Mijin Malama Book 2 Page 44
Da sauri cikin wata kakkausar murya General Alpha ya ce “Ƙarya kake! Cikina ne a jikin Hawwa’u ba naka ba, Liar, maƙaryaci” Lokaci guda suka kalli direction d’in sashin da General ɗin ke tsaye, domin babu wanda ya hankalta da zuwan nashi cikin parlourn. Ba wanda ya furta ko alifun balle ya ja doguwar maganar da zata ɗauki hankalin jama’a, ko wanne a parlon wani razanannen tashin hankali ne ya mamaye masa zuciya, rashin madafa da sanin abin yi, akan aure biyun dake bisa mace ɗaya! Mene GASKIYAR LAMARI? Wake da haƙik’anin samuwar cikin na Majeederh? Wani abu ne mai kama da kunya a sa’ilin da akai yunƙurin binkan asalin uban, ALLAH YANA GANI, shi zai basu haske wajan fahimtar abinda ke cikin duhu.
“Ni ne wanda yake da nasaba da cikin Hawwa’u, saboda ita ɗin mallakina ce She’s my wife, kenan babu doubting a ɓullowar ciki a jikinta? Tunda tana iya yiwuwa na kaɗaita da matata” Babu shakka,ko tsoro a fuskar General! Yanayin fuskar shi na tabbatar da asalin abinda ya bijiro daga ƙasan zuciyar tasa ne, bisa rikiɗewar ƙaryar daya shirya zuwa sahihiyar gaskiya wacce ya yi mata rajista da kansa. Uncle Isma’il ya juya ya kalli Dr Khalil wanda yake danna wayarsa haɗaɗɗiyar iphone 15 promax wacce aka launcher ta, not too long ago. Idan kaga yadda Khalil ke acting da basarwa ba zaka ce shi ake ƙaryatawa ba, ta hanya ɗaya zaka san kalaman sun ratsa zuciyarsa yadda gargasar hannunsa ke mimmiƙe ita kaɗai tana zubewa, Abbu bashi da hurumin magana domin batu ne akan ƴarsa daya shafi ɗan, ɗan uwansa, ita kuma Majeederh ya shafi mijinta da kuma jininta, dole ya zuba Idanu yaga yadda al’amarin zai wakana, baya da magana tun fil azal dama.
“General zauna, maganarka ta sanya firgici ina son kar mu shiga hak’ƙin Ubangiji, duk da cewa bamu da masaniyar Ibrahim yana raye, ALLAH YANA GANI”
General ya zauna yana jin wani ƙarfin quiwa da ganin alamun nasara, wacce da ita zaiyi amfani wajen kassara zuciyar ta uban girman kan nan da tsaurin idanu.
“Ya akai cikin ya zama naka? Shin bayan aurenku yaushe ka samu nutsuwar keɓewa da Majeederh? Tunda kasan mun san cewa taƙi yarda tayi accepting naka matsayin mijinta ko? Ya akai hakan ta faru?” General ya yi shiru can zuciyarsa yana tunanin “What should I do?” Majeederh kuma mamaki da tu’ajjubin lafiyayyiyar ƙaryar da General ya shimfiɗa take, wanda ya hanata magana sai kallon shi da take.
