Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 31-32

Sponsored Links

*31-32*_

 

Harara Hajjah ta watsa  mata tace “shine me don na watsawa wannan yar  matsiyatan yarinyar barkono kama godewa Allah daba  ruwan zafi na zuba na saliketa ba tunda aikinyi kake  nema  na nemo  maka Asararre sallamamme yanzu kai saboda bakada mutunci akan wannan yar iskar watsattsiyar yarinyar zaka wulaqanta Maryam meye zakaci da wannan ragowar talaucin yar matsiyata”
Ganin hajiyan batada niyyar yin shiru shikuma yanada abinda yafi wanda take fada muhimmanci yasashi nufar cikin dakin ya dago Asmah da taketa gursheqen kuka bathroom ya nufa da ita ya zubanta ruwa ta wanke maimakon taji sauqi sai ninki azaba, fitowa yayi da ita ya zaunarta gefen gado yace “ina zuwa” fita yayi ya nufi motarsa ya bude ya dauko wani magani ya dawo ya diganta a idon yanajin hajiya tanata sababinta amma bai tankata ba saima kulle qofar part din asman da yayi ya rinqa shafa bayanta yana hura mata iska a idon hardai ya samu bacci ya dauketa.

Related Articles

 

Part din mimee ya nufa cikin saa Hajjah ta tafi ya kuwa rufeta da bala’in da bata taba sanin ya iyaba kashedi kam tashashi har ya juya zai fita kuma ta kadansa ya dawo yace “karki gyara kuma kada ki daina kai qarata gurin Hajiya wlh zaki jawa kanki abinda baki taba tunani ba nayi tunanin kinada hankali shiyasa na sakoki cikin lamura na so tunda bakisan mutuncin ba aikin ma daga yau kuma daga yanzun na sauke itama matace kamarki ba yar aiki ba ki rinqayin abinki idan kinso daganan ki kaini inda yafi gurin hajiya tunda kina ganin akwai maganin da zatayi miki” ficewa yayi a hassale ya shiga motarsa ya fice a gdan.
Bai dawo ba sai dare ya jima a motarsa kafin ya fito ya dauki ledar da ya dawo da ita ya nufi part din Asmah ya shiga ya aje ledar da magungunan da ya taho mata dasu lkcn tana bayi ta dauro towel ta fito sukayi kicibis taja baya da sauri ta dauka hijjab dinta tasa yaja ajiyar zuciya ya fito da magungunan ya farayi mata bayani.

 

Bayan ya gama ya sake kallonta yace “idan kinsha ki kwanta idanma da wani abu da yayi saura zai fito” jinjina masa kai tayi tace “na gde ta juya ta dauki mai ta fara shafawa, miskilin shima fita yayi batayi tunanin zai dawo ba tajishi yana taba qofar ta bude ya miqo mata wata ledar yace “kisa wani abun a cikinki kafin kisha maganin” tana karba ya juya itama ta rufe dakinta ta murda masa key ta bude ledar bata wani iyacin abincin na kirki ba tasha maganin ta koma ta kwanta.
Fita yayi ya koma dayan part din yayi wanka yayi sallah ya kwanta zuciyarsa tayi baqi mimee bata taba bata masa rai irin yau ba ita kishin nata na hauka zatayi qarfi da yaji so takeyi ta hadashi da mahaifiyarsa qwafa yayi ya sake gyara kwanciya yanaji tana taba qofar ya shareta tunda yasan batada wani amfani da zatayi masa

Ta jima tana buga qofar yaqi budewa dolenta ta hqr ta koma dakinta zuciyarta cike da tsanar Asmah tanajin takaicin hada matsayinsu da yakeyi dole ta shirya yaqar yarinyar ta ruwan sanyi don ta lura fadan dole saida hikima a cikinsa, da safe daga masallaci ya wucce duba jikin Innah dake asibiti bashi yabar asibitin ba sai goma na rana ya wucce gdan Aunty Aseemah suka gaisa yayi mata sannu da gajiyar biki don kusan duk itace qarfin hidimar bikin nasa sai qanwarsa sun jima suna hira tana fada masa irin fadan da Hajja ta kirata tanayi jiya wai taje gdansa ya wulaqantata ya tafi gurin matarsa.
Murmushin takaici yayi yace “to me takeson nayi mata Maryam ta zayyana mata qarya da gsky tazo tana neman nakasa yar mutane” sosai Aunty Aseemah ta jinjina abinda akace mahaifiyar tasu tayi koda yake tasan zata iya yafi hakama don ta lura da gaske takeqin Asmah.

