Hausa NovelsNi da Almajirina Hausa Novel

Ni da Almajirina 11

Sponsored Links

NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

A BIG THANKS TO MY SUPPORTIVE READERS

Me awaran yan gayu
Mrs Suleiman
Mrs Chief
Sofiyah Muhammad Abdullahi
Umu Afrah
Mrs
Amina Kabeer’s Caps
Mum Khadijah
Maman Nabila
Ibar Hlamu
Fatima Musa
Ummu Shureim
Ummu Najma
Jeddah Ismaeel
Fateemah Xahrah
Anty Fatty
Fateema Pretty

Related Articles

Da sauran su HajjahKaka na gaisuwa 😂🤣 kuma tana godiya ga masu COMMENTS AND SHARING 🥰💕

Episode 11

HajjahKaka tace uwarki kika yi, ke da nace ki zama jan wiya a gaban sa, amma shine kika je kina shagwaba. Yo ba dole ki zo min da warin gawasa ba?

HajjahKaka don Allah ki gayamin yadda zamu kubuta daga hannun mutane nan

HajjahKaka tace idan zaki dena wannan shagwabar ki jajirce to, zamu bar wujen nan amma kika tsaya shagwaba Allah dura maki ciki zeyi kuma kin ga shikenan ke da barin nan sai mutuwa.

HajjahKaka Walhi kallon sa kadai yana tsorata ni balle kuma musayan baki, na rasa yadda zanyi.

Mtchews maganar kike son yi, da ina maki kallon me spiriyens ashe de ke Dodi minal Dodi ce ban sani ba? Shekara dai dai har sha hudu a kasar turawa ace baki da wayo? Kuma ai shekara daya da kika yi dani ya kamata ace kin biyo halina, nan take ta bani wasu shawarwari harda rantsewa wannan shine na karshe

Nagode HajjahKaka ta Allah yabar min ke

Murmushi tayi ta amsa da Amin, kafin tace ki zuba kamoniyan Walhi yayi zuwai kamar ni nayi, ba wani karni balle kwari

Daukar plate nayi na zuba hade da ruwan tea..

Maiduguri Government House

Yan Majalisu da me gimar Gwamna ne zaune a senate house, duk jikin su yayi sanyi ganin newspaper’s and news dake ta yawo a kasar
Har fargaban bude social media suke, dan farmaka da akayi a Damasak ya tashi hankali jama’a
Sun ce baza su bar gun harsai sun samu mafita.

Itako Journalist Binta da tawaganta sune gaba wajen daukar rohotu a garin Damasak

Kai tsaye Binta ta shiga gidan Dr Bukar sabida harbi duk ya farfasa bango,Katanga ya fadi, bayan sun gama suka nufa zauren Malam Garba, abin yayi muni mata ne kawai basu taba ba.

Binta was live on tv saide batan sa da cewa video ba inda yaje a kasar sai tv station dinsu, bayan ta gama ogan ta yay mata kiran na gaggawa, ba shiri ta koma ma’aikata inda ya kwace duk wani rohotu da ta dauka kuma ya bata hutun wata shida

Cike da mamaki take kallon ogan nata, miye sa zamu zuba ido ana zubar da rayuka da dukiyoyi mutane? Wannan wani irin kasa ce? Binta tayi maganar tana hawaye

A hassale ogan ta yace ke kin dauka ke daya ce wadda tasan da wannan labarin ? koko ke kadai ce kika iya aikin jarida?
idan kina son kanki dana familyn ki to kija bakin kiyi shuru.

Cikin bacin rai Bintou ta bar office, kwashe sauran kayan ta daga seat tayi ta bar ma’aikatan, tana cikin tuki wani kiran unknown number ya kira, har kama ba zata picking ba, kawai tayi picking, ko 1min talk beyi ba me kiran ya yanke kiran.

Cikin fargaba da tsoro Bintou ta taka birki tana nazarin abinda me kiran yace..

