Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 28

Sponsored Links

[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *_Arewabooks@Nimcyluv_*
_Follow my account_
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv
A rikice a cikin kuma tsakiyar daren sakaliyya gari ya yi shiru sai ƙarar kanaru da sauran tsuntsayen da suke makeken gidan na Dr Ibrahimul-khalil Abraham, ya ɗakko ta da hannunsa cikin hali na suma, yana jin ba zai iya yi mata komai ba, Despite the fact that he is a great gynecologist and psychiatrist amma kiɗimar da yake ciki na ganin Jee a halin da take da jinin dake zuba har yanzu yaƙi tsayawa, ga kiran da Uncle Isma’il ke masa babu ƙaƙƙautawa duk cikin tsakiyar daren ya sanya ba zai iya aiwatar da komai ba, ganin yadda Khalil ya taho da sauri ya sanya wani soja dake tsaye ƙyam! Kamar haka aka halicce shi ya yi saurin cewa “Oga do you need some help?” Ko inda yake Khalil bai kalla ba, ya shiga wata mota yana kiran driven sojan shi a gaggauce, ya zo da sauri lokacin tuni ya shige bayan motar yana ƙara rungume Jee gani yake kamar she will die and leave him, wannan ya ƙara bawa Khalil tsoro domin tabbas idan aka wayi gari babu Jee a duniya he most die, tunda shi ne ya zama silar mutuwar nata. Sai da suka ɗauki titi Driver ya ce “Oga ina muka nufa?” Khalil ya runtse idanuna ya ce “Aminu Kano teaching hospital” Ya faɗi hakan da ƙyar, hannunsa yana shafa sumar kanta, ganin kuma halin da Dr Ibrahimul-khalil yake ciki ya sanya driver take giyar motar yana wani irin azababben gudu kamar zasu bar garin, suna isa hospital ɗin Emergency suka amsheta Khalil da kansa ya rungume matarsa tare da ɗora ta gadon marasa lafiya aka nufi ciki da ita, gabaɗaya a birkice yake ya manta da yanayin shigar dake jikinsa, a hankali kuma ya ɗauki wayar Uncle Isma’il yana ɗagawa Uncle Isma’il ya yi magana, Khalil ya lumshe idanunsa muryarsa bata fita sosai ya ce “Ohk” Ta cikin wayar akai magana calmly Khalil ya ce “We are in the hospital, Uncle” yanayin yadda yake rausayar da kai ya sanya zaka fahimci Uncle ya ruɗe a taushashe Khalil ya ce “My wife is sick, she was admitted to the emergency room” Ya kuma cewa “Jee” Daga nan ya kashe wayar…. Washegari wajan 10 na safe a hankali yake tafiya cike da nutsuwa da kamalar dake kwance a jikinsa da kuma izzar daya ginu a kanta shekara da shekaru, sky blue ɗin shadda ce jikinsa wacce ya zauna masa ya ɗora hula jaddara sai ƙamshin turare yake bazawa, hannunsa zube cikin aljihu magana Jawaad ke masa amma baya fahimta slowly kawai yake jinjina masa kai, without even knowing what Jawaad say’s, a harabar emergency ɗin suka tsaya Jawaad na ƙoƙarin kiran Uncle Isma’il yaga sun fito shi da Uncle Bello har suka ƙaraso bayan sun gaisa Jawaad ya ce “Uncle ya jikin Anti Jeederh?” Uncle Isma’il ya ce “Allhamd, wai jini za a saka mata” Jawaad ya jinjina kai, har sun kai wanda suke tare da Jawaad bai ce komai ba wayarsa yake dannawa a hankali, Uncle Bello ya juya zuwa gefe ya kalli Khalil dake zaune a saman kujera tun ɗazu ya kuma fi awa a wajan ya ce “Khalil kaje ka yi wanka kaci abinci, she’ll be fine In sha Allah” Khalil ya kalli Uncle bai ce komai, domin ko kayan jikinsa da ƙyar yaje ya sauya ya dawo har yanzu kuma yaƙi faɗa musu komai da abinda ya sameta har tayi doguwar suma haka, baya fahimtar komai baya ganewa Uncle Isma’il ya ƙara cewa “Ibrahim ka je ka huta, kada wani abu ya sameka kai ma” Khalil ya sake ɗaga jajayen gajiyayyun idanunsa a taƙaice ya ce “My wife is sick, how can I get peace?” Sai a lokacin wanda ke tsaye tun shigowar shi emergency ɗin ya ɗaga kai ya kalli Khalil na wasu seconds yana ɗauke kansa gefe, Yaya Bilkisu ta ƙaraso hannunta riƙe da basket Jawaad ya nufeta da sauri yana amsa tare da gaisheta, su Uncle’s suka