 

Koda ya koma gdan bai nemi kowa cikin matan nasa ba ya gama abinda zaiyi ya tafi asibitinsa da dare ma da ya dawo ya wucce Mimee a parlournta tana chat yanaji tana masa sannu da zuwa baiko saurareta ba yayi hayewarsa sama  Itanma bata bisa ba kasancewar sunyi waya da Hajjah tace mata ta watsar da iskarsa dake sakarya ce hakanan ta hau ta yarda.
Washegari ne da safe ya shiga Part din Asmah ya taddata a kitchen tana hada break dake baya cikin walwala takarda kawai ya aje mata ya fice, gabanta ya fadi sosai ta dauki takardar jikinta na rawa ta bude admision ne Jamb ce ya biya aka zana mata ta zaro ido cike da murna ta rungume takardar tana dariya kashe gas din tayi murna bazata barta ta qarasa girkin ba ta shige daki ta kira aminiyarta ta sanar da ita sosai ta tayata murna tace mata “nima na zana amma banje na duba ba”

 

Sun jima suna waya sannan sukayi sallama ta kashe wayar ta kira Innah itama tayi mata sannu da jiki Inna tace “kiyiwa Aseem gdy yayi dawainiya sosai a asibiti yau zasu sallame mu sunsa mana rana idan hoton da akayimin ya fito zaayimin aikin ido” sosai yau Asmah take cikin farin ciki.
Bayan sun gama wayar kamar zata kirashi tayi masa gdy amma tsoro takeji karya jizgata saqo ta tura masa na gdy ta ajiye  wayar ta sake komawa kitchen ta hada tea tasha ta zauna tana game da wayarta ,
Haka rayuwar taci gaba da tafiya babu wata jituwa tsakanin Asmah da Aseem duk da ta rage yimasa rashin kunya saboda arziqin aure itama Mimee ko a harabar gdan basu cika haduwa ba tsayin watanni biyar

 

Ranar wata laraba ta dawo daga makaranta ta shiga wanka taji hargowar hajiyan Aseem inda sabo har Asmah ta fara sabawa da halinta bata gama wankan ba haka ta katse ta zuro hijjab ta fito ta bude dakin tana tsaye riqe da qugu a parlourn tana ganin Asmah tayi kanta tana cewa.
“Ai dama yan magana sunce halin tsiya gadone na arziqi ma gadone yanzu ke duk abinda yaron nan aseem yakeyi muku kunmai dashi Injin ATM dinku duk wata dawainiya taki data iyayenki ya dauke amma saboda baqin ciki Matarsa abar qaunarsa tayi bari har saida takai ga anyi mata aiki an cirenta cikin daya zama qari amma ki kasa zuwa kiyi mata ko sannu”
Hawaye ne ya zubowa Asmah zuwa lkcn ta fara hada hankalinta tace “haba Hajiya nifa musulma ce ko zaman gaba mukeyi ai bazan kasa yimata sannu ba da nasani wlh bansani ba toma a gurin wa zan sani Hajiya me gidanne kuma ya shafa’a bai sanar dan…..” Dauketa tayi da mari tace “rufemin baki baqar munafuka ni zakiyiwa dadin baki to ni bama wannan ne ya kawoni ba nazo ne nayi miki kashedi kiyi gaggawar sakin mata mahaifa bazamu idan ba hakaba wlh zaayi biyu shegiya baqar mayya aini dama tunda naga yaron nan Aseem ya nacewa aurenki jikina ya bani ba banza ba ashe irinsu Alasan ce an lashe masa kurwa anzo zaa lashe ta matarsa to nidai nafi qarfinki…….”

