Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 47

Sponsored Links

XLVII…
(47)

 

*MunayaMaleek is Five hundred naira, via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566*
_(Don’t call me. Only chat please)_

Related Articles

Sai dai ayoyi sha biyar Maleek ya iya karantawa Muryar sa ta shiga rawa, hawaye ya cika idanun sa, ya dakata hadi da ciro hankici ya goge idanun, ya kara saita abin maganar domin ya cigaba ya kasa, amon sautin Muryar sa dake fidda alamun kuka ya karade kunnuwan jama’ar wajen, da yawan jama’ar wajen sai da zuciyoyin su ya karye, wasu suka fidda kwalla, yayinda wani sabon imani na kara shigar su, kusan kowa so yake ya masa video da wayar sa hasken Camera ya cika ta ko ina, duk da akwai *Camera man* da aka dauko musamman Domin yin video recording.
Ɗaya daga cikin babban malamin makarantar ya zo ya riƙe hannun sa ya dawo da shi wajen zaman sa, yana dan bubbuga kafadar sa, abokan saukan sa kuwa suma patting bayan sa suka yi domin they know how it feel, Maleek kuwa ji yake dama Shakur dinsa na nan, Lallai daya fishi farin cikin ganin wanna ranar, tabbatuwar wanna rana Shakur ɗin sa ne sila, ya furzar da wani numfashi mai Dumi daga bakin sa, a ransa yace “dear brother I wish you re here with me”
Ya dago kansa daidai lokacin daya hango Alhaji Dawood na masa murmushi har yanzu da kwalla a idanun sa, ya mayar Wa mahaifin sa da murmushin.

Alhaji Dawood ya kasance da dan nasa har taron ya watse, suna hanayar komawa gida yayinda Maleek ne ke tuka su, Alhaji Dawood yace “You made me a proud father, Ina alfahari da kai AbdulMaleek, Allah ya maka albarka”

“Ameen Dad” Maleek ya amsa yana cigaba da murza sitiyarin mota cikin kwarewa, a yau yana jin farin ciki, wanda rabon daya yi ji hakan tun sanda ya rasa Shakur.

“Cikin next week zaka Kai ni gidan da jikata da take, it’s high time she knows I’m her grandpa”

Maleek Bai yi tsammanin wanna maganar daga wajen Daddyn na sa ba, ya shafa kansa da hannun sa na hagu kana ya kara mayar wa kan sitiyarin yace “okay Dad”

 

Kamar yadda Alhaji Dawood ya fada ranar juma’a ya saka Maleek kai shi gidan doctor Aaban, ya kira Munaya Domin ya sanar mata duk da yasan ba zata daga ba, sai kuma ya samu wayar ta a kashe, dole haka suka taho gidan, biyar da yan mintuna suka isa gidan.

Bayan an musu iso, Alhaji Dawood yayi godiya sosai ga barrister da mijin ta da kuma basu hakuri kan abinda ya faru tsakanin MunayaMaleek, domin a tunanin sa barrister Abrar aunt ɗin munaya ce ko kuma doctor Aaban ya’yan ta ne.

A sanyaye Munaya ke shafa soso a jikin ta kasancewar har yanxu bata dawo daidai daga rabuwa da doctor Abbas ba, kawai taji little ta shigo dakin tana kwalla mata kira “mummyyy kizo, Daddy na ya zo da wani tsohon Daddy”

Munaya ta yi katse ki, da tunanin wani tsohon Daddy Kuma? Ta dauraye jikin ta hadi da daura towel ta fito, sama sama ta shafa mai, ta murza turaren ta na maiko mai daɗin kamshi a jikin ta kana ta saka wani pencil skirt baki da yellown riga, sosai hadaddiyar surar ta ya fito, musamman hips ɗin ta, ta kara gyara gashin ta, sannan ta dauko dogon hijab dinta kalar ruwan toka ta sanya, kafin ta karaso falon ta hango Maleek zaune da mahaifin sa domin ta riga ta shaida shi, hankalin ta ta ji ya tashi, tsoro ya shige ta toh Meya kawo su, tunani mabanbanta ya cika zuciyar ta ciki har raba ta da little suka zo yi.

