Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 17

Sponsored Links

WARNING❌*
_Only matured ahead🔞 idan kika zageni ban yafe ba domin banyi littafina don ƴammata ba idan kinga zaki iya go ahead._

 

Mal Wada ne yace “Komai fah yana tafiya ne bisa bigiran ƙaddara kiyi hƙr kada kiyi abinda zai dameki zaki samu canjin daya fisa alkhairi”kallon Mal Wada tayi da sauri tace yanzu har akwai wanda yafimin Abdu alkhairi a duniyar nan? Ina mal babu wlh bazaa sameshi ba saboda haka ko a hannun wa zuciyarsa take saina ƙwatota”
Jinjina mata kai kawai yayi suka fice dukkansu babu ɗaya dake cikin hayyaci napep suka hau suka tafi gda babu me cewa wani har sukaje gdan suna shiga Hanisa ta ɗauki buta ta nufi bayi, tana shiga ta buɗe wayarta kiransa ya shigo ta katse ko kaɗan bata sha’awar ɗaga wayar to shima ganin taƙi ɗaga wayar tasa ya turo mata test yana cewa “Wyf kinƙi ɗaga wayata ko ki nemi mijinki kiji lfyrsa.
Wani Gwauron numfashi ta sauke yace “Na sauka lfy ina cikin ƙoshinta kefa?” Shiru ta sake yi masa yayi murmushi yace “bazakice komai ba?” Fasali ta ajiye tace “Alfarma zan roƙa a gurinka don Allah ka fita a rayuwata kwata² bazan iya baka haɗin kai mu cutar da ƴar’uwata ba” murmushi yayi yace “ko?” Da ƙarfin gwiwa tace masa “Eh” dariya sosai yayi yace “Ranar biyan bukata rai ba bakin komai yake ba inji ƙuda Ni inada zaɓi kuma bazan taɓa bari saboda farin cikin wani na rusa nawa ba”

Related Articles

 

Ƙit ya kashe wayar daya samu aka ɗaga masa daƙyar taja numfashi tace “sai kayi ai” gama abinda zatayi tayi ta fito daga bayin ta nufi ɗakinsu baba ya shigo da sallamarsa ta amsa masa tare da durƙusawa ta gaisheshi ya amsa yana cewa “Aneesatu na ina kikaje ne yau gdan shiru ko ɗakin nawa ma ba’a gyatta min ba” dariya tayi tace “ina sauri na manta Baba bari nayi sallar la’asar nazo na gyara maka am Baba nace kamar magungunan ka sun ƙare ko?” Jinjina kai yayi yace “sun kare Aneesah an ɗauki adashin ne?” Murmushi tayi tace “Aa Baba kawai dai na samu wasu manyan kuɗaɗe ne shine nakeso idan zai yiwu na kaika asibiti a gwadaka agani idan jinin ya sauka itama sugar ta sauka sai a rubuta maka samfurin wasu magungunan”
Zubanta ido yayi yace “Aneesah ina kika samu manyan kuɗaɗe?” Gabanta ne ya faɗi tayi saurin cewa “Lah Allah Baba ba abinda kake tunani bane wani saurayin Yaya Hasina Abdu shine zaiyi tafiya so sai yabani wasu kuɗaɗe yace mu kula da kanmu bayason tallanmu harma yace idan yaje ya dawo zaizo ku gaisa ƙilan ma yazo maka da mgnr auren Yaya Hasinan”

 

Jinjina kai yayi yace “shikenan Aneesatu tabara yayi miki albarka ya tsare gabanki da bayanki yayi miki tsari da dukkan abin ƙi bari na shiga ciki” amsawa tayi da Amin ya shiga ciki ita kuma ta shige ɗakinsu tayi salla ta zuba masa abinci takai masa dama ita kaɗai ce a gdan ta damu da cikin mahaifin nasu lkcn da yaje yana kishingiɗe ta ajiye masa ta gyara ɗakin ta fito sukayi kiciɓis da Hasina ta fito a ɗaki tace “ina zaki Yaya?” Kallonta tayi hawaye ya zubo mata tace “Haba Hanisa meye yasa Abdu ya zaɓi wulakantani ne tun safe nake kiran wayarsa yaƙi ɗagawa na tura masa test not reply nayi masa mgn ta whattsAp shima yaƙi buɗewa”
Daƙyar Hanisa ta haɗiye wani yawu me ɗaci tace “To yanzu da kika fito a fusace haka ina zaki?” Gaba tayi tanacewa “Waya zanje na nemo na kirashi” murmushi tayi tace “Kina son kina zubarwa da kanki ƙima Yaya mgn ta girman Allah Abdu baya sonki tunda kikaga yana miki haka da nice ke da tuni ma na manta da babins…..

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button