 

Dukan da kalaman Hajja sukayi mata saida suka sanyata zama babu shiri gabadaya ilahirin jikinta ya dauki rawa tabbas ko iya haka Aseem da danginsa sun cucesu tunda take a duniya bata tabajin baqar kalma irin ta Hajjah ba wai ita da iyayenta ne mayu? Qwafa taji Hajja tayi ta juya tana cewa “idan an isa a shigar damu qara na fada domin na tabbata”
Ficewa tayi daga parlourn Aseem dake tsaye tun shigowarta ya kauce ya bata hanya saboda ya lura neman dukansa ma Hajja takeyi ba Asmah ba shi kansa kalaman Hajja sunwa kansa nauyi balle kuma ita cikin sanyin jiki ya haura saman ya isheta ta dora kanta saman kujera tana wani irin kuka me tsuma zuciya tana ambaton sunan Allah tare da sunan innanta ya jima tsaye kanta cikin kukan yaji tana cewa “Allah na roqeka idan har babu rabuwa tsakanina da wannan azzalumin bawan naka ka qadartamin mutuwa cikin gaggawa ko ruhina zai huta Allah da wanne zanji wa zan fadawa ya bani mafita…..”
Wata iska ya furzar me zafi ya fara janyewa da baya da baya har yakai step din ya sauka ya zauna a qasa.

 

Miqewa tayi tana layi ta fada dakinta ta janyo akwatu cikin akwatunanta yau kam kome Aseem yake bata a duniyar nan zata hqr da zama dashi tagaji da cin mutuncin nan shi yayi mata uwarsa tayi mata dangin matarsa idan tsautsayi ya hadasu suyi mata dole zatabar musu gidan su huta idan suka daina ganinta kowa sai hankalinsa ya kwanta.
Mayafinta ta dauka ta yafa ta janyo akwatunta ta sauko daga saman tana saukowa yana shigowa ba qaramar faduwar gaba yajiba ganinta da akwatun yaja ya tsaya a bakin qofar batako kallesa ba sai hawaye da taketa tsiyayarwa tana isa gabansa yakai hannu ya riqe trolley din ya mayar da qofar ya rufe, suka tsaya kallon kallo zare mukullin yayi yaja trolley din ya shiga parlourn ya zauna a kujera yace “idan kin fita ina zaki?” Shiru tayi masa tanaci gaba da shassheqar kukanta ya taso ya matso bayanta ya rungumota jikinsa ya dora hannunsa saman hips dinta yace “zakije kice musu meyene nasan bai wucci kice zaki gda ba garama ki zauna anan din zaifi miki sauqi domin ko Innah ta goyi bayanki Mal saiya dawo dake kasancewar yana saka ran ta dalilinki hajjin bana dashi zaayi kinsan shi mutum me arziqi yana tutuya da arziqinsa ne wajen shuka duk abinda yakeso zaifi miki sauqin Rayuwa ki tsaya kici Arziqi kibarshi inda yake iyayenki bazasu iya riqek……” Dafe kuncinsa yayi saboda saukar yatsunta da yaji a kuncinsa taja da baya da sauri ta nunasa da yatsa tace “iyakar tsiya kawai kuke iqirarin akwaita ga iyayena tabbas na yarda Mal Hussain daya dauki aurena ya baka saboda kwadayi shi matsiyaci ne domin tsiyar ke bibiyarsa tasa ya fansar da mutuncinsa da nawa so inaso ka tsaya iyashi da yake nema a gurinka kamar abinda na fada maka a farko ne uwata talaka ce amma tanada wadatar zucci domin bata qyamatar duk wani abin halitta Aseem zan iya jurewa komai a rayuwa banda taba martabar mahaifiyata domin na hanga na hango banga ta inda taka tafi tawa quality ba……”

 

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

 

_*Oum Hairan*_

[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

 

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

 

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button