Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 18

Sponsored Links

Arewabooks; hafsatrano

Page 18

***Dukkannin su babu wanda yayi ma wani magana a cikin su har suka isa part din su, shi Rafeeq baya mood din yin magana ne gaba daya shi kuwa Asim bakin sa har kunne saboda farin ciki, duk yadda ya dauka sai an sha fama dashi da su mummy amma sai yaga ba haka ba. Kenan ta karbi abinda yake so zata shige masa gaba kenan?

Related Articles

“Me yasa ka bar musu zabi?”

Asim yace ganin sun zauna Rafeeq din be ce komai ba.

“Bana son mahanar Asim, please ba yanzu ba.”

“Ok.” Yace jikin sa na yin sanyi. Ya dade da sanin Rafeeq din dauriya ce kawai amma yana da tarin damuwa chunkushe a ransa, sun dan dade a haka kafin ya mike tsaye yace

“Zan wuce, idan na shigo office din da wuri tam, idan kuma ban zo ba kayi abinda ya dace.”

“Ba zaka kwana anan ba?” Yace yana mikewa shima

“No, inaso na zauna ni kadai ne.”

“No please, ni sai na tafi ka zauna.”

Dafa kafadarsa yayi yana tattaro dukkan jarumtar sa sannan yace

“Karka damu, i will call you da safe.”

Yana tsaye har ya fice duk sai ya rasa ma menene yake masa dadi. Ya rasa dalilin da yasa AJI yake tsaurara ma Rafeeq din komai, bayan shi ba haka yake masa ba. Zama yayi shiru yana ta tunani ganin tunanin ba zai masa ba sai kawai ya dauki wayar sa ya fice daga gidan.

***Sanda ya koma hotel room dinsa sai yaji gaba daya duniyar ta ishe shi, gaba daya be san menene yake masa dadi ba, wani irin heavy feeling me wahalar fassarawa ne ke dawainiya dashi, ga wani irin jiri jiri dake neman kayar dashi, gashi Saddam baya nan dan tunda ya ajiye shi dazu yace zai fita sai kawai yace masa sun hado gobe. Yana zaune yana nazari da lissafin rayuwar sa har dare yayi sosai ba tare da ya sani ba, da kyar ya mike yana addua ya dan yi abinda zai yi ya kwanta.
Da safe ya tashi sakayau sai damuwa me tarin yawa dake chunkushe a makoshin sa ko yaya ya hadoye yawu sai yaji kamar ya hadiyi wani abu me daci da bauri. Shiryawa yayi ya fito Saddam rike da yar karamar jakar kayan sa da yayi amfani dasu suka sauka zuwa wajen parking.
Ranar za’a yi ma Baban Noor aiki dan haka direct asibitin suka wuce domin shine zai saka hannu sannan a shiga aikin shiyasa ya daure ya fito da wuri duk da yanayin nasa da yake jin mara dadi. Office din head Dr din suka shiga aka bashi duk abubuwan da ya kamata ya cike yasa hannu sannan ya fito harabar asibitin suna tafe suna magana da likitan har suka hauro barandar da zata maida ka wajen da ake yin parking motoci.
Taxi ce ta sauke ta a gate din ta bashi kudin sa sannan ta sauko ta shiga asibitin tana ta dan sauri kar a shiga aikin bata nan. Yadda take saurin yasa bata lura da kowa ba ita dai burin ta kawai ta isa dakin tunda an ce karfe takwas za’a shiga dashi yanzu kuma saura yan mintuna shiyasa burin ta kawai ta karasa. Magana zai yi daidai lokacin da ta hawo barandar da suke kai, wani irin daukewa yawun bakin sa yayi gaba daya ya nemi maganar ya rasa ta kwata kwata. Kallon sa Dr yayi sai yaga ya dauke kansa gefe da sauri daidai lokacin ta wuce su. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juyo yana kallon Dr.

“Lafiya dai oga?”

“Me fa?” Yace kamar be san abinda ya faru ba.

“Shikenan toh, duk yadda ake ciki zan sanar dasu sai su fada maka.”

“Ok Dr, nagode.”

“Nima nagode.”

Ya mika masa hannu suka yi musabiha sannan ya juya ya koma shi kuma ya saika zuwa wajen motocin ya shiga suka bar asibitin.

