Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 2

Sponsored Links

[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Latifa was shock and speechless tayi zuru tana kallon Intisar da Haseena , sai kuma ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Kuna ganin hakan babu matsala?” Intisar ta ce “Mene abin matsala? Rama mugunta ga macuci ai halak ne, ni naga ƙoƙarin yadda kika ci-gaba da zama da ita duk da cin amanar da tayi miki ki sameta turmi da taɓarya da mijinki? Tab ai wallahi ni zuciyata bugawa zatai kuma In sha Allah sai auren nan ya mutu murus na aure His Excellency, haka kurum an ƙaƙaba masa masifa da bala’i” Latifa Omar ta ce “Haka ne, shi ya sa na faɗa muku domin ku iya zama da ita, akwai ta da shiga rai Ubangiji ya mata baiwar farin jini kuma ni na daƙushe shi” Murmushi Hassenatou kawai ta yi kana sukai exchange na Digits suka shige mota daman shopping za su a shoprite.
Aaliyyah sukai clashing da Latifa ta bita da idanu trying to understand her situation, sai kuma ta ce “Na fito naga ba ke ba Anti Jeederh” Latifa Omar ta ɗan yi murmushi ta ce “Wajan marasa kunyar can naje danni bana ɗaukan raini yanzu zan haɗawa mutum jini da majina” Aaliyyah ta buɗe baki da mamaki domin bata gama fahimta ba, ta ce “Allah ya kyauta ga lunch ɗin an kammala yana dining area” Latifa ta ce “Anya?”
“I’m full ci kawai” tana faɗin hakan ta nufi bedroom ɗin Majeederh ta sameta zaune ta yi wa Baby Khalil wasa tuni ta mance da abinda ya faru, daman tana shigowa ɗaki suratul yasin ta karanta da addu’ar yaye damuwa da ƙunci sai ta ji zuciyarta fes. “a’a, babu ko kunya ɗan fari ne fa” Majeederh ta mata shiru ta ce “Na bi waɗancan tsageran, ni i can’t take it wlh i hate nonsense” Majeederh ta zubawa Latifa sexcy eyes ɗinta ta ce “To ribar me kika ci?” Ta ɗaga shoulder’s ta ce “A’a ba batun cin riba bane, ni bana ƙaunar baka fini da komai ba kace zaka ɗaga mini kai sai naci uban mutum sarai, ni na fi so always ace ni ce a gaba idan ina mu’amala da mutum” Majeederh ta jinjina kai da ɗan yin baya ta ce “Kowa watarana zuciyarki zata buga, You will have a heart attack one day, ki dinga nightmares da kala-kala” Latifa ta kalli Majeederh kawai ta ce “Ai na gyara musu zama” A hankali majeederh na miƙewa ta ce “Kina haƙuri da rayuwa, watarana za kiga ribar hakan” Latifa ta taɓe baki ta ce “Ni dai ba wannan ba zan kira Barrister ki lallaɓa mini shi” Tana faɗin hakan ta ɗauki wayarta tare da kiran number Aliyu sai da tayi kira uku kafin ya ɗauka tun kafin ya yi magana ta bawa Majeederh wayar tare da ɗaukan Baby Khalil tayi waje abinta. Majeederh ta dinga kallon wayarsa cike da fargaba da zullumi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ita bata ma san mene zata ce masa ba. Aliyu jin shiru ya sa ya ce “Hello?” Ta sauke ajjiyar zuciya kafin tayi magana ta ji ya ce “Hawwa’u” A hankali ta ce “Let by gone be by gones Aliyu, ku zauna lafiya da Latifa please” ya tari numfashinta da cewa “Untill when you’re my side Hawwa’u shin ban cancanci zama mijinki bane? Ni ba irin mijin da kike addu’a Allah ya kawo miki bane?” Ya yi ƙasa da murya ya ce “Think Hawwa’u, i love you i so much loves u” ta kasa cewa komai sai bakinta dake rawa wai yau ita ake cewa i love you sai taji kalmar bata birgeta bata ɗaɗata da ƙasa. Latifa na fita ta zauna saman kujera babu jimawa ta ji ƙamshin perfume Dolce and gabbana tana juyawa suka haɗa idanu da Latifa ta ce “Sannu da zuwa” Ya ɗan faɗaɗa fuskar shi ya ce “Kina lafiya?” Ta ce “Allhamd” Ya juya idanunsa sai kuma ya yi jim ya ce “Yake ɗaya?” Ta ɗan yi murmushi ta ce “Eh ta ɗan ari wayata ne zatai kira, kuma naga tana buƙatar privacy that’s why i am here” ya ce “Oh” Ya nufi bedroom ɗin nata tsaye ya yi cak lokacin da ya ji Majeederh na cewa “U misunderstanding Aliyu, i am married now” Ta cikin wayar Aliyu ya yi wata dariya ta kin raina mini hankali ya ce “Funny, stop kidding me dear ko dana bar gidanku ciwo ya kwantar dani sosai shi ya sa ban dawo ba amma yanzu haka kin san