Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 18

Sponsored Links

18

 

“Bansan ta ina zan fara ba anni…matar aure aka bani,bansan me zance ba” abinda ya iya fara fada mata kenan saboda shi kansa baisan ta ina zai fara ba,idanunta ta saka tana kallonshi saboda yadda taji maganar tashi banbarakwaii,tana tunanin tayaya haka ta faru,saidai koma meye ta sani cewa zaiyi mata bayani,hakanan bazai taba yin wani abu daba dai dai ba kozai haifar da dana sani,zamanta ta gyara tana qoqarin fahimtar dan nata kamar yadda al’adarta take,bata yankewa koma waye hukunci kai tsaye,murmushi ne bisa fuskarta
“Matar aure a ina?,kaji gorin haidar kenan?” Murmushi shima ya danyi yana ture kwanon abincin gefe duk da ba wani mai yawa yaci ba
“Zaki iya tuna alhajin nan da na taba tsintar wallet dinsa,wanda ya taba biya miki kudin aikin da aka yi miki shekara goma da suka wuce?” Kai take kadawa
“Qwarai kuwa….ya za’ayi na manta muhammadu?irin wadan nan mutanen dan halak bai manta halaccinsu a gareshi”
“A gidanshi take…shine mariqinta”
“Ikon Allah” ta ambata cikin mamaki,a hankali ya zauna ya warware mata komai,babu abinda ya boye mata,tun daga yadda ya dinga neman aure ta sigar DAURIN BOYE,har zuwa neman asma’u yadda mu’amalarsu ta kasance sa kuma yadda ta qulla lamarin shi da aysha,sannan yazo ya bata labarin rayuwar ayshan kamar yadda itama ta bashi.

Related Articles

Ta jima anni tana jinjina kai,falon ya jima shuru shi da ita babu wanda yace wani abu,labarin ratsata yake tun daga kanta zuwa tafin qafarta,lallai duniya,inda ranka kasha kallo,idan kana da rai babu abinda ba zaka gani ba,tsahon wasu mintuna ta dauka kafin ta dubeshi
“Koda baka karbi aurenta ba,ko babu niyyar haka a zuciyarka khalipha ina mai baka umarnin ka aureta khalipha….,Allah ne kadai yasan manufarsa daya kawo silar haduwarmu da ita ta wannan sigar,me yiwuwa Allah ya turomu ne muma cikin rayuwarta,aurenta shine hanaya daya tak da zata zama bamu damar sauya mata rayuwa” Ta fada tana jin lafuzan nata har cikin zuciyarta,wani irin tausayi da qauna ta ayshan na na ratsata duk da bata ganta ba,duk mutumin daya fuskanci rayuwa irin wannan abun a tausaya masa ne,a dubeshi a kuma juyawa a dubeshi,sun taba dandanawa da kalar tasu daban,ba zasu taba mantawa ba.

Kanshi yake jinjinawa,shi kansa yana jin cikin zuciyarsa tamkar haduwarsu daga Allah ce,tamkar Allah ya tsara komai ne don ya sama ma rayuwarta farincikin da bata taba dandanarsa ba tun tasowarta
“Allah ya bani ikon sauke dukkan haqqin mai haqqi dake kaina….” Ya ambata,saidai wani bari na zuciyarsa yana fasalta yadda aure zaiyuwu babu soyayya,bayaso ta amincewa zama da shi saboda ta samu matserar rayuwarta bawai don ta nutsu da hakan har zuciyarta ba.

Kafin kowa yace wani abu a cikinsu zeenart ta shigo falon fuskarta qunshe da fara’a
“Anni…alhaji yazo” tana nufin mahaifinta kenan
“Toooh….maraba” ta ambata tana miqewa daga zaman da take,shima khaliphan miqewa yayi ya sakata a gaba zeenart na bayanshi suka sauko zuwa qasan.

