Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 26

Sponsored Links

Arewabooks; hafsatrano

Page 26

MUFEEDAH’S FRAGRANCE

GIDAN KAMSHII!!!

WATO JAMA’A MUFEEDAH’S FRAGRANCE TA KAWO  KAYAN TURARE MASU INGANCI DA KWANTAR DA HANKALI A KUDI QALILAN  MUNA TURARUKA KAMAR HAKA

07040986690

Turaran wuta
Turaran kabbasa
Turaran jiki
Turaran moping
Turaran wanka
Kindykay

Humrah milk
Humrah black
Brown kwalacca
Black kwalacca
Cream kwalacca
Oil perfume golden
Freshener
Diffuser 07040986690

Mufeedah’s fragrance  Muna da tsarın wholesale wato sarı Kenan Muna Bada sari sticker Kawai Zakiyi kısa a jikin kayan ki yazama kamar kece kikayii Abinki mufeedah’s fragrance na zaune a garin Abuja da kuma kano zaku iya tuntubar mu ta wannan number

07040986690
Bissalam

****

“Ango kasha kamshi.”

Mummy tace tana dariya

“Barka da safiya, an tashi lafiya?” Ya tambaya yana kin bada muhimmanci a maganar ta

“Lafiya lou son, ya amarya?”

“Lafiya lou.” Ya fada yana kallon side din da Noor din ke zaune

“Toh ya kaga amargar?” Ta tambaya cikin sigar tsokana

“Alhamdullillah, dama kira nayi, nayi godiya. Angode Allah ya saka da alkhair.”

“Toh Amin, ga dai amarya nan ka ganta, sai ka lallaba dan kasan matsalar talaka be iya samun waje da cin hatsi ba, sai kayi hakuri duk da nasan dama ai ka saba hakurin, afa yi hakuri a lallaba dan za’a sha fama.”

Ta karashe tana shekewa da dariya dan ta hango kalar tashin hankalin da zai shiga idan yaga yarinyar da baya so yasa ta kora itace a matsayin matar sa, tun jiya take hasaso kalar bacin ran da yake ciki tana sheka dariya dan tasan duk hakurin sa sai ta kaishi karshe amma shine dan iya bariki hadda kiran ta kai tsaye wai godiya. Yanzu jira take Asim ya dawo ta karasa abinda ta faro dan ta tabbatar sai an yi dan karamin tashin hankali dan ba zata taba barwa Asim din kofar da zai zargeta ba, sai dai ya zargi Rafeeq din da cin amanar sa.

“Uhmm, shikenan toh zamu zo har gidan muyi godiya.”

“Toh sai kunzo, Allah ya kawo ku.”

Tace tana ajiye wayar. Duk tunanin sa yasan dama akwai manufar ta na yi masa wannan auren, tabbas akwai shirin ta amma ko ma menene shirin ta sai dai tayi ta hakura,abinda yake so da kauna ne matuka duk da ya cire rai ta taimaka masa wajen kawo masa shi har tsakiyar dakin sa, yana ganin wannan shine mafi girman kuskure da zatayi domin idan burin ta, ta hada shi da Asim toh fa ita ce da kanta zata dauki wuka ta dabawa kanta da kanta dan me raba shi da Noor a yanzu sai dai mutuwa.
Sanda suka isa office din sai yace su jirashi a mota ya shiga ya fito. Duba abubuwan da zai duba yayi ya saka hannu a wanda zai saka sannan ya dauki notebook dinsa ya fito ya jawo office din.
A jingine da kofar ya sameta kamar ma bacci take ji yadda jikinta yake a mace, zama yayi yana ajiye notebook din a tsakiyar su sannan suka bar harabar office din.
Gidan nasu kuwa suka wuce daga office din dan dama ya fadawa Saddam da suka fito. Ba kamar yadda yake parking a chan nesa ba yau a gaba gaba sukayi parking motar na tsayawa ta kama handle din zata bude amma sai ta jita a rufe. Juyowa tayi ta kalle shi alamun ya bude mata amma sai taga yayi relaxing sosai yana mata wani irin kallo da idanun sa kamar me jin bacci.

“Kofan a rufe take.” Tace tana rike still da handle din bata saki ba. Motsa bakin sa yayi a hankali kamar me tsoron magana yace

“Open it.” Da sauri driver ya danna lock ya cire taja ta bude ta zura jikinta gaba daya sai ta tuna da kayanta.

“Kayana fa?”

“Za’a shigo miki dasu.”

“Zan iya dauka ma.”

Tace tana tsaye alamun a bude mata booth ta dauka.

“Idan kin shiga ki fadawa Baban zan shigo.”

Yace mata yana kin bata amsar maganar kayan da tayi. Dawo da kafafunta cikin motar tayi da sauri..

“Ba sai ka shigo ba dan Allah, ku tafi kawai ni dai.”

