Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 24

Sponsored Links

Arewabooks;hafsatrano..

Page 24

**** Turo kofar yayi ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofar yana kallon yadda aka sauya dakin. Mayafin ta dake ajiye ya kalla sannan ya kalli kofar toilet din dake makale a cikin dakin, dan jim yayi daga kofar sai kuma kawai ya saki kofar ya juya yana raya tunda tana gidan ko ba yau ba zasu hadu. Komawa falon yayi ya zauna yana duba wayarsa, bayan kamar minti sha biyar akayi ringing door bell din, mikewa yayi yana maida wayar cikin aljihun wandon sa ya nufi kofar a tunanin sa Saddam ne.

“Sir gashi inji Saddam.” Ya fada yana mika nasa ledojin manya dake hannun sa. Kallon ledojin yayi sannan ya zaro wayar sa ya kira Saddam din dan be gane komai ba.

“Switch off?” Ya furta yana kallon screen din

“Yaushe muka fara irin wannan da Saddam?”

Shiru yayi yana juya wayar a hannu ya ma rasa me zai ce, takaici kamar me dole ya matsa ya bawa get man din waje ya shiga da ledojin falon sannan ya russuna ya juya ya fice. Takowa yayi bayan ya rufe kofar ya dawo falon ya tsaya yana tunanin abinda zai yi, baya son kiran drivers din gidan su dan baya son abinda AJI zai samu wani labari kuma baya so yayi Bolt ko Uber. Samun waje yayi ya zauna kawai yana jin dole ne ma Saddam ya karbi hukuncin sa dan be san ranar da suka fara irin wannan shirmen ba.
Mikewa yayi ganin zaman ba zai masa ba, ya wuce bedroom dinsa ya hau zare kayan jikinsa da suka takura shi dama tun dazu, ya zaro bathrobe sabuwa ya daura sannan ya wuce toilet bayan ya kara dialing Number Saddam din amma still dai amsar daya ce. Wanka yayi hade da alwala sannan ya fito yana goge jikinsa ya zauna gefen gadon yana kallon screen din wayar sa ganin message ya shigo. Budewa yayi yana cigaba da goge sumar kansa da dan karamin towel.

“Kayi hakuri Sir, zanzo da safe da wuri wani uzuri ne ya taso kuma gashi wayata charge din ya dauke.”_ Tsaki yaja ya mike zuwa gaban mirror ya dauki CeraVe moisturizing lotion ya shafa kadan dan baya son zafi ya takure shi sannan ya dauko wani sweetpant dinsa da farar over size tshirts ya saka ya fesa turaren imperial majesty kadan sannan ya dauko wayar tasa ya komo living room din.
Zama yayi yana daukar remote ya kunna sabuwar smart TV da Saddam ya sauya ya harde kafarsa yana bawa tv din attention dinsa gefe daya na zuciyar sa na tuna masa bashi kadai bane a gidan akwai wata, watan kuma zaune take a mazaunin matarsa.
Mikewa yayi yana zura hannun sa cikin aljihun wandon ya nufi hanyar kitchen yana jin idan ya samu dan abu da zai jika makoshin sa zai samu saukin tunanin dake addabar sa. Fridge ya bude ya dauki soft drink ya daga kai ya kwakwade sannan ya jefar da tin din a dustbin ya juya ya fita. Ya dade da shan carbonated drinks amma yau haka kawai yaji son shan, gashi yayi wani irin sanyi a tunanin sa zai taimaka masa yaji dan dama dama amma tunda ya dawo ya zauna abun ya cigaba da dawo masa. Tsaki yaja a karo na ba’adadi ya mike yana kallon ledojin kamar zai bude sai kuma kawai ya wuce bedroom din sa.

***Sai da ta tabbatar ya fita daga dakin sannan ta fito tayi saurin zuwa wajen kofar yasa key tana dafe da kirjin ta da take jin wani irin tsoro da fargaba. Zama tayi a jikin kofar jikinta na cigaba da rawa dan duk in da tunanin ta yaje ya dawo dai akan abu daya dai, abunda take jin zuciyar ta ba zata taba iya dauka ba, idan har tunanin ta ya zamo gaskia ya zatayi kenan? Sannan ya akayi hakan ta faru ma? Girgiza kanta ta dinga yi tana sakin kuka, kukan makomar ta idan har ya tabbata shine mijin ta ba Asim ba, ina zata saka ranta kenan? Ina zata iya zama da mutumin da baya kaunar ta, wanda yasa aka koreta daga aikin ta be duba halin da zata shiga ba, me yasa zasuyi mata haka?
Kuka taci sosai kafin ta tashi jiki a mace ta dauko wayar ta, tayi dialing number da Asim ya kirata dazu domin tana son ta tabbatar da abinda take tunani kafin zuciyar ta, ta karasa bugawa.

