Mijin Malama Book 2 Page 54
Takawa da Majeederh a mota ɗaya wata babba ta zamani black colour, Alhassan da Al’hussain da Yaa K suna mota ɗaya ta bar su Soha da Noha wajen Nanny, sai motar masu kula da lafiyar Takawa Khalil data iyalansa, a haka suka bar gidan jikin Majeederh gabaɗaya ya yi sanyi ta rasa me Mijin nata ke ɓoye mata, ta ɗago ta kalle shi tasan ba lallai ya sake magana ba tunda ya yi kafin su fito can ta ce “Takawa meke faruwa ne?” Ya numfasa a hankali ya juya ya kalleta ba tare da ya ce komai ba ya kama hannunta ya matsa alamar Ki kwantar da hankali, Ganin ta sake ƙoƙarin magana ya rufe mata baki tare da janta jikinsa ya rungume.
Har suka isa gidan Abbu ba wanda ya sake magana, gabaɗaya an sauya gidan zuwa ginin zamani wanda Takawa ya zana da kansa, Majeederh ta sake rikicewa ganin motoci kala-kala a harabar gidan Abbu, bata jira shi ba ta fito shi kuma ya tsaya a motar yana zubawa motar gwarazan mazan yaran nasa ido. Cak ta yi ganin Gawa shimfiɗe a parlor ga Aaliyyah zaune tana kuka ga Raihana da sauran matan familyn Khan, sun zagaye gawar sai kuka suke, Mami idanunta jajur ba kuka take ba amma halin da take ciki gwara ta mai yin kukan da ita, Maman Alpha ta yi shiru idanunta akan mamacin, Yaya Bilkisu, Innati sai maƙota mazan kuma suna ɗaya parlourn. Cikin rashin sanin wanda ya mutun Majeederh ta zube gaban gawar jikinta na rawa bakinta na kakkarwa ta ce “A…a…a Abbu?” Innati ta ce “Ba dai Audil azizu ba, Allah ya tsare shi da yin wulaƙantacciyar mutuwa irin wannan” Majeederh bata karaya ba ta cigaba da zame zanin da aka rufe gawar da shi idanunta ya sauka akan fuskar Ruma wacce ta yi baƙiƙƙirin ta sauya kama ta zama wata ƴar firit da ita, Majeederh ta saki zanin tana rufe bakinta saboda kukan da ya zo mata a fili ta ce
“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ruma ce? Ruma ta rasu yaushe? Garin yaya? Innalillahi!”
Ta sake fashewa da kuka cikin wani irin firgitaccen tashin hankali, Yaya Bilkisu ta ce “Awa ɗaya da suka shige aka kira mahaifinku a waya ana nemansa a hukumar hisba, yana zuwa suka labarta masa gawa aka kawo musu tun daga garin Lagos, su kuma suka amsheta a details ɗin da take yawo da shi a jaka, sun tabbatar ciwonta ne ya kasheta da kuma Shaye-shayen data fara babu ji ba gani wanda ya taɓa mata huhunta” Majeederh ta runtse Idanunta tsamtsam tausayin ƴar uwarta ya kamata da kuma dalilin mutuwarta ta.
“Allah ya jiƙanki Rumaisa, Ubangiji ya yafe miki zunubanki ya kai ranki zuwa Aljanna maɗaukakiya” Ta juya ta ce “Me ake jira ba a yi mata wanka ba?” Sukayi shiru Aaliyyah ta ce “Wai tsoran taɓa ta suke ji” Da mamaki take kallon su bata ce komai ba, ta miƙe tsaye ta ce “Akwai ruwan zafi ko? Sabulu? turare?” Aaliyyah ta ce “Eh” Jee ta ce “Aaliyyah ku sauya parlour ki duba handbag ɗina za kiga Kur’ani mai ƴa ƴa ki bawa kowa inda zai karanta” Ta miƙe duka sauran suka bita, su Yaya Bilkisu ma fita sukayi, Majeederh ta zauna cike da ƙarfin zuciya da kuma dakiya ta wanke Ruma tas da taimakon Zaleehat sukai mata sutura, hawaye na fita daga idanun Majeederh ta shiga zuba mata addu’o”in samun rahamar Ubangiji tana zaune, tattausar muryarsa ta fara shiga kunnenta ta hanyar yin sallama sai kuma Barrister Aliyu Sufyan, daga nan sai Akeeth sai kuma Jawaad sune suka kama Ruma tare da sanyata cikin makara, idanun Takawa zube akan Jee ganin yadda take ta kuka idanunta har ya kumbura duk abubuwan da Ruma ta yi mata amma yanzu kukan rashinta takeyi? Lallai tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa sai Allah.