“Ku haka kuke qulewa kubar gida ba kowa…..ba don zeenatun na kusa ba kenan saidai ka gaji ka koma….yo ai wannan gwara da take zaune a gidan ma” ya fada yana saba babbar rigarsa,idonsa na kan khaliph wanda fuskarsa take ba yabo ba fallasa,idanunshi na kam anni bai dauke ba sai da yaga ta zauna sannan ya dauke nashi idanun ya samu hannun kujerar da take kai ya zauna yana sauraren gaisawarsa da anni
“Barka da yamma” khalipha ya fada,waiwayowa alhajin yayi yana dubansa
“Kai wato ba’a isa a ganka gidan kowa ba saidai a naku gidan ko?” Murmushi ne ya subuce masa,sai ya kada kansa kawai yana duban alhajin,idan maye yaci ya manta uwar da ai ba zata manta ba,shi alhajin ya manta furucinsa na qarshe a garesu kenan
“To ni gani nazo da kaina da nacewa zeenatu tace ina nemanka kayi funfurus kaqi zuwa” alhajin ya sake fada yana tsatstsareshi da ido
“Yanayin aiki ne,ba kowanne waje yake barina naje ba….gani…Allah yasa ba laifi nayi ba” ya qarashe maganar ta sigar gatse,gyara zamanshi yayi bayan ya gyara zaman babbar rigarsa
“Wato muhammadu so kake kafi qarfinmu ko?,ka tasamma qin aure qiri qiri kasa qafa kayi fatali da sunnar ma’aiki,kana girma shekarunka na ja qannanka na tasowa,ga ‘yar uwarka nan jiddin tana gidan nan tana qaunarka amma ko wannan baisa ka duba ba?….yanzu haka ka zaba kenan?” Murmushi ya sake yi,abubuwa masu yawa na dawo masa cikin kwanyar kansa,yana sake godiya ga Allah kan komai da yayi masa a rayuwa,baiwa masu tarin yawa da shi kansa baisan adadinsu ba,miqewa yayi tsaye hannayensa zube cikin aljihunsa,idonsa ya sauka kan zeenart da kanta ke sunkuye tana wasa da yatsunta ita ala dole kunya sai faman zuba murmushi take
“Kayi haquri alhaji ba haka na zaba ba…..idan Allah ya kaimu ranar asabar kwana biyu masu zuwa za’a kaimin kudin aure harma da sadaki….shikenan?” Baki ya soma budewa,yana jin zallar farinciki,ga tunaninsa komai ya fada ne tsakaninsa da zeenatun,amma maganar da khaliphan ya dora da ita a sanda yake yunqurin barin falon ita ta kadar da duk nutsuwarsa ta kuma sanya gumi ya soma karyo masa
“Duk da ban sanar da mahaifin yarinyar ba,amma zanyi qoqarin shaida masa yau zuwa gobe in sha Allahu” daga haka ya fice ya bar alhajin cikin rudani
[1/6, 11:50 AM] Om Muhammadiyya: Shiru ne ya ratsa falon kafin daga bisani kukan zeenart ya karade falon,kuka take sosai mai sauti tana raba ido tsakanin mahaifinta da anni,hakan ya sake tunzura alhajin wanda yaketa qoqarin share gumin goshinsa,miqewa tsaye yayi cikin banbami yake cewa zeenart
“Ke,tashi mu tafi….tashi nace maza….mu za’a yiwa wulqanci aci mana mutunci?,mu za’a nunawa qaryar arziqi,dadin abin ai tun kafin ayi daran akai kwandi” a tausashe anni ke dubansa
“Haba bashir….abun baikai haka ba don Allah…ka zauna”
“In zauna inyi me hajiya A’i?….me zan zauna inji?,ina cewa a gabanki ya fadi komai baki dakatar da shi ba…ina tsammatarma hadin baki ne kukayi saboda kada a auri yaranmu…to babu komai….shi yasa zumunci ya shiga halin ni ‘yasu,dole zumunci ya lalace,tashi ki wuce mu tafi” kada kai anni take can qasan zuciyarta mamaki na kaikawo na maganganun da alhajin keyi,duk da haka ta danne
“Kayi haquri dai duk da haka,ka barmin zeenatun”
“Mai zata zauna tayi muku…ai magana ta riga ta qare”ba yadda annin bata yi ba amma ya qeqashe qasa yaqi,tana zaune tana kallonsu ya tasata ta hada kayanta suka zo suka fice,ajiyar zuciya kawai ta saki,me hali baya fasa halinsa,lallai khalipha shi yasa meya gani…shi yasan wanne tunani yayi daya sanyashi qin duk wata yarinya dake cikin ahalin nasu.

