Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 27

Sponsored Links

Arewabooks;hafsatrano

Page 27

***
AJI ne ya turo kofa ya shigo abunda ya katse maganar da Asim din zai yi, tashi yayi daga riginginen da yayi sannan yace

“Zan kiraka.” Ya katse wayar.

Cigaba da aikin sa yayi bayan sun gama maganar yana yi rabin hankalin sa na wajenta yana jin son zuwa ya dubo ta amma baya son rigimarta. Shi mutum be da ko kadan baya son hayaniya shiyasa komai yake bin sa a hankali.
Sai da ya gama aikin ya tattara notebook din ya rufe sannan ya mike yana yin salati saboda yadda ya gaji sosai. Dakin nata ya kwankwasa a hankali sannan ya tura kofar ya shiga. Tana kwance yau ma a kasan saman abun sallah daga gani sallah ta idar bacci ya dauke ta a wajen. Yanayin yadda ta kwanta ya tabbatar mata da ta saba kwanciya a hakan cike da tausayin ta ya karasa kusa da ita a hankali dan kar ya tada ta. Yana so ta tashi daga kasan ta kwanta sosai amma kuma yana tsoron rigima sai ya kyale ta kawai ya saka hannu ya dauki pieces din wayarta dake kusa da ita ya juya ya fita. Dakin sa ya shiga ya ciro sabuwar wayar da ya karba dazu daga charge ya zare sim card dinta ya saka a wayar sannan ya kunna ta.
Message din Asim ne suka shiga jerin shigowa a jajjere wanda ya turo wayar na kashe. Daya bayan daya ya bude su ransa na sosuwa duk da yayi musu uzuri dukka ba kuma zai bari abun yayi tasiri akansa ba sai kawai ya goge su dukka sannan yayi copying contact din kan sim card din da basu wuce goma ba, ya maida su kan icloud ya zare sim din ya dora shi saman mirror sannan ya dauko new sim card ya saka mata.
Har ya fita sallar magriba ya dawo ya lekata still baccin take, gashi yana so su fita daga nan su biya gida kamar yadda yacewa mummy zasu shigo.
Zuwa yayi gabanta ya zauna dirshan sannan a hankali ya shafi gefen fuskar ta, motsawa tayi ta bude idonta akansa sai ta tashi zaune tana jingina da jikin gadon.

“Anyi magriba.”

Gid’a masa kai tayi alamun toh dan wani irin azababben magraine ne yake damun ta shi ya sakata baccin dole bayan tayi amai.

“Kanki?” Yace yana kallon yadda ta dafe kan tana dan yamutse fuskar ta. Hawaye ne ya taru a idon ta, ta sake daga masa kai tace

“Umm.”

“Karki kuka, kara miki ciwon kan zai yi, tashi ki lallaba a hankali kiyi sallah sai kisha magana. Sannu.”

“Let me help you.”

Yace yana mika mata hannun sa. Bata musa ba ta karba ya mikar da ita tsaye ta wuce toilet tana jin kan kamar zai fado shi kuma ya fice zuwa kitchen.
Warming abinci yayi mata, ya hado da ruwa da paracetamol ya ajiye a tsakiyar falon dan baya son zaman dakin da take gashi kamar ciwon kan yasa tayi laushi zai yi amfani da damar wajen sakata sakin jikinta ko yaya ne.
Dakin ya koma ya sameta ta fito har ta tayar da sallar ma a zaune dan bata jin zata iya yin sallah a tsaye dan ko ya idanun ta suka kalli kasa sai taji kamar kan zai fado. Tsaye yayi jikin kofar har ta idar tayi addua sannan ya karaso ya taimaka mata ta tashi, ya kama hijab din zai zare mata shi amma ta rike tana marairaicewa. Kyale mata yayi yace ta biyo shi. Jikinta a sanyaye ta bi bayansa zuwa falon ya zauna sannan yace ta zauna itama. Zama tayi ba tare da musu ba, ya jawo mata plate din abinciin ya tura mata gaba yana saka mata spoon.

“Ba zan iya ci ba.”

“Daurewa zaki, ko kadan ne kinji?”

Shiru tayi tana kallon abincin dan bata da appetite din ci ko ruwa tasha idan tana wannan irin ciwon kan sai ya dawo. Matsowa yayi sosai kusa da ita ya matso da plate din gabansa ya debi abincin ya nufi bakin ta.
A hankali ta dinga karbar abincin da kadan kadan har ta ci ba dan laifi sannan ya bata maganin tasha ta tashi zata koma daki ya zaunar da ita yana girgiza mata kai.