Abbu ya ce babu zaman makoki ranan uku za a mata sadaka da bakwai kowa ya tafi gida. Ummie na zaune a wani parlour dake gidan ita kaɗai ce sai Takawa daya shigo ba jimawa ya ɗan shige jikinta, dauriya kawai take amma sam bata son ƙamshin turarensa cikinta wani irin juyawa yake ta ce “Ina Fulanin?”
“Wa?” Ummie ta harare shi domin tasan maganar ce baya son yi doguwa, ta ce “Ka je ka ɗauki iyalanka ku tafi gida dare ya yi sosai, ga Prince Alhassan nan sai jan yaran jama’a yake da faɗa” Takawa ya yi shiru bai san ta inda zai fara mata bayanin cewa Majeederh taƙi sauraren shi ba, ita dole tana nan har sadakar bakwai da sauri yaga Ummie ta ture shi tana riƙe ciki ta nufi toilet kai tsaye wajen sink ta shiga kwarara amai. Takawa ya yi tsaye yana kallon ikon Allah shi dai ya san Ummie ƙalau take tun kafin su zo Naija yana shan tambayarta a waya tana lafiya? Yana tsaye ta fito ta kasa haɗa ido da shi, ya dinga kallon yadda ta sake haske ta yi kyau sosai da wata ƙiba sai kawai ya lumshe idanunsa ya ɗan yi murmushin gefe, Ummie ta ce “Me kakewa lumshe ido?” Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba ya fita a hanya yaci karo da Uncle Isma’il ya yi saurin juyawa ya bi ta wata hanyar Uncle Isma’il ya samu Ummie zaune tana ganinsa ta ɗan miƙe tsaye ya ƙarasa inda take yana kama hannunta ya ce “Aman kika sake?” Ta yi shiru sai kawai ta shige jikinsa ya rungumeta sosai yana jin zafin da jikinta ya yi ya ce “Kai, bari na kira Khalil ya duba ki the temperature is too high” Ummie ta girgiza kai a hankali ta ce
“Zaiyi noticing ina da juna biyu banaso” Ya ce “Miye baki so ɗin?” Ta ce “Yasan ina da ciki, yasan me na yi” Uncle Isma’il ya yi dariya sosai ya ce “Kuma kina da gaskiya, amma ai ya san ba a shan ciki a ruwa ko? Kuma yasan kina da aure” Wayar Uncle Isma’il data fara ƙara ya sanya Ummie yin shiru ya ɗauka yana sawa a handsfree muryar Khalil ya ratsa kunnen Ummie da yake cewa “Uncle ka ɗauki Ummie zuwa gida, ta sha paracetamol zazzaɓin zaiwa babyn illa” Yana faɗin hakan ya kashe kiran, Ummie ta fashe da kuka ita daga yau ba zata sake bari su haɗu da Khalil ba.
Rayuwa ta fara gangarawa har aka manta da Ruma sai mikin abin dake maƙale a zuciyar Abbu yana ganin kamar shi ne silar faruwar komai, ya dinga neman yafiya wajen Ubangiji. Ko wanne ɓangaren na zaman gidan auren suna yin sane cikin kwanciyar hankali sai abinda ba’a rasa ba, Musamman Fatymerh da Akeeth ya cike mata dukkan gurbin data rasa bai taɓa mata gori na daga ƙaddarorinta ba, da rashin samunta a cikakkiyar mace ta yi kuka sosai ta bashi haƙuri ya ce “Ba komai, ba don haka ya aureta ba kawai sonta yake” Kasancewar shi jinin Yoruba yasa muguwar soyayyar shi ta kama zuciyar Fatymerh bata ganin kowa sai mijinta Akeeth. Haka Zizi da Badi ko wacce rayuwar aure ta yi mata daɗi lokaci zuwa lokaci suna zuwa wajen babarsu taƙi yarda ta musulunta har lokacin. Rukunin Gang team suka sake haɗewa a wannan karan zuwa nagartattun mutane suka haɗa hannu wajen buɗe company ɗaya mai suna MIJIN MALAMA Oil and gas… John yaransa biyu da mai sunan Takawa da mai sunan Majeederh a cewarsa sune ƴan uwansa sun gama yi masa komai a rayuwa.
