Daurin Boye 50
50
“duk yadda kika ce haka za’ayi madam,amma mu qarasa dake can gida”
“Shikenan” ta fada tana matsawa hanan ta soma shigewa sannan ta mara mata baya.
Tunda suka shigo layin mamaki ya cikata,saita kasa tantance gidan,don ba gidansu take gani ba,wani gida take gani mai dauke da ingarman katanga wadda duk girmanta mulmule take da sumunti da fenti mai kyau da daukar ido,sanda motar ta tsaya sanya kai kawai tayi cikin gidan cikin rashin qwarin gwiwa,don bata da tabbacin gidanne,hakanan bata da tabbacin jama’ar gidan har yau sune mazauna gidan.
Kamar ko yaushe mafi yawancin matan gidan suna qarqashin bishiyar da zamanta ga zame musu kamar al’ada,saidai a wannan karon bishiyar tafi kyau da qawata gidan fiye da lokutan baya,sakamakon siminti da aka yiwa ilahirin fadin gidan,sallamarta ita taja hankalin duk wanda ke zaune a wajen,gaba daya ido yayo kanta yayin da suka mimmiqe tsaye wasu sukayo gaba inda take
“A’ah,lale maraba sannu da zuwa”
“Maraba da matar allaji halifa”
“Sannunku da zuwa indo,indo mutanen birni”irin wadan nan kalaman dake nuna maraba da mutum su suka dinga furta mata,kowacce fuskarta wasai da fara’a,karo na biyu a rayuwarta da taga soyayya makamanciyar wannan.
Gaba daya suka dunguma dakin inna yelwa,wanda a yanzun ya zama babban falo da dakuna guda biyu a cikinsa,an sauya shi bayan gyaran da aka yi masa lokacin bikinsu,gaba daya mamaki ya cikata na waye ya iya irin wannan aikin a dukka gidan duk da kyau da yake dashi.
Tamkar inna yelwa zata goya ayshan haka ta rasa inda zata ajeta,kyakkyawar daddurma mai girma da taushi aka shimfide mata,kana ta umarci biyu daga cikin matan ‘ya’yanta suje su dorawa ayshan wani abun
“karki wahalar dasu inna yelwa,mukam a qoshe muke”
“Ke ba irin cimar da kike zato bace” inna yelwar ta fada tana dariya,murmushi aysha tayi
“Allah mun qoshi inna,amma ban sani ba ko zuwa anjima”
“Toh ina zuwa” ta fada tana ficewa don ta bada sautu a samo mata fura da nono mai kyau,saboda ta sani indon mai son fura da nono ce a baya,saidai sum ranar kasuwa idan ‘ya’yanta suka kawo haka za’a dama a rabawa kowa fana kallo bata da rabo duk yadda takai ga son furar,saidai ta sude a kofin wasu,sai tayi saurin kauda wannan tunanin daga zuciyarta,sau tari idan ta tuna saita dinga jin babu dadi ita kanta cikin ranta.
“Gaskiya aysha ke ‘yar gata ce,kowa sonki yake?”
“Hmmm,hanan kenan” aysha ta fada tana dan qaramin murmushi,haka rayuwa take