Nihaad 57
💖 NIHAAD 💖
57
This page is dedicated to my one and Only Deejah me lamurje, she is a sister from another Mother, ina kuma sonta har cikin raina, Allah ya bar xumuncinmu har aljanna🥰😍
Hajiya Zahrah Me gari naji labarin Najar Jikamshi ya siya maki sabon kasuwar cikin garin dutse, to su kuma yan dutse su yi yaya? Ko da yake ga dai kasuwar Hakimi. 🤔
Khalil na zaune gefenta ya jinginar da kansa jikin gado yana kallonta ko kiftawan kirki bai yi, gaba daya a sanyaye yake kamar ba shi ba, bai taɓa jin haushin kansa irin yau ba, he know she will ever trust him again because he never fulfilled the promise he made to her, he can’t tell what came over him that way, he didn’t take it easy on her, and all this is making him feel so bad, duk motsin da Nihad zata yi idonsa na kanta, even in sleep she doesn’t look alright, baccin karfin hali kawai take, duk tayi laushi saboda wahala, wani mugun tausayinta yake ji har ransa, a karo na farko kuma yaji yana son sanin ta yanda video dinta ya fita, yaji yana son yasan who is behind the leakage of that video of her, da kuma a inda aka yi sa, this he is going to find out by all means…. Bacci take amma restlessly, kana ganinta kasan she is in severe pain, he wish he can help her more than the way he did, but babu wani abinda xai iya mata bayan wanda yayi mata don ko kwayar magani babu a gidan, ji yake dama zai iya mayar da pain din nata zuwa jikinsa, duk ya kagu gari ya waye ya bata full care din da take bukata, ya kamo hannunta a hankali ganin ta kasa kwanciya guri daya sai juye juye take, he is been sitting there for almost an hour now, and bai damu ya zauna a hakan har gari ya waye ba just to keep an eye on her, hannunsa ya kai goshinta yaji temperature dinta is gradually getting so high, hakan da yayi yasa ta bude idonta da suka kumbura a firgice tana kokarin tashi zaune ya kwantar da ita, cikin sanyin murya me cike da damuwa yace “I am only feeling ur temperature” Taki bari su hada ido ta juya kanta tana sauke numfashi a hankali ta kulle idonta, ya duka dai dai kunnenta cikin sanyin murya that is full of remorse yace “I am sorry Nihad, i never meant to hurt you this way…. Don Allah kiyi hakuri…. I was just…” Sai kuma ya kasa ci gaba, he felt so bad because he is making her pass through much pain, ya kife kansa saman gadon ya kasa cewa komai, Ita dai bata bude idonta ba duk da hawayen dake zuba ta gefen idon nata a hakan, bayan few minutes ya dago kansa a hankali yana kallonta da idanuwansa da suka kada, ya ga alamar ta koma baccin, ya kalli agogo da yayi strucking karfe biyu da minti sha biyar, ya sake kallonta yaga baccin take yi, a hankali ya kai hannu ya goge hawayen dake fuskarta sannan ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa, karfin hali kawai yake don ji yake kamar zazzabi na neman rufesa, har ya fita ya dawo ya dau Hijab dinta ya ajiye saman bedsheet din sannan ya juya ya fita daga dakin ya kulle kofar a hankali, nasa dakin ya koma, ya shiga bandaki ya tara ruwan dumi yayi wanka sannan ya fito, a daddafe ya goge jikinsa ya saka Jallabiyarsa sannan ya kwanta ya rufa da duvet feeling feverish, ga wani sanyi da yake ji, yana son tashi ya koma dakin nata to check on her amma ya kasa tashi, lokaci daya zazzabi ya rufesa, yana ta kwance cikin duvet yaji kamar tsayuwar motoci a waje, ya bude fuskarsa wanting to be sure of what he heard, Bai san sanda ya yunkura ya mike ya nufi windown dakin da sauri ya bude curtain din, sosai gabansa ya fadi jin ana taɓa gate din gidan, da hanzari ya shiga parlornsa ya bude kofar balcony dake wajen don ta nan ne kadai zai iya hango kofar gidan da kyau, still yayi yana kallon motocin wa enda yake hangowa a kofar gidan, lokaci daya hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fito ya koma bedroom dinsa ya dau wayarsa zuciyarsa na bugawa, nan ya ga missed calls din Mami ya kusa sha biyar, Ga kuma