“Zauna ki kalli TV idan kin koma boredom ne zai dame ki.”

Zama tayi shi kuma ya wuce bedroom dinsa ya zura farar jallabiya da hula ya fito rik’e da karamin blanket ya rufa mata kafarta dashi sannan yace mata yana zuwa. Ta gefen ido ta bishi da kallo tana mamakin calmness dinsa. Yadda yake tafiyar da abubuwan sa da wani irin class gashi sam bashi da hayaniya ko rawar kai komai a kamile yake yin sa. Cigaba da kallon TV tayi tana kokarin dauke tunanin nasa daka kanta. Doorbell din ce tayi kara, ta kalli kofar tana of
Aneesa,Ummita da Laila ne sai Asmeey cousin din su Aneesa. Kokarin bangaje ta Ummita tayi, tayi baya da sauri, ta basu hanya suka shigo.

“Samun waje diyar talakawa.”

Laila tace tana karewa falon kallo hade da watsawa Noor din wani banzan kallo.

“An samu waje an mike kafa, kamar gidan uban mutum.”

“Kinsan yayan talakawa basu iya cin arziki ba, ji be ta kamar wata yar aiki ba shiga ba kama abun takaici, an zo an maka uban gida an saka yar matsiyata ni banga amfanin plan din Mummy ba wallahi.”

“Wai dama wannan ce matar Ya Rafeeq din? Tabbin sam ba class wallahi.”

“Laifin Mummy ne, bansan me yasa ta shirya auran nan ba, amma dai zamu gani dan ya Rafeeq sai Laila itace daidai shi.”

Wani girma kan Laila yayi ta haye kujerar da Noor din ta tashi ta zauna tana crossing kafarta.
Bata tanka musu ba, tayi tsaye kawai tana jin cin mutuncin da suke mata, hawaye ne yake son fito mata amma tana daurewa dan bata so ta kulasu ko tayi kuka su sake samun lagon ta sai kawai ta tsaya kanta a kasa tana ta kokarin hana kukan zubowa.
Kofar kitchen ce ta bude, ya shigo yana rik’e da wasu ledoji a hannun sa, ya dora su a saman dinning sannan ya nufi wajen da take tsaye.

“Ya Feeqq welcome.” Aneesa tace tana tashi tsaye.

“Jeki dakin ki.”

Yace mata yana wuce ta zuwa tsakiyar falon. Da sauri ta nufi bedroom din nata kukan da take tarewa na zubowa tana shiga ta rufe kofar ta zauna ta shiga rera kukan cikin jin zafi da radadin zagin da sukayi mata ita da mahaifin ta.
Zama yayi a daya daga cikin kujerun falon yana kokarin danne bacin ransa dan yaji komai da suka fada. Masallaci yaje yayi sallah yana dawowa yaga motar gidan nasu ya tabbatar wani ne yazo yayi tunanin Mummy ce amma sai driver da ya kawo su yace masa su Aneesa ne. Fasa shiga ta main entrance din yayi ya koma ta baya ya shiga ta kitchen shine yaji duk abinda suka fada wanda dama abinda yake so yaji din kenan.

“Aneesa.”

“Na’am Yah, ina ta maka sannu da zuwa baka amsa ba.”

“This should be the first and the last time da zaki kara dauko min useless mutane ki kawo min gidan nan.”

“Yah??” Tace tana kallon sa hankali a tashe.

Fuskar sa a dinke tsaf babu alamun wasa ya daga mata kai

“Yes, yau ya zama na farko. Zan bar shi ya wuce amma idan kika sake, zaki san dayan side din nawa da baki sani ba.”

“Ku tashi ku fita kafin nasa a fitar min daku, bunch of fools.”

Mikewa sukayi suka bi hanyar da suka shigo amma sai Laila ta zauna tana kallon sa

“Feeqq wai me nayi maka ne? Akan wannan banzar yar kauyen zaka ci mana mutunci ka kore mu? Ko sonta kake ne?”

Laila tace tana nuna tsantsar bacin ranta.

“Yes ko kina da matsala da hakan ne?”

“Ina dashi, menene matsayi na a wajenka toh ni?”

“Matsayi? Ke har kin dauka kina da wani matsayi wajena dama?”

“Eh.”

“Toh bari kiji, baki da wani matsayi a wajena,kuma wannan ya zama na karshe da zaki kara tako kafa zuwa in da nake, ko kice zakiyi insulting matata, wallahi wallahi sai kin gane baki da wayo.”