“Menene matsalar ki ne wai?”

Yace yana dan bude muryar sa, da sauri Saddam ya kama kofar motar ya fita shima driver ya fita.

“Ehen? Tell me your problem. Kince zaki zo gida na kawo ki, nace zan shigo kin ce a ah, me kike so toh.”

“Kawai ni ka tafi, idan ka shigo Baba fada zai yi min.”

“Me yasa zai miki fada? Kinyi laifi ne?”

Turo bakin ta, tayi tana kallon kofar ta juya masa keyar ta dan bata san amsar da zata bashi ba, ita dai kawai kar ya shigo ya tafi.

“Tell me, akan me zai miki fada?”

“Ba komai.” Tace

“Dole sai kayi laifi za’a maka fada ai.”

“Ni banyi komai ba.”

“Toh ki shiga kice masa zan shigo, idan kuma ba haka ba sai mu juya in da muka fito.”

“Na’am?”

Daga mata kai yayi yana maida kansa jikin kujerar ya rufe idon sa yana kokarin hana abinda yake ji akanta tasiri akansa, idan ta cigaba da zama a wajen zai yi mata abinda ba zata so ba shiyasa yake ta kokarin hana kansa din amma yaga kamar gata ganewa.

“Ni dai dan Allah karka…”

“Ya salam.” Yace yana tashi zaune sosai sannan fisgota jikin sa da wani irin hanzari, zatayi magana ya hade bakin su waje daya ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. Jikinta ne ya dau rawa gaba daya, gashi yayi mata rikon da duk bala’i bata isa ta kwaci kanta ba, sai da ya gaji dan kansa sannan ya cikata yana yin baya da kansa, murmushi kwance saman kimtsatsiyar fuskar sa.

“Idan kin shiga kice zan shigo.”

Ya maimaita mata yana kulle idonsa gaba daya. Kasa motsawa daga inda take tayi, wata masifaffiyar kunyar sa da kunyar su Saddam dake waje ta yi mata dabaibayi, hakan ya hanata yin kurin fita daga motar gaba daya sai ta chusa fuskarta cikin kafarta tana sakin dan karamin kuka. Be kulata ba sai da ta gaji dan ganta sannan ta goge fuskar tata, ta kama kofar ta fito daga motar. Babu kowa a kusa da motar suna chan nesa da wajen ma baki daya, gaba kawai tayi yana kallonta ta shige lungun nasu sai ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina girman rigimarta.
Wajen minti biyar da shigarta sannan ya kira Saddam a waya yace ya zo ya rakashi ciki, zuwa yayi ya bude masa motar ya fito yana gyara rigar sa sannan suka jera suka bi bayanta.
Baba ne kadai a tsakar gidan ta shige daki yana tsaye yana kiran sunan ta yana tambayar ta lafiya amma taki bashi amsa sai kuka kawai take yi, sallamar da akayi a a wajen yasa shi kyaleta ya nufi zauren yana amsawa.

“Wai wai wai, sannun ku da zuwa.”

Yace fuskar sa na fadada da farin ciki ganin Rafeeq din da Saddam.

“Sannu Baba.”

“Yawwa sannun ka dai, Bismillah ku shigo.”

Ya wuce ciki suka bi bayansa ya bude dakin sa yace su shiga dan tsakar gidan akwai rana kasancewar rana ta soma yi. Da sauri ya dauko darduma ya shinfida musu sannan ya zauna a kasa yana cigaba da yi musu sannu da zuwa. Gaisheshi sukayi ya amsa sannan ya tambaye su mutanen gida da aiki Saddam ne me amsawa shi Rafeeq nauyi da kunyar dattijon ta cikashi ga wata irin kaunar ta musamman da yake yi masa.

“Ashe kuna tafe, ta shigo fuu tana kuka ina ta tambayaar ta kalou amma bata ce komai ba sai gaku, ina ganin ku nace toh sokantar tata ce ta motsa idan ba haka ba, menene ma ya kawota gida yanzu daga tafiya jiya jiyan nan?”

“Ba komai Baba, dama zan zo na gaishe ka shine tace zata zo kuma.”

“Sai ka biye mata? Aure fa yafi karfin wasa, karka sake biye mata da irin wannan shirmen dan su mata ba hankali ne dasu ba.”

“Haka ne Baba, za’a kiyaye in sha Allah.”

“Yawwa, kuma zan mata fada dan nasan ba lallai kayi mata ba, tunda har ka biye mata tana wannan shiriritar.”

Murmushi kawai yayi suka dan yi jum, kafin Baban ya cigaba da dan sako masa tambayoyi yana kara sani akansa da kan harkokin sa. Sosai ya zama open ya dinga fada masa komai har abinda ma be tambaya ba sai da ya fada dan yana so ya gamsu na ba zai cutar masa da Noor ba. Sosai ya kara birge Baban ya kuma yaba mishi sannan ya saka musu albarka gaba daya.

