Daurin Boye 17
17
Tashin hankali na gaba dana sake fuskanta shine shirin aurar da ni da ake ga dan ladi,wanda babu wanda ya tambayeni ko ya tsaya jin ra’ayina aka bada ni gareshi,tamkar auren sadaka zance aka shirya yimin,domin babu abinda dan ladin ya kawo gidanmu da sunan kudin zance kayan sa rana da sauransu,hasalima sake tunzurashi ake akan cewa ya taimaka su rabu da qaya,domin wai na tasamma tsufa a gabansu,duk da cewa duka duka a sannan ban wuce shekara goma sha uku cikin ta sha hudu ba,duk da lalacewa irin ta dan ladi wai mahaifiyarsa qyama take ya aureni,tana cewa za’a joganawa danta ni,danta yafi qarfin aurena,amma da yake dai Allah ya hukunta cewa sai na shiga gidansu na dandani tasu kalar azabar haka aka daura aurena da shi,babu wani abu dake nuna cewa bikin yarinya budurwa ake,duk wani gata da akewa budurwa yayin auren fari ni ban sameshi ba ban ganshi ba,a wannan lokaci nayita zuba idanu ko zanga ummi na amma shiru,bama ganinta ba,naso ace ko wani motsi nata da zai nuna tana sane da ni ko tana sane da aure na nasamu daga gareta amma maqatau,hakanan dangin mamata suka hado kayan da zasu iya dai dai qarfinsu suka kawo amma inna yelwa ta aje gefe tace sam ita da taba kayan zuri’ar gidansu ummina,ta hadamin buta tukunya da kwanukan cin abinci,sai katifa da labulaye da fulalluka iya abinda aka jera min kenan aka daukeni ziqau babu gyara aka kaini,hana rantsuwa dai ranar an sakani nayi wanka da kyau.
Tunda aka kaini dakina qwaya daya wanda aka jawa katangar kara da makewayi kusa da shi nake zaune ina raba idanu,santin dakin nake a raina saboda sau dubu yafi bolar da nake kwana kyawun gani,tun ina jiyo hayaniyar jama’a har gidan ya dauki shuru,ina nan zaune bansan sanda tsohuwar gajiya ta sanyani na sulale nabi lafiyar ledar da aka malalawa tsakar dakin ba.
Faduwar abu da naji yif a kaina shi ya farkar da ni a zabure nayi yunqurin miqewa,saidai nauyin da yake kaina ya fi qarfina,sai dana lura da kyau naga ashe dan ladi ne,wanda maganganun da yake furtawa kawai sun isa su gaya maka a make yake qwarai…”qasa aysha tayi da kanta,cikin jin nauyi da kunya tace
“Nayi alqawarin bazan boye maka komai ba…..idan nace komai ina nufin harda rayuwar aure na da danladi….a wannan daren dan ladi ya nemi karbar haqqinsa ta qarfi,saidai sam naqi yarda,haka muka dinga artabu da shi cikin dakin,wanda daga qarshe da yaga ina neman gajiyar da shi ya kamani ya yimin duka dan gaske wanda sai da naji a jikina,duk da na saba da duka kusan ni jakarsa ce amma wannan ya shiga jikina matuqa,saboda an yishi ne cikin fitar hayyaci,kafin kace meye fuskata ta kumbure haka jiki na,yadda naga rana haka naga dare,amma duk da hakan ban fasa tashi sallar asuba ba yadda na saba,bayan na gama na samu na rabe gefe guda ina maida numfashin wahala,idanu na kan dan ladi dake baje saman katifata,ni kuwa gani kwance kan dandanyar ledar daki.