zan zo na ganki ki jira zuwana i on my way” Da sauri ta ce “Aliyu listen, listing to me….” Ta kasa ƙarasa maganar sbd shadow ɗin data gani ta juya da sauri idanunta ya sauka akan His Excellency dake tsaye kamar an dasa shi idanunsa jajur ta kasa cewa komai kanta a ƙasa ya taka har zuwa ida take yana kallonta kafin ya ce “Kin riga da kin saba, kuma ki ɗauke wannan shegen ɗan ki fitar da shi daga cikin gidan nan, You really disappointed me Jiddo, kin san lokacin dana ɗauka ina son ki? Lokacin dana samu labarin kin haihuwa bai iya bacci ba, wani ya sameki bani ba duk da haka na jure na yi accepted naki da ƙaddarar ki ashe i was mistaken, duk wanda ya saba zina ba zai iya dainawa ba, yanzu sbd kinga bana kulaki ban taɓa sauke hakƙin ki dake kaina ba shi yasa ki yi deciding kiran mazinacin naki ko?” Jikinta ya ɗauki rawa da ƙyarma idanunta a kansa ko ƙiftawa ba tayi ta ce “U misunderstanding, baka haka bane Lati…..” Hannu yasa ya zabga mata mari ya ƙara zabga mata mari ya ce “Bana magana ana katse mini numfashi, wannan dalilin yasa na amshe wayarki shi ne kika amshi da ƙawarki? Jiddo zina da aurenki?” Tunda ya mareta ta riƙe fuskarta ta kasa motsi yatsunsa ya fito kwance a fuskarta ta juya zata bar wajan ya saka hannu ya dawo da ita baya a hankali ta ce “Cika mini hannu Abuturab” Ya buɗe baki ya ce “Abuturab?” Ta kalle shi idanunta cike da hawaye ta ce “Ba Sunanka bane? Wannan dalilin yasa na ce ba zan aure ba, na yi zaton da gaske sbd Allah ka auri da kuma so na da kake amma nayi ganganci ba kuma laifinka bane, na iyayena da suka baka ni, baka da tabbaci ina zina ko bana yi, kuma ka sani aure da zargi haramun ne kana ƙoƙarin datse igiyar aurenka dake kai na, na yi zaton ana samun farin ciki da aure amma shi ma na yi kuskuren fahimta, Sunanka na mijina sai na yi sati ban saka ka a Idanuna ba, baka san ya nake ba” Hawaye kawai take sosai ta ce “hakkin ka kuma maybe you’re not interested, daman ba dan Allah kake so na kawai sha’awata kake” Ya buɗe idanu ya ce “Ni kike faɗawa haka?” Ta ce “Bani na faɗa ba, fassarar abinda ka faɗa ne, har gobe zan ci gaba da yi maka biyayya whether you like it or not” Tana faɗin hakan tabar wajan tare da shigewa bathroom ya jima yana bin ƙofar da kallo, he don’t even know what comes over him yana abu madly ya juya yabar wajan… Da daddare Majeederh ta kasa bacci juyi kawai take, Abuturab ya riga daya saba mata da maganin da yake ba, ta rufe idanu nan ma ta kasa ta miƙe tsaye taga wajan 2:34 ta ɗauki hijabi ta saka ta nufi part ɗinsa luckily taji ƙofar a buɗe tana shiga ta same shi zaune yana operating system sai tea dake gefensa bai kalleta ba ya ce “why are you here? Hakƙin naki kika biyo amsa?” Ta yi masa banza ya ce “Oh, i can relate ki je kawai Jiddo if i need something, I’ll call” Calmly ta ce “Medicine” Da sauri ya kalleta tana ɗauke idanu ta ce “Na kasa bacci, i couldn’t sleep” Ya miƙe tare da shigewa wani ɗan corridor kamar bedroom ba jimawa ya dawo hannunsa riƙe da kwalba bayan ya yage takaddar jiki ya bata tana amsa ta shanye tas tare da dropping empty ta juya ya bita da kallo deep down na zuciyarsa yana tunanin wani abu. A duk sanda ta sha maganin she just immediately forget everything, more especially her father and his bads words, she just realized baccin da take yasa take jin sauƙin zuciyarta. Cikin ikon Allah kiran sallar farko ya farkar da ita bakinta ɗauke da addu’ar tashi daga bacci, idanunta sun yi jajur sbd baccin bai gama sakinta ba da ƙyar ta miƙe tare da sakarwa kanta shower tai wanka sosai ta ɗaura alwala raka’atul fjr tayi kafin ayi sallar asuba ta jima tana addu’ar neman ɗaukin Ubangiji,idan aurenta da Abuturab alheri ne Ubangiji ya daidaita tsakanin su idan ba alheri bane Ubangiji ya zaɓa mata abin da yafi zama alheri ga rayuwarta, ita ɗin me biyya ce ga dukkan wata Jarrabawar Ubangiji a kanta. A hankali ta ɗaga hannunta sama idanunta na zubar da hawaye ta buɗe zuciyarta sosai ta samu kaɗaici da mahaliccinta cikin siririyar muryarta ta ce.

