jawaad ya yi saurin barin wajan yana zuwa ya saka hannu ya buɗewa Majeederh bayan mota. “Bismillah” majeederh ta juya ta kalli Uncle Isma’il idanunta ya yi rau rau a hankali ta ce “Plx Uncle kai kazo muje” Ya zare idanu ya ce “Rufa mini asiri da abin kunya, kin ga shiga gobe ai zaki ganmu” Hawayen da take riƙewa ya shiga sakko mata ta ce “Shikenan kamar mayya” Yana riƙe dryrsa ya ce “A’a bamu haifi mayya ba” Shi kansa ya yi tunanin Abuturab ɗin zai fito daga motar ya kama hannun matarsa sai yaga shiru a hankali ya ce “Ki yi haƙuri, haka ko wacce mace take jin zafin rabuwa da gidan iyaye kin manta har wata ƙasar kika je shekaru 8 ba uwa ba uba babu kowa naki balle kuma gidan miji? Gidan biyayya da samun aljannarki?” Ya lallaɓata tana kuka sosai haka ta shiga bayan motar Hammad ya rufe ya zaga da sauri bayan sun yi sallama da Jawaad akan idanun Uncle Isma’il,da Uncle B Jawaad suka fice daga cikin gidan sai a lokacin tausayin Majeederh ya kama Uncle’s ɗin, Uncle I duk abin nan hankalinsa yana kan Abraham tun ɗazo yake neman Digits ɗinsa ya shaida masa Maminsa tayi aure kada ya sake dawowa da maganar aure, amma magana ɗaya ake ta faɗa masa number a kashe yake.
Tunda suka ɗauki hanya take shassheƙar kuka, tana da juriya da zurfin ciki da iya riƙe kanta amma tunda wannan ƙaddarar ta faɗa mata ta samu kanta ta saurin karaya da al’amuran rayuwa saurin kuka da shiga tunani, tana jin rayuwar babu daɗi ta kuma riga data saddaƙar bata da rabon farin ciki a duniya. His Excellency Abu-turab ya ɗan lumshe idanunsa yana jin nutsuwa na saukar masa a hankali ya juya ya kalleta ya ce “Jiddo, Mrs kuka kamar yarinya?” Ta yi masa shiru ya miƙa hannun ya riƙo nata mai taushi sosai ya haɗe da nasa ya ce “Stop haka nan” Ya faɗa can ƙasa, ya ƙara ɗan matsawa drawing her more closer to himself daidai kunnenta yana ɗora kansa a shoulder ɗinta ya ce “Common baby Jiddodo, haba Wifey” Ya faɗa yana riƙota bakiɗaya ta tura baki tana ƙasa da kanta, ta rasa me ya sa zuciyarta bata da sukuni da Gwamna ɗin? Tana so ta amshe shi hannu bibbiyu matsayin mijinta hakan ba zai faru ba sai ta saki jikinta da shi. Bai ƙara ce mata komai ba yana riƙe da hannunta har suka isa Government house. P.a Hammad ya buɗewa Abuturab ƙofa ya fito yana fitowa kuma kai tsaye cikin gidan ya shige ganin haka yasa Hammad buɗewa Majeederh ƙofa ya ce “Fito ki bisa kada ya shige” Ta fito a hankali tana jin faɗuwar gaba tayi bismillah dai ta shiga cikin gidan, babu kowa a main parlour tuni kuma His Excellency ya shige upstairs ta bisa a baya har zuwa ɓangaren shi ya buɗe ƙofa tare da zama saman kujera ta nemi waje ƙasan carpet tare da zama sun jima a haka kafin ya ce “Yaushe zaki arba’in?” Ya faɗa without looking at her ta bashi amsa ya miƙe yana ɗaukan wayarsa ya ce “Oh good night” ya shige Bedroom ya barta nan zaune tana binsa da kallo, a hankali ta gyara zamanta tare da jingine kanta da jikin kujera ƙirjinta na ɗagawa taya zata fara rayuwar aure da wanda bata san halinsa ba? Ta fahimci yana sonta amma shi ɗin kamar ba mutum ne mai bada kulawa da nuna damuwarsa akan iyalan shi ba. Ta ɗauki niyyar kyautata masa ko hakan zai sanya ta manta abubuwan baya tayi facing future life ɗinta, haka ta raya daren idanunta biyu ta kasa koda runtsawa fitowar Abuturab uku yana ganinta zaune a fitowa ta ƙarshe taga ganshi da cup da magani bai ce mata komai ba kuma, ana sallar asuba ya fito sanye da jallabiya sai ƙamshin perfume ɗin Dolce and gabbana yake ko inda take bai kalla ba ya nufi fita zuwa masjid.
