Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 33

Sponsored Links

Arewabooks hafsatrano

Page 33

***Kukan takaici tayi sosai bayan sun gama waya da baba. Takaicin ta da abinda ta aikata wa dan bawan Allah bata duba yadda ya karbe ta ba, bata duba matsayin sa ba da komai. Da kyar ta daidai ta kanta ta wuce bedroom dinsa ta gyara ko ina ta wanke toilet tsaf sannan ta fito ta wuce kitchen ta hau shirye shiryen dora lafiyayyan lunch wanda tasan dole zai masa dadi duk da bata san likes dinsa ba amma zata dauki abinda mutane da yawa suka fi so, rice. Lafiyayyar lamb mandi rice ta hada masa da pineapple juice, coconut milk shake taso hada masa taga babu shine kawai tayi amfani da pineapple sannan tayi hadin salad ta kammala komai ta ajiye sannan ta wuce dakin ta, tayi sallah ganin azahar tayi. Tunda tazo gidan ta lura da gayun sa da son kasancewa tsaf tsaf ko sau daya bata taba ganin sa wani iri ba ko yaushe mayataccen kamshin nan nasa take shaka sai ta mike tana jin wani kaimi da kwarin guiwa tana son gwada abinda zata siyar ma kanta mutunci da girma bayan wanda ta bara a jiya da ranar farko. Wanka ta shiga, ta wanke jikinta tas da gashin kanta sannan ta fito ta zauna tana kallon kanta da fatar ta a mudubi. Yan kwana biyun da tayi har ta soma chanjawa fatar ta, ta sake wani irin fresh da wani irin fari fari da laushi, bata sani ba, ruwan gidan ne ko AC ce dan ance itama tana gyara jiki. Cikin mayukan da ya siya mata ranar ta dauko daya ta bude wani kamshi ya buge ta, ta lumshe idonta tana jin dole masu kudi suyi kyau idan dai irin wannan rayuwar suke yi. Man ta shafa a ko ina ja jikin ta sannan ta bishi da wani hadadden oil perfume. Kanta ta gyara ta busar dashi ta shafa masa mai ta tattare shi waje daya ya kwanta luf sannan ta dauki wata black abaya ta saka ta tsaya tana kallon kanta da kanta a mudubi, babu powder ba komai amma tayi wani irin kyau me sanyi. Murmushi tayi ta dan shafa powder din kadan da lipstick sannan ta dora veil din abayan a saman kanta ta zura slippers ta fito falon gidan.
Kallon time tayi a wayarta tana fata da burin ya shigo a yanzu ya ganta tasan dole ya yaba, hakan zai bata kwarin guiwar cigaba za kuma ta yi amfani da wayar ta shiga abubuwa da zata kara samun sani akan rayuwar auren gaba daya da yadda zata kula da kanta ya kula da shi kuma.
Tashi tayi ta kunna tv ganin tunanin na neman hanata sukuni duk yadda ta motsa sai ta dinga ganin handsome fuskar sa tana mata murmushi sai kawai ta zubawa tv din ido amma still kwakwalwarta taki ta kyale ta.

Related Articles

***A gida yaje ya samu AJI yana breakfast Mummy na zaune gefen sa suna hira. Ita ya fara gaisarwa ta amsa tana tambayar sa gida da family sannan ya gaida AJI ya zauna a gefe yana jiran ya gama. Sai da ya gama gaba daya ya sha ruwa yayi hamdala sannan ya juya wajen Rafeeq din yana goge baki da tissue

“Baka gama hutun angoncin bane ba? Kwana uku baka zauna office ba.”

Murmushi yayi ba tare da yace komai ba, sai AJIn ma yayi murmushi kawai yana cewa

“Ai gaka nan har ka kara kiba, jairi ashe kana son auren kayi shiru da kai, ina sane nayi maka haka ai.”

“Gashi nan yayi tsaf dashi ai.” Mummy tace tana dariya itama

“Barshi mana Hajiya, wai shi ja’iri.”

