Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 35

Sponsored Links

Arewabooks; hafsatrano

Page 35

***Bubbuga kofar tasa ta hau yi jin ta rufe sanda ta karasa kofar dakin nasa.

“Asim, Asim. Bude mana.”

“Mummy please ki rabu dani.”

“Na rabu da kai Asim? Nice fa?”

“Please, zuciya na zafi take, just let me be please.”

“Akan me? Wani abun Rafeeq ya fada maka?”

Shiru yayi duk sai hankalin ta ya kara tashi

“Dan Allah ka bude min kofar nan, hankali na ba zai kwanta ba idan baka yi min magana ba, dan Allah bude.”

Zare lock din yayi yana matsawa baya ta shigo dakin da sauri tana riko shi ganin yadda yake layi kamar zai fadi

“Na shiga uku, menene haka Asim? Kasha wani abun ne?”

“Me yasa baki hana shi ba, me yasa kika biye masa bayan kinsan komai, kinsan tashin hankalin da nake ciki kuwa? Zuciya ta kamar zata buga, komai baya min dadi rayuwa ta, ta zama meaningless, so nake kawai na mutu ma!”

“Tas.” Ta dauke shi da mari tana huci

“Mahaukaci ne kai akan wata banza mara asali da tushe zaka dinga yiwa kanka wannan fatan? Kanka daya kuwa? Ko ka dauka dama zan amince maka ka auri yarinyar ne?”

“Na sani, dama nasan bakya so na. Ki barni kawai na mutu din tunda kowa ya juya min baya. Sau daya baki taba yaba min akan kokari na ba, sau daya AJI be taba yaba min ba bare ya nuna nayi wani abun bajinta. Kullum ina daukar kaina kamar bani da wani amfani , duk da haka nayi kokari sosai wajen kula da rayuwa ta, ban bari wani tunani ya shiga raina ba, me yasa ba zaki min abinda nake so sau daya ba? Me yasa kika biye masa kuka hadu kuka cutar dani cuta mafi Muni.”

“Na shiga uku na lalace, dole kaga Dr Asim, ban yarda haka Rafeeq ya barka ba, me ya fada maka? Wani abun ya fada maka da ya bata maka rai?” Ta juyo shi ya fizge yana daga murya

“Rafeeq, Rafeeq, Rafeeq! Kullum maganar daya ce, na gaji na gaji. Please na roke ki..” sai ya hade hannun sa waje daya

“Ki barni nayi rayuwa ta irin wadda na saba a dah, ki daina tunzura zuciya ta, ki daina kokarin saka min kiyayyar sa bayan wadda nake ji a yanzu. Na yarda ya fini, ya fini ta ko ina kuma bana burin karawa dashi, na roke ki dan Allah.”

Sai ya saka mata kuka yana zubewa akan guiwar sa, da sauri tayi kasa tana rungumo shi jikinta tana kukan ita ma

“Bansan da gaske son ta kake ba, wallahi ban dauka abun ya kai haka ba, dan Allah kayi hakuri. Na maka alkawarin zan sota, zan dawo maka da ita rayuwar ka, dan Allah karka saka kanka a matsala dan Allah.”

Sake kwacewa daga rikon da tayi masa yayi yana nuna masa kanta

“Har abadah matar Rafeeq ta haramta a gare ni, har abadah. Karki musu komai, ki barsu dan Allah.”

“Innalillahi, wannan wace irin masifa ce take neman kunno min cikin rayuwa?”

Mummy tace tana mikewa, ta fice da sauri dan tabbas bata ga ta zama ba, ba zata bari rayuwar Asim dinta ta lalace akan wata banza ba, dole tayi wani abu, idan ma hakuri zata bawa Rafeeq din ya saketa Asim din ya aura zatayi, dan tasan playing nasu kawai yake ba sonta yake ba.

Tana fita ya tashi ya maida kofar sa ya rufe ya murza key, yana bukatar kasancewa shi kadai, baya so ta dawo ta sake dalula masa kai shiyasa gwara ya rufe yayi kamar bacci yake ko ta dawo zata hakura ta tafi.

Dakinta, ta shiga ta dauki waya ta kira Hajiya Lubabatu, ita kadai ce zata nemo mata mafita a daren dan yadda taga Asim ba zata iya hakura sai da safe ta kirata ba.
Sau wajen biyar tana kiran ta amma bata picking,a lokacin ma tana tare da wani senator da yayi mata alkawarin wata kujera me tsoka a zaben dake gabatowa dan haka sam bata ji kiran ba wayar na chuse cikin handbag dinta kuma a silent take. Kamar zata zare haka ta sake kwasa ta koma dakin Asim din ta samu ya rufe haka ta karaci bugun ta, ta hakura ba dan ta so ba.