Germany, Schloss Bellevue.
Schloss Bellevue shi ne sunan dake maƙale a jikin Hammerschmidt Villa in Bonn, babba gida wanda zai yi unguwa guda white house komai na gidan fari ne, fenti, gate glasses everything. Sai green grass da flowers da duk suka kasance green sai rufin gidan da yake cofie ga red ɗin ƙaramar ƙofa a tsakiya wacce data kai ka har ciki, iya gidan tsakiya abin kallo ne balle wanda suke gefe da gefe, ga wasu tarin windows da doors birjik hawan benen gidan ba zai irgu ba, ga totar ƙasar Jamani a maƙale, ga kwalta kwance tako’ina securities da Escorts kamar ana yaƙi.
Cikin sauri sauri yake taka ƙafarsa idanunsa a lumshe hannunsa ɗaya a sumar kansa ɗayan kuma a aljihu a haka yake rasata Escorts ɗin dake bashi hanya suna ɗaga masa hannu babu wanda ya kula, dake yasan the process of entering the house har zuwa part ɗin President bai sha wahala ba, har ya ƙarasa haɗaɗɗan parlourn wanda ya ji Italian furniture’s, komai fari ne the chairs are all white. Yana shigowa parlourn ya saka ƙafarsa ɗaya ya daki ƙofa glasses ɗin jiki ya tarwatse. Dad ya ɗago idanunsa ya sauke akan Abraham yana ɗan yin murmushi wato mai hali baya taɓa fasawa.
“Wlcm back Son” A hargitse ya ce “Dad!” Ya faɗa yana lumshe idanunsa sai kuma ya ware su tas akan Dad ɗin ya nufe shi tare da zubewa a gabansa muryarsa na ɗan rawa ya ce “Dad!” Dad ya ce “Yes sweetheart, go on” Abraham ya sake haɗe fuska yaƙi kallon mutumin dake ta Kallonsa ya ce “Dad! She’s my girlfriend, ita ina so, ni ne zan aureta” Ya yi shiru, ya ƙara haɗe fuska a dole baya son raini musamman ganin yadda Dad ɗin nasa yake ta Kallonsa yana murmushi ya ce “Plx Dad I’m begging u ban so na rasata, Dad I’m matured enough” Dad ya ce “You’re too young dear, ba zan bari ba, babba dalili Musulma ce, kai yaro ne baka isa aure ba” A fusace Abraham ya kalli Dad ɗin idanunsa har ruwa yake ya ƙara tarwatsa wani Glasses ɗin ya ce “I’m matured enough” Dad ya ce “ABRAHAM u’re not, kai yaro ne, baka ka kai ka riƙe mace ba, baka kai ka riƙe gida ba, ba kai ka zama mijin wata ba, watan ma wacce take older than you” Dad ya girgiza kai yana murmushi tare da ɗauke kai zafin zuciyar ɗan nasa na bashi mmki ya ce “And the worst part of it har yanzu u’re dependant” Cikin zafin rai sosai kamar zai daki Dad ɗin nasa ya ce “Dad, I’m not dependant; Allow me to from convert from Islam, na auri ƴar madara” Dad ya ce “Ahh ƴar suger, baka isa riƙe mata ba” Abraham ya ce “Na isa, ka bani dama na aureta in 9mnts za kaga ta bani babies bama ɗaya ba, zan iya riƙe mata” Mutumin dai kallon Abraham kawai yake. Dad ya girgiza kai yana haɗa rai shi ma nasa zuciyar ya motsa ya ce “Ka tashi ka bani guri kafin na saka Escorts kulle mini kai, har yanzu kai yaro ne baka shige a raineka ba, u’re still young” Wani irin kallon Dad ɗin Abraham yake yama kasa ce masa komai me ya sa Dad ɗinsa baya son farin cikinsa ne? A hankali ya ce “I’m not a kid anymore, ka yi mini aure kaga idan ban ma jee ƴar madara ciki ba…