Khalipha ne ya sake dawowa falon,harararshi annin tayi sai ya saki murmushi yana takowa inda annin ke zaune,duk sanda yaga ta harareshin yasan ya aikata mata laifi kenan
“Kaji dadi…..ka hadani da dan uwan mahaifinka” gabanta ya qaraso dariya tana kubce masa,kan gwiwoyinsa ya durqusa ya kama hannayenta
“Ki cire dukkan wata damuwa anni dangane da mutanen nan,kin dade da sanin cewa babu wani abu da zakiyi ki fita a wajensu,Allah shine shaidarki,mutane masu adalci suma sun shaida hakan….banda ke anni da wata ce ko kallo basu isheta ba bare su jibanceta ko su jibanci nata yaran,anni…..bazan iya auren kowacce yarinya data fito daga zuri’armu ba ko daga sama ta sauko kuwa….kiyi haquri karki tambayeni dalili saboda suk duniya kinfi kowa sanin dalilin….ki manta da su da lamuransu….kici gaba da duk abinda kikega zaki iya kuma shine dai dai hat a gaban mahaliccinmu” shiru tayi tana tunani,ba shakka duk maganar khaliphan haka take tana bisa hanya,ita kanta tafi kowa sanin wuyar data sha da shi kafin yaci gaba da mu’amala da dangin nashi,amma a yanzun saika rantse babu komai tsakaninsu basu taba aikata musu komai ba,don indai anni ta bada umarnin yayi abu zai cikashi duk wuyarshi
“Yanzu ina kayan abincin da za’a kaima baffan ka”
“Wannan maganar an gamata….haidar kawai nake jira yazo ya kai” ya qarasa fadi yana duban idanunta
“Yanzu jibin za’a je gidansu yarinyar?”
“Eh anni…in sha Allah…inason mutanen nan ne su qyaleni suda yaransu…koda kika ga zeenat ta tafi ina mai tabbatar miki zata dawo…ko bata dawo ba wata na nan zuwa”kai take kadawa sannan ta bude baki
“shikenan,Allah ya sanya alkhairi yasa a yi a sa’a ya kade dukkan fitina…..saika gayawa dukan wanda ya dace kada wani yaji daga baya yayi qorafin bai sani ba”
“Ko sunzo ma mota daya zan bada,sauran suje a motar haya…..har yau bani da komai sai rufin asirin Allah da shi zanci gaba da neman aurenta idan har zata iya zama da ni a haka” dariya ya bawa anni…khaliphan ya fita daban da matasan zamani…matasan dake neman kayan aro da zasu sanya ariqa musu kallon masu arziqi su yaudaro yarinya su aureta,yau shi gashi da dukkan wani abu da ake da buqata amma boyesu yake yana maida kansa ruwa da zubin maqasqanciyar rayuwa,bai bar falon ba saida haidar din yazo ya miqa masa saqonnin duk wadanda za’a kaiwa abincin sannan ya fice zuwa gidan babban wan mahaifinsa suyi maganar zuwa gidansu ayshatun.

????????????????