***Zagaye sosai sukayi a garin daga wannan titin su sauka wannan yana cike da jin dadin yanayi sai da yaga dare ya soma yi sannan ya tsaya ya siya musu abubuwan ciye ciye sannan suka yo gida.
Da kansa ya kwaso kayan suka shiga ciki ya zube su saman centre table ya zauna yana mikewa saboda gajiyar da yaji ta saukar masa gaba daya. Zama tayi a gefen sa tana jan dankwalin kanta baya da ya ishe ta da nauyi. Hannun sa ya kai saman kan nata ya karasa zare mata shi gaba daya yana dora hannun ya shiga shafa gashin nata a hankali yana lumshe ido.

“Bacci?”

“Ummm… Na gaji na dade banyi driving da kaina ba.”

“Ku yan gata ne ai.” Tace tana kokarin mikewa ta wuce dakin ta, maida ta yayi da hannu yana juyowa dukka ya dora kafafunsa a saman kujerar sannan yace

“Gatan me?”

“Komai ma, kunji dadi.”

“Kema haka ai, yar gatan Baba ce yana son ki, ko shekaran jiya sai da ya ce min na kula masa da ke.”

“Baban?”

“Eh mana.”

“Umm, Allah sarki Babana.”

“Nifa?”

“Me?” Tace tana kallon sa

“Kice Rafeeq dina.”

Zaro ido tayi,

“Please kinji, ko ba naki bane?”

“Ni ba ruwaana”

“Sai kin fada kuwa.” Ya kama ta gaba daya ya jawota jikinsa yana kokarin yi mata chakulkuli. Dariya ta shiga yi sosai har da kusan shidewa, sannan ya kyaleta yana murmushi shima. Tashi tayi ta gudu dakin ta, ta barshi a falon yana mata dariya. Kayan ta fara cirewa sannan ta shiga ta watsa ruwa tazo ta saka wasu marasa nauyi a cikin sabbin kayan ta shafa turare ta daura zanin ta akan rigar da bata da tsawo sosai tasa hijab ta tayar da shafa’i da wutri. Tana sallar ya shigo ya yi shirin kwanciya shima ganin tana sallah sai ya fita ya duba kitchen ya hada plain tea ya zauna yana sha dan baya jin zai iya cin wani abu me nauyi da zai kwanta.
Yana zaune ta fito sanye da hijab din da zani tazo ta kwashe ledojin da suka shigo dasu ta kai kitchen ta gyara kowanne a wajen da ya dace sannan ta fito tazo ta sake wuce shi zuwa dakin ta. Ta kai kofar zata shiga ya tsaida ita

“Kwanciya zaki?”

“Um, bacci.”

“Ok, bari nazo na nuna miki wani abu.” Yace yana dira cup din, ya kashe duk abinda zai kashe a falon yabi bayanta.
A gefen gadon ya sameta a zaune tana jiran shi baccin na daukar ta, maida kofar yayi ya rufe yasa lock ya kashe full light din sannan ya tako zuwa gabanta. Gefen ta ya zauna yana jawo ta jikinsa gaba daya suka kwanta a saman gadon.

“Let’s cuddle.”

Yayi whispering mata a kunnen ta. Kwanciya tayi luf a saman chest dinsa tana jin wani irin warmth. Lumshe idonsa yayi a hankali ya shiga caressing soft gashin kanta gently bakin sa na saman kunnenta yana hura mata iska me dumi a cikin kunnen wanda ya haifar mata da wata irin kasala ta kara shigewa sosai jikin sa tana kankame shi hakan ya bashi dama sosai ya cigaba da tafiyar ta ita cikin salo da kwarewa.

“I love you.”

Ya rada mata a kunnenta da muryar sa da ta sake chanja salo.

“I love you.” Ya sake maimaitawa, da sauri ta makalkale hannun ta a wuyan sa ta kara tura kanta sosai kamar zata shide.

“Kinsan me?” Yace yana birkito ta gaba daya ta dawo saman sa, girgiza masa kai tayi tana sake kwanciya luf akan nasa kamar wadda za’a kwace shi.

“So nake muyi hira, karki ce komai just listen to my heart beat, zan baki wani labari.”