Bashi ya farka ba sai tara na safe,zuwa lokacin har tsakar gidan gidan ya cika da hayaniya kala kala ta yara da manya,da alama kowa ya shiga sabgarsa,tashi yayi yana hardewa wanda hakan ke nuna bai gama wartsakewa ba ya dubeni ya watsan harara gami da jan qwafa,da alama yana sane da abinda ya faru jiya kuma yana qufule da ni,ficewarsa yayi,tunda ya fice din kuwa ba wanda ya nemi ni hatta da shi kanshi,sai da sha biyun rana ta kusa naga yunwa na shirin hallakani na miqe na debi ruwa na shiga makewayi nayi wanka,na cika kofi da ruwa na sha,na danji dama dama a jikina sannan na saka hijabina na fito cikin gidan,gida ne kamar namu na mutane da yawa,matan yayye da matan qanne da uwar miji,haka aka dinga bina da kallo wanda nasan baya rasa nasaba da sanin wace ni da kuma kokawarmu ta daren jiya da.nasan mafi yawa sunyi zatan wani abu ne ya faru,nidai na gaidasu na wuce wajen mamar dan ladi da suke kira da fatsi,tun daga yanayin amsa gaisuwarta nasan cewa akwai wata a qasa,ilai kuwa hakanne,domin kuwa na sake fadowa jahannama ta biyu ce,duk wata bauta ta gidan kusan a kaina take,zagi hantara da gori kuwa babu kalar wanda ba’a yimin,babu wanda ban haddace ba cikin qwaqwalwata,gefe daya kuma idan dare yayi mu hadu da dan ladi wanda kullum sai yayi yunqurin karbar haqqinsa ni kuwa naqi bada hadin kai,saboda bala’in qyanqyaminsa nake ga tsoro dake tattare da ni,uwa uba qiyayyar da nake masa,idan ya gama yunqurinsa haqarsa bai cimma ruwa ba sai ya kamani yamin duka,wansa hakan bazai hana gobe da sassafe na tashi aikin gida ba koda wanne irin ciwo naji wannan ba ruwan mama fatsi bane,sau tari takanmin habaici da gugar zanar ita bata ga me nakeyi a gidan ba bata ga amfani na ba,ashe rashin tarbiyyar dan ladi ta kai ya gaya mata cewa har yau bai karbi haqqinsa a wajena ba,randa na gane hakan takaici kunya da baqinciki sun sakani kuka mai yawan gaske.
A haka naci gaba da zama cikin wannan uquba,ko qofar gida ban taba leqawa ba bare nayi tunanin zuwa gida,duk da suma gidan ba ruwansu da ni,ba wanda ya taba takowa inda nake idan ka debe yan qananun yaran gidan da basu san me ake ba,idan yawonsu ya debosu zasu shigo gidan,a nan zanta jin dadi in riqesu ina aiki muna hira ina tambayarsu mutanen gidan suna bani labarin abubuwan da suka faru da bana nan,koyaya dan uwa yake yana da dadi,hakan na yimin dadi kuma yana deban kewa.
Ranar data zamemin ranar yayewar wani bangare na hijabin rayuwata shine ranar da dan ladi ya yimin wani irin duka wanda da qyar na qwaci numfashina,naji ciwo matuqa na sha wahala,hakan ya sanya da asuba na gudu zuwa gudanmu karon farko,abinda ban taba yi ba,kusan da qyar na kai kaina gida ina nishi ina numfarfashi,sanda na shiga ana sallar asuba,dakina na shiga nada na lafe a can,har baccin wahala ya daukeni ba tare da na sani ba,salatin da naji a kaina shi ya farkar da ni na bude idanuna,mutanen gidanmu na gani a kaina inna yelwa na akan gaba,ita ta saka hannu ta finciko ni sai gani a filin tsakar gidan,idanuna basu sauka akan kowa ba sai kan dan ladi da mama fatsi,yana wani cika yana batsewa,ashe abinda ban sani ba shine zuwa sukai nemana,wai na yiwa dan ladi sata na gudu,ba wanda yayi duba da ciwukan jikina sanoda tsabar sonkai kowa ya hau tofin ala tsine
“Gata nan munafukar Allah,inda zaka san cewa babu gaskiya ba wanda yasan da shigowarta cikin gidan….kayi haquri don Allah don annabi dan ladi ka dauketa ku koma” inji inna yelwa kenan
“A’ah…ku riqe yarku,don ni banga abinda aurenta ya qarawa dana ba sai jaraba da masifa” cewar mama fatsi tana tafa hannu da yada baki gefe,nan suka hau roqonsu har suka amince zan koma,ni kuwa a sannan na tubure kan babu abinda zai sanyani komawa,abinda ban taba aikata makamancin irinsa ba tsahon zamana da su su duka
“Dauketa dan ladi koda tsiya,uwar me zaki tsinana mana,dauketa ku tafi” inna yelwa ta fada cikin nuna qyama tamkar ba jininta ba,haka dan ladi ya dinga figata cikin bainar jama’a har zuwa qofar gida,inda ya cilloni ya biyo bayana da niyyar sungumata mu tafi.