A daren washegari daddy ya kira mummy sa’adah ya sanar mata zuwan masu neman auren ayshan,a zahiri ta nuna zumudi da farinciki,amma a badini baki kawai ta tabe,madadin ta gaya mata tayi musu tanadin abin tabawa kamar yadda aka yiwa maneman auren asma’u sai taja bakinta ta tsuke,taqi ma shaida mata bare tayi qoqarin yin wani abu,sai asma’u data gayawa,dariya asma’un ta dinga yi tana cewa
“To dama mommy me za’a bawa wadan nan?,…nasan yadda dansu yake suma haka suke..qilan ma gwara shi sau dubu a kansu….,mummy ki shirya kina da gagarumin biki….don wallahi tun yanzu ma kisan ya zakiyi da daddy Allah karma ya wani ce zai hada mana biki,don bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane ehe” fuskarta qunshe da murmushi saidai tana harararta,don itama harga Allah tafiso a barta a bikin auta su raqashe,ba zata yarda ya hade musu biki da ayshan ba ya jawo musu zubewar mutunci
“Saiki gayawa daddyn naku ai” buga qafa tayi tana duban mummyn
“Allah mummy yace zai hada mana biki fasa auren zanyi,sawa sweet hamid zanyi yacewa daddyn ya qara wata daya ko biyu ai dole ya haqura”
“Kwantar da hankalinki,babu mai hada mana biki ma” tsalle tayi ta ruqunqume mummyn
“Sai mummy na….” Dariya suka sanya baki dayansu.

***** ***** ***** **** **

Sha daya na safe tana kitchen tana hada breakfast din asma’u wadda takeson fita da safen,sam bata masan da cewar yau za’a zo wani neman aurenta ba,ta riga ta bayar da cewa khaliphan yayi tafiyarsa ne abinsa,saboda tayi imanin babu yadda za’ayi mutum yaga mace kamar asma’u,wayayya mai kyau nasaba da dukiya sannan ya zabeta,ita hakanma yafi mata,zuciyarta tafi nutsuwa sosai,don batasan ya lamarin zai kasance ba idan har ya karbi auren nata ba,ta yaya zasu zauna bayan babu wata kalma data jibanci soyayya wadda ta taba shiga tsakaninsu,basu taba za su yi magana mai taken ta fahimtar juna ce a tsakaninsu ba,basu suka zabi juna ba,ba wanda yasan kowa sani tun daga na halayyar zuwa na ra’ayi,wannan gambizar dame tayi kama?,tafiyarsa tana jin maslaha ce kawai a rayuwarsu su duka,gabaki daya a duniyarta a yanzu ta zurfafa karatunta shine kawai burinta,ko sau daya bata taba darsawa kanta tunanin yin aure,wannan ta baiwa kanta cewa sai cikakkun mata masu abinda zasuyu tutiya da shi,itakam me take da shi?,me ta mallaka,taji ma da tarin tulin matsalolin dake neman shaqe rayuwarta su kaita kushewarta wanda har yau bata samu magani ba.

Motsin data ji shi ya sanyata juyowa,mummy ce ta shigo,ta rusuna cikin girmamawa ta gaidata,ta amsa kana ta juya ta fice ba tare data dauki komai ba,daddy ke maganar baqi sun iso a kawo musu abin tabawa,ta shigo ta kuna rasa me zatayi,ayshan zata roqa ta rufa mata asiri ko ko yaya?,itakam bata san ma me ake ba,daga bisani dai taga daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta shirya lemuka da ruwa kan faranti ta fita da su,itama tana gama hada break din ta diba zuwa dining ta soma shiryawa a can.

