Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 44

Sponsored Links

XLIV…
(44)

 

*Munayamaleek is 500 naira via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, evidence of payment to 07082281566(Dan girman Allah idan baki shirya siya ba don’t chat Me please)*

Related Articles

“Mun tashi lafiya Maleek?” Hajiya Sa’adah data fito daga dakin ta ta fada.

Maleek yayi kamar bai san da halittar ta a wajen ba, ya wuce ta zuwa dinning table.

Jikin Hajiya Sa’adah yayi wani mugun sanyi, ta juya zuwa dakin ta, kila da Maleek ɗin ya kalle ta daya tausaya mata, domin wata rama da duhu data kara yi, zaman gidan ya daina mata dad’i tuntuni saboda kadai ci daya mata yawa.

“Abinci bai baka bane Maleek?” Alhaji Dawood ya fada ganin yana rike da cokali shi bai ci abincin ba.

 

“Maleek ya ajiye cokalin hannun sa, ya saka hannu yana yamutsa goshin sa, yana jin yunwa, sai dai bashi da appetite din cin abinci, duk haduwa da dandanon abincin ji yake kamar magani ne.

“AbdulMaleek!” Alhaji Dawood ya sake kira sunan sa cikin kulawa kana yace ” ko baka son abincin yan aiki?” Nan ma yayi shiru, Alhaji Dawood ya kara da cewa “haka zaka yi hakuri zuwa lokacin da zaka yi aure kaga ka huta da cin girkin su ko?” Alhaji Dawood ya fada domin a tunanin sa damuwar Maleek din kenan.

Kalmar auren da Alhaji Dawood ya ambata sai ya motsa masa Abin da yake caccakar zuciyar sa ya kuma hanata sukuni, amma har yanzu ya gagara fahimtar Asalin abinda ke dagula zuciyar ta sa.

“Maleek” Alhaji Dawood ya kara kiran sa a karo na uku domin zuwa yanzu ya gama fahimtar cewa dansa na Cikin damuwa.

“Menene yake damun ka?” Ya fada shima yana ajiye cokalin hannun sa.

“Babu komai” ya amsa yana murza yatsun sa cikin na juna.

Alhaji Dawood yace “tell me what’s your problem son, na san cewa baka da abokin shawara sai maragayi Shakur, tunda Allah daya fimu son sa ya ɗauke shi, then make me your best friend, ba iya mahaifi nake a gare ka ba, nima abokin ka ne mai iya baka shawara, so feel free and talk to your new friend Maleek” Alhaji Dawood ya fada yana dafa hannun sa.

“Dad ban san abinda ke damuna ba, kirji na nauyi yake min” ya fada yana dafe saitin zuciyar sa.

“Subhanallah! Ka yawaita addua da karatun Alqur’ani, nima zan taya ka kaji ko? Sannan idan ka taba bata wa wata ko wani rai ko yin wani abu na cutar wa ga Mutum, ka nemi yafiya, kada ka taba raina hakkin dan Adam komai kankantar sa, idan kayi hakan You will find peace in your heart, ka yi amfani da Shawara ta ka gani, domin ina gaya maka hakan ne from experience”

“Thanks Dad” yace, yayinda yake son fahimtar maganar mahaifin na sa da kyau, domin magana yake masa mai kama da gugar zana.

Alhaji Dawood yace “You re welcome”

Shiru ya ratsa tsakanin su tsawon mintuna goma sannan Alhaji Dawood yace “menene asalin sunan yarinyar wajen ka?”

Cikin jin nauyin mahaifin na sa yace “Nabeelah”

“Madallah, Allah ya raya ta, Ni tana min kama da bilkeesu, dan dai hasken ka ta dauko, bansani ba ko Ni kadai ke ganin hakan? Na san da bilkeesu na raye da sai taji kamar ta hadiye ta ɗan son, tana matukar kaunar fararen yara, gashi Allah ya bata amma bata rayu da shi ba, Allah ya jikan ki bilkeesu” ya cikin sanyin murya, domin kuwa har gobe yana kaunar bilkeesu Sa, kuma mahaifiya ga Maleek.

Maleek ya dago kansa yace ” Ameen, I wish na San ta”

“Daka so ta sosai Maleek domin tana kyawawan halaye, macece mai Addini, i miss bilkeesu” Alhaji Dawood yace domin tsohuwar soyayya ce ta motsa, gashi bata raye ɓalle ya nuna mata son.

“How much did you love her dad?”

“With All my heart son”

Maleek ya rufe idanun sa yana son tambayar mahaifin sa wani abu, amma yana fargaban amsar da zai bashi.

Ya daure yace “how do love feel dad?”

Alhaji Dawood yayi murmushin jin dadi, domin tunda Shakur ya rasu shekaru kusan uku kenan basu kara zama sun yi hira irin na Yau da Maleek ba”

“It feels great and amazing, musamman idan kuna son junanku, ka san when I first met your mum, ban san ina son ta ba, domin yaya Laraba ce ta haɗa mu, sai bayan mun zauna inuwa daya da ita, i mean after our weeding muka fahimci muna son juna, gaya min ka fara son wata ne?”