“Yawwa gata nan ma” barrister Abrar ta fada tana kallon Munayan dake tsaye.

Idanun su ya dawo kanta,
Hakan ya saka Munaya boye damuwar ta, ta taho a hankali, tayi sallama, kana ta tsugunna dan nesa da Alhaji Dawood ɗin tace “ina wuni”

Lallai ƙaddara ce ta fada musu kamar yadda maragayi Shakur ya fada, domin nutsuwa mai tarin yawa ya gani a tare da munayan.
“Lafiya Lou, ya aiki da kokari?” Alhaji Dawood din ya fada.

“Lafiya Lou” munaya ta amsa kanta a kasa sosai.

“Toh Allah ya miki albarka”

“Ameen” Munaya ta amsa, yayinda tsoran na ke raguwa, musamman ganin Alhaji Dawood na mata fara’a sosai.

Little ta baro wajen Daddyn ta ta dane jikin Munaya tana cewa “mummy kin ga abinda tsohon Daddy nan ya bani” ta fada tana nuna mata bandir din dari biyar dake hannun ta,
Sai yanxtu ta lura ashe har da su mimi aka bawa.

“Kin yi godiya?” Munaya ta tambaye ta kasa kasa.

Little ta bude murya tace “eh nace angode, ko tsohon Daddy?”

“Haba matata nine tsohon?” Alhaji Dawood ya fada cikin barkwanci.

Little ta kwalalo ido “kai mummy wai nice matar sa?” ta ce kamar zata saki kuka.

Aka kwashe da dariya, Munaya ta ɗora hannun ta kan labban ta, surutun little yayi yawa, wani zubin har kunya take ji idan tayi magana ita yar ba ruwana ce.

Munaya ta dago kanta jin ana knocking kofa, kawai sai idanun ta suka sarke dana Maleek daya Zuba mata rikatattun idanun sa, ta kauda kanta gefe tana tsuke labban ta, ya bi ta da kallo yayinda ta nufi Kofar, ta saka hannu ta bude.

“Ammi!” Munaya Tace tana murmushi Hadi da bata hanya.

“Munaya ya gida?”

“Lafiya Lou Ammi, sannu da zuwa”

“Yawwa yar albarka”ta amsa tana sallama.

Aka shiga gagaisawa, yayinda doctor Aaban ya durkusa gaban Ammin yana gaida ta cikin girmamawa surukar ta sa, ta amsa da saka masa albarka, barrister ma sai murmushi take Ammin ta ta zo gidan ta wanda takan jima kafin ta yarda ta zo, sai dai su je can wajen ta, Munaya ta je ta kawo mata abinci da abin sha, ta na jera mata taji barrister na cewa “Ammi ga fa Daddyn little Amnah” ta fada tana nuna Maleek.

“Allah Sarki” Ammin ta fada tana kallon Maleek.

Munaya na gama jera wa Ammi abincin ta koma dakin ta, domin haushin irin kallon da Maleek ke Binta da shi take.
Maleek kuwa ji yayi kamar ya hana ta tafiya, gaba-daya ya rasa sukuni, sosai zuciyarsa ta yi nutso da kamuwa da mugun son ta da bai san yaushe ba, amma yanda yake jin ta cika kirjinsa gani yake tamkar ya rayu da son ta tsawon lokaci ne.

*Bayan sati biyu*

*MALEEK*
_9:01am_

“Ya zaka tashi baka ci komai ba, ka daure ka saka wani abu a cikin ka” Alhaji Dawood ya fada wa Maleek.

Maleek ya girgiza kansa domin wani azababen ciwo yake ji daga can wajen haƙoran sa na ƙarshe, ko ruwa baya son sha saboda radaddin har ciwon kai yake saka masa, kwana uku kenan yana fama da ciwon amma na yau yayi worst.