“Ya Allah kasa ba amfani zasuyi da raunin mu ba su cutar dani.” Ta fada a hankali tana jan kuka.

“Hello.”

Kawai Asim yace katin ya kare dan dama ba wani na kirki bane ba, yana katsewa kiran shi ya shigo a take, ji tayi hannun ta na rawa, yana kakkarwa kamar ba zata iya dagawa ba saboda tsoron amsar da zata samu. Daurewa tayi ta sa hannu ta daga tana toshe bakinta da dayan hannun.

“Hellooo… Beautiful.” Yace yana sake relaxing sosai akan makeken gadon sa dake hotel room din nasa cikin jin dadin kiran da tayi masa.

“Hello.” Tace murya a dashe

“Are you ok?” Ya tambaya yana sake tantanma dan muryar ta ta bayyana yanayin ta gaba daya

“I’m fine, please tambayar ka zan.”

“Ok go ahead, ki tambayi koma menene.”

“Emm dama, wannan brother din naka…”

“Feeqq, Rafeeq kenan. Ehen ina jinki.”

“Yawwa shi, yana ina yanzu?”

“Yanzu? I can’t say gaskia, but nasan kila yana gidan kinsan an daura auren sa 3days back.”

Mayafin ta, tasa ta danne bakin ta jin kukan na sake taso mata gaba daya… Be jira jin tayi magana ba ya dorw

“Kinsan shine first born toh duk wani strictness akan sa AJI yake gwadawa, yana zaune kawai yace ya kawo mata ko a zabo masa, toh shi da yake yana da I don’t care attitude yace kawai suyi komai shikenan fa aka shirya komai aka gama within a week, kai ai ni ba zan taba yadda ma ayi min haka ba, coz I can’t settle with wacce bana so, I can’t even imagine kaiii, suicide kawai.”
Yaa karashe yana dariya, mikewa tayi da sauri, ta jefar da wayar ta bare a kasan tiles din, bata tsaya bin ta kai ba, ta dauki jakar ta karama da dan kudin ta yake ciki sannan ta zura takalmin ta, tana kuka tayi hanyar waje. Ba zata iya zama dashi ba,gwara ta koma gida ta fadawa Baba komai tasan zai saurare ta. Bude kofar tayi kanta tsaye dan gaba daya hankalin ta yayi gida, baya falon sai tv dake kara ita kadai ta tsallake ta bude kofar ta fice tana zuba sauri, lokacin karfe tara har da yan mintuna gateman na zaune saman bench dinsa ya hango fitowar ta daga part din tana kuka tayo gate din, mikewa yayi da sauri yana kallonta har ta karaso bata kalleshi ba ta nufi gate din ta kama zata bude amma sai taji shi a rufe, kallon sa tayi da rinannun idanun ta tace

“Bude min.”

“Ma it’s already late, oga yace kar a budewa kowa gida without his permission.”

“Dan Allah ka bude min, ba zan iya zama a gidan nan ba.”

Tace muryar ta na karyewa, tana jin da gaske an ci amanar ta, tana jin dole akwai wani kulli da suke kulla mata shi da mahaifiyar sa tun daga maganganun da ta fada mata dazu, gwara ta gudu tun kafin su yi mata illa su cuci rayuwar ta.

“Kayi hakuri Hajiya, I need to tell Oga first.” Yace yana shiga dakin sa ya dauko wayarsa. Durkusawa tayi kasa da sauri ta hade hannunta waje daya sannan tace

“Dan Allah Dan Allah karka kirashi, bude min kawai zakayi na tafi dan Allah.”

“Ma I can’t oo, bana so na rasa aiki na, just wait na kirashi.”

Yace yana dialing number din, tana durkushen tana jin sanda kiran ya shiga, sannan taji sanda ya daga yace

“Hello John, what’s the problem?” Cikin calm muryar sa

“Sorry to bother you sir, it’s madam oo.”

“Madam? Me ya faru?” Yace yana so ya fahimci kan maganar

“She’s here with me sir, tace sai na bude mata gate ta fita, naga kuma dare yayi, shine nace let me ask you first, should I open?”

“No don’t, I’m coming.”

Yace yana kashe wayar. Tsaki yaja yana mikewa, bayan ya duba time din sannan ya zura slippers dinsa ya fito.

Daga nesa ya hango ta a durkushe ta chusa kanta cikin kafafunta tana cigaba da kukan tana jiran yazo dole ma ya barta ta tafi ko yaki ko yaso dan ba zata koma gidan nan ba.
Takowa ya shiga yi a hankali yana nazarin ta har ya karaso ya tsaya daidai kanta yana rataye hannun sa a bayan sa.

“Tashi.”