Tana tsaka da gyara wajen taji muryar daddy yana shigowa falon,da alama waya yake,takun takalman asma’u suka karade falon,kai tsaye ta nufi dining din ta ja kujera ta zauna tana duban ayshan fuskarta qunshe da fara’ar da batasan ya meye ba,kallo daya ayshan ta yiwa fuskarta ta dauke kai,hakanan taji fara’ar bata gamsheta ba
“Me kika dafa?” Ta fada tana latsa wayarta,bata ce komao ba ta bubbude kwanukan,sai data daga kai ta dubesu sannan tace
“Zuba maza da sauri fita zanyi” faranti ta jawo ta soma zuba mata dai dai sanda daddy ya gama wayar suka soma magana da mummy
“Mun gama sun tafi”
“Nawa suka kawo?”
“Dubu talatin ne” daddy ya fada yana ciro kudin da suka kawo din daga aljihunsa,wani sanyi ya ratsa mummy a badini tana jin cewa lallai Allah ya yiwa diyarta gyadar dogo,yayin da a zahiri kuwa ta cunkushe fuska tana cewa
“Haba daddy…yanzu kai ya za’ayi ka bada auren yarinya akan dubu talatin kaman wata atamfa….haba sai kasa a zagemu ace muna sane”
“Babu komai sa’adatu…albarka auren ake nema ba tarin dukiya ko qyale qyale ba,yaron kuma yana da dukkan nagartar da za’a iya bashi auren kowacce diya wannan kawai ya isa”
“Amma aysha indo a dubu talatin daddy” saida mummy tayi furucin qarshe sannan ta ankara,mummunar faduwar gabanta tazo dai da sanda asma’u ta bushe da dariya har tana neman qwarewa da farfesun da take diba da cokali tana sha
“Wai…..dubu talatin….kudin takalmi na” asma’un ta fada tana dariya qasa qasa don kada daddyn ya jiyota,sosai jikin aysha ke rawa da jin abinda bata tsammata ba haka nan bata shirya masa ba,aure?…aure a irin wannan lokacin?…..wanne irin mutum ne shi da ya amince zai aureta a haka?.

Abincin da bata gama zubawa ba kenan ta saki sarving spoon din ta wuce dakinta.

Kuka ta zauna sosai tayi a bakin gado,tsoro da firgici yana kamata,tunanin makomarta take,ya kuma rayuwarta zata sake juya mata,auren da babu soyayya a karo na biyu,auren da babu sanayya sabo ko fahimtar juna,ya sunan zamansu?,ya zata kasance shine kawai abinda ta dinga juyawa cikin ranta,wayarta ta jawo,a yau tana jin buqatar abokin shawara fiye da kullum,yau tana fatan idan ta kira aliya ta sameta a waya,ba kamar ragowar kwanakin ba da bata samunta,saidai yau dinma data kira haka aka sake gaya mata layin a kashe yake,jikinta a sanyaye ta aje wayar ta qura mata ido,bakinta cike fal da addu’ar neman yayewar qunci da haskawar lamuranta baki daya.

??????????????

Tun safiyar ranar bata sake takowa falo ba bare ta leqo wajen gidan,tana nade kan gado,sallah kawai ke sauko da ita data gama zata koma ta sake kwanciya.

Qarar bude qofar dakinta ya sanya ta daga kanta tana duban bakin qofar,inna laraba ce,da sauri ta miqe ta zauna saman gadon fuskarta qunshe da murmushi tare da nuna zumudi take saukowa daga kan gadon
“Inna….yaushe kika dawo?”
“Ban wuce minti talatin ba cikin gidan nan…komawa kuma zan sakeyi ma” ta fada tana murmushi,tunda babbar ‘yar mummy cuta aka kai inna laraba take can gidan,ba qaramin kewarta aysha keyi ba,don kusan da ita kadai take zama ta taba hira cikin gidan,saboda yadda inna ke janta a jiki tare da nuna mata qauna,haka nan jininsu ya hadu sosai da innar,gaisheta ta fara yi innar ta amsa tana cewa
“Baqo gareki fa ‘yata….inajin surukin namu ne yazo….yau bakina har kunne nazo na tadda abun alkhairi…ubangiji yasa abokin arziqin ki ne”kanta a sunkuye jikinta a matuqar sanyaye ta amsa
” ki maza ki fita…idan ban koma ba kafin ki gama ma gaisa sosai”
“Toh inna” kawai ta fada innar ta fice ta barta tsaye gaban kayan sawarta tana neman hijabi,bawai don bata ga hijabin bane,hakanan jikinta yayi wata iriyar mutuwar ga fargabar data cika mata zuciya.

Har zata fice a falon sai ta koma kitchen ta qofar baya,ta hado masa lemo da ruwa ta dora cup ta wuce da shi.