“Zamu tafi.”

Yace yana mikewa sai Saddam ma ya mike da sauri ya riga shi fitowa waje, tare suka fito da Baban ya dan russuna kadan yayi godiya sannan yace ta zauna da yamma zai dawo sai su tafi.

“Wa? Akan wanne dalili?”

“Ba komai Baba.”

“Jira matar ka, ku tafi gida. Bata da hujjar dawowa gidan nan yau”

Ya wuce gaba zuwa dakin nata ya daga labulen yana kallonta a zaune tana sauraron su. Fuskar Baban a hade yace

“Tashi maza kizo ki bi mijin ki.”

Karon farko da taga fushi sosai kwance akan fuskar Baban gashi ko bayanin da zatayi masa batayi ba wanda dama tasan in dai yace sai ya shigo Baba ba zai saurare ta, tashi tayi kawai dan tasan halin Baban idan yayi fushi dan haka gwara kawai ta bishin idan yaso daga baya sai tasan me zatayi. Yana tsaye tazo ta wuce tayi hanyar waje sai ya sake yiwa Baban sallama yabi bayanta kawai.
Saurin da take yasa kafin ya kai har ta shige motar ta zauna tana kumbure kumburen fuska, shigowa yayi ya zauna sannan ya kalleta yaga ta kalli glass gaba daya sai kawai yace wa Saddam su wuce gida.
Karfe daya da rabi suka shigo gidan nan ma suna tsayawa ta bude kofar tayi ficewar ta, ta shige ciki da sauri dan kar ma ta tsaya wani abun ya hada su.

“Sir kayan da aka saka a booth fa?”

“Shigo min dasu.”

Yace yana yin gaba, be tarar da ita a falon ba sai kawai ya ajiye hular kansa ya wuce bedroom dinsa ganin lokacin sallar azahar yayi.
Tare sukayi sallah da su Saddam sannan yace su bar masa mota biyu a gidan suje sai gobe dan yana so da magriba su fita yayi mata shopping din kaya baya so kuma su fita dasu Saddam din tana bata masa rai a gabansu.

***Tunda sukayi wayar nan Asim yaji ta dauke yake ta gwada number amma switch off, gaba daya ya damu zuciyar sa na gaya masa akwai matsala amma be san wanda zai samu ya taimaka masa wajen sanin me yake faruwa ba, haka ya tattara ya hakura kawai gashi dama sun shiga busy sosai saboda AJI yace ya gaji ya gama hada komai zuwa kwana uku zasu tattara su bar kasar zasu biya Ethiopia su yi kwana biyu sannan su dawo Nigeria maimakon sati ukun da ya ce da. Wannan abun yasa ya sake shiga busy sosai yana fatan koma menene dai idan ya dawo zai je suyi magana a san me ake ciki.
A gajiye ya dawo dakin sa bayan magriba, sai da ya fara yin sallah sannan ya kira Rafeeq. Kwana nawa basuyi waya ba wai irin ya bashi space din nan tunda yayi amarya. Rafeeq na zaune kiran Asim din ya shigo ya dauka a nutse yana yin sallama.

“Angoooo.”

“Kana da matsala.” Yace yana murmushi

“Sai ango, kwana biyu shiru kayi luf abun ka mutumina.”

“Ka ganka ko? Abinda ka kira ka fada min kenan na kashe wayata ko ya ya?”

“Allah ango kana cikin alkhairi dumu dumu, how I wish.”

“Baka da kunya fa Asim, idan baka da abin fade zan yi gaba. Ina da aikin yi dan naga kaman kai kana da time din surutu.”

“Dawowa ta fa kenan, AJI ya matsa ashe haka kuke fama wai? Wai a kwana uku zan gama hada komai zamu taho, in 5days dai in sha Allah muna Nigeria, ji nake kaman an daure ni anan na gaji wallahi.”

“Toh ka nutsu kayi abinda ya dace, kasan AJI baya wasa da harkar business idan yaga kayi abinda ya dace sai kaga ya sakar maka ragamar gaba daya.”

“No bana son irin wanna nauyin wai, na bar maka dai wallahi. Nafi son soft life malam, wannan rayuwar haka duk ba dadi.”

“Aiko dole kayi yaro, ka riga ya fado a gidan mu dole ka tashi tsaye ba’a zama in ba haka ba ka shiga black list din AJI, kasan dai me hakan ke nufi.”

“Ni ai bore zan masa wallahi, ba zan yadda ya tula min aiki ba, ni aure ma nake so nayi kawai, kusan kullum sai…”

“Kana karasawa zan kashe wayata.”

“Aah karka kashe, kira nayi muyi magana me muhimmanci, nasan babu wanda zai taimaka min sai kai.”

“Ina jinka.” Yace yana gyara zama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button