“Toh yanzu dai duk ba wannan ba, a koma bakin aiki shine mafi a’ala. Zamu dauki sababbin ma’aikata inaso ka shirya yadda abun zai kasance sai ku yi magana da daily trust su buga, ga Asim nan duk abinda ya faru a tafiyar mu ku zauna ya sanar da kai, sai kayi handling komai.”

“Ai zan iya ma kula da wannan bangaren, ba sai ya taimaka min ba.”

Asim yace yana shigowa falon, wani kallo AJI yayi masa sannan ya kalli Mummy data dauke kanta kamar bata san me ake ba.

“Ayi hakuri AJI, na shigo ban nemi izini ba.”

“Ina sauraron ka.”

“Dama cewa nayi, zan iya kula da duk abinda ya faru a tafiyar mu, bana jin akwai bukatar shi i can handle everything.”

“Yaushe muka fara haka Wakili?”

“AJI a barshi yayi kawai,tunda yace zai iya nima aikin dama zai min yawa, kuma ina bukatar taimakon sa.”

“Naji, amma ban yarda yayi komai shi kadai ba, ya nemi shawara da taimakon ka dan kafi shi sanin komai ka fishi experience.”

“In sha Allah.”

“Kaji dai Wakili ko?”

“Naji AJI.”

“Kai kuma, inaso anjima bayan isha kuzo kai da Yar tawa. Inaso naga surukata sannan sai muga yaushe zan saka bikin, kafin nan amma inaso kuje Geidam.”

“Geidam?” Mummy tace tana kallon AJIn

“Eh kwarai, yaje ya gaishe su sannan ya kai musu matar sa su ganta, ko laifi ne?”

“A ah babu laifi, mutum da dangin mahaifiyar sa, yana da kyau hakan.”

“Zaku iya tafiya, duk da dama kai Wakili ban neme ka ba, gayyar sodi ce.”

Haushin maganganun suka bawa Mummy, har yanzu AJI shi dai kawai Rafeeq komai shi komai shi ya iya, gashi da shegen iyayi shima duk abinda uban yace sai ya wani ce toh baya so ko kadan yaga laifin sa. Tare suka fito ita da Asim da Rafeeq din, shi Rafeeq yayi waje dan babu abinda zai cikin gidan su kuma suka shige ciki.
Gida yaso wucewa amma dole ya fara bi ta office din ya dauki abubuwan da zai bukata a weekend din ya dan zauna zuwa bayan sallar la’asar sannan ya tattaro ya taho gidan.
Sallah ta idar ta dawo falon ta sake zama tana fatan ya shigo a lokacin. Tana zama taji an bude gate ta mike da sauri ta daga curtains din tana leken wajen. Shi din ne kuwa, ya sakko daga motar calmly as always ya nufo kofar yana magana da Saddam. Komawa tayi ta zauna kirjin ta na bugawa amma ta daure ta cije duk da nauyi da kunyar sa da take ji ta zauna tana jiran ya shigo. Bude kofar yayi bayan ya sallami Saddam din ya shigo fuskar sanye da sunglasses da ya kara fito da kyawun sa. Tsaye ta mike tana murmushi a kunyace ta shiga wasa da hannun ta.

“Come on, please.” Yace yana bude mata hannun sa dan yaga alamar kamar abinda take son yi kenaan tana jin kunyar sa. Kamar wadda aka tunkuda haka ta tafi kunyar na neman tarde ta , ta kayar da ita. Shigewa tayi jikin nasa ta saki ajiyar zuciya tana jin wata irin nutsuwa da bata taba jin irin ta ba. Kakam ya rik’e rungume ta yaana shakar kamshin jikin ta me dadi yana lumshe idonsa, Allah ya sani yana kaunar baiwar nan ba kuma kadan ba har ya kanyi mamakin kansa da kansa. Da kyar ya zareta yana mata wani narkaken kallo ganin yadda tayi wani kyau me daukar ido bakar abayar tayi mata kyau kamar yar balarabiya.

“Kinyi missing dina ko?” Yace yana kama hannun ta suka karasa cikin falon ya zauna yana sake jawo ta gaba daya jikinsa.

“Ka dade.”