na Aunty Maryam duk few minutes ago, he was just confused at this stage, gaba daya ya rude, ya koma dakin da Nihad take da sauri, rasa yanda zai yi yayi, ya jingina da bango zuciyarsa na bugawa sosai, da shi kadai ne gidan sai dai su shigo su dau hotonsa da za su gani manne a parlor amma ba dai shi ba, definitely sai ya sami hanyar fita cikin lokaci kankani, he will surely find a way out for himself, but yanzu bazai yi hakan ba ga Nihad, yaji kafafuwansa sun kasa daukansa ya karasa da kyar ya zauna gefen gadon ya rike kansa da yayi masa nauyi sosai, duk wani tunaninsa ya kwance a lokacin, bai kuma sannua zai yi ba, his father really caught him unaware, yana jin suna ta kokarin bude gate din gidan babu kakkautawa, can yayi karfin halin tashi ya tafi dakinsa ya dauko duvet ya fito ya dawo dakin da Nihad take, lulluba mata duvet din yayi a jiki a hankali, don riga ce iya gwiwa da ya sa mata daxu a jikinta, ta bude jajayen idonta da sauri tana kallonsa, yayi kissing goshinta yaji jikinta yayi mugun zafi, ya lumshe idonsa yayi kissing lips dinta a hankali yace “I don’t want you to be cold…. I am sorry i made u sick Nihad” Ta rufe idonta don muryarta ma a dashe yake, bata taɓa sanin akwai irin wannan wahalan ba a duniya sai dazu, ya mike a hankali ya fita daga dakin, ya zura wayarsa a aljihu sannan ya sauka downstairs duk da yanda kansa ke juya masa, ya nufi kofar parlor ya bude ya fita, direct gate din ya nufa, ya ɗan tsaya for few seconds, can ya runtse ido lokaci daya ya bude gate din yana kallonsu, Sojoji ne sun kai su goma a bakin gate din, daya daga cikinsu yayi gripping din hannunsa yana kallonsa, Khalil ya hade rai yace “Easy Mr Man, kai ka kamani ko ni na kawo kaina??” Tuni wani ya miko handcuff, shi dai kallonsu kawai yake kirjinsa na sama da kasa, ganin yanda sojan ke kiciniyar saka masa handcuff din kamar wanda yayi sata, Khalil yaki bari ya saka, yana huci yace “Ce maku aka yi nayi sata ku zo ku daureni?” Duk cikinsu babu wanda ya kalli fuskarsa balle su ce masa komai a wajen, har sai da suka makala masa suka yi hanyar mota da shi, wani sojan ya tafi ya kulle gidan Khalil na kallonsa, anyi masa ire iren haka ya fi a kirga don haka ba sabon abu bane wannan a wajensa, kuma yanda Janar ya basu umarni su yi haka suke yi, shi sa duk bakaken maganar da Khalil zai gasa masu basa daga kai su kallesa balle su ce masa komai, don ko dungurinsa Najar bai basu umarni su yi ba, iyaka su saka masa handcuff su kawo masa shi har gida…. (au Janar xan ce wai Najar
😂)
wajejen karfe hudu na asuba suka isa gida da shi, direct Guard room dake cikin compound din suka kai sa suka turasa ciki sannan suka rufe wajen da kwado, leaving him all alone, Khalil ya rike kansa dake sara masa, why didn’t he think twice kafin ya shiga gidan, he just forgot who his father is, babban damuwa da tashin hankalinsa yanzu bai wuce Nihad ba, she needs to be taking care of, she needs him by her side, yasan baxata iya yin komai ba, wannan tunanin yasa yaji zazzabinsa ya dawo da karfinsa, har aka yi kiran sallah na biyu ko gyangyadi khalil bai yi ba, ga sauro sai abinda suka manta ne basu masa ba a jikinsa, ko kwanciya mutum bashi da damar yi a guard room din, wajen ne ɗan tsut da shi, ana tada sallan asuba sojoji uku suka zo suka bude karfen Guard room din, fitowa yayi da kyar yana jin kansa na juya masa, ya dafa bango da sauri, ɗan cell ne wajen kafin ainahin guard room din, shi cell din ba laifi yana ɗan da sarari duk da shi din ma dai ba babba bane, a cell din kuma har da bandaki a ciki, yasan dalilin budesa da suka yi bai wuce ya fito yayi alwala a cikin bandakin dake cell din ba yayi sallah, yayi namijin kokari wajen shiga bandakin, ko kafin ya fito ya ga darduma an ajiye masa nan cell din, ya dauka ya shimfida, suna ta tsaye bakin kofa har sai da ya idar da sallah, suka sake maida sa cikin guard room din suka kulle sannan suka