Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 1-2

Sponsored Links

1-2

*_MAFARI_*
Hanisa ke Hanisa wato yauma saikin jamin asarar da kika saba ko nikam narasa irin ki kullum aita maimaita miki mgn ɗaya doɗɗiyar ƙwaƙwalwa irin ta kifi to wlh yau ki tabbatar idan kika dawomin da kwantai na Shinkafar nan saina nakasaki Yayarki Hasina yanzu haka ta kusa dawowa amma ke kinanan kina iskanci” fuuuu Baba Indo ta zari buta ta shige bayi Wata matashiyar Budurwa ta fito daga ɗaki sanye da riga da zani na atamfa kyakkyawa Chocolate me matsakaicin tsayi me dirararren jiki.
Ɗaukar bahon Shinkafar tayi ta ɗora akanta ta nufi ƙofa tana cewa “Na fita Baba Indo Bata saurareta ba dama kuma bataji a ranta zata kulata ba ta fice a gidan ta tsari ɗan sahu ta hau tace masa yan taya zai kaita. Suna tafe tana kalle²nta suka isa gurin ta zaro kuɗinsa ta basa ta ɗauki kayanta ta ƙarasa yan abincin ta zauna a gurbinta.
Can nesa da ita ta hango Hasina tanata danna waya ta miƙe da sauri ta isa gabanta ta tsugunna tace “Yaya Hasina Ina kika samu waya?” Ɗagowa tayi ta kalleta tayi mata dariya tace “Sai yanzu kika fito Ni abincina har ya ƙare” buɗe bohon abincin tayi taganshi jingim ko taɓashi baayi ba ta ɗago da sauri ta dubeta tace “ai Bama ki fara taɓawa ba” yatsina fuska Hasina tayi tace “Eh ban taɓa ba jira nake azo a bani kuɗinsa ki bari kema idan yazo zance ya haɗa ya biya da naki”

 

Related Articles

Zaro manyan idanunta tayi tace “Waye shi Yaya Hasina?” Rufe mata baki tayi lkcn da wani matashin saurayi kyakkyawa yake nufosu Hasina ta nunawa Hanisa shi fari tas dogo me dirararren jiki faffaɗan gaske yana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinsa sosai. Ajiyar zuciya Hanisa ta sauke lkcn da idanunta ya sarƙe cikin nasa tayi saurin janye nata kanta na sarawa gabanta na faɗuwa ta miƙe zatabar gurin Hasina ta riƙo hannunta tace “Ta Baba Ina zaki?” Dubanta tayi ta dubi matashin daya tsaya akansu yanata zuba ƙamshi tace “Zan koma gurin abinci na”
Sake riƙe hannunta tayi tace “Wannan da kike ganinsa sunansa Abdul-Ahad Anace masa Abdu zan baki lbrnsa sai munje gda yanzu dai ki tsaya mu samu almajiri muyi musu sadakar abincina da naki duk yace zai biya” sake dubansa Hanisa tayi tace “akan me Yaya Hasina nifa kinsan banason juye haka kawai kina ganin Ladidi da Tabawa daga juyen nan aka juyesu fita ma ta gagaresu saboda sunyo shegu nikam a’a abarmin nawa zan siyar banson san zuciya…..”

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button