Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 51

Sponsored Links

[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Da sauri ya kalli Akeeth ya ce “Boss binsan zaka yi? zuwa can Saudiyya ɗin?” Akeeth ya dinga kallon yaron nasa mai suna Ziyad, ganin baiyi magana ba ya sanya Ziyad cewa “Idan babu damuwa kuma ba zan shiga rayuwarka ba, yau ɗaya ina son ka bani dama na baka shawara a matsayina na musulmi kuma ɗan uwanka, wanda yake ci a ƙasan ka” Akeeth ya ɗan yi gyaran murya hakan yasa driver ya ja suka nufi asibiti, Ziyad ya sake cewa “Ka bani dama please” “Ina jinka Ziyad, amma a cikin shawarar da zaka bani banda rabuwa da Malama Majeederh ok”
Da sauri Ziyad ya ce “Dole a kanta ne, ka saurare ni a karo na farko, ba zaka taɓa nadama a cikin shawarar da zan baka ba” A hankali Akeeth ya ce “Ina ji” Ziyad ya ce
“Kai babba ne, kuma mai hankali kasan menene ya dace da wanda bai dace ba Boss, yanzu menene ribarka idan ka auri wacce bata son ka?” Akeeth ya yi shiru, Ziyad ya ɗora da “Kai ne da matarka harda yara kuna rayuwa ta farin ciki, kwanciyar hankali da jin daɗi sai rana tsaka wani ya kawo kai da nufin rusa wannan farin cikin, da nufin rabaku rabuwa ta har abada bayan kuma duk duniya banda iyayenka ba wanda kake so sama da matarka don Allah ya zaka ji?” Akeeth ya rufe ido yana dafe kansa dake juya masa, a zaune yake amma jinsa yake kamar zai kifa, a hankali ya girgiza kansa ya ce “Ba zan barshi ba”
“Good, kuma tayaya kake tunanin Khalil zai barka ka raba su da Malama Majeederh? Idan da wanda zai fara bada shaidar soyayyar da sukewa junansu tun kafin su kasance miji da mata bai shige kai ba, zata kawo shi gidan marayunka, ya yi sati zuwa wata da ƙyar suke rabuwa, balle yanzu da yake ganin cewa ita ɗin matarsa ce? Kasan waye Khalil? Idan ransa ya ɓaci shi da mahaukaci bashi da banbanci, ina tunanin kamar ka shiga cikin hurumin Ubangiji ta hanyar nuna maitarka ta son matar aure, matar wani, kuma ba ƙiyayya tsakanin su balle ka ce” Akeeth kallon Ziyad kawai yake, sosai ya fahimta amma zuciyarsa ta kasa fahimta ko gane abubuwan da Ziyad ɗin ke faɗa masa a nutse ya ce “Amma na riga shi son ta, tun a lokacin da take kawo shi gidan marayun nake son ta, i don’t know what comes over me dana kasa fuskantar ta da soyayya wallahi”
“Hakan yana nufin ita ɗin ba alheri bace gareka, ita ba kowa bace face ƙaddararka (Your destiny)” A hankali ya ce “Destiny? Fate? Ƙaddara kuma?” Ziyad ya jinjina kai ya ce “Ko shakka babu, Majeederh is your destiny ita ce ƙaddararka, duk abinda Ubangiji zai jarabci bawa da shi har yake wahalar da shi to tabbas abun nan shi ne ƙaddarar shi, kuma kar ka bari hakan ya yi tasiri a zuciyarka akwai mata da yawa a duniya masu ilimi, aji, kyau, da duk wasu Qualities da kake buƙata” A taƙaice Akeeth ya ce “Qualities ɗin Malama Majeederh da ban yake, she’s different from others, daban take da sauran matan, kawai na yi sake ban taɓa zaton Abraham zai girma ya ce yana son Majeederh ba, ban taɓa zaton zata iya auren shi ba, na ɗauka za ta yi tunanin yarintar shi ta dubi ƙanƙantar shi” “Me zaka nuna masa a yanzu Boss? Dame zaka fi Khalil ɗin? Da shekaru ne dai kawai, su kuma shekaru are just a number” Akeeth ya kalli Ziyad kamar yana son gasgatawa, Ziyad ya girgiza kai ya ce “Kuma shi namiji a duk inda yake namiji baya ƙanƙanta, zanen sunan shi na namiji zai ta kasancewa cike da iko, kamar yadda Ubangiji ya faɗa a cikin Alkur’ani, suratul Nisa’i, maza gaba suke da mata zasu iya jagorantar su a komai, don Allah Boss karka raunata zuciyar Khalil yana tsananin so da ƙaunar matarsa, yadda ya shaƙu da matarsa ko da iyayensa bai shaƙu ba, ni nake bibiyar shi nake ganin komai, yana da ɓoyayyen sirri fitar shi kawai ake gani, amma yana da wani irin Qualities wanda ba ko wanne namiji ke dasu ba, yana yin abu don Allah shi ya sa bai damu daya faɗawa jama’a waye shi ba, yadda ba a haifeka mahaifa ɗaya da Majeederh ba, haka ba zaka taɓa mutuwa saboda baka sameta ba, believe me” Akeeth ya ce “Abraham bashi da hankali, yana da zuciya bai cancanta da zama Mijin Malama ba, ina tsoran watarana ya yi mata illa nafi kowa sanin waye shi wallahi, Ziyad kar kaga laifina ko ban auri Majeederh ba, kawai ta samu wanda zai dace da ita but Majeederh ba tayi deserving auren mutum kamar Abraham ba, duk wahalar nan data sha” Ziyad couldn’t speak, ya kasa magana gabaɗaya sai kawai ya ja bakinshi ya yi shiru, hospital suka nufa aka bawa Ziyad gado saboda karayar hannunsa yana buƙatar resting bed.