Ummie ta haifi kyakkyawar yarinya mace zallar kyau na yarinyar ya ɓaci, taci suna Nana A’ishah ana ce mata Diyanerh, haihuwar Ummie da kwana biyar Majeederh ta sauka wannan karan ma namiji ta haifa jajur da shi so ma sha Allah, cikakken Balarabe haka yaron ya tashi suka sanya masa Sunan Abbu ana kiransa Arjun, Idan Takawa Khalil ya juya yaga Yaa K, yaga Alhassan da Al’hussain yaga Soha da Noha ga kuma Arjun sai ya rungume Majeederh yana cewa “Thank you” Daga nan kuma haihuwar ta ɗan tsaya mata ba tare da planning ba kawai daga Allah, tuni ta sauke farali da aikin hajji haka su Alhassan duk sun jima da zama alhazawa.
After 5yrs
Abubuwa da yawa sun faru hadda rasuwar Innati, Bayan Diyanerh Ummie ta sake haihuwar yara twins daga nan kowa ya fahimci haihuwar tagwaye a jininsu yake, rayuwar ta sauyawa Uncle Isma’il albarkacin zumuncin daya riƙe, Aaliyyah yaranta uku ta ɗauki ɗaya ta bawa Latifa suna zaune lafiya har yanzu dai Aliyu bai sake mata sosai ba, he just believed yana sonta tunda ya kasa manna mata takardar saki,ya ƙara zama cikakken lawyer wanda samun ganinsa ma aiki ne, ya tashi daga gidan nan ya koma G.R.A
Jawaad ya zama babban Ɗan jarida (ALLAH YANA GANI). Akeeth kuma yana riƙe da kujerar Gwamna domin harkar Demokrad’iyya ya shiga ba ji ba gani, Fatymerh ta zama first lady. Maryam ta gano asalin waye mijinta Almustapha ta tayar da hankali ya saketa gashi yana sonta kamar rai sai da taga zai zauce ta koma gidansa bayan ta tabbatar ya daina abinda yakeyi. Gidan Uncle Bello lafiya suke zaune Bilal ya dawo gidan da zama gabaɗaya.
Majeederh na tsaye tana haɗa fruits salad,ta idar da sallar zhur ɗinta kenan ga zuma a wani ɗan silver kwano mai kyau tun daga bakin ƙofa ta ji ana cewa “Aby, Mimi we’re back” Ta sauke lallausan murmushi tana juyawa idanunta ya sauka akan jaruman yaran nata wanda suke da shekaru 20 20, amma girman jikinsu yafi na ɗan 25 zuwa 30 Al’hussain ya ƙarasa ya rungumeta ya ce “I miss you so much Mimi, Our Fulani Kingdom” Ta rungume shi ta ce “Welcome darling” Alhassan ya haɗe fuska hannunsa zube cikin Aljihu suit ɗinsa sai ɗaɗɗaga shoulders yake daidai nan Takawa ya fito an fara manyanta ya ɗan saki tattausan murmushi idanunsa akan Alhassan da sauri Alhassan ya rungume Takawa ya ce
“Aby..” Takawa ya ce “Prince! my photocopy” Gabaɗaya suka zauna Arjun ya shigo ya nufi wajen Majeederh domin jin kansa yake kamar auta gabaɗaya a lokacin shi kansa Takawa bai san akwai shigar ƙaramin ciki a jikin nata ba, ta ce “To ƴan Singapore ya ƙasar?” Al’hussain ya ce “Good” Alhassan baiyi magana ba idanunsa rufe bacci ya ke ji can ya buɗe ido ya ce “Where is Soha?” Daga baya aka ce “am here brother” cikin masifa ya ce “How many times zan faɗa miki ki daina posting pictures ɗinki a social media, more especially Twitter? How many times eh?” Ta yi shiru Yaa K ya ce “Masifaffen gidanmu ya dawo, Allah ya baka haƙuri ba zata sake ba daga yau” Takawa Khalil kallon yaran nasa yake musamman da Noha ta shigo yanzu daga school itama ya juya ya kalli Majeederh ya lumshe idanunsa a hankali ya ce “Alhamdulillah” Da daddare Takawa yana turakarsa ya gama shirin kwanciya Majeederh ta shigo ya bita da kallo sosai can ya ce “You’re pregnant” Ta buɗe ido sosai ta ce “How do you know?” Ya ɗan watsa mata kallon So kafin ya ce “Idan kina da ciki kinfi buƙatar Takawa fiye da ko wanne lokaci” Ya miƙa mata hannu ta kama ya zauna tare da ɗorata a cinya yana shafa cikinta can ya ce “Queen Majeederh” Ta ce “Sarkina” Idanunsa rufe ya ce “ALLAH ya yi miki Albarka, ke ɗin ƴar Aljanna ce” Ta rungumesa ta ce