“Ina magana? Bamu da cikakken lokaci” General ya ce “Uncle binciken sirrin ma’aurata haramun ne fah, faɗin yadda akai daidai yake da furta kalaman batsa a gabanku” Uncle Isma’il ya rasa bakin magana, General ya girgiza kai cike da tausayawa ya ce “Ita ta sani, tasan ni ne uban” Sai a lokacin Khalil ya ce “Ƴar Shaye-shaye ce ita, irinka da zata sani?” Khalil ya ajiye waya ya Kalli General sosai da kyau ya ce “Yadda Ubangiji ya tsarkake ni daga shiga gonar matar wani, haka ya tsarkake matata wani ya shiga gonata” Khalil ya saka hannu ya hargitsa kansa, a hankali ya miƙe hannunsa a bayansa like yadda Mai martaba Ajlaal yakeyi, tafiya yake sai kuma ya juyo ya kalli General ya ce “Kasan ko gaskiya za ta yi ajalina sai na faɗa, ban taɓa furta ƙarya ba da wasa ko akasin haka” Ya juya ya kalli Innati da Yaya Bilkisu ya ce “Ko sanda kuka ɗauka ni fatalwa ne, tarayya na gama yi da matata ita kanta zatonta mafarki take but it was reality” Kunya ta kama Majeederh tana jin kamar ta nutse, ya akai Khalil har ya yi mata wayo haka? Ta kasa kallon kowa, a hankali Abbu ya miƙe tare da ficewa,Yaya Bilkisu tayi tsuru da Idanu Innati ta hangame baki tana jin zunzurutun rashin kunya irin ta surukinsu Dr Ibrahimul-khalil Abraham. Uncle Isma’il girgiza kai kawai yake yana jin da ana mutuwar gaske a dawo Khalil ba zai taɓa sauyawa ba, hali zanen dutse, cikar mutum suffar shi, gaskiyar ka nagartarka.
“Maƙaryaci, ka shirya zancenka ne, amma ciki nawa ne” Khalil daya fara birkicewa yana ɗan nufo General shi kuma yana yin baya tare da riƙe kansa, ya ce “Haba? Ashe kai ne ka farke ɗinkin haihuwar da akai mata?” General ya ce “Ohho dai ai ni ba ɗan iska bane da zan dinga rashin kunya a gaban mutane, Majeederh is my wife dole mu kasance tare” Khalil ya fara tattare hannun riga idanunsa jajur ya ce “Ni Ibrahimul-khalil cikakken ɗan iska ne akan matata, tunda gashi daga dawowata na bata wani cikin, ka tabbatar ni da kai akwai bambanci nayi abinda ka kasa a shekara biyu, Loser!” Kunya ta kama kowa na wajan, Innati ta share zufa ta ce “Balkisa ɗakko mini ruwa mai ɗan iskan sanyi suma nake ji”
“Innati lafiyarki lau ba wata suma, sha ruwa ki nutsu” Ta fashe da kuka ta ce “To tsakani da Allah a nemo abu a toshe min kunnuwana” Khalil ya fara hauka jikinsa yana jijjiga, Yaya Bilkisu ta miƙe ta nufi wajen Khalil tana zuwa ya saka hannu ya ɗauketa cak! Ya nufi wani bedroom da ita ya kulle, ya dawo Gadan-gadan kan Alpha da sauri Majeederh ta shiga tsakiya yaƙi kallonta, domin ƙwayar Idanunta sune weakness dinsa masu raunata masa zuciya, ta saka hannu a hankali ta juyo da fuskarta tare da sanya idanunta cikin nasa, ya ɗan kwaɓe mata fuska ya kasa cewa komai,ta kama hannunsa ta ɗora a cikinta a hankali daidai shi ta ce “We’re one single family, no one can separate us ok? Ni da kai jini ɗaya ne, ma’aurata ne, kai Mijin Malama ne, ni kuma Mrs Ibrahimul-khalil Ranka ya daɗe,mu ɗin masoya ne KHALJEED💖” Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana damƙe hannunta cikin nasa, ya dinga kallonta shi kansa baya da zarafin faɗa mata yadda yake jinta a zuciyarsa.