Yace da ita kawai. Kin tashi tayi ta cigaba da kukan. Tsaki yaja da karfi, uana fama da ciwon kai zata zo ta haddasa masa wani, idan auren ne bata so da kansa zai dauke ta ya maida musu yarsu dan dama shima dan babu yadda zai yi ne. Sake maimaita mata ta tashi yayi amma ko gezau, ransa ne ya kara baci, ya saka hannun sa daya ya mikar da ita, saura kiris jiri ya kayar dashi saboda wani irin shock da ya shiga. Kanta ta sunkuyar kasa tana cigaba da kukan a hankali. Iyakar rikicewa yayi amma sai ya dake ya sake kallonta sosai dan da tunani yake mafarki yake ko kuma gizo take masa dan yasan babu abinda zai kawo ta gidan a wannan lokacin..

“Dan Allah ka barni na koma wajen Babana, wallahi zan tafi ba zan sake shiga rayuwar ku ba.”

Kasa magana yayi, dan yadda ya shiga shock har baya jin abinda take fada, kallon ta yake babu dauke ido irin kallon kece kuwa? Magiyar ta cigaba da yi masa shi kuma ya tsaya kawai yana kallon ta kamar a yau ya fara ganin ta.

“Dan Allah Dan Allah.” Tace tana kallonsa

Wani irin karfi da karsashi ne yazo masa, cikin abinda be wuce dakika biyu ba ya isa gabanta, ya hade dan gaf din da ya rage tsakanin su. Jitayi kawai ya rungume ta, da karfin gaske.

A guje gateman ya fada dakin sa, dan ganin abun da be yi tunani ba

“Dan Allah Dan Allah.” Ya maimaita abinda ta fada hankali, sannan yace

“Dan Allah karki tafi.”

Mutsu mutsu ta shiga yi zata kwaci kanta, ya sake riketa gam ya hanata motsi ko kadan, sai da ya tabbatar ya samu daidaiton bugun da zuciyar sa take sannan ya saketa, yana sakin ta tayi baya da sauri tana matsawa jikin gate din

“Dan Allah ka barni na tafi.”

“You are not going anywhere.” Yace yana kokarin rike hannun ta, kamar wadda taga abun tsoro haka ta ja baya tana boye hannun. Fasa rike hannun nata yayi yana yarfe su sannan yace

“Wuce ki koma ciki.”

“Ba zan koma ba, ni ba zan zauna ku cutar dani ba.”

“Cutarwa?” Ya maimaita kalmar

“Ok, ki koma idan safiya tayi sai ki tafi, yanzu kinga dare yayi it’s too risky ki tafi.”

“Zan iya tafiya a haka, ni dai dan Allah a bude min gate din.”

“Ya Allah.” Ya furta yana kallonta da shanyayyun idanun sa.

“Shikenan naji, muje ciki na kira Saddam yazo ya kaiki.”

Make kafada tayi alamun ba zata koma ba har lokacin kuma tana cigaba da kuka.

“I promise you.”

Yace yana son convincing dinta amma fafur taki, dan yadda ta fito gani take idan ta koma zai iya yi mata wani abun.
Juyawa yayi zuwa cikin gidan ya barta a wajen, waya ya dauko ya kira Saddam. Suna tare da Ammar a Central Park sunyi order abinci suna jiran a kawo musu kiran sa ya shigo.

“Oga ne.” Yace wa Ammar yana nuna masa wayar.

“Just pick, it’s already late ba zai ce kazo ka kaishi ba.”

Dagawa yayi yana sakata a handfree yadda Ammar din zai ji

“Oga sir.”

“Where are you?”

“Emm, muna nan hospital munzo duba wata Aunt din Ammar ne, bata dan jin dadi, akwai wani abu ne Sir?”

“No it’s ok, I will call you da safe, make sure ka samu amsar da zaka kare kanka kafin goben.”

Ya kashe wayar yana shafa kansa, Saddam yasan komai kenan, shiyasa yake cike da farin ciki a yan kwanakin, but how comes? Ya akayi hakan ta kasance. Fitowa yayi ya koma wajenta, baya son kukan da take shiyasa ya kira Saddam din da yana kusa sai yazo su kaita gidan may be da safe idan ta nutsu sai yaje but tunda Saddam din baya kusa abu daya kawai zai mata, duk da yasan ba zata so ba kuma hakan na iya kara yawan kukan nata.
Yana isa wajen da take a tsaye be yi wata wata ba, ya dagata sama ya juya da ita zuwa cikin gidan tana kuka tana rokonsa be tsaya ba har sai da ya kaita bedroom din nata sannan ya dire ta a saman gadon yana sauke ta, ta tashi da sauri zata koma fita ya tarota ya sake matse ta gamgam a jikinsa yana sauke gagarumar ajiyar zuciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button