Idanunsa rufe ya shigo cikin haɗaɗɗen parlourn gidan nasu, ya yi tsaye, magidanciyar matar dake zaune saman kujera da counter a hannunta ta kalli Akeeth a hankali ta ce “Baka sameta ba?” Ta faɗa a taushashe Akeeth ya yi saurin cillar da wayar hannunsa ya ƙarasa gaban Nenne ya zauna yana ɗora kansa a cinyarta ta shiga shafa kansa tana jin yana sauke ajiyar zuciya “Zaka haƙura yanzu dai ko? Ka tabbatar ba rabo tsakaninku?” Akeeth ya ɗago kai ya kalli mahaifiyarsa ya ce “Tayaya zan iya haƙura da ita Nene? Nida ita kamar ɓarin gyaɗa ne how can you imagine zan rayu without her eh?”
“Me kake so yanzu Akeeth?” A hankali ya ce “Your help, your support, and your prayer” Ta riƙe hannunsa ta ce “Addu’ata kullum tana zagaye da kai, ina yi ba ranar fashi”
Da sauri ya ce “Call Majeederh and ask her to love me, please Nene” Nene ta ce “Karka zama mai tsananin son kanka a cikin al’amarin rayuwa Akeeth, babu rabo tsakaninku tunda har bata kasance matarka ba, ka yarda cewa ba kai ne MIJIN MALAMA ba, Idan Rabo ya rantse ko babu ciwo dole a tafi, haka Idan Rabo ya rantse duk wahala duk ƙiyayya dole ta kasance matarka ka nutsu ka kwantar da hankalinka”. A hankali idanunsa na cika da wasu hawaye masu zafi sosai ya ce “Nene!”
“Ka yi haƙuri” Ya damƙe hannunta sosai yana kifa kansa a cinyarta ya ce “Nene, zuciyata ba daɗi na yi kuskure” A hankali itama idanunta na cika da hawaye ta ce
“Babban kuskuren shi ne amfani da sunan Mr no name, da Akeeth ka sanya maybe da tasan da zamanka, kayiwa kanka uzuri kayiwa Majeederh uzuri idan da wacce ta cutar da rayuwarku bai huce Latifa Omar ba, ka yi addu’a ka manta” Ya yi shiru kawai, Nene ta shiga damuwa Akeeth kawai ta mallaka a duniya shi ɗin maraya ne ubansa ya mutu ya barshi da arziƙi kamar ba zasu ƙare ba, bashi da aiki sai na bata labarin Majeederh, ranar da aka ce Majeederh tayi cikin shege a sume suka nufi asibiti da shi, kuma shi ne wanda ya yi rubutu a media domin kare hak’ƙinta, tana ganin al’amarin shi kamar zaucewa irin na masu fama da shigar sabuwar Soyayya. Ta ce “Akeeth ga ƴar uwarka? Ga Rusul?” Ya girgiza kai kawai ya ce “ALLAH YANA GANI Idan har ban auri Majeederh ba to na haƙura da aure” Ta zare ido ta ce “Idan baka yi aure ba sai me? Ka rufa mini asiri kada Aljana ta aureka (ALLAH YANA GANI)”. Bai furta komai ba ya miƙe ya nufi part ɗinsa idanunsa rufe yana jin wani irin zazzafan zazzaɓi na rufe masa jiki.