Daga nesa ta hangoshi,ya baiwa qofar shigowa baya,qafarsa daya na saman kujera daya tana qasa,bata iya hango abinda yake amma dan duqe yake gwaiwar hannunsa kan gwiwar qafarshi,takowa take idanunta a kanshi,gabanta na faduwa duk sanda nisan dake tsakaninsu ya ragu
“Assalamu alaikum” tayi sallama tana tsaye daga bayanshi kanta na kallon qasa,a nutse ya sauke qafafunshi sannan ya waiwayo inda take tsaye,dubanta yayi sau daya sannan ya amsa sallamar yana nemawa kanshi wajen zama,bata motsa ba har sai data tabbatar ya zauna sannan ta dora farantin,tq bude robobin duka ta zuba masa ruwa da lemon sannan taja kujerarta can baya ta zauna
“Ina yini” ta furta a hankali cikin sanyayyar muryarta da sai ka zaci da gayya take yinta,idanunsa ya dauke daga kan kofunan ya maidasu saman fuskarta da take kallon qasan wajen ya amsa mata da lafiya lau,daga haka shuru ne ya biyo baya,ya zuba mata idanunsa yana karantarta,yayin da tausayinta ya dinga ratsa zuciyarshi,sai ya dinga kwatanta ace qaramar qanwarsa ce haka a gabansa ta fuskanci rayuwar data bashi labari koma take kan fuskanta,hajar ya tuna,harbkwanan gobe bai mantawa da ita,bai manta yadda ta tafi ta barsu,tabon yana nan a zukatansu bai goge ba.

Duk da bata kalleshi ba hakanan take jin idanunsa a kanta,tunda take bata taba ganin namijin da yake mata kwarjini irinsa ba.

Batasan yaushe ya taso ba,sai tsintsarsa tayi zaune saman teburin,hannayensa sarqafe da juna,tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,hakan ya sanya zuciyarta soma bugawa da sauri da sauri,don kaf rayuwarta ba zata iya tuna sanda ta zauna haka da namiji tsakaninta da shi da qaramar tazara ba.