Bansan ya akai na fada jikinsa ba,bansan ya akai na rarumeshi ba da hancina dake digar jini saboda jana da dan ladi ya dinga yi yana wujijjigani,dattijo ne mai kimanin shekara hamsin da biyar,tsam ya tsaya yana duban dan ladi dake takowa inda muke cikin isa da qafafa tamkar shi ya haifeni,dakatar da shi daddy yayi da hanashi tabani yana son jin ba’asi,matata ce daya fada ya sanya daddy bashi ni,har ya juya zai tafi sai yaji zuciyarsa bata aminta ba,hakan ya sanya ya dawo ya nemi jin ba’asi,yanayin shigar da suka gani tattare da shi ya sanya jama’a yi masa bayani na gaskiya game da rayuwata….magana ta gaskiya….tsaiwar da daddy yayi yasa alqali ya tilastawa dan ladi ya sakeni kawai ko iya ita kadai daddy ya yimin bani da abin ce masa a rayuwa,karamcinsa mai tarin yawa ne,alkhairinsa har yau bai daina bibiyata ba,ya karbi takardata ya kuma zauna da yan uwan mahaifina yace zai tafi dani,da sunso su turje,amma da yabi kowanne da hasafi cewa sukayi sai mun dawo,inna yelwa ce kawai taso taqi,yaranta suka tanqwarata ta amince
Daddy shi ya tsayan tsayin daka daya fuskanci ina son karatu,ya hadani da malamin dakewa asma’u lesson nima yake min,na zana common entrance na samu shaidar kammala primary,naci gaba da lesson na zana placement sannan aka kaini makarantar da asma’u ke zuwa,ya hadamu aji daya na fara daga ss one,har na kammala na samu shaidar kammala secondry,takarduna sunyi kyau fiye da zaton daddy,direct na samu wucewa B.U.K wadda ban jima da kammalata ba.
Zuwa na gidan daddy na fuskanci tsangwama qarara da qyama daga wajen asma’u da mummy,saidai ita na mommy har yau bai bayyana ba,bana zarginsu bana kuma jin haushinsu…saboda a wajensu na samu rayuwa irin wadda dangina suka kasa bani….na samu ‘yancin da a baya ban samu kwatankwacinsa ba,na hutu na gangar jiki koda ruhina bai samu wannan hutun da nake kwadayi ba….”idanunta suka cika fal da qwalla wadda bata iya adanata ba sai data gangaro
“Har kwanan gobe ina fatan na samu hutu na ruhi,ina son na samu salama a ruhina….amma ba zata taba samuwa ba har sai ranar dana samu soyayyar mahaifiya…har sai ranar dana san dadin dumin mahaifiya wanda tunda na tashi ban sanshi ba….tunda na tashi bansan dadin soyayyar uwa ba,saidai na hangota daga nesa,kona ganta daga wajen wasu uwayen zuwa yaransu” kanta ta kwantar saman teburin muryarta na rawa,hawayenta na qaruwa zuciyarta naci gaba da karyewa
“Wannan ita ce aisha….itace ainihin aysha,aishan da kakesom cusa taka rayuwar cikin tata qazantacciyar rayuwar,ka taba cin karo da mutum mai tarihin baqar rayuwa irin tawa?….ka taba ji?” Ta qarashe maganar tana sakin kuka mai cin rai,duk da yadda taso danne kukan.