gaidata ta nemi waje ta zauna ta ce “Wallahi tallahi a gigice na ƙaraso hospital ɗin nan, hankalina ya gama tashi jin Hawwa’u ba lafiya gashi babu wani driver a gidan ni na tuƙa kai na, ina tafe ina tunani saura kaɗan na bige wani yaro” Uncle Isma’il ya ce “Ayya ina da kin yi zamanki yaya” Ta ce “Ba zan iya ba Isma’ila” A hankali ta ji an ce “Morning Yaya” Ta ɗaga kai tana murmushi ta ce “Sannu General ya jikin naka?” A sanyaye cikin riƙe fuska Alpha ya ce “Good” Yaya Bilkisu ta ce “Ai naga har yanzu baka gama dawowa daidai ba, gashi dai wajan kwana uku fa kusan huɗu da dawowar ka, kai Ubangiji ka ƙara yi mana katangar ƙarfe da dukkan wani azzalumi Ubangiji ya bi maka hakƙinka” Shi dai bai ce komai ba, babu alamar ma zai ce, ta juya kan Khalil da yake ta yatsuna fuska alamar hirar ta dame shi ta ce “Mijin Malama zo ga tea mai zafi na san baka ci komai ba” Ya zuba mata idanu bai ce komai ba, Uncle Isma’il ya ce “Alpha zauna mana kafin Dr ya fito ku shiga wajan nata a gaisa” Yaya Bilkisu ta ce “Majeederh ta san ɗan uwan nata ya dawo kuwa?” Uncle Isma’il ya ce “Ranar dinner ɗin su da Khalil ya dawo cikin dare fa kamar korarre, cikin ikon Allah kuma a hankalinsa abinda ya sanya ban faɗa mata ba kinga ai babu dacewar ta fito daga shigarta ɗakin miji, to shi ne jiya da daddare na kasa jurewa na kira na faɗa mata sai nake jin suna asibiti a time ɗin” Yaya Bilkisu ta ce “Allah sarki, Allah kaɗai yasan murnar da za tayi” Ta ƙara juyawa ta kalli Khalil daya miƙe zai bar wajan ta ce “Ga shayin” A hankali ya girgiza kai, sai a lokacin Khalil ya lura da General dake tsaye cike da kamala kallon juna sukai ba tare da sanin kai ba, Khalil bai san Alpha ba shi ma kuma Alpha bai san Khalil ba, domin ko lokacin da yake yaro suna samun saɓani idan Alpha yana gari to Khalil na orphanage wajan Akeeth, General Alpha ya miƙawa Khalil hannu alamar musabaha yana cewa “hi” kamar zai share kuma ya zaro waya tare da ɗauke idanunsa yana cewa “Sannu” Yana faɗin hakan ya juya yana ɗaga kiran ganin sunan Ajlaal Sultaan a hankali ya ce “When?” ya yi shiru sai ya ce “Zan zo airport ɗin” Yana faɗin hakan ya kashe wayar daidai nan Dr ya fito yana kallon Khalil fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce “Dr Ibrahim ya akai ka rikice jiya ne? Ka manta matsayinka na Dr” Khalil ya ɗan yatsuna fuska ya ce “Forget ya Madam take?” Ya ce “She is awake now” Khalil bai san time ɗin daya nufi room ɗin ba, Dr ya yi masa dariya ya ce “Zaku iya shiga kafin a gwada jinin wanda zai iya yi mata” Khalil ya kalleta taƙi yarda ta kalle shi idanunta sai hawaye yake musamman idan ta tuna kisses ɗin data gani ya kai hannu zai taɓa ta tayi saurin ce wa “Don’t you dare touch me Khalil” Ya kalleta jin yadda ta faɗi Khalil wanda kamar bai taɓa ji ta faɗa ba, tun sanda akai musu aure daga Abraham har Khalil ba abinda ta taɓa faɗa idan har ba mancewa ya yi ba, Cike da damuwa domin yasan koma mene shike da laifi ya cancanta da komai a hankali ya ce “Don’t hurt me” Tayi masa banza duk da wani irin tausayinsa da take ji a ranta, ya ɗora kansa akan pillow ɗin da kanta yake daidai kunnenta ya ce “I deserve to be punished” Ta juya tana zabga masa harara ya mannawa idanun nata kiss yana riƙe hannunta ya ce “U misunderstood everything Madam” Tayi shiru bata kula shi ba, a hankali kuma ta ji ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi ga cikinsa na ƙugi bata kalle shi ba ta ce “have you eaten?” Ya buɗe ido cike da rainin hankali ya ce “What?” Ta ce “Food” Ya lumshe idanunsa hannunsa ɗaya a cikinta yana shafawa cikin raɗa ya ce “No, maybe now” Ta juya ta kalle shi ya ɗaga mata gira ya ce “Kishin nan na jiya zan sauke hakƙin shi yanzu, you will be my food” Ta haɗe fuska ta ce “You’re not serious Khalil” Yana