“Ya kamata Kaje asibiti a duba maka ”

yace “eh yanzu zani ”

“Allah ya sauke wa ”

Maleek yace “Ameen” kana ya dauki mukullin mota ya fita.

Alhaji Dawood ya cigaba da cin abincin sa ya ji fitowar mutum, amma bai ko kalli wajen ba domin ya san ko wacece.

Ta dawo wata bakuwa a gidan, yayinda yan aiki ma sun fi ta sakin jiki a gidan, kamar basu taba rayuwar aure a tsakanin ta da Alhaji Dawood ba, babu wanda ya ce mata komai ko hattarar ta amma ita a karan kanta bata da sukuni a ran ta, a hankali tace “Alhaji dan Allah ina son zuwa asibiti ne”

“Okay, zan tura miki kudi yanzu” daga haka Alhaji Dawood din bai kara cewa komai ba, kamar yadda bai kalle ta ba.

Hajiya Sa’adah ba haka take son ji ba, domin kudi ba matsalar ta ba bace, tana da kudaden ta, duk da Babu aure a tsakanin su amma zuciyar ta na muradin kulawar sa, Lallai son zuciya ɓacin ta, domin da ace da ne, da kansa zai dauke ta ya Kai ta asibiti, amma yanzu ta rasa soyayya da yarda dake tsakanin su ɓalle ts samu kallon arziki, ta tarwatsa gidan, ta rushe kyawawar halaka dake tsakanin su, ta juya jiki a mace ta koma dakin ta.

*Smile brighter at Abuja’s best*

Shi ya gani a rubuce a gaban wani babban symbol din dental clinic ɗin.

Babban waje ne sosai, ya nufi haraban wajen da motar sa kana ya fito ya shiga.

Yayi musu complaining abinda ke damun sa, wata dentist ta yankar masa card da yin duk wani cike-cike da tsarin cilnic ɗin ya tanada, Maleek na tsaye ta nufi wani daki, inda wata dentist ɗin ke zaune Cikin gogaggun uniform din ta, wacce ta shigo tace “M jabir, ga wani patient, Ni ina da appointment da wata yanzu, sauran ma na ga they are busy ”

“Okay ba matsala” dentist ɗin dake zaune ta fada, yayinda wacce ta shigo din ta sanar da Maleek zai iya shiga.

Dentist din nan ta mike ta dauki Safar hannu zata saka kenan aka turo kofar da sallama, ta saki Safar hannun kasa, yayinda shima Maleek ya waro idanun sa, domin he wasn’t expecting ganin ta, har wani sauki ya ji ya samu daya ga abinda bai yi tsammanin gani ba,

“Daddy!” Ya ji muryar yarsa, ya kalli inda take zaune, ya nufe ta, yana cewa “my angel”

“Daddy kai ma ba ka da lafiya kamar Ni?”

Ya kalle ta da sauri yace “baki da lafiya?”

“Eh Daddy, jiya dadaddare na dinga amai sosai fa, shine yau da mummy zata zo aiki na dinga kuka zan bita shine ta zo da ni”

Ya taba goshin ta yaji na zafi yace “how are you feeling now?”

“I’m fine now Daddy ”

“I’m glad you’re fine now ” ya fada yana mikewa.

Ya kalli Munaya data koma ta zaune, ya nufi ta, ya saka hannu a gefe da gefen kujerar da take zaune yace “baki fada min yarinya ta bata da lafiya ba, why?”

Sai da Munaya ta ɗauke numfashi a boye domin ƙamshin sa ya cika mata hanci, ta daure fuskar ta fiye da yanda tayi a lokacin ɗaya shigo tace
“Saboda me zan fada maka?”

Kamar mai yin rada yace “saboda ni mahaifin ta ne ina da hakkin sani”

“Kin yi shiru” ya kara faɗa

“Toh Baga shi ka sani ba” tace tana kauda kanta gefe amma babu abinda ya sanja domin har kayan jikin ta take jin kamshin sa ya kama.