A hankali tamkar mai sanda ya miqe daga kan kujerar kana ya zare jikinsa ya soma takawa a hankali yana barin lambun,taji a jikinta tafiya yake kuma bata da sha’awar daga kai ta kalleshi,me ya rage dama me yayi saura?,babu mutum mai hankali da zaiji gundarin rayuwarta yayi sha’awar zama da ita,shin idan an zauna da itan ma me za’a qaru da shi,me ta mallaka wanne abun sha’awa ne ko jan hankali cikin rayuwarta,har ta daina jin takunsa bata daga kai ta dubi gurbin da ya tashi ko yabi ya wuce ba.
Batasan yawan lokacin data dauka a wajen ba,har sai data ji sautin dariya bisa kanta
“Ya arce ne shima yaron ogan yaga bazai iya ba?” Ta tambaya cikin izgilanci,bata motsa ba bare ya nuna mata taji don ba itace a gabanta ba,har ta gama babatunta tayi gaba nan ta barta.
Bai nemi komai ba ha dinga takawa a hankali hannayensa zube cikin aljihunsa,duk taku daya yana tariyar labarin da ya gama saurara ne a yanzu,labarin da yake jinsa tamkar hikaya,haka ya dinga takawa har ya isa inda ya bar mutanensa,cikin hanzari suka nazir ya iso cikin girmamawa ya bude masa murfin motar ya shiga sannan ya rufe,PA dinsa nata masa magana ta window din motar bai amsa ba sai hannu da ya daga masa,hakan ya sanyashi komawa cikin daya daga cikin motocin yabi bayan sauran motocin.
“Gida zan koma” ya furta a hankali ganin sun nufi hanyar kamfani,wanda hakan ya tsara da farko,saidai baijin a yanzu zai iya,yana buqatar kebewa baya son hayaniya,hakanan drivern ya sauya akalar motar zuwa gida.
Ta qofar baya ya shiga gidan,don bai shirya haduwa da anni yanzu ba,ya tabbata da zarar ta ganshi zata karanci sauyin yanayi tattare da shi,yanzun itama zata shiga damuwa ta kuma nemi jin ba’asi,sam baisan da harshen da zai fahimtar da ita ba.
Kacibus sukayi da zeenart yaja baya da sauri suna duban juna,ita dressing din jikinsa take kallo cikin mamakin kayan jikinsa,yayin da shi kuma rashin jin dadin ganinya yayi,a irin wannan shigar idan yayi baiso kowa ya ganshi bare ya tambayeshi ba’asi,yanzun ma bai kaucewa tambayar zeenart din ba
“Bro….lafiyanka kuwa?” Dan hade rai yayi kadan ya qarawa fuskarsa kwarjini saboda baison tambayar tayi tsaho
“Me kika ga?”
“Ka duba kayan nan da kyau kuwa kafin ka saka?” Ta fada tana dudduba jikinsa da idanunta kamar mai neman wani abu,sake duban kanshi yayi kamar baisan kayan da ya saka din ba sai data fada
“Meye a ciki?…..ammm..idan kin shiga ciki karki cewa anni na dawo….zan shigo nan da anjima akwai abinda na dawo yi” ya qarashe fada yana gewayeta gami da wucewa yayin data bishi da kallo har ya bacewa ganinta bai waiwayo ba,tunda taga haka tasan yana nufin abinda ya fada din,hakan ya sanya tasa kai ta wuce itama inda ta nufa.