Maleek ya girgiza kansa cikin sauri.
Alhaji Dawood yace toh “Meyasa kake mun tambayoyi irin haka, sannan yarinyar nan Munaya ba soyayya kuke ba, why cant you settle down with her tunda har ƙaddara ta fada kuna y’a a tsakanin ku?”.

“Kawai ina son samun ilimi ne Dad, ba soyayya muke ba” yace yana shafa kansa

“Toh yayi kyau, Allah ya maka zabi na alkhairi”

“Ameen Dad” Maleek ya amsa.

Sai kuma ya ƙara cewa “Dad, menene ma’anar idan ka ga mace tare da wani kuma ka ji ranka ya sosu ”

Alhaji Dawood yayi wani murmushi na manya sannan yace “kishi kenan, idan kuma ana kishin mutum TOH lallai akwai so a wanna muhallin”

“So!?” Yace cikin widening rikatattun idanun sa da mutum Baya sanin suna da girma har sai ya ware su, kasancewar a lumshe suke all the time.

Ya mike cikin sauri yace “Dad zan yi shirin aiki” Alhaji Dawood ya masa fatan dawowa lafiya yana binsa da kallo.

Maleek na Zaune cikin motar sa yayinda yake tunanin hirar su Alhaji Dawood, ya ƙasa yarda cewa zuciyar sa ta kamu da son Munaya, yarinyar daba shiri suke ba tun daga ranar daya fara ganin ta, har yanxu da ƙaddara ta fada musu bata sanja zani ba, lallai zuciyar sa bata yi masa adalci ba, domin data yi shawara da shi da bata kamu da son yarinyar nan ba, domin ta hana zuciyar sa sukuni ba tare da ya sani ba sai yau, ya sauke wani karfaffan ajiyar zuciya, daidai lokacin ya ga wani yaro a babur ya rine kansa, hannun sa kuwa zanen tattoo ne, ya tuna da yana da burin zana tattoo, Amma not anymore, domin mutuwar Shakur ɗin sa da kuma zurfin da yayi a ilimin addini yanzu ya rushe wanna burin na sa, domin kuwa babu abinda ke burge shi kamar ya bude Kur’ani ya ga yana iya karanta wa, dadin da yake ji a zuciyar sa baya mistaltuwa yayinda yake cigaba da juya steering din motar da hannu daya cikin kwarewa, da tunanin munaya a ransa ya isa Companyn sa.

 

Da misalin ƙarfe tara na dare ya fito daga toilet daure da blue din towel a kugun sa, yayinda wani karamin ke kan wuyan sa, ya nufi gaban closet din sa domin fiddo kayan baccin sa, ya mika hannunsa domin janyo tattausan pyjamas mai launin fari ya ji wayarsa ta fara ringing, ya dakata hadi da waiwayowa, bakuwar lamba ya gani, hakan ya saka ya cigaba da abinda ya ke, sai dai har ya sanya kayan ana cigaba da kira, ya saka hannu ya dauki wayar ya daga hadi da karawa a kunnen sa ba tare da yayi magana ba.

“Daddy!” Ya ji karamar Muryar little Amnah kasa kasa.

Ya samu waje ya zauna yana fadin “angel, oh I’m sorry ban san ke bace”

“Daddy Ina ta kiran ka, ina kiran ka baka dagawa, so kake ta kama ni?” Ta ce cikin yarinta tana Turo labban ta.

Ya dafe kansa yana murmushi yace “i said I’m sorry angle, wayar waye kuma waye zai kama ki?”

“Mummy” tace kasa kasa.

“Ina take?”

“Wanka take” little Amnah tace kasa kasa kamar mai yin rada, ya lumshe idanun sa yace “kinyi homework ko?”

“Eh mummy ta koya min, Daddy Ina ta missing dinka shine na kira ka fa”

Yace “i miss You too and I love you my little angle, but how comes kika samu number na”.

Amnah ta kalli kofar toilet din kana tace “ai ranar da aka ce ka bada lambar ka a school dinmu shine har yanxu na riƙe, ka tuna ko Daddy?”

“Yeah yeah yeah, na tuna my angel, mummy ki bata fito ba?” Yace yana kwanciya flat kan gadon.

Ta kai idanun ta ga Kofar tana cewa eh da…” Karaf idanun ta suka tsarke dana Munaya data fito daure da towel a kirjin ta fuskar ta a daure tamau, cikin daga murya tace “da wa kike waya?” Ta tambaye ta, hakan nan ta ji ɓacin ran domin tun Daga lokacin data fito ba tare da sanin little Amnah din ba ta fahimci da baban ta take waya.

“Mummyyy dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba”

“Nace wa kika kiran mun da waya ta?” Munaya ta fada a tsawace, little Amnah ta fashe da kuka tana yarfe hannun ta, Munaya ta cigaba da matsowa kusa da ita yayinda ita kuma little tsanani tsoron ya saka take takurewa jikin bango.

Maleek ya Mike tsaye yana jin zuciyar sa na bugawa, a hargitse yake cewa “angel Meyasa kike kuka, dukan ki tayi?”