“Mata da yawa na cewa; duk wacce ta ɗauki Miji uba zata mutu marainiya, Jarumin mijina ya rusa wannan faɗar tasu a zuciyata, haƙika babu wani abu mai muhimmanci ga rayuwar mace wanda ya a shige gidan mijinta, domin shi ne ni’imarta, kai ɗin tsagina ne, kamar yadda bango ba zai zauna ba sai da tsaginsa, kamar yadda kifi ba zai rayuwa ba sai yana cikin ruwa, haka zalika rayuwa bata yiyuwa sai da numfashi a ƙirjin mutum, mizani da idan ba ruwa ba ɗan adam gwargwadon yadda ƙaddarori suke juyewa zuwa abu mai kyau shi ne tubalin yadda Majeederh ba zata iya rayuwa babu mijinta Mai martaba Ibrahimul-khalil ba, duk wanda yake tunanin zai rabamu ya ɗauka mafarki yakeyi, kamar yadda duk wanda ya ce wutar kara ta kwana to shi ne ya kwana bai yi bacci ba, Malama da MIJIN MALAMA mutu ka raba, ko ita ina fatan ta fara ɗauke ni kafin Takawa”. Takawa ya rasa bakin magana sai kawai ya rungumeta sosai yana jin ta cike masa komai na rayuwa baya buri daya shige ya kyautata mata ta zama cikakkiyar House Wife bata da aiki sai na kula da mijinta da yaranta, a hankali ya shiga kissing ɗinta tun suna zaune har suka zame suka sauka ƙasan carpet daga nan kuma suka faɗa wata duniyar ta daban, kasancewar sun jima rabon su da Naija ga kuma yanzu Fatymerh ta haihu yasa Takawa saka Alhassan ya fara musu shirye shiryen tafiya cikin kwanaki biyu jirginsu ya ɗaga, Alhassan farin cikinsa ɗaya akwai wacce idanunsa yake son gani, Soha bata wani farin ciki domin bata damu da wasu family ba. A gidansu suka sauka a daren kuma Majeederh ta nufi gidan Fatymerh domin shirye-shiryen suna, Takawa ya dinga juyi ya kasa bacci matarsa kawai yake buƙatar gani da jin ɗumin jikinta ya duba agogo yaga ƙarfe biyu, jallabiya ya saka ya fito ya shiga mota, yana fita Alhassan ya fito a daidai lokaci guda suka isa gidan Akeeth kowa ya yi parking motarsa daga nesa da gidan, Khalil ya manta matsayinsa na sarki ya leƙa yaga ba kowa sai mai gadi ya kama katanga ya durga ciki, Alhassan ma ya durga Khalil bai san da zuwan Alhassan ba, amma shi Alhassan yana ganin mahaifin nasa. Ɓangare daban-daban suka nufa Alhassan wajen Abra, ya bi ta window ya shiga bedroom ɗin ta. Majeederh na tsaye tana ƙoƙarin kwanciya a gajiye take sosai kamar daga sama taga an diro ta window an kuma kashe switch na bedroom ɗin, tana ƙoƙarin yin magana aka rungumeta ta baya, a hankali ya manne mararsu waje guda a kiɗime ta ce “Who are you, wa..waye?” Yaƙi magana hannunsa ya sanya ya farke ƴar rigar baccin dake jikinta yana sake rungumeta tare da shinshina wuyanta ta ce “Waye?” Muryarsa na rawa saboda abubuwan da yake ji da ƙyar ya iya furta maganar cikin ƙasa da murya ya ce “MIJIN MALAMA”.