Sanda ta shiga dakin an shirya komai har ya sauya kayan sa zuwa na operation, rungume shi tayi tana kuka sosai, yaso an shiga dashi kafin tazo ashe tana hanya dama yasan sai tayi kukan dan baya mata wahala dan ma bata san takamaimai aikin da za’a bane yasan da sai kukan ya fi haka. Da kyar wata nurse ta bata baki tayi shiru aka dora Baban akan wheel chair aka fita dashi. Har kofar theatre room din ta raka shi sannan ta tsaya tana cigaba da kukan a hankali, gani take kamar shikenan zata rabu da mahaifin ta bayan bata da kowa yanzu a duniyar nan sai shi. Haka ta cigaba da zama a kofar har aka kwashi hours masu dan dama kafin daya daga cikin Drs din ya fito

****Ba wani abun kirki da ya iya aikatawa a office din ba gaba daya, ganin zaman nasa bashi da amfani sai kawai ya ture komai ya mike ya dauki blazer dinsa dake rataye saman kujerar. Turo kofar akayi, Asim ne rike da wani katon folder. Tsayawa yayi yana kallon sa har ya karaso ya dora a saman desk din sannan yace

“Ba dai fita zakayi ba?”

“Yes akwai wani abu ne?”

“Eh akwai abubuwan da suke bukatar sa hannun ka, if possible yanzu.”

Idon sa a shanye yake kallon Asim din, yana tuna duk sacrifice din nan saboda shi yake yi, girgiza kansa kawai yayi ya rataya Blazer din akafadar sa sannan yace

“Take care of everything.”

Sai yayi tapping bayan ya raba ta gefen sa ya fice. Tsayawa yayi ya rasa me zai yi, ya san dauriya kawai Rafeeq din yake amma yasan deep down he is hurt. Kasa fita yayi daga office din Rafeeq din ya samu waje ya zauna duk babu dadi.

***Yana fitowa wayar sa tayi kara, ya kalla ganin Ammar ne ke kira sai ya tsaya daga tafiyar ya daga wayar

“Ya ake ciki Ammar?”

“Sir an fito dashi.”

“Masha Allah, hope komai normal?”

“Eh Alhamdullillah, aikin yayi kyau.”

“Masha Allah. Thank you for everything.”

“You are welcome sir.”

“Tell me duk wani abu da ya taso, and make sure sun samu duk wani abu da ake bukata, and please…”

Sai yayi shiru yana jin nauyin abinda zai fada din a harshen sa

“Sir?”

“Forget it, just call me idan ana bukatar wani abu.”

“In sha Allahu sir, zaka shigo ne?”

“Eh, but ba yanzu ba, may be da daddare idan ta tafi.”

“Ok.”

 

***Hajiya Maryam na zaune a office dinta a babban restaurant dinta dake Wuse 2 motocin Mummy suka parking, ta CCTV din dake office din take kallon harabar wajen abincin. Tana zaune suka shigo reception din sai ta daga waya tace a shigo dasu office dinta.
Shigowa sukayi ita da Hajiya Lubabatu ta tashi da sauri ta tare su, suka rungumi juna cikin farin ciki

“Yau manyan baki ne a dan a kurkin namu?” Tace suka saka dariya

“Ban da ba’a dai Hajjaju.”

“A ah gaskia ne ai, Bismillah ku zauna. Me za’a kawo muku?”

“For now dai mu zauna Hajjaju, magana ce me muhimmanci tafe damu.”

“Toh, toh Masha Allah.”

Sai ta zauna tana fuskantar su. Hajiya Lubabatu ce ta soma magana tace

“Neman aure muka zo.” Tace tana murmushi

“Aure Hajiya? Ni da ba ya ba jika Hajjaju?”

“Shige mana gaba za’a yi Hajiya.”

“Toh aina ne? Wanne taimakon zan iya yi muku?”

“Auren Noor muke so ki shige mana gaba mu samu.”

Dan zabura ta, ta maimata kamar bata ji sosai ba tace

“Fatima dai?”

“Ita Hajiya.” Mummy tace tana murmushi

“Tirkashi, na zata itace dai…”

“A bar tuna wannan maganar Hajiya, ashe daya daga cikin masu aiki na ne suka dauka suka kala mata ganin yadda yaran gidan suke kaunar ta,yanzu da na gano shine nake so mu wanke kanmu, dan mu yan siyasa kowa namu ne.”

“Gaskia ne, toh yanzu me zanyi ni?”

“Tunda nasan akwai alaka ki da iyayen ta, inaso ki shige gaba wajen tsaya mana a bamu, kuma so samu kar abun ya dau lokaci, dan ko sati biyu ne mu muna so.”