Kayan jikinsa ya fara cirewa sannan ya wuce direct zuwa toilet,yana tara ruwa yana dafe da bathtube din,labarinta yake jujjuyawa cikin kwanyarsa daya bayan daya,a haka ruwan ya cika ya shige ciki,kusan mintina talatin ya dauka kafin ya baro bayin ya dawo cikin dakinsa,shiryawa yayi cikin riga da trouser,hakanan yaji kasalar data sanyashi tilas ya koma saman gadon ya kwanta dai dai,tamkar yanzu take bashi labarin haka ya dinga ji yana dawo masa kansa
“Haka rayuwar take,kowa kansa ya sani,kowa son kai yayi masa yawa,wacce iriyar uwa ce wannan?,wacce iriyar uwa take da ita?,wanne laifi tayi mata mai girma data wofantar da rayuwar diyarta?,wanne irin dangi ne haka,me yasa ahali suka zama haka?,wanne irin dangi Allah ke jarabtar mu dasu a yanzu,wadanda basu san damuwar kowa ba sai tasu,mirginawa ya dinga yi daga wannan gefe na gadon zuwa wani gefen,cak ya miqe daga kwanciyar da yayi tamkar wanda aka tsikara,agogo ya duba,qarfe biyar da mintina ashirin da takwas na yammaci,dirowa yayi daga saman gadon ya zira takalmansa ya fito daga sashen nasa.
A hankali yake takawa har zuwa sashen anni,a parlour ya sameta zaune ita da zeenart,amsa sallamarsa anni tayi tana dubansa,tana son tambaya amma tasan babban dalili ne zai dawo dashi gida ba lokacin dawowarsa ba,rusunawa yayi ya gaidata sannan ya miqe kai tsaye ya wuce samanta ba tare daya zauna parlourn ba,hakan shi ya nuna mata yana son magana da ita mai muhimmanci,saidai bazai iya tada ita ba tunda ya sameta a zaune ita da zeenart
“kaiwa yayanku abinci sama”anni ta fada tana duban zeenart,tsam ta miqe ta shiga kitchen,tani ta yiwa umarnin ta hada komai,tana tsaye ta gama hadawar ta dauka tayi saman da su.
A miqe ta sameshi kan doguwar cusion dake falon yana latsa waya,a gabansa ta aje fulasan cikin kissa tace
“ya…ga abincinka na zuba maka?”
“Bana jin ci yanzu…barshi zuwa anjima” ya amsa mata ba tare daya dubeta ba,labarin aysha na yawo ya dawo masa kaf da tabon dake cikin tashi rayuwar tamkar yanzu komai ke gudana,wannan ya sanya ko kallon zeenart din baya son yi
“Ka daure yaya kaci”
“Later” ya sake fadi a taqaice,taga alamar ‘yan miskilancin ne suka motsa,indai kuma yana cikin wannan mode din baya son dogon zance,hakan ya sanyata ta miqe ta fice daga falon.
Tana qoqarin sauka anni na hawa,ta wuce ita kuma ta shige ciki,yunqurin tashi yayi ya zauna sanda yaji sallamarta,idanunta a kansa saita kadar ta kalli kayan abincin da bai taba ba,bata ce masa komai ba ta isa gaban abincin da kanta ta soma kiciniyar zuba masa,da hanzarinsa ya taso ya karbeta yana murmushi,itama murmushin tayi sannan ta sakar masa yaci gaba da zubawa,ta koma da baya ta samu waje ta zauna tana cewa
“Ah to…naga alamun ‘yan sarautar ne yau a kusa” murmushi kawai yayi bayan ya gama zuba dai dai yadda zai iya ci ya rufe komai ya koma gabanta ya zauna ya soma ci
“Uhmmm….ina jinka ya akayi?” Ta tambayeshi kai tsaye kaman daman ya gaya mata zasuyi wata magana ne,murmushi ya saki yana jin dadi har cikin ransa,mahaifiyarsa ta karanceshi fiye da kowa a duniya,aysha ce ta fado masa a hankali fara’ar fuskarsa ta dan ragu,ya motsa bakinsa yana duban annin yace.
*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *DB*