Fadar Ya Amir

Sai after 12 nadare Baana ya shigo dakin da HajjahKaka take,
Ya same mu duk muna barci, a hankali ya tako zuwa gadon ya kai hanun ze tabani HajjahKaka tayi saurin cabko hanun sa

Sannu maye? Nace sannu ko maye kai kai wannan jaraba da me yayi kama ni Bintu?HajjahKaka tayi maganar tana kokarin mikewa.

Dariya abin ya so bashi amma ya murtike fuska yace na zo daukar matata.

Uwar mata ce ba mata ba kaji ko, wai kai ko kunya kiran ta da mata baka ji ba? Yarinya da ta wanke ka da Sabulu da soso yanzu kayi klin shine zaka bude burmame bakin ka, ka wani kira ta da mata.. bata karasa maganar ba ta tsaya kallon ikon Allah

Jin an dauke ni yasa na bude ido mukai ido hudu dashi, murtike fuska nayi ina kallon sa ido cikin ido, nace put me down!

Cike da mamaki yake kallona, can kuma yay gaba dani.

Kai me tsiyayen duwawai ka dawo min da jikata ko kuma nai maka baki kai mutuwar wulaqanci.

Be ajiye ni ko ina ba se samar bed, nayi saurin sauka daga bed nace idan kana son jikina ya hallata agare ka to muyi aure Kamar yadda kowa ce mece muslima ake daura mata aure, sannan dangi ta su raka ta gidan miji.

Baice dani kome ba sai ma kallona da ya tsaya yi.

Ba tare da na sake cewa kome ba na fara takowa zan nufi kofa fita kawai naji ya cabko hanuna.sanan yace

You’re rightfully mine Falmata..!

I was dumbfounded and loss for a words.

Saida ya sake cewa I’ve gone all through the process of making you my wife in a lawful way fa Falmata.

Wai ALMAJIRANA ne wannan koko wani ne wannan, coz nasan Baana kazami kuma dakiki ne wanda ko come go be iya ba balle yay making English sentence.
Who are you?

Murmushi yayi kafin yace ALMAJIRAN Hajjahn sa. Fito da waya yayi ya kuna min yadda aka daura auren na da shi, ganin yan uwan Mamana su Bulama da Waziri yasa kafufuwa na suka kasa rike jikina, na tafi suuu zan fadi yayi saurin taro ni.

Kome tsaya min cak yayi jin yadda suka bada aurena ga wa’inan mutane, nasan ba tsoro yasa suka bada aurena tsanar da sukai wa mahaifina da ni yasa suka salama ni.

A hankali ya taimaka min na zauna a samar bed sanan ya mikamin ruwa na sha.

Son da nake maki baze sa na mallake ta haramtaciyar hanya ba Falmata, I think I’m breathing just for you.

Kallon sa nayi for the second time jin yayi turanci amma tashin hankali da nake ciki ya hanani na tambaye sa ina yaji turanci?

Kinyi wanka yayi maganar cikin taushin mirya

Banza nayi dashi ina jimamin abinda idanu na suka gani

Ina nufi wakan tsarki nasan ana uku kike tsarki yayi maganar da izza

Cike da mamaki na mike ina kallon sa, can kuma nace idan kana kallona a matsayin Hajjahn ka, you dare not repeat that, dan ko da aka daura maka aurena that will never change the fact, har yanzu a matsayin kazami ALMAJIRANA dan aike wanda na ke biya duk wata ba.
Idan ma kana tunanin na a matsayin matar ka maza ka kawar da wannan banza tunanin a ranka. Dan nafi karfin na zama matar ka kuma nafi karfin na zauna inuwa daya dakai
Idan kaji haushi ka kashe kowa nawa da kake fadin zaka kashe rubbish. Ina gama magana na nufi kofa zan fita saide ban kai ga unlocking ba, naji an fizgo ni da mugun karfi

Idonsa kadai abin tsoratatea ne kuma duk da bakin sa hakan be hana jijiyo goshin sa fitowa ba.

A yau zaki gane ni waye ne kuma da matsayi na a wurin ki.yana gama fadin haka kawai……

 

 

Pharteema(DMK)
THANKS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button