mata dariya ƙasa ƙasa while yana zagaye lip’s ɗinta ya ce “I knw Madam” kafin tayi magana taji saukar bakinsa a nata tayi saurin rufe Idanu tasan tunda ya fara zagaye bakinta haka ne zai biyo baya, He was gently kissing her lips, his breath falling on her face, idanunsa a cikin nata kamar yadda take kallonsa, yanayin da yake kissing ɗinta zai tabbatar da how much he loves his wife from the bottom of his heart the kiss he was giving her proves dat, a hankali ya ji hawaye masu zafi ya ziraro mata zuwa gefen fuskarta, ya zame bakinsa a hankali yana tallafe da fuskarta ya ɗora tashi akan tata ya saka fuskarsa daidai kamar ɓarin gyaɗa, ya zuba mata rikitattun idanunsa a nutse zuciyarsa na buɗewa sanyi na ratsa shi yana jin kamar shi ma za a bashi gado ne ya share hawaye da tongue ɗinsa gently ya sake mata small kiss cikin muryar marasa lafiya irin wanda suka galabaita ɗin nan ta ce “Ka haɗa da yawu fa” Ya yi wani irin murmushi underneath his breathe yana manna hancinsa a nata muryara narke ya ce “am sorry, na ja miki ciwo” Uncle Isma’il dake tsaye tun ɗazo ya ce “Ibrahim baka da kunya ko kaɗan” Jee na jin haka ta rufe ido kamar mai jin bacci, Khalil ya zame jikinsa kansa a ƙasa ya haɗe fuska sosai kai ka ce bashi ya yi laifin ba, Uncle Bello murmushi kawai yake ya ce “Marasa kunyar ai nada yawa Yaya kalli yadda tayi pretending bayan yanzu muka ji muryarta” Yaya Bilkisu ta ce “Majeederh ga ɗan uwanki Alpha ya dawo” Majeederhn ta buɗe Idanunta jin maganar Yaya Bilkisu da kuma sunan wanda ta kama wanda da gaske bata san zata sake ganinsa ba, duk da cewa a kullum tana wanzuwa da tunanin halin da yake ciki, ta juyo tana bin jama’ar wajan da kallo kamar yadda suke kallonta banda General Alpha, ta kalli Uncle I da Uncle B ta dawo kan Jawaad da kuma Yaya Bilkisu a hankali kuma ta sauke ganinta akan Alpha wanda daidai lokacin shi ma ya ɗago nasa idanun, cikin sa’a ganinsu ya sarƙe waje guda zuciyar ko wannen su na harbawa, Majeederh wani irin firgitaccen yanayi ta shiga mai kama da shakku, ji tayi jikinta ya fara rawa a sanyaye ganin Alpha da yadda ya ƙara nutsa idanunsa cikin nata ya sake ruguza ɗan ƙarfin quiwa da kuzarin data fara samu, kallon ashe zaka dawo take masa,the way he looks at her is different from hers, it’s a look that you cheated on me and ruined my happiness for years and years. Zuciyarta bata gama gasgata mata shi ɗin bane tabbaci kawai take nema daga wajansa, majeederh ta mance duk wani abu da ya yi mata kulawar daya bata a baya shi ne ya fara ɗawainiyya da ita a yanzu, jikinta na rawa da ɓari ta saka hannu zata tsige ƙarin ruwan Khalil ya yi saurin riƙeta ta saka hannu ta fisge da ƙarfi jini ya fara fitowa, ta miƙe tsaye akan ƙafafuwanta hawaye tuni ya gama wanke mata fuska ta nufi wajan General Alpha, Khalil dai ikon Allah yake gani yana mamakin who is he? Domin bai ma san ɗan waye ba, Majeederh ta kalle shi kamar yadda yake kallonta ya kasa ce mata komai sai kawai ya ji ta faɗa jikinsa tana sakin wani irin raunataccen kuka, lokaci guda Alpha da Khalil suka runtse idanu, nan da nan kuma idanun Khalil ya jirkice, jijiyoyin kansa sukai kwance a saman goshinsa, tashin hankali da gigita da ya yi wa Majeederh yawa tana ganin abun kamar wani mafarki ya sanya numfashinta sarƙewa jikinta ya saki tayi baya luu zata faɗi a sume da sauri cikin rashin sani G.A ya saka hannu zai dawo da ita jikinsa Khalil ya miƙe yana jawota nasa jikin ya rungumeta da kyau yana ɗan hura mata iska a hankali yana danna ƙirjinta ya ce “Madam, wife” Maganarsa ta hanata ƙarasa sumewa da yadda yake danna mata ƙirjin amma gabaɗaya a rikice take, Khalil bai gama sanin hujjarta na sumewar ba a wannan ya yi ƙasa da murya ya ce “Sorry” Dr ne ya shigo ya ce duka su fita. Alpha ne ya fara ficewa.