“(Allah) Abin bautana! Ta yaya ba zan kira ka ba alhali nifa nice baiwa ƙasƙantaciyya? Kuma ta yaya zan yanke tsammani daga gare ka alhali kaifa kai ne Allah mai iko? Abin bautana! Idan har ban roƙe ka ka bani ba, to, wa kuma zan roƙa koma bayanka ya ba ni?Abin bautana! Idan har ban kira ka ka amsa min ba, to, wa kuma zan kira koma bayanka ya amsa min? Abin bautana! Idan har ban ƙasƙantar da kaina gare ka don girma da isarka ka tausaya mini ba, to, ga wa kuma zan ƙasƙantar da kaina gare shi koma bayanka wanda zai tausaya mini?” Wani irin kukan zuci take tana ƙara buɗe zuciyarta sosai da faɗawa Ubangiji damuwarta ta ɗora da. “Abin bautana! Kamar yadda ka keta/tsaga Teku ga Musa aminci ya tabbata a gare shi yayin da Fir’auna ya bi shi ka tseratar da shi, to, nima ina roƙonka da kayi salati ga Muhammadu da Iyalansa, kuma ka tseratar dani daga abinda nake cikinsa na damuwa da ƙunci,kuma ka yaye min shi cikin gaggawa ba bisa jinkiri ba, domin falalarka da tausayawarka ba don halina ba yaa mafi tausayin masu tausayi, Allah ka zama mini mafi daidai, Ubangiji yafe mini bisa laifin sani dana rashin sani, Ubangiji kada ka hukuntani bisa zunuban wasunmu, Asstagafirullah yaa Allah! Ni Hawwa’u na zo gareka da ƙoƙon barata ka taƙaita mini ƙaddarorin idan ina da rabon farin ciki kafin mutuwata ta riskeni ka sadani da shi, daga yanzu zuwa ko yaushe duk yadda kayi da rayuwarta na amsa bani haufi domin ka fini iko da ita yaa Allah!” Tana gamawa ta shafa a hankali ta ji nutsuwa na saukar mata wacce ta daɗe bata ji irinta ba, ta ƙara yadda babu abinda yakai Kaɗaita da Ubangiji daɗi da kuma imani da shi, idan ta tuna yadda Annabawan Allah suka tsinci kansu sai ta ji ita babu abinda yake a sameta na daga ƙaddara domin sun fita sanin Ubangiji da riƙe addini amma a haka Allah ya yi ta jarabtar su….. Washegari ta shirya sosai cikin abaya kamar ko yaushe fuskarta fresh ba baƙin ciki ba farin ciki ta nufi part ɗin Abuturab tana zuwa taga baya nan sai ta dawo parlour ta zauna watching sunna t.v tunanin Abbu tuni ya kau a ranta…
Germany.