A can Ikot Ekpene Prisons Mr President ne zaune shi da Latifa Omar bayan ya samu kaɗaicewa da ita, ta hanyar wani Gandiroba mai bala’in son kuɗi ta kalle shi ta ce “Amma Sir Khalil ya tsaneka” Ya girgiza kai ya ce “I knew my son more than anything, nasan waye shi yana so na, nasan kalar son da yake mini I just need your help” A hankali ta ce “Name?”
“Ya yafe mini, na yi regretting komai bani da tabbacin zan bar gidan nan ko a’a, idan har na bari to tabbas zan dawo ga iyalina idan ban bari ba to zan zauna a nan har zuwa mutuwata” Latifa ta ce “Sir kun yarda zaku mutu kenan?” Ya kalleta da mamaki a fuskarsa sosai sai kuma ya ce “Mun sani, a littafinmu ai mun san mutuwa gaskiya ce duk wani wanda ki kaga yana aikata abu wanda yake ba daidai ba ya sani, son kuɗi ta rufe idona na banbanta kuɗi da iyalina, wanda a yanzu ba kuɗin kuma iyalin nawa nake buƙata su nake son gani, amma bani da confidence na zuwa inda suke bani da confidence na neman yafiyar su” Ya ɗan saurara sai kuma ya ce “Ina son Gimbiya so mai yawa, komai nata birgeni yake amma rashin kishi da masifar son kuɗi nake son sadaukar da ita ga wani? Wanne irin miji ne ni?” Ya runtse idanunsa a hankali hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa kafin ya ce “I am ashamed, I have failed as a father” A hankali ya lumshe idanunsa tears running down his cheeks”I made a mistake and I regret doing all the things I did in the past, dama lokaci ya bani dama na tariyo bayana domin gyara goben da bani da tabbacin kyanta, duk da ban kasance musulmi ba, amma nasan abubuwa masu kyau wanda littafinmu ya zo da shi” A hankali Latifa Omar ta ce “Kana cikin lokacin ka Sir, zaka iya amsar shahada, idan ka yi believing da addininmu” Ya girgiza kai ya ce “Da alama bani da rabo, ban ji son hakan a raina ba, Musulunci bai cancanta dani ba”
“A’a Sir!” Latifa ta faɗa a ɗan gaggauce ta ce “Addinin Musulunci mai sauƙi ne, ga ma’abota soyayyar shi, baya da wariya wajen bambance wanda zai shige shi, kyakkyawar niyyar da tsarkakkiyar zuciya kawai ake buƙata, abu mafi wahalar shi ne da wacce kalar zuciya kake son musulunta? A nan kuma sai ka saurari zuciyarka abinda duk kayi imani da shi, to shi ne daidai kayi amfani da damarka domin baka da tabbacin kawai anjima ko gobe” Da sauri ya ce
“Ina son musulunta ƴata, tsoro ne kawai ya hanani ina ganin kamar addinin ba zai amshe ni” Murmushin jin daɗi Latifa tayi, ya yi alwala a wajen aka bashi kalmar shahada yana faɗa idanunsa na cika da hawaye duk duniya yanzu iyalansa yake buƙata, Gimbiya, Khalil, Clara, Zizi, Badi, da kuma Kiristi ko mutuwa ce ta ɗauke shi a cikin su, Latifa Omar ma kukan take sosai zuciyarta babu daɗi, envelope din daya bata ta ɗauka ta nufi part ɗinsu na mata a asirrince ba tare da ankarewar kowa ba. Cikin dare zuciyar Mr President ta buga ko motsawa bai ba Ubangiji ya zare ran shi a ranar daya karɓi shahada, daman haka ne idan kakan aikata aikin ƴan wuta, idan Ubangiji ya soka da rahama kana dab da mutuwa ka koma aikin ƴan aljanna, idan na ƴan aljanna kake kaso taɓewa sai ka koma na wuta, su Latifa na kwance aka dinga tashin su ana fita ta wata ƙofa har suka fice daga cikin prison aka sanya su a wata ƙatuwar mota tare da ɗaukan hanya da su.