Jirgin su Mai martaba Ajlaal Sultaan bai sauka ba a ranar kamar yadda ya shaidawa Khalil sai washegari wajan 8 na safe, Kasancewar a wannan karan ma zuwan na Mai martaba Ajlaal Sultaan a sirrince ne ya sanya daga jama’ar Saudiyya har na Naija ba wanda yake da labari balle ƴan jarida su yaɗa kamar yadda suka saba, Khalil na tsaye cikin ƙyakƙyawar shiga na manyan kaya lallausan wani Brown ɗin Kashmir ne a jikinsa wanda ya yi tsananin fidda kyan shi na Ba’amurke baƙar fatarsa sai ɗaukan Idanu take, hannunsa zube cikin Aljihu ka ɗauka wani babban mutum ne mai yara wajan goma Yadda yake feeling kansa, da yadda jikinsa a kullum yake ƙara buɗewa, akan Ƙhulud Arzaan idanunsa ya fara sauka, sai wasu fararen yara masu masifar kyau dake riƙe da hannunta tana musu murmushi, Zaytoon ce ta biyo bayan Ƙhulud Arzaan, sai kuma ƙanin Mai martaba Ajlaal Sultaan Rohaan dake bin bayan Zaytoon, Khalil bai gama mamakin ganinsu ba yaga Ajlaal ya sakko hannunsa ɗauke da wheelchair yana tura ƙyakƙyawan matar da kamar ka taɓa jini ya fito, ya ƙarasa da sauri yana rungume Ajlaal ya ce “baka ce duka ba” Ajlaal dai murmushi yake, Khalil ya kalli matar dake saman wheelchair ya ce “Asslam Alayki, ya jiki?” A nutse take binsa da kallo sai kuma yaga tayi murmushi ya matsar da Ajlaal ya amshi wheelchair ɗin suka nufi wajan mota, wayar Khalil ya fara ƙara ganin Dad ɗinsa ne ya sa a gaggauce ya ɗaga Khalil ya zare Idanu ya ce “Dad but baka faɗa mini kana zuwa Naija ba?” Ta wayar Dad ya ce “Surprising naka nake son yi, yau jirgi na zai sauka ina son kuma na sauka a gidanka” Khalil ya girgiza kai yana dariya ya ce “Then, this is no longer a surprise” Ya kashe wayar kai tsaye kuma gidansa na Lafiya Round ya nufa da su duk da Mai martaba ya ce a hotel zasu sauka Khalil ya yi kamar bai ji ba, yana driving lokaci zuwa lokaci yake kallon matar dake kwance a gefen jikin Ajlaal idanunta rufe a hankali yake lura da yadda Ajlaal ɗin ke mata karatun Alkur’ani yana kuma bata zam-zam Khalil mamaki kawai yake a ransa kuma yana jinjina girma da Kaɗaitar Ubangiji haɗi da buwayar shi….

 

Allah ya nuna mana Monday Lafiya, a ƙa’ida labarin 100 Page’s amma ban san me gaba zata haifar ba wannan page 79 muna 83 kuma kafin Monday zaku samu har 90 a arewabooks akwia show💃🏻💃🏻💃🏻[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *_Arewabooks@Nimcyluv_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button