“Hawwa’u!” General ya kira sunanta da ƙarfi ya ce “Cin amana? Akan shi zaki mallaka masa jinina?” Khalil ya sake damƙe hannun Majeederh kamar zai raba gida biyu naman jikinsa duka rawa yake. Maman Alpha kasancewarta barrister ta gama fahimtar komai ta ce “Ok a zubar da cikin kawai” Ta faɗa tana kallon kowa tana son ganin reactions ɗin su, a gigice Khalil ya kalleta idanunsa na shigewa ciki da ƙarfi ya ce “Maaa, cikin nawa za a zubar? Kamar cikin shege?” A fili kuma General ya sauke numfashi ya ce “Better! A zubar kawai kowa ya huta zanfi jin daɗin hakan” Maman Alpha ta girgiza kai ta ce “You are ashamed, You are a liar” Uncle Bello ya ce “Ka bani kunya, ka bani mamaki, daman tabarmar kunya da hauka ake naɗeta, kaga duk duniya ba abinda zaka sake faɗa mini na yarda, Firstly ka ce Majeederh na sonka har muka ɗaura aure, ashe ƙarya ne, secondly ka ce Zuleehart ba matarka bace nan ma ƙarya kake, thirdly, ka ce cikinka ne shi ma ƙarya ne, When will you stop lying? when will you be an honest person? you are nothing but a liar”
Innati ta saki baki sosai sai kuma ta ce “Tirr! Amma ka ji jiki sosai soja ƙarya zagin Allah ka bani kunya, ya akai kamar wannan yaron mijin Malama da yake tun farko Ahlul kitabb ya fika iya faɗin gaskiya?” Ta girgiza kai ta ce “ALLAH ya isa a gaskiya zaman jiran jin matsiyaciyar ƙaryar da kake zabgawa, yanzu da za’a zungura tsinke a kunnena wuta za a tsokalo” Uncle Isma’il ya kalli Khalil da General a hankali ya ce “Ku zauna” Khalil ya nemi waje ya zauna, Jee ta miƙe ta bar wajan, Uncle Isma’il ya fara ta kan Khalil ya furta.
“Da yawan lokaci dole ne ka koyi tanƙwara zuciyarka Ibrahim, ba komai ne zaka ce zaka fara duka ko faɗa ba” Khalil bai kalli Uncle ba, yana tunani to shi me ya yi? Bayan bai damu da hayaniya ba yaushe ma yake duka? Uncle ya sassauta muryar shi ya ce “Lokacin da ba ku da ikon sarrafa tunaninku, tunaninku da motsin zuciyarku na iya yin ta’adi. Kuna iya samun kanku kuna yawan jita-jita akan abubuwa da yawa, kuna shakkar kanku akai-akai, ko kuma kuna fuskantar matsala game da motsin zuciyarku. Bai kamata ya kasance haka ba! Kuna iya sarrafa tunaninku kuma ku maye gurbin tunani mara kyau na rashin kulawa tare da tabbatacce, daidaitattu. Bayan lokaci, za ku fara jin daɗin farin ciki, ƙarin daidaitawa, da kuma kula da yadda kuke ji da tunaninku, Khalil na san a haka Ubangiji ya halicceka sauya mutum ɗabi’a ko wani hali nasa wanda ya ginu a kai abu ne mai matuƙar wahala, amma ka dinga haƙuri Plx!” A hankali ya kwantar da murya kamar ba zai ce komai ba tsayin seconds kafin ya ce “Thank you!” Uncle Isma’il ya ce “Allah ya yi maka albarka” Ya ɗan yi jim sai kuma ya ce “Zamu tafi Palace” Uncle Bello ya ce “Yaushe?” Khalil ya ɗan shafa kansa domin sam ya gaji da magana wallahi “Gobe” Suka ce “Da wuri haka?Ina a nan za ku yi Ramadan gabaɗaya bai fi saura kwana uku ba a fara” Khalil bai ce komai ba, ya miƙe tsaye tare da ficewa daga parlourn.
Uncle Isma’il ya juya kan Alpha da yake durƙushe zuciyarsa kamar zata fito haka yake ji, shi kaɗai yasan wanne so ya kewa Majeederh ba kowa zai fahimci ko gane hakan ba, kalaman Zuleehart ne suka shiga yi masa amsa kuuwwa! A cikin kunnensa. Uncle ya ce “General kai da kanka baka ji nauyin Ibrahim ba? Ka dinga shirga ƙarya bisa son ranka? Saboda cikar burinka, duk lalacewar mutum idan ya riƙe gaskiya da amana wallahi yafi haiba da kamala cikin mutane nagarta ta ban mamaki mene ribarka akan yin ƙarya? Kasan hukuncin masu ƙarya bisa son rai ba don kare kai ba? Ka ji tsoron Allah tun kafin lokacin ya ƙure maka kaje ka nemi matarka” General ya ce
“I am sorry Uncle, zan gyara yanzu a bani matata” A hargitse Uncle B ya ce “Kasan Allah idan baka daina kiran Majeederh matsayin matarka ba, hukuncin da zan ɗauka akan ka mai tsauri ne” Yaya Bilkisu data fito ta ce “A’a yana da ikon faɗar haka saboda an ɗaura musu aure, bayani za ku yi masa yadda ya kamata” Ta zauna ta ce “General kasan ba a aure akan aure ko? An ɗaura maka aure akan rashin sanin mijinta na raye, kuma Allah ne ya ƙaddara babu rabon wahala da samun zunubi shiyasa bai ƙaddara ka ɗora mata idda ba har kawo yanzu, kuma idan an samu matsalar aure a irin wannan maslahar ba wani babbar maudu’i za a ja ba, idan mace tana son mijinta na farko shikenan sai na biyun ya saketa ta komawa mijinta, ko ma bai saketa ba ya zama dole ta koma, idan tana son ko wanne sai a bata zaɓi na zama da wanda take so” Yaya Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayin General ta ce
“Kalaman Majeederh a kullum sun isa su sanya ka fahimci irin son da takewa mijinta, a tarihi na soyayya ban taɓa ganin kalan tasu ba, shi yasa nake musu uzuri da rashin kunyar su a wani sa’ilin, ka yi haƙuri ka amshi hakan matsayin ƙaddara, kana son Majeederh wannan ra’ayinka ne, Majeederh bata son ka Khalil take so wannan ƙaddarar ka ce, our destiny depends upon whether we live in harmony with God, following His moral teachings, baka da ikon sauya ƙaddararka, rashin samuwar Majeederh hakan na nufin Zuleehart ita tafi dacewa da rayuwarka ita ce alheri ga duniyarka”
Murya can ƙasa yana kallon Yaya Bilkisu ya ce “How do i know my destiny?” Yaya Bilkisu ta taɓa kafaɗarsa cike da ƙwarewa irin tata ta tsohuwar ƴar boko ta ce “Destiny can never be figured out it can only be revealed by trusting and following what feels right, a Karan kanka za ka ji wannan abun kana son shi ne har zuciya, to wannan abun shi ne ƙaddararka, da yawanci abinda mukewa mugun so ko tsana shine yake kasancewa ƙaddararmu” Ta kama hannunsa domin haƙiƙa son wanda baya sonka jarabta ce, ko da iya haka nan Ubangiji na iya yi maka azaba da laifukan ka. Ta ce “Your destiny is determined by your decisions, abu ne mai sauƙi cire Majeederh daga ranka idan ka nutsu ka fahimci dalilin daya sanya kake jinta a ranka, wanda kake so shi ne wanda kake jin motsin shi a zuciyarka a kullum, wanda kake so shi ne wanda ko sunan shi aka kira sai zuciyarka ta girgiza, wanda kake so a kullum shi ne zaka ji ko yana nesa dakai kake jin shi kusa da zuciyarka, wanda kake so da gaskiya shi ne wanda zaka sadaukar da komai saboda da shi, yana da kyau ka sadaukar da soyayyarka ka Khaljeed sau ɗaya kawai su samu nutsuwa da farin ciki”
Hawaye na zuba a idanunsa yana kallon Yaya Bilkisu muryarsa na rawa ya san ba zasu gane su fahimta ba a hankali ya ce “Can i change my destiny? Ta dafa shoulder ɗinsa ta ce ”
“Why not? Wata ƙaddarar daman mu ke ɗorawa kanmu, wata kuma jarabawa ce daga Ubangiji,In simple terms, your destiny is decided by your karma. Every human has the power to change his destiny by changing his karma, karma means “Action” Ya yi shiru a hankali kuma ya tashi yabar parlon yana zuwa daidai ƙofa ya yanke jiki ya faɗi a sume. A gigice sukayi kansa ganin jini na fita ta hancinsa da baki, haƙuri da juriyar da Maman Alpha keyi ta ƙare ta fashe da wani irin kuka na tausayin ɗan nata, tasan Soyayya jarabta ce kuma addu’ar Zuleehart dole ta bisa saboda ya cutar da ita bisa yardar da tayi masa, a mota aka saka shi zuwa hospital.
Innati ta sake kallon Yaya Bilkisu ta ce “Balkisa sake miƙo mini ruwa don Allah don Annabi, wanda yafi na ɗazu ɗan iskan san yi” Har dare suna hospital Majeederh na son cewa Khalil zataje amma tana tsoro tana lura da yanayinsa a sama yake, kuma yanzu jinin sarautar ke aiki a jikinsa, yana zaune hakimce a tsakiyar gadonta daga shi sai red ɗin gajeren wando, cinyoyinsa masu ɗauke da kyawawan gargasa a bayyane a tanƙwashe su jikinsa babu riga gefen cinyarsa Alhassan ne ke kwance yana bacci bayan ya gama fashe mata plate da sauyawa ɗaki kama, Khalil na kallon faɗan da takewa Alhassan hadda tsawa shi dai bai kulata ba, saboda bai san yadda ta kula dasu ba tsayin shekaru biyu, ga kuma ciki daya ƙara mata masifa. Hannunta riƙe da ƙaramin cup mai ɗauke da black tea da Honey ta zauna gefen gadon tana ajiye cup ɗin akan table ta kalle shi taga hankalinsa yana kan system sai ba tayi magana ba, ganin kallon ya yi yawa ba tare daya kalleta ba ya ce “Uhm” Can ya kalleta suka haɗa ido sai kuma ya kalli system clamly ta ji ya ce “Meye MATA A YAU?” Jee ta juya idanunta ta ce “A ina kuma?” Ya juya mata system ɗin yana matsawa kusa da ita ya ɗora kansa a cinyarta kamar mai jin bacci Alhassan ya dawo dashi ƙirjinsa Jee ta ce “Oh wani program ne a Arewa24, naga sunyi inviting nawa tun last week” Ya yi shiru Ta shafa kansa a nutse ta ce “Ban zuwa ai” idanunsa rufe ya ce “Uhm, kuma na yi Accepting request gobe” Tai jim domin bata ɗauka zai amince ba, ta ci gaba da juya yatsun hannunta a cikin sumar kansa ya yi saurin riƙe hannunta ya ce “Kina son taɓa ni? Zaki jama kanki? Mun samu yaro mai wayo fa” Jee tayi dariya cike da kwanciyar hankali ta ce “Photocopy ɗinka ne, harsu haura katanga da fashe cups da yake da su plate da ɗan banzan ci” Ya mirgina gabaɗaya ya kalleta yana kwaɓe mata fuska kamar zaiyi kuka ya ce “Kuma ni ne ɗan banza? Ba na daina ci ba?” Ta shafa fuskarsa zuwa kwantaccen sumar ƙirjinsa ta ce “Hucewa salamun Ranka ya daɗe” Ta faɗi hakan tana kifa fuskarta a tashi tana ƙoƙarin kissing ɗinsa suka ji an banko ƙofa a gigice an shigo Maman Alpha na kuka sosai wanda ya sanya Majeederh miƙewa shi kansa Khalil zuciyarsa ta girgiza ta zube a gabansu da ƙarfi ta ce “Alpha is dead”
Allah ya a nuna mana Monday Lafiya, labari yana ta jana bana son skipping shi ya sa yanzu nake tunanin sai shekara zuwa shekara zanna new book, gashi dai a 2023 shi ne kawai Novel ɗin da nayi, kuma an hanani na ƙara samun costumers sai fitar mini da littafi ake kamar bani da gata😂bana son fiye surutu wlh tallahi ƙimata ta zube amma dai ba komai….. 08119237616