“Wallahi, office naje bayan naga AJIn, yanzu ma gudowa nayi.”

“Sannu.” Tace a hankali ya amsa yana shafa gefen fuskar ta

“Yau ma kinyi kuka?”

“Um um, banyi ba. Munyi waya da Babana.”

“Babanmu dai ko?”

Dariya tasa ta gid’a masa kai

“Akwai labari kenan.”

“Umm.” Sai ta yunkura zata tashi ya riketa yana hanata tashin

“Ina zaki?”

“Abinci zan kawo maka.” Tace a kunyace.

“Wow, girki kikayi min?”

“Eh.”

“Lallai zanci dadi, bari na rage kayan jikin nan nazo, bani 5mint.” Yace yana mikewa, kitchen ta wuce shi kuma ya shige daki. A saman dinning ta jera masa komai, yazo ya sameta ya tayata suka kwaso suka dawo dashi tsakiyar falon ya zauna ya zuba ya soma ci yana santi. Murmushi kawai take na jin dadi har ya gama sannan ya sake tayata suka kwashe kayan suka kai kitchen ta tattara hannu zata fara wanke wa, ya nuna mata dishwasher dake tsakanin fridge da washing machine yace just for today kafin su dawo bakin aikin su. Sam bata ma lura da ita ba kwata kwata dazu da tana kitchen din dan tayi baya Kuma kitchen din yana da girman gaske, zuba su tayi kawai a ciki nan da nan ta gyara ta maida komai muhallin sa sannan ta zo ta sameshi a falon yana duba abu a cikin system dinsa. Gefen sa ya nuna mata ta zauna tana kallon yadda yake operating computer din har ya gama shigar da komai daf da magriba sannan yace su je suyi sallah. Shi ya jasu magribar be fita masallaci ba suna idarwa yace taje ta shirya zasu fita unguwa. Dakin ta , ta shiga shima ya tafi nasa ta duba cikin sababbin kayan da suka siya ranar ta dauko wata HKG Vlisco mix and match da tayi mata kyau ta saka ta samo matching veil, shoe da bag ta hada tayi wani irin azababben kyau kamar ita tayi kanta. Tabbas ita din me kyau ce sai rashin kayan gyara da zasu fito da ainahin kyawun nata amma a yau ta kara tabbatar da hakan dan gani ta dinga yi kamar ba ita, kamar an sauya ta da wata daban. Turo kofar yayi yana karya hular sa, sai ya tsaya chak yana kallon ta.

“Wow.”

Ya samu kansa ta furtawa yana kare mata kallon tayi masa kyau kwarai gashi kayan sun yi fitting dinta sosai both colour din da dinkin.

“Kinyi kyau sosai.”

A kunyace ta amsa masa tana kokarin saka takalmin nata. Matsowa yayi ya taimaka mata ta saka sannan suka tashi a tare ya bi fuskar ta da ido zuwa bakin ta da ta shafawa lipstick. Kasa resisting yayi ya rikota ya shiga kissing din lips din nata gently, rirrike shi tayi da karfi tana jin kamar zata fadi ya saki murmushi yana cigaba da yi cikin salon burgewa yana kuma karantar response dinta. Ba kamar wadanchan lokutan ba, sai yayi murmushi kawai yana yin baya yadda zai kalli kwayar idon ta sosai. Kin yadda tayi su hada ido kunyar sa na mamaye ta.

“Stop pretending.” Yace yana yin dariya me sauti

“Ana so ana kaiwa kasuwa.” Ya dora

Bubbuga kafa ta fara yi kamar zatayi kuka ya dinga mata dariya kawai dan ya gano gaba daya ma akwai yarinta a tattare da ita. Kama hannun ta yayi suka fito zuwa compound din. Da kansa zai yi driving ya bude mata gaban motar ta zauna sannan ya zagaya ya shiga ya daura seatbelt suka wuce. Gidan Baba ya so su fara zuwa Amma ganin time din da AJI yace su zo ya kusa sai kawai suka wuce gidan nasu idan suka gama da wuri sai suce wajen Baban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button