kulle cell din ma daga waje, Khalil ya hade kansa da karfen Guard room din, duk da yanayin da yake ciki Nihad ce kawai a ransa, he is so worried because of her, banda ita he don’t mind being in the guard room for weeks tunda dai ya saba zama ciki, kuma yanda Abba yasa aka ajiyesa a nan zai iya tafiyarsa ya mance da batunsa har sai randa Allah ya dawo da shi, iyaka a dinga kawo masa abinci da ruwa, for the sake of Nihad yaji zai iya mayar masa duk abinda yayi seizing, duk da zafin da guardroom din shi sanyi yake ji…. Yana nan a haka har wajen karfe takwas ya ji ana bude kofar cell din, ya daga kansa, sojan na gama bude cell din Mami ta shigo ciki tana kallon ɗan guardroom din, Sojan ya karaso ya bude karfen guardroom din… Khalil ya kasa fitowa saboda zazzabin da ya ci karfinsa, Mami ta karasa tana kallonsa, cike da karfin hali ya fito, Mami na ganin yanayinsa taji hankalinta ya tashi tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Yanzu meye amfanin haka khalil, kaga abinda nake ta gudar maka ka kasa ganewa….” Sai kawai ta fashe da kuka, Da sauri taga ya shiga bandakin cikin cell din wanting to throw up, ta bi bayansa hankalinta a mugun tashe, tana rike da hannunsa suka fito daga bandakin don ya kasa aman, ya zauna nan kasan cell din ya jinginar da kansa jikin bango ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, Mami dai sai hawaye take barin yanda taji jikinsa yayi zafi, it’s rare aga yana rashin lafiya shi yasa ma hankalinta ya tashi yanzu, to kiran Abban nasa zata yi tace bashi da lafiya yanzu kenan, tana yin hakan kuma zai ce ita ke supporting dinsa yayi duk abinda yake yi, gaba daya she is confused, ta durkusa gabansa tace “Abinda nake ta gudu kenan, kasan waye Abbanka Khalil, kasan abinda zai iya aikatawa, ban san me yasa zaka shiga gonarsa ba…” Sai kuma ta fashe da kuka, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace “I am sorry Mami….” Tace “Ka fada min wani maganin za aje a siyo maka idan kayi breakfast yanzu sai ka sha” Ya girgiza mata kai kawai, tace “You don’t look okay, so kake ciwon ya kwantar da kai a nan? Ka gaya min maganin da za a siyo maka in je yanzu a siyo” Yayi kasa da murya yace “I am not sick, i am just worried, i am disturbed, not because ina cikin guard room” Mami na kallonsa tace “What is making you worried then?” Ya kasa hada ido da ita, sai ma sunkuyar da kansa da yayi, da damuwa tace “Talk to me son, meye damuwarka? Ni mahaifiyarka ce kar ka boye min” Lokaci daya idanuwansa suka kada ya dago kai cike da karfin hali yace “Na maku laifi during my stay in kano” Mami ta dinga kallonsa tace “Laifi? Laifin me son?” Ya kamo hannunta gathering all sort of courage, muryarsa na rawa yace “I got married while in kano” da wani expression Mami ta dinga kallonsa kamar me son fahimtar abinda yace, can tace “Ban fahimta ba, menene married?” Ya kasa kallonta with shaky voice yace “I am sorry Mami, Allah ne ya kaddara min haka, but i never bargained for it” Mami ta janye hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tana kallonsa with a weird expression tace “Zazzabin ne yasa kake wannan sumbatun Khalil? Kasan me kake cewa kuwa” Hawaye ta gani idonsa, cike da karfin hali yace “Mami i am in my right senses, i am telling u the fact, kuma tana can gidana yanzu haka” Mami na zare ido tace “Ita wa?” A hankali yace “Matar, kuma sojojin sun kulle gidan, she is inside the house” Mami ta fi minti daya tana kallonsa with shock, shi dai ya kasa hada ido da ita, burinsa kawai aje wajen Nihad a bata kulawar da ya kamata a bata, A hankali Mami ta juya ta nufi kofar cell din, kana ganinta kasan jikinta yayi mugun sanyi and she is speechless, ya bi ta da kallo zuciyarsa na bugawa har ta fita……
kuyi manage yau ruwa aka yi tayi in gaya maku a kano 😯
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don’t like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114