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: _*Arewabooks@Nimcyluv*_
*MIJIN MALAMA*
BOOK 2 PAGE 51
Kukan ta ya shiga ratsa dukkan wata jijiya dake kan His Excellency Abu-turab zuwa tsakiyar ƙwaƙwalwar shi, me ya sa ta kuka har haka? Bata son shi ne ko yaya? Ko kuma kukan farin ciki ne ta same shi a matsayin mijinta? He couldn’t understand why she was crying, deep down na zuciyarsa yana jin faɗuwar gaba. A hankali ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake parlourn ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, ya jima nan zaune He was thinking about where to start?? Ya miƙe yana gyara zaman babbar rigarsa ya nufi Main parlour ya samu Uncle Isma’il zaune shi da Jawaad ya zauna yana rusinawa ya ce “Sannu Uncle” Uncle I ya ce “Yawwa Ur Excellency, har ka fito? Fatan lafiya? Ta dai fito ko?” Ya jinjina kai cikin nutsuwa ya ce “Eh, daman nace yanzu zamu ta fi ne?” Uncle I ya girgiza kai ya ce “To ni dai san samu ka tafi da matarka, tunda babu amfanin wani zaman tana ƙarƙashin ikonka a yanzu, to amma kasan bidia’a irin ta mata yanzu sai ka ji wannan surutu, kuma ni ma a karan kai na ina son sai mun zuba mata furnitures ɗin ta da komai ai ba a kai ta haka ba” His Excellency ya ɗan kalli Uncle I can ya ce
“No need Uncle,I have fixed the part where she will sit, added new furniture’s that was ordered from Turkey” Uncle Isma’il ya yi jim sai kuma ya girgiza kai ya ce “I don’t think that would be possible, gwara dai ka bari akai mata na iyayenta wanda za mu yi, daman ai responsibility ɗin mu ne” His Excellency kallon Uncle I kawai yake bai san yadda zai masa bayani ya fahimta ba. Ganin hakan yasa Anti data fito daga bedroom ta nemi waje ta zauna tana ɗan murmushi ta ce “Ba aikin lada zamu hanaka ba, kasan mu mata muna da gutsiri tsoma, ina tsoran watarana a goranta mata rashin kayan ɗakin ace kai ka yi mata komai” A hankali Abuturab ya ce “Haba Anti, ko ban auri Majeederh ba zan mata komai, plx na yi niyya” Ta girgiza kai ta ce “Baka san mata ba ne Ur Excellency, musamman dangin miji kaɗan daga cikin halinmu ne gori” Ya lumshe idanunsa ya buɗe calmly ya ce “Oh, a bari na tafi da ita, after that sai ku kawo mata tunda kun matsa” Uncle Isma’il ya ce “Better, hankalina sai ya fi kwanciya da hakan” Anti ta ce “Amma kayi mana alfarma, ko zuwa Magriba ne sai ka dawo ku tafi not now” Abuturab ya ce “if you are more comfortable with that, Allah ya kaimu” Ya miƙe tsaye Uncle Isma’il ma ya miƙe suna haɗa hannu ya ce “Thank you, Uncle”
Daga nan ya fita yana rufe Idanu, sbd daman bai gama warkewa ba ya matsa dole sai ya zo. Tun kafin ya ƙarasu P.a Hammad dake tsaye shi da Jawaad suna hira zaka ɗauka abokai ne, sbd Hammad he’s so funny and nice person friendly to everyone. Driver ya buɗewa His Excellency Abu-turab back seat ya shiga ya zauna, Hammad ya ce “Jawaad see you soon” Ya ce “Ok Dear bye” driver yaja motar bayan Hamma ya shiga gaba, slowly suke tafiya bisa umarnin Abuturab ɗin.