Sai ya mike tsaye

“Idan kin gama zaman ki rufe mana kofa.”

Iyakar shaka ta shaka, tana kallo yabi hanyar da Noor din tayi, ya shige ciki ya barta a wajen. Tashi tayi tana gayawa kanta zatayi nasara wallahi ko baya so dan ba zata iya hakura ba. Shi da kansa ya koya mata sonsa daga baya kuma yace ba haka ba, ba zata sabu ba dole ta samu cikar burin ta.

***Kuka ya sameta tanayi, ransa ne ya kara baci duk da dama ya san abinda zata shigo tayi kenan.

“Kuka baya miki wahala ne?”

Ya tambaye ta ganin ta dago. Bata ce komai ba sai rage kukan da tayi

“Idan kika ce komai kuka zaki masa kowa taka ki zai, stand for your self duk wadda ta fada miki magana ki mayar mata.”

“Oya tashi ki wanke fuskarki kizo na nuna miki wani abu.”

“Ina kayana?”

Tace tana goge fuskar da bayan hannun ta.

“Me zaki dasu?”

“Chanja wannan zan yi.”

“Ok, zo ki karba.”

Ya juya ya fita. Tashi tayi ta zura hijab dinta tabi bayansa. Bedroom dinsa taga ya shiga kamar ba zata bishi ciki ba amma sai ta bishi din kila kayan suna ciki. Shiga tayi da sallama mayataccen kamshin nan nasa ya riga shi amsa mata sallamar wani irin sanyi ya bugo ta hade da kamshin sai ta lumshe idonta tana jin dadin yanayi.

“Gata chan.”

Ya nuna mata karshen dakin in da akwatin take a ajiye. Wuce shi tayi da sauri zuwa wajen akwatin dake a bude an fiffito da kayan ciki harda underwears dinta sabbabi. Kunya ce ta kamata ganin white bra dinta a saman akwatin bayan da kanta ta jera kayan kuma a kasa ta saka ta, kenan bude mata kayan yayi?

Tattara su ta shiga yi tana jin takun sa na karato ta, ta hade su ciki zata rufe ya rike hannun ta yana rankwafowa kanta.

“Wanda zaki saka kawai zaki dauka ki bar sauran, chanja su za’a yi.”

“Dukka nake so.”

Ta kara ja zata rufe amma ya hanata gashi ya rankwafo gaba daya kanta har jikinsa na taba nata.

“Sun zama nawa.”

Sakar masa tayi a kunyace ta dauki wata doguwar riga da Hijab zata tashi ya rik’e ta yana kallon kwayar idon ta.
Kafadarta ya kama ya mikar da ita tsaye ya juyo da ita tana fuskantar shi.

“I want you to be strong, karki kara yarda wani ko wata yace zai taka ki, duk wanda ya fada miki magana ko waye, ki bashi amsa daidai dashi.”

Da sauri ta gid’a masa kai ganin yadda ya matso daidai fuskar ta yana maganar hucin maganar tasa na taba fatar fuskar ta.

“Good girl.”

Yace yana kai bakin sa kan kumatun ta, yayi mata peck ta damke idonta da sauri. Murmushi yayi yana jin da gaske ba zai iya jurewa ba, duk yadda ya kai da daurewa yana neman gazawa gashi baya so yayi abinda zata kara jin haushi sa duk a gaba daya yau tunda suka dawo batayi wani abu ba be sani ba ko fadan Baban ne ko kuma hakura tayi kawai.

“Zan tafi.”

“Ba wanka zaki ba? Kiyi anan kawai.”

“Na’am?”

“Yes, akwai komai anan kiyi kawai anan idan kin gama zan nuna miki wani abu.”

“A ah nafi so nayi chan.”

“Why?”

“Ni kawai nafi so nayi a chan.”

“Ban yarda ba, anan zakiyi.”

“Bari kiga.” Yace yana kama hijab din jikinta, ya cireshi ya jefar a gefe. Da sauri ta hade hannun ta kirjinta gabanta na faduwa dan gaba daya wani irin banzan dinku Salamatu tayi mata a kayan da ta dinka mata sababbin dan da ta saka ma ita kanta kunyar kanta ta dinga ji. Hannun ya kama ya rike gaba daya yana kallon ta sosai wata masifaffiyar kunyar sa ta kara lullube shi. Runtse idonsa yayi yana kokarin dauke kansa daga kai yayi gaba yana cewa

“Kiyi wankan kafin na dawo.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button