Kamar ya karanci zuciyarta ya dan sake ja baya tare da bada wata tazarar a tsakaninsu
“Bansan da sunan da zan dinga kiranki da shi ba….saboda sunan mama na kenan” ya fada cikin nutsuwa,shuru ne ya biyo baya kamar yana jiran yaji abinda zata ce,hakanan itama bata ce komai ba saboda bata da abinda zata ce din…tsahon sakanni sannan ya dora
“Sai kikaji an kawo kudi ba tare dana sanar miki ko na nemi jin ra’ayinki ba” ya sake furtawa still idanunshi a kanta,yanzun ma shuru yaga tayi ba tare da tace komai ba bayaga motsa jikinta kadan da tayi gami da cewa
“Uhmmm”
“Duk da banji ta bakinki ba amma bata baci ba…idan ba zaki iya aurar mutum irina ba kina iya fada saboda ‘yancinki ne….kin ganni talaka ne ni bani da komai sai rufin asirin Allah,bamai kudi bane ni haka nan ni ba wani bane…..naga ba irinmu asma’u keso ba ban sani ba kema ko ra’ayinku daya”
“Asma’u kace….kana magana ne kan yara masu gata…masu nasaba…..masu kudi….masu kyau….”
“Da ace kema duka kina da wadan nan zabinki zaizo dai dai da nata kenan?” Ya tari numfashinta ba tare daya bari ta gama fadin maganarta ba,kai ta kada
“Rufin asiri da mutunci shine biyan buqatata,da ace ina da ‘yancin zabar kalar mijin da nakeso to miji na gari zan roqa…..” Har cikin tsakiyar zuciyarsa kalaman ta suka sauka,sai yaji maganganunta sun burgeshi qwarai,yanayin yadda kalamanta ke a tsare kadai ya bayyana masa tsantsar nutsuwar da Allah ya mallaka mata,sai yaji yana son hirar tasu ta dore saboda haka yace
“Bayan kin samu miji na garin alal misali,taya zaki zauna da shi koda baku taba soyayya ba?” Shuru tayi tana juya tambayar tasa,itakam gaba daya soyayya ba matsalarta bace,abinda kawai ta sani shine mutunta juna,tausayi da jin qai,qauna ta haqiqa su take buqata,inama zata samu hakan?,take qiyastawa a ranta
“Soyayya Allah ne yake jefata cikin zukatan bayinsa,duk da ban dan danata ba amma nasan da haka,tunda na samu soyayyar inna laraba da Aliya ba tare da sun zamo jinina ba….amma mutunci da karamci sanin qima suna daga cikin jigon dake riqe zaman tare” baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ta iya magana ta hikima taqaitacciya kuna dunqulalliyar dake isar da saqo a dan qaramin lokaci
“Humaira…..zan kiraki da shi idan babu damuwa…..daga sanda aka daura mana aure sunanmu miji da mata a idon duniya…..”katseshi tayi
“Ina mamakin ta yadda zaka iya aure na wai…..” Girgiza kai take duk da ba dubansa take ba
“Kada ka yaudareni kada ka yaudari kanka…..ba aurena zaka iya ba….” Qaramin murmushi ya sake
“Ni dake gaba daya lamarinmu na hannun ubangiji,bamusan yadda zaiyi ba….ban taba kawoki cikin qaddarata ba kamar yadda kema nasan hakan ne…..bazan boye miki ba,hajiyata ita ta yimin izini neman aurenki,wanda na tabbata ta hangi abinda mu kanmu babu lallai mu hangeshi” shuru tayi tana jinjina qarfin hali da jarumta irin na mahaifiyar tasa,ita a karan kanta hankalinta da shekarunta da iya abinda take gani tasan uwa na nufin wani abu mai girma a rayuwar dukkan wani abu mai rai,duk da cewa ita din batasan dadin hakan ba amma tasan ita din ba qaramin abu bace….
“Zaki iya rayuwa da talaka?”ya sake fada yana katse mata tunaninta
“Ni din wace?”
“Hajiya ce mana” ya fada yana murmushi,itama batasan sanda siririn murmushi ya qwace kan fuskarta ba,abinda ta jima rabonta da shi,sai kuma ta maida fuskarta ta gintse,miqewa yayi tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihunsa sannan ya sake cewa
“Daddy ya saka rana gashi ni kuma ban shirya ba,infact ma ban soma shiri ba,kinsan abun talaka,lefe ma kawai aiki ne a wajenmu….ga wajen zama….toh..Allah muna gareka” ya fada yana dan daga kanshi sama,murmshi ta saki,ita din daba kowan kowa ba,ita din da aka cusa masa,ita ayshan daba wani gata ba,ita dinma tana ga Allahn,bata ga abinda zai damu kanshi ba akai wai wani lefe da wajen zama,tana daga kai suka hada ido da shi,ya jima yana dubanta ya kuma.karanceta tsaf ba tare data sani ba,sai ya dauke idanun nasa yana jin tausayinta,har ya danyi gaba sai ya dawo ya dauki lemon,irin lemonsa ne da yake yawan sha
“Bari naji zan iya shan kalar wannan,kinsan abinka da baka saba ba” ya fada yana kurbar lemon,bai aje ba sai daya shanye sannan ya aje cup din
“Zan wuce gida…..amma ba lallai ki sake gani na nan kusa….saboda muna tare da oga koda yaushe….kinsan qarqashin wani nake” yayi shuru yana jira ko zata ce wani abun a wannan gabar,saidai babu abinda tace illa
“Karka takura kanka…..”
“Ki gaida mutanen gidan”ya fada yana takawa zai bar wajen
“Ka gaida hajiya” ta furta ba tare data shirya ba,sai data fada din sai kuma tayi shuru tana raba ido kanta a qasa,tana jin kamar tayi azarbabi,gabanta na faduwa sanda taji tsaiwarsa,zuciyarta na kwabarta na ta cika azarbabi da yawa
“Zataji na gode” ya fada har cikin zuciyarsa yaji dadin kulawar data nuna.

_ina godiya a gareku,kuci gaba da yimin uzuri kan yanayin gajeran typing don Allah,na gode_

 

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*KO KUMA*
07067124863

 

*DB*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button