Majeederh har yanzu tana zaune bakin ƙofa, tana jin kamar bata kyautawa Abuturab ba na rufe ƙofar da ta yi amma gabaɗaya she’s Uncomfortable da shi, zuciyarta ta kasa ganinsa matsayin mijinta na sunna, what should I do?“ Think, Majeederh”
Zuciyarta ta bata amsa, ta ƙara sunkuyar da kanta kamar ƙaramar yarinyar, her heart broke, she hugged her knees even righter. Nothing hurts like they words, maganganun mutane da surutun su akanta suke damunta, taya zata ya fewa Abraham? Duk duniya ta tsane shi wallahi bata ko ƙaunar jin sunan shi balle sake ganin mai kama da shi. Kukan Baby Khalil ya sanya ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi inda yake tana zuwa ta ɗauke shi, haka kurum ta samu kanta da ƙura masa idanu, wani kyakkyawan bugu zuciyarta tayi sbd wani mahaukacin kama da yake sake yi da Abraham, ya juye sak Abraham komai da komai musamman yadda yake tsotsar lip’s ɗinsa da saurin kwaɓe fuska, tayi saurin rufe Idanunta,tare da rungume Baby Khalil a hankali ta ce “Allah ya isa, ba zaka taɓa ganin daidai ba a rayuwarka, Ubangiji ya rusa maka farin cikinka kamar yadda ka rusa nawa, Allah ya hanaka kwanciyar hankalin kamar ka hana nawa kwanciya Ubangiji ya raba ka da iyayen…,” Anti data murɗa ƙofa ta shigowa da spare key ɗin dake hannunta tayi saurin cewa “Subuhanallah! Ya isa haka” Kalmar da ta tsayar da Majeederh daga mummunar addu’ar da take akan Abraham. Ta nemi waje ta zauna idanunta akan Baby Khalil tana ƙara ganin kammminsa da Abraham ɗin kafin ta ce “Why? Wannan muguwar addu’ar ta mece Majeederh?” A hankali ta ce “Ya rusa mini rayuwa Anti” Anti ta girgiza kai kawai kafin ta sauke numfashi ta ce “Idan Abraham ya lalace still ke ya lalacewa tunda uban ɗan ki ne khalil, kina ganin yadda suke muguwar kama” Majeederh ta haɗe fuska tare da yin ƙasa da kanta. Anti ta ɗora da cewa “Bai kyauta, bai kyauta, bai kyauta amma hakan baya nufin ki yi mummunan alkaba’i akan shi, idan ki ka ce kin barsa da Allah kaɗai ya wadatar, wlh duk wanda ya buɗe baki ya ce ya barka da Allah to mutum ya shiga uku, no need ki yi wannan addu’ar ko dan Khalil ɗan ki plx, Majeederh ke malama ce kin fi kowa sanin me ya dace da wanda bai dace ba, Majeederh Ubangiji ne ya amshi addu’armu ya dubi halin da kike ciki ya haɗaki da miji na kece raini, kaf familyn Khan! Babu wanda ya yi dace da miji irin naki” Ta ɗan yi shiru tana ƙara girgiza ƙafa ta ce “Wlh yanzu baki da wanda ya shige Abuturab, yana son ki sosai Majeederh ki yi ƙoƙarin kyautata mu’amalar ki da mijinki, ki duba yadda idanun duniya ke kan ki ko? Kada ki yarda ki bada wata ƙofa da zaku samu matsala da mai gidanki yanzu shi yake da iko akan ki, yi na yi bari na bari, ki riƙe uwar mijinki hannu bibbiyu da sauran dangin miji, babu ruwanki da kowa balle a ƙara saka mini wani tension ɗin kizo jininki yana mugun hawa zuciyarki ta buga a iska, ƙaddarar data same ki ita take ta trending a duniya kiji na faɗa miki bawai iya Kano ko Nigeria ba, da kin shiga Google ki Twitter za kiga shi ne the most trending news” Gaban Majeederh ya faɗi ta runtse Idanunta, ita kam taya zata daina tsinewa Abraham? Babban takaicinta wai ɗan cikinta shi ne yaga tsaraicinta? Ya yi mata Fyaɗe ya tuzarta ta a idanun duniya shikenan yaga komai da komai nata duk irin killace jikinta da take, takaici ya sanya ta ƙara