Little Amnah na girgiza kanta tace
“Daddy ka cewa wa mummy tayi hakuri, bazan sake ba”

“Angel give her the phone, bata wayar!”
Munaya ta ji yana fada,
Daidai lokacin kuma ta karaso inda ta takure, little Amnah ta Saki ihu.

Maleek ya ji notikan kan sa sun kunce, ya ɗauki mukullin mota da bai san na wani mota bane, yana kokarin bude motar ya ji Muryar Alhaji Dawood ya kwala masa kira.
Ya juyo ba tare da ya iya amsa wa ba.

“Ina zaka a daren nan?”

“Dad Ina zuwa, yanxu zan dawo” yace yana kokarin bude murfin motar.

“Dakata! Ka hakura da koma ina zaka je zuwa gobe idan Allah ya kai mu”

“Dad! Ko da waje mai muhimmanci ne?”

“Duk muhimmancin wajen ka jira gobe, amma yanzu dare yayi” Alhaji Dawood ya fadi haka da juyawa zuwa ciki.

Maleek ya runtse idanun sa, ya jingina Bayan sa da mota, ya fiddo wayarsa daga aljihu ya shiga kiran lambar Munayan, amma taki dagawa, ya kira sau biyar ba response abinda bai taba yiwa ko wani mahaluki ba, saboda tsarin sa ne hakan, idan ya kira mutum sau daya bai yi picking ba baya sake na biyu sai dai a biyo kiran, amma yau Munaya make him break the rule.

Ya shiga ɓangaren message ya shiga typer mata

_idan kika yi kuskuren taba min yarinya bazan gyale ki ba, baki da tausayi ko? Dan me zaki dinga taba min lafiyar yarinya, baki ga tayi kankanta ba_

 

Daga can ɓangaren little Amnah ke kwance a gado sai shesheka take, yayinda munaya ke Zaune bakinciki da takaici ya mamaye zuciyar ta, ta ji shigowar sako, da fari ta share, can kuma ta dauko wayar ta shiga massage din, ganin cewa Maleek ne ya sanya hannun ta na sauri Wurin bashi amsa, ɓacin ranta ya Karu da abubuwan daya ce mata.

_ina ruwan ka da duk abinda nayi mata, ai nina haifi abata_

_baki da kunya ko?_ yace mata.

_wai kura ne yake cewa ƙare maye?_ Munaya ta mayar sa.

Kasancewar Hausa bata wani wadace shi ba ya sanya shi hasala yace

_nine kura da karen?_

Ta yi masa Banza bata ce masa komai ba
ya kara turo wani sakon yace

_ki godewa Allah ban zo gidan nan ba, da kin gane kuran ki_

_Babu abinda ka isa ka min!_

_haka kika ce munaya_

_haka nace Maleek!_

Maleek ya saki wani murmushin takaice, wato yarinyar nan ta gama raina sa, yace

_kina gwada hakuri na ko?_ ya tura yana cije labban sa.

_ka goge lamba ta daga wayar ka, domin ba kowa ke samun mallakar sa ba, sai wanda ya dace ya Kuma cancanta_

Ransa ya ji dadi da abinda tace masa yace _shi waccan da yake da ita cancanta yayi?_

_yafi kowa cancanta_

_kina yaudarar kanki Munaya, ba son sa kike ba_

_ni kuwa nake kaunar ya Abbas, kauna mai tarin yawa_

Halin da kalaman ta suka sanya zuciyar sa ya saka bai cigaba da yi mata text din ba.

Ya dora kansa saman motar, tsawon lokaci ya dauka a haka yana tunanin abin yi.

Munaya kuwa sai data gama biye masa ta ji haushin kanta, da shiru tayi masa, amma yadda ranta ke a bace ya saka ta kasa rike kanta, zuwa Wanna lokacin bai kamata ta bari Maleek yana saka ranta ɓaci ba, halin kuncin daya sanya ta a shekarun baya ya ishe ta, amma taya zata kaurace masa? Bayan little Amnah na nan, duk yanda tayi domin kauracewa duk abinda zai haɗa ta da shi amma sai little tayi wani abin da dole zai haɗa su, ta share wasu hawaye da suka zubo mata, kana ta kalli little Amnah da baccin dole ya ɗauke ta, ta rufe mata blanket, sannan ita ma ta mike domin yin shirin kwanciya, kasancewar tana da wani patient da zata yiwa wankin hakori gobe da safe, so take ta samu tashi da wuri domin fara shirya little, domin bata son makara zuwa aiki, bayan ta goga turaren ta na maiko mai daɗin kamshi ta sanya kayan ɓaccin ta ta kwanta kusa da little Amnah, ta duba babu misscalls ɗin doctor Abbas, tun safe daya kira ta Basu sake waya ba, ta tsara masa gud night massage Ta tura masa sannan ta ajiye wayar kan beside drawer ta lumshe idanun ta tunani mabanbanta na kai kawo a zuciyar ta.

 

#MunayaMaleek 2023
#NoorEemaan
# hatred
# sympathy
#virginity lost
#selfishess
#love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button