“Ah da gaske kuke Hajiya, toh shikenan zan samu mahaifin ta da maganar in sha Allahu, nasan yadda ya yarda dani zai amince, kuma dai Hajiya ai babu gidan da zaku je neman aure a hana ku.”

Dariya suka saka dukka, suka cigaba da maganar yadda suke so abun ya kasance, da abubuwan da Hajiyan zatayi kafin auren saboda so take ayi biki na gaske, sai da sukayi convincing dinta sosai suka tabbatar da babu wata kofa da zata sakata doubting dinsu. Taji dadi sosai ta rakosu har mota sannan sukayi sallama suka tafi.

***Sai da suka yi sallar isha sannan suka tafi asibitin bayan ya tabbatar da tafiyar ta, daga shi sai Saddam yana zaune a wajen me zaman banza yana kallon tv dake gaban motar yana sauraron wa’azin sheik Isah Ali Fantami da yake yi live a daidai lokacin, hankalin sa gaba daya ya bayar yana sauraro, yana magana ne akan hukunce hukuncen aure da duk abinda ya shafi zamantakewa har suka karaso asibitin, zama yayi a motar sai da ya karasa ji sannan ya fito Saddam ya rufe motar suka jera zuwa cikin asibitin.
Babu kowa a dakin sai shi kadai Habu yana toilet yana wanke kayan Baban suka shigo. Yana zaune an saka masa pillow a bayan sa sai kafar dake rufe da bandage. Fuskar sa ce ta fadada da fara’a ya hau yinkurin gyara zaman sa sosai. Da sauri Rafeeq ya karasa ya gyara masa sannan ya durkusa ya gaishe shi a ladafce.

“Lafiya lou Alhamdullillah.”

“Masha Allah, Allah yasa anyi aikin a sa’a.”

“Amin ya Allah, nagode muku kwarai Allah yasa ka da Alkhairi, Allah ya raba ku da iyayen ku lafiya.”

“Amin.”

Ya amsa yana jin nauyin Baban sosai. Shiru ne ya ratsa dakin har habu ya fito, ya duka ya gaida Rafeeq din sannan ya fita ya shanya kayan a baya ya dawo dakin. Ammar ne suka shigo tare da Dr, suka gaisa da Rafeeq din sannan Dr ya yi musu bayanin komai akan kafar da abubuwan da ya kamata ayi, ya dan dade yana bayani kafin ya fita. Yana fita Rafeeq din ma ya mike yayi musu sallama ya fita, Baban na ankare da irin respect din da suke bashi dukkan su. Tun ranar da Ammar ya fada masa shi ya dau nauyin aikin sa yake ta nazari akansa, yana kallon fuskar sa yana jin kamar ya taba ganin shi amma ya manta aina. Har mota Ammar ya rakasu suka sake magana da Rafeeq din sannan suka tafi shi kuma ya koma ciki saboda aikin Rafeeq din da zai karasa sannan ya tafi gida. Dakin ya koma ya ja kujera gaban gadon Baban sannan yace

“Baba wata magana ce dani,.”

“Toh dana, wacce magana ce?”

“Magana ce akan ogan mu, wannan da ya fita yanzu, wanda nace shine ya dauki nauyin aikin da komai.”

“Toh toh Allah sarki, mutumin kirki. A kullum idan na kwanta sai nayi tunanin me yasa shi yi min wannan kirki? Ban san shi ba, ban taba ganin sa ba sannan ace ya dauki nauyin aiki me tsadar gaske irin wannan, sannan yace kar a sanar shine yayi, kai ina tantanma.”

“Saboda Allah yayi maka Baba, dan idan yana so ka sani ba zai boye ba, sai dai akwai wata damuwar sa da kai kadai ne zaka iya magance masa Baba.”

“Ni kuma? Wacce irin damuwa ce haka?”

“Duk da baya son ayi mahanar, ya kuma gargadi duk wanda yayi maganar a cikin mu zai fuskanci fushi sosai, amma ba zan iya ganin sa a cikin damuwa haka ba wallahi, damuwar tayi masa yawa”

“Tabbas, mutumin kirki irin wannan, be kamata a barshi cikin damuwa haka ba.”

“Shekaru masu yawa yana bibiyar rayuwar yar ka Baba, har ta kai ta kawo yana iya danne damuwar sa domin ganin farin cikin ta, duk da haka be taba furta mata ba, be taba sanar da ita halin da yake ciki ba, amma tabbas idan ya rasata zai iya shiga halin da mu kanmu ba mu san yadda zata kasance ba.”

“Tirkashi!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button