“Zan yi miki hukunci matukar kina min wasa da yarinya”
Ya fada yana mikewa tsaye, munaya ta balla masa wata harara, karaf ya kama ta yace

“Ni kike wa haka?”

Ta masa Banza, ya ɗan dafa gefen kumatun sa jin Wajen ya kara motsa masa da ciwo, ita kuwa ta shiga danna wayar ta, yace “haka ake tarban patient?”

“Na ga kalau kake”

Ya san magana ta gaya masa, ya riga ya san zai sha fama da ita, yace “da gaske ban da lafiya, zo ki duba min”

Bata masa magana ba ba ta nuna masa gadon da zai kwanta da hannu, bai ja magana ba ya nufi gadon ya hau, ko Safar hannu bata saka ba ta nufi shi, wanda ya saba ka’idar aikin ta, amma bata son duba sa ne, ɗan dai rashin duba sa zai iya shafar aikin ta.
Ta dauko wani karamin na’ura dake jona jikin wani madaidaicin computer, fuska da muryar ta a daure ta ce

“bude bakin ka”

Sai ta ga labbansa ya tale da murmushi yana kallon ta, ta turo labban ta tace “kana bata min lokaci”

“Na Kama ki, dama ke kika koyawa angle turo baki ko?” yace yana bude bakin sa, amma bai mata yanda take so ba tace

“widen your mouth again”

ya kara ware baƙin hakan yasa ta hango dukkanin haƙoran sa da cikin su babu datti ɓalle sauya kala, ta saka dan na’uran nan a bakin sa, take Cikin Bakin sa ya bayyana a allon computer nan, ta hango inda ya tara wani ruwa mai kauri daidai wajen haƙorin sa na ƙarshe.

Ta cire na’uran ta zura hannun ta domin yin aikin ta ta ji ya kamo yatsan ta daya sha jan lalle da lallausan harshen sa mai Dumi, wani abu ta ji yammmm ya ratsa jikin ta, saboda yanda ranta ya ɓaci bata san lokacin data dan buge gefen kumatun sa da hannun ta ba, ya saki dariya mara sauti yana sakin yatsan ta, ta saka tissue tana goge yatsan na ta, ganin da gaske barin sa zata yi ya sa shi cewa “na daina”

Ta dawo fuskar nan a haɗe little Amnah data ji su shiru kasancewar akwai labule a jikin gadon tace “mummyyy allura kike wa Daddy ne? Dan Allah kar ki yiwa Daddy na allura”

“Will you keep quiet” Munaya da ta leko kanta daga cikin labulen ta fada, little ta tabe baki alamun kuka zata yi.

A hankali Maleek yace ” ai ta damu da lafiyar Daddyn ta ne ya zaki ce tayi shiru, tunda ke ba ruwan ki da lafiya ta”

Ta masa Banza, ta saka hannu ta ta danne Wajen yayinda Maleek ya runtse idanun sa, tuss wajen ya fashe, Maleek ya ji dumin ruwa mai kauri ya cika bakin sa, Munaya ta wanke masa hadi da yi masa treatment din daya kamata.

Ta shige toilet din ta ta wanko hannun ta da handwash ta fito, ta tarar ya zauna kan kujerar ta, bata ko yi kusa da wajen da yake ba ta nufi inda little Amnah take ta zauna gefen ta.

MALEEK ya kasa dauke idanun sa daga kanta domin ta matukar yi masa kyau cikin uniform ɗin.

“Zaka iya tafiya” Munaya tace ba tare da ta kalle shi ba, domin kallon sa duk ya hanata sukuni.

Budar bakin sa yace “yunwa nake ji” ya fada yana shafa cikin sa.

Munaya ta watsa masa wani kallon, irin ina ruwana, ni ke baka abinci da?”

Mayyar baban ta little kuwa tace “Daddy mummy ta zo mana da abinci da yawa wanda zamu ci anjima, Kai ma zaka ji?”

Ya jinjina kai yana murmushi, little jiki na rawa ta kimkimi warmer zata kai masa Munaya tace “mayar min!”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button