runtse Idanunta ta nemi hawaye ta rasa. Anti ta ce “Kuma da kike ta tsinewa Abraham akan me? Sbd baki yadda ƙaddara ba? Kada ki tsawaita ƙiyayyarki akan shi domin abin da ka tsana watarana shi kakewa mugun son da ba zaka iya controlling kanka ba,I am advising you as a mother and not your uncle’s wife, ko da wasa kada ki faɗawa kowa matsalarki sai wanda kika yarda da shi, Abuturab ɗin nan ya fi Abbu a wajanki, Abbu ya kureki shi ya amsheki hannu bibbiyu da ƙaddara data faɗa miki yanzu ne lokacin daya dace ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa da mijinki Majeederh” Ita dai Majeederh was speckless ta kasa cewa komai. A hankali ta ce “Anti Abbu ya tsine mini, kada na lalace” Anti ta girgiza kai ta ce “A’a in sha Allah ba zamu ga wannan rana ba, zai sakko ne, naso Abuturab ɗin ya bari an ɗan gyaraki amma ina, ko arba’in ma kiyi sai ki tare” Da wani irin sauri ta ce “Kamar bani da gata Anti? Yau ɗin nan zan wani bisa” Anti ta ce “Hakan ma ce Allahamdulillah, gata kowa kina da shi gaba da baya” Tana faɗin hakan ta miƙe bayan ta amshi Khalil daya koma bacci tana cewa “a sauya masa suna, uba Khalil ɗa Khalil?” Majeederh ta haɗe rai ta ce “Uwa kawai yake dashi” Anti bata sake cewa komai ba ta fice daga bedroom ɗin. Grandpa na zaune a parlour shi da wasu manyan mutane, ya ɗaga kai a hankali idanunsa ya sauka akan Abraham dake tsaye kamar kurarre ya zubawa gefe ɗaya jirkitattun idanunsa wanda sukai wani kala. Grandpa ya kalli mutanen ya ce “This discussion has come to an end. We will meet tomorrow morning at the office” Suka miƙe tare da kwasar ducoments sukai waje, Grandpa ya miƙe yana isa inda Abraham ke tsaye frm head to toe yake kallonsa ganin gabaɗaya ya sauya kamar bashi ba, ya yi sanyi ba zafin ran nan, shi ya ɗauka da gaske ya samu matsala a ƙwaƙwalwar shi, shi ya sa bada shawarar kai shi can asibitin mahaukata ashe depression ne kawai. Zai kama hannunsa ya ji ya ce “I want a plane that leaves in an hour to Germany” Grandpa ya yi murmushi, so Finally ya haƙura da Majeederh kenan? Ya haƙura da auren Mamin tasa? Ya ce “Right now my grandson” Wayarsa ya ɗauka ya yi danne-danne na wasu daƙiƙo kafin ya ce “Done, nan da 30 minutes jirgin zai tashi daman” Abraham bai kula Grandpa ɗin nasa ba ya nufi upstairs kai tsaye, Grandpa na zaune ya ganshi ya fito cikin sabuwar shiga nrml shiga ya yi ba wacce ya saba ba, Camouflage-print cargo trousers da Gymashark sports t.shirt kansa na nan a hargitse har gefen goshinsa duk ya cukurkuɗe amma hakan bai hana wani irin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious fita daga jikinsa ba, ya shiga sakkowa daga upstairs ɗin fuska kamar ya ce ya shiga uku, hannunsa zube cikin Aljihu sai ka ɗauka wani babban mutum ne he just 20yrs ko gama rufata bai ba. “Ka shirya tafiya wajan Denial kenan?” Ya yi masa banza, murmushi Grandpa ya yi tare da miƙewa yabi bayansa, back seat suka shiga bakiɗaya driver ya jasu zuwa airport sai da sukai nisa ya ce “Grandpa” Ya ce “Yes dear” Ya ɗan yatsuna fuska sosai ya ɗauki seconds bai ce komai ba sai da sukai nisa sosai ya ce “About the Gang team, Where’s Taj?” Grandpa ya yi shiru sai kuma ya watsa hannu yana ɗaga shoulder’s ya ce “I don’t know where he is, after you left the country, the Gang team was gone” Abraham ya yi shiru yana buƙatar ganin