Allhamdulillah!
Komai ya yi farko yana da ƙarshe, ba zan ce labarin nan ya yi 💯 hundred patient ba, duk iyawarka dole ne ka samu kuskure ta wani gefen, ɗan adam ajizi ne mu zama masu uzuri. Bana da ƙarfin qiwar cewa na iya, amma ina da yaƙini na abinda zuciya ke ayyana mini harna rubuta, ba zance Rubutana yafi na kowa ba, domin ban san kowa ɗin ba, abu ɗaya na sani nawa Al’ƙalamin a kaifafe yake musamman ta ɓangaren zanen ƙaddara, ban yarda akwai happily ever after ba, ba kuma zan taɓa gasgata akwai zama na har abada tsakanin ma’aurata babu wani tasgaro ba, ba zan lamunci rashin jarabta ba, domin ƙara gasgata imanin mutum ƙaddara take, ban yarda jarumi baya mutuwa ba, domin kullum akan idanunmu mutane sun sha mutuwa, Miji ya mutu, mata ta mutu,ko iyaye, kenan zanen ƙaddara na rubutun ƙagaggen labarin daya samu nagarta ga mai yinsa done zanen ya zo mana haɗe da sunan mutuwa, a zamantakewa dole mu yarda da Sadaukarwa kuma tilastawa kanmu fahimtar ba komai muke nema mu samu ba, ko da alheri ni garemu SOYAYYA a zane take da rubutacciyar Tawada a rayuwar ko wanne. Kullum mata sune masu rauni, kullum sune suke wahala a labari shin baza kuzo rawar ta sauya zani ba? Kullum cikin force marriage ake ba zaku so wani abu wanda ba wannan ba? Me ya sa kawai namiji ke ganin mace ya ce yana so, ita macen bata da zuciya ne?…. Mu tara a littafina na gaba.
Na gina labarin Mijin Malama akan tasirin Ƙaddara, yarda da ita a matsayin mutum Musulmi, illar da ƙawaye sukewa aminansu, da kuma sadaukarwa, komai girman tawadi’unka da ilimin Addinin da kake da shi Ubangiji na iya jarabtarka, haka JINKIRIN AUREN na zuwa ta hanya daban-daban.
Godiya.
Na gode sosai bisa jumirin bina da kukai tun daga farko har ƙarshe, godiya ga Arewabooks followers wanda bakwa gajiya da sanya kuɗinku wajan siya, ALLAH ya ƙara arziƙi wadata da imani y sanya kuci gaba da bibiyata a ko wanne littafi.
Tambaya?
1.Mene kuskuren labarin?
2. Dame ka ƙaru a labarin?
3. Mene yafi birgeka a labarin?
4. Mene saƙonka zuwa ga marubuciyar MIJIN MALAMA?
5. Wanne kallo ku kaiwa rayuwar Malama Majeederh Abdul’aziz Khan da Dr Ibrahimul-khalil?
6. Wanne salo kuke son na sauya a labarina zuwa gaba?.
Ina da labarai uku masu inganci ko wanne yana da amfani kuma sun sha banban da Mijin Malama na rasa wanne zan muku next faɗi zaɓi ka wanne kafi so?
1.JOURNALIST LATIF
{Allah yana gani}
2. RUHI BIYU
3. MUNAFIKIN MIJI
4. ƊAN MALAM
Yi comment da wanda ka fi so, wanda aka fi zaɓa shi za a fara yi, kuma zai fara sauka ne a Arewabooks.
COMMENT
FOLLOW MY ACCOUNT ON AREWABOOKS
NA’IMA SULAIMAN SARAUTA
NIMCYLUV
08119237616
Kuyi magana na yi adding naku group ɗina mu tattauna.