Gyara mata kwanciyar yayi sosai yadda zata ji dadi sannan yace

“Sunana Rafeeq kamar yadda kika sani, nayi karatu na zuwa matakin masters sannan nayi wasu courses din akan business administration. Ni ne first born a gidan mu, sai Asim da kanwar mu Aneesa. AJI ne mahaifi na amma Mummy ba mahaifiya ta bace. Mahaifiya ta fulanin Geidam ce ta auri Baba bayan auran shi da mummy wadda a lokacin shekarar su shida da aure Allah be bawa Mummy haihuwa ba, mahaifiya ta na zuwa sai ta samu cikina tun daga lokacin AJI ya dauki soyayyar duniya ya dora mata saboda shi mutum ne me tarin dukiya dan haka yana da burin samun da namiji da zai taimaka masa wajen kula da dukiyar, shi kadai iyayen sa suka haifa kuma suka rasu yana matashi tun daga lokacin zuciyar sa ta sike ya zama baya tausayin kowa kansa kawai ya sani domin babu wanda ya taimaka masa sanda ya rasa iyayen sa. Tun farko babu zaman dadi tsakanin Mummy da Ammi ta saboda tana ganin zata kwace mata gida da miji bayan daga baya aka auro ta lokacin wani aiki ya kai AJI Geidam anan ya ganta. Tun da Mummy ta fuskanci Ammi na da juna biyu ta dau karan tsana ta dora mata fiye da da, ta fitini kowa a gidan dan dai ma AJI mutum ne shi tsayayye baya daukar raini da wargi musamman a wajen mace shiyasa duk abinda Mummy zatayi sai ya taka mata burki har zuwa sanda aka haife ni, shikenan sai AJI ya sake maida komai hannun Ammi yana ganin itace matar sa kawai gashi ta haifa masa namiji abunda ya kara tunzura mummy kenan ta dauki karan tsana ta dora min duk da duk abun nan da ake Ammi bata so tana kuma matukar yi mata biyayya dan ita din ba me son fitina bace amma AJI ne yake kara taimakawa wajen raba kan gidan nasa dan yadda ya nuna fifiko abayyane hakan ke kara tunzra Mummy din. Wata tara cif tsakani Mummy ta haifi Asim, tayi murna sosai amma kuma sai taga still hankalin AJIn yana kaina da Ammi be yi wani murna da haihuwar Asim din ba kamar yadda yayi a tawa, hakan ya kara girman rigimar har ta kai Ammi ta gaji tana maida mata. Duk da haka AJI be chanja halin sa ba, sai ma gaba da abin ya kara har muka kai wasu shekaru komai Rafeeq duk wani company da zai bude da sunana yake amfani komai. Ni da Asim akwai wata shakuwa me girma a tsakanin mu, mun taso kamar yan biyu ne duk in da daya yake dayan yana nan ko da kuwa mummy zata raba mu sai mun sake haduwa musamman Asim da shi yana da hayaniya da karaf karaf tun muna yara shi yake gudowa part din Ammi yayi zaman sa da kyar Mummy take maida shi wajenta wata ran har da duka take hada masa. Bana mantawa wata rana mun dawo daga school na shigo na samu Ammi a kwance tana ta juyi ciwon ciki babu kowa a sashen nata sai ita kadai, da sauri na fita naje na fadawa Mummy amma sai tace ba in da zata zo , haka na koma na sakata a gaba ina kuka har sanda mai aikin ta, ta dawo ita ta taimaka ta kirawo driver yazo aka kaita asibiti. Suna zuwa aka kwantar da ita ni kuma ina gida ina kuka har dare ba wanda ya san halin da nake ciki bare na san halin da take ciki nima, sai da AJI ya dawo da daddare sannan ya dauke ni ya maida ni dakin sa a chan na kwana ina jin su suna fada da Mummy har nayi bacci. Washegari na tashi da zazzabi ina kwance aka kira AJI a waya aka sanar dashi rasuwar Ammi! Ba zan iya tantance kalar tashin hankalin da AJI ya shiga ba, yayi kuka ina tayashi duk da ban san ainahin maraicin da ya tunkaro ni ba a lokacin. Tare muka je asibitin aka dauko ta, aka zo akayi mata sallah aka binne ta, ba tare da an jira yan uwan ta sun zo daga Geidam ba, abinda ya jawo rikici tsakanin su da AJI kenan suna ganin be kyauta musu ba, shi kuma yana ganin daidai yayi, karshe basuyi rabuwar dadi ba, dan sun nemi ya basu ni amma ya fafure yace da ransa babu wanda zai rike masa da haka suka hakura suka tafi shikenan, na cigaba da rayuwa ta a hannun Mummy da AJI.”.

Jan hanci yaji tayi alamun kuka takeyi, da sauri ya dago ta yana kallon fuskar ta.

“Laa kuka?”

“Shikenan na daina baki labarin, da ina so na baki wani labarin me dadi kuma amma na fasa.”

“Kayi hakuri na daina kukan toh, tausayi naji.”

“Tausayi na ko? Bawan Allah.”

“Toh ka cigaba.”

“Um um, dare yayi sai da wani lokacin, yanzu time dina ne.”

Yace yana zame hannun rigarta, da sauri ta kalle shi tana tuno ranar, sai ta yunkura zata tashi yayi saurin matseta, ya lalubi bakinta ya hade shi da nata waje daya. Ba zai iya jurewa ba tun ranar yake so ya kara amma yana jin tausayin ta, amma yau kam hakurin sa ba zai kai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button