Taj, ya ji ina yakai al’ƙawarin da ya yi masa na wasiƙa? Ina yakai envelope ɗin? Har suka isa airport Abraham bai sake ko buɗe ido ba balle magana, suna isa jirgin na shirin rufe ƙofa bai tsaya jin me Grandpa zai faɗa ba, da sauri sauri ya shiga taka steps ɗin benen har ya shiga yana shiga ƙofa ya rufe, Grandpa ya yi murmushi yasan Abraham fushi yake da shi, yana kuma fatan this time around ya samu daidaito da mahaifinsa Denial. Yana tsaye har jirgin ya tashi kana ya shiga mota yabar wajan shi ma… Maman Alpha ce zaune ita da Anti sai Yaya Bilkisu a hankali ta ce “Daman komai ya yi farko yana da ƙarshe, gwara Majeederh muna ganinta munga Irin ƙaddarar daya faɗa mata,amma ɗan uwanta ba? Babu wanda yasan duniyar da Alpha ya shiga” Ta faɗa cike da damuwa. Yaya Bilkisu ta ce “Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawan daya zalunci kansa da kansa, Allah kuma baya ɗorawa bawa abinda ba zai iya da shi ba, sai dai bawa ya ribaci ƙaddarar daya jawa kansa, mu duka muna addu’ar Ubangiji ya dawo da hankalin Alpha zuwa gida kullum da shi nake kwana nake tashi ki duba shekara nawa yanzu?” Maman Alpha ta yi shiru tana wani irin murmushin takaici Anti ta ce “Haka ne, In sha Allah yana nan lafiya ma” Kafin su yi magana suka ji sallama da mamaki Anti ke kallon Latifa Omar wacce ta shigo ɗauke da damuwa bayan sun gaisa ta ce “Anti don Allah ku yi haƙuri dan gane da reported ɗin da na yi a gidan jarida, raina ne ya ɓaci duk yadda na yarda da Majeederh nake kareta a gaban jama’a da iyayenmu amma hakan bai hana taci amanata ba, na ɗauka Majeederh tana sane da cikin jikinta ta rufe ni shi yasa raina ya ɓaci, Apparently I a made misunderstanding, without stopping to research the matter, ku yi haƙuri plx” Yaya Bilkisu ta ce “Allahamdulillah, tunda kin gane kuskure ne, kuma ke ɗin aminiyya ce ta gari ga Majeederh” Ta ƙara basu haƙuri kafin ta shige bedroom ɗin da Majeederh take ciki. Ta sameta zaune riƙe da Baby Khalil da idanunsa yake buɗe ta ƙura masa idanu, tayi murmushi ta ce “Mai jego” Majeederd dai bata ce komai, Latifa ta shiga bawa Majeederh haƙura Exlty yadda ta bawa su Anti hadda kukanta, ganin Majeederh bata ce komai ba ta ce “Plxx Bestie let by gones be by gones sharrin shaiɗan ne” A hankali tana rufe ido ta ce “No bad” Tana jin a ranta tabbas sharrin shaiɗan ɗin ne, tunda ta yarda da Latifa ita ɗin ƙawar arziƙi ce wacce samun kamarta zai wahala musamman idan ta tuna har mijinta ta bata opportunity na aura, ta ƙara lumshe idanunta damuwarta biyu ce a yanzu yadda abu ya tsine nata ya kureta kuma ya cireta daga cikin yaran daya haifa ya sadaukarwa da duniya ita yafi komai ɗaga mata hankali, idan ta tuna wai little ɗan data raina da hannunta shi ne ya yaga rigar mutuncinta sai ta ji zuciyarta ta mata nauyi bata jin daɗin komai a duniyar, tana fatan mutuwarta ta risketa amma da alama kamar yanzu ta saka hannu a fata na rayuwa, suna ɗaki su Anti kuma na parlour suna jiran har dare ya yi Abuturab ya zo tafiya da matarsa…. Zaune take tayi wani irin zama kamar zatai sujjada ta yafa wani jan mayafi akanta, mutumin dake gabanta ya ce “Ke la’ananniyya ce, ke muguwa ce, yake azzaluma me kuma ya kawo ki yanzu bayan sharaɗin da nayi miki?” Ta ƙara sunkuyar da kai tana shakkar haɗa idanu da mutumin sbd muninsa bakinsa har wani hayaƙi yake ta ce “Kamar yadda ka sani tun farkon zuwana wajanka akan Aminiyyata ne, ta hannun damana, bana buƙatar duk wani cigaban ta tunda na fahimci ta fini komai na rayuwar duniya, tana da kyau tun muna raya ta tashi da farin jini duk da baa ganin fuskarta, wannan dalilin yasa na da ƙushe wannan farin jinin nata, danginta na sonta tana kare mutuncinta, ta fini ilimi nesa ba kusa ba, har tazo taci gasar Kur’ani ta duniya, na mayar da ita mujiya a wajan maza, ban san tana da ciki ba kai ne ka fara ankarar dani, a sanda na koma gida bayan na bar nan sai dana kashe dubu ɗari biyu na maganin da zai zubu mata da jinin al’ada duk dan kada ta gane, sannan ka ƙara yin aiki da jinin zai dinga fita duk wata, kai ne ka sanya Aljanu kwantar da jiki, kuma kai ne kasa Aljanu suka tashi cikin kuma suka haɗa ɗan cikin motsi duk da yana cikin ƙoshin lafiya, kai ne ka hana likita ganin cikin Majeederh, kullum results zai nuna she’s good….” Da sauri mutumin ya ce “Tsinanniyya la’ananniyya dai na yi mana turanci a nan ko na turɓuɗeki ki zama toka ko ɗan akuya” Jikinta na rawa ta kwaso wata ashar ta maka alamar ban haƙuri ta ce “Kuma ni na ƙara rura wutar son da takewa Abraham har take sake masa jikinta, kada ka manta kafin aikin yanan ya ci sai dana zubar da ɗan cikina babu adadi, kai ne ka sanya na fara bin mata ƴan uwana sbd duk aikin da kake mini akan rusa rayuwar Majeederh, kai ne kace na sanya mijina ya aureta yadda zan fi jin daɗin durƙosar da rayuwarta kai ne….,” Ya yi saurin dakatar da ita da faɗin “To cikakkiyar azzaluma Ubangiji ba zai barki ba, lallai zaki girmi abinda kika shuka yanzu na haka wani cikin ne dake gashi nan ina Kallonsa a ƙasan mararki kuma ya zama dole ki zubar da shi” Gaban Latifa ya faɗi ta sha cikinta tana lumshe idanu ta ce “Zan zubar idan zaka mini abinda nake so” Ya ce “Bayan mugwayen abubuwan da kikai mata me kike buƙata yanzu?” Ta ce “Kada ka taɓa bari Abuturab ya kusance ta balle ta haihuwa har ɗan ya samu gadu, kada ma su haɗa gado har abada sannan ina son sanin waye MIJIN MALAMA na gaske??
Littafin mijin malama na kuɗi ne. Ka biya ka karanta hankali kwance rubuta zan yi a nutse ba skipping yadda za ku ji daɗi har a fara zuba love soon☺️☺️☺️08119237616
*Aunty Zee MOM MUJAHID KATSINA*
*08162859027*
*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYIN KASHI CIWON BAYA CIWON KAFA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA WARIN GABA KURAJEN GABA KURAJEN JIKI KAIKAYIN JIKI RASHIN HAIHUWA BASUR MAI TSIRO CIKIN IKON ALLAH ZAIMAGANCE MAKI/MAKA ZAKIJI DADIN MAGANIN SANYINNAN SOSAI A BANGAREN GYARAN AURE BA A MAGANA DAN ZAI SAUKAR MAKI DA NI IMA ZAKI JI SHA AWA KODA SHA AWARKI TA DAUKE ZATA DAWO KIJI KE KIKE MARMARIN ABAR KEDAI KINEMI AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
4k
*MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA* *JIKINKI NONUWA ZASU CIKO SOSAI ANMA BANCE ZASU TSAYABA WANNAN MAGANI ANGWADA ANDACE HANZARTA KI MALLAKI NAKI YAR UWA 8K*
*TAREDA MAGANIN CIRE TUMBI DUK INDA KIKAI KAMAR KIN KUSA HAIHUWA AITA TAMBAYAR KI WATA NAWA IDAN KINSHIGA MATE KIZAMA KAMAR BABARSU DAN ALLAH KIZO KIJARABA 7k *INA AIKAYA KOWANI GARI DA YARDAR ALLAH INBAKI SHIRYA BA KIBARI KI SHIRYA SAI KUNZO NAGODE KAYAN* *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
*KI TUNTUBENI A WANNAN LAYIN*
*08162859027*