Abraham na zaune a haɗaɗɗan parlourn shi yana drawing kamar yadda ya saba shi kaɗai yake ɗauke masa damuwa riga ce fara a jikinsa wacce ta kama faffaɗan ƙirjinsa Sleeveless jersey tank top sai wani trousers iya laps ɗinsa ga wasu gargasa da sukai kwance luf saman dark skin ɗinsa, kamar kullum sumarsa a curkuɗe ya saka wata red ɗin bandana saman goshinsa wacce ta tare sumar ta kwanto a gefen goshin nasa zuwa wajan kunne ga farin bluetooth dake kunnenshi, sassanyan ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious na tashi a jikinsa. Slowly ya lumshe sexy eyes ɗinsa hannunsa riƙe da water colours da wani ɗan ƙaramin pen yana using dashi wajan zanen, idan ya lumshe idanu sai ya buɗe yana tuna yadda zanen su da shap ɗin idanunta yadda suke. Knocking aka shiga yi a karo na uku ya yi banza jin kamar za a ɓalla door ya sa shortly ya ce “In”
Aka murɗa handle ɗin tare da shigowa. “Hi” Ta faɗa tana ɗaga masa hannu, ya ware idanu kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, it’s a girl ba zata shige 12 yrs ba, tana da tsayi da jiki irin nasu na ajeboters bata da fara ce tas idanunta mitsi-mitsi amma tana da kyau mai sanyi idan an kula. Ganin yaƙi cewa komai ta ce “My name is Zizi” Ya yi mata banza bama zaka ce yana jinta ba ta ce “Dad is looking for you” tana faɗin haka ta juya tsoransa fal zuciyarta. Ta samu Dad ɗin zaune da wata yarinyar itama kusan 12yrs take kamarta da Dad ya ɓaci sosai “Dad na yi masa magana for almost 3times, but he just ignored me” Dad ya ce “Ya jiki, zai fito” Ta ɓata rai sosai ya ce “Oh common Zizi, stop bothering yourself” Ta zauna a armchair tana saƙale wuyan Dad ɗin babu jimawa Abraham ya sakko yana haɗe fuska yadda yake tafiya majestic ɗai-ɗai zai ja hankalin mutum ya nemi waje ya zauna. Dad ya ce “greeted me first” Ya haɗe fuska calmly ya ce “Evening” Dad ɗin ya yi murmushi ya ce “Shi ne ka kulle kanka yau? Anywhy mu yi magana mai muhimmanci, let’s talk” Ya gyara zama ya ce “Me ya sa kake son musulunta?” Abraham ya yi shiru a hankali kuma ya ce “because Islam is the true religion, which we want to believe in,They believe that nothing can happen without Allah’s permission, but humans have free will. Islam teaches that Allah’s word was revealed to the prophet Muhammad through the angel Gabriel” Abraham ya gyara zama ya ce “Dad tun ina ƙarami ka sani, i love Islam shi ne yasa ka tsane ni ba, rayuwa da Jee da sauran Musulmai ya sa na fahimci addinin sosai, na ji na yarda dashi 💯 hundred patient, Dad idan suna cikin damuwa addu’a suke su yi karatu da holy book, Bible it’s an old version, jesus is already past, we believe yana nan bai mutum ba kuma zai dawo, amma shi ba kowa bane nace Annabin Allah bawai ɗan Allah ba, A duk sanda na ɗauki kuɗi na bada sadaƙa ina jin nutsuwa a raina, kuma You what Dad” Dad ɗin ya girgiza kai Abraham ya ce “Musulmai na da zuciya mai kyau, basu da gudun Christa’s ko kaɗan, ko bikin sallah sukai suna inviting namu, muma idan charismatic tayi muna inviting nasu, they most comes with a gifts, kaga Uncle ɗin Jee? Sunan da wahala Uncle I yana da yanayi mai kyau he was a charismatic figure with great appeal to the public” Ya ƙarasa maganar a wahale ya jima bai magana mai tsayinta ba. Dad ɗin ya ce “Zan barka ka musulunta son, zan barka if that you make you happy, but in one condition zuwa 2” Abraham ya ƙurawa Dad ɗin idanu yana jiran ya ji me zai ce masa. Ya ce “Idan ka amince zaka auri Debaka after you married your first love, idan ka amince zaka zauna dani muna kwana tare da yawo tare” Abraham ya yi shiru kawai Dad ya ce “About the night” Abraham ya he “Ban so” Dad ya ce “Kiristi is my wife son, matata ce not my whore” Ya nuna masa Zizi ya ce “Her name is Zizi ur younger sister, ga twinny ɗinta nan Badi, they’re my daughter’s tagwaye ne” Dad ya kalle su ya ce “Zizi, Badi meet your brother Abraham” suka miƙe da sauri suna zuwa suka faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi, Abraham was speckless ya kasa cewa komai…. Cikin dare Dad na kwance yana bacci ya ji an kwanta kusa da shi, a hankali kuma aka shige jikinsa murmushi kawai ya yi Abraham ya yi bacci sosai a jikin Dad a ransa yana jin he will neva ever accept Kiristi as his stepmom, haka suka kasance more than a weekes kafin Dad ya bawa Abraham damar musulunta, Abraham na zaune farin ciki sosai yake amma ya kasa nunawa so yake ya sauya ya zama babba mutum mai nagarta na gaban kwantace he just want to change completely, apple laptop ɗinsa ya ɗauka yana searching best imam in the world was the first abin da Google ya nuna masa shi ne Sheykh Ajlaal Sultaan Saudiyya’s King, second kuma shi ne Sheikh Aliyu haydar Aliyu, third kuma shi ne Sheikh Imam Hamdan Balarabe. Sune manyan malamai na duniya, ya dinga duba bayanan su Sheikh Aliyu nada mata Halisa da manyan yara Sheikh Imam yana da mata Fannah da yaransa kuma Sheykh mai martaba Ajlaal Sultaan kuma yana da mata Ƙhulud Arzaan da yara twins haka kurum ya ji ya gamsu da Ajlaal Sultaan ɗin a karo na farko zai je ƙasa mai tsarki zai amshi Shaahada wajan sarkin Makkah….

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button