Related Articles

“Sister ina za a kaimu?”
Latifa ta tambaya a tsorace, wacce ta tambaya ɗin ta ce “Haka ake mana duk sati ko duk wata, sunan an kawo mu nan da niyyar gyaran hali ko yanke mana hukuncin zaman gidan kaso gabaɗaya har mutuwa ko mu yi shekaru mu fita, amma an mayar damu saniyar tatsa” Latifa ta ce “Pardon! Ban fahimta ba” Ta ce “Ina nufin yanzu haka kaimu wajen wasu manyan gari za a yi su kwanta damu, bamu da wani option wanda ya a shige obey, yanzu hatta ƙwayoyin maye da ake karɓewa wajen mutane sune suke amsa, to da irin haka taya rayuwa zata gyaru? Wani ma laifinsa bai kai matsayin da za a kaisa prison har haka ba…,” Ta kasa ci-gaba da maganar saboda kukan daya ƙwace mata… Saukar yamma duk Khalil sukai Majeederh tunda jirgi ya tashi ba taga Khalil ba sai yanzu da suka sakko, ya kasa haɗa Idanu da ita, kunyarta yake ji sosai bai san mene ya sanya ya kasa controlling kansa a lokacin ba, ya kama su twins Yaa K na tare da Majeederh daman already ta faɗawa Zaytoon zuwan nasu sai dai bata shaida mata da Khalil bane, motocin Palace a jere wajen biyar, a nutse Gimbiya ta fito daga motar tana sanye da wata milk ɗin alkyabba wacce ta amshi jikinta sosai, fuskarta a kame kamar kullum, sai Clara wacce take tsaye a gefenta ta saka baƙar abaya tare da zagaye fuskarta da veil, sai Rohaan, ɗaya motar Zainab da Badriyya ne suka fito gabaɗaya cikin abaya iri ɗaya, Zizi da Badi. A kusan lokaci ɗaya cikin daƙiƙa guda idanun Gimbiya dana Clara wacce itama ta musulunta ta koma Fatymerh ya sauka akan Khalil duk yadda Gimbiya ta kai ga jan ajinta da riƙe kanta kasawa tayi, ta saka hannu ta murje idanunta still Khalil take gani tsaye yana mata murmushi ga yaransa da matarsa zagaye dashi, Jee ta nuna kamar babu komai, Gimbiya komai nata ya tsaya ta kasa yarda ko gasgata abinda take gani da ɗan sauri cike da nutsuwa Khalil ya nufeta yana zuwa ya rungumeta, suka sauke ajiyar zuciya “Ummie” Ya furta a taushashe tana jin muryarsa mai cike da kamala ta rungumesa a jikinta tare da sakin wani irin raunataccen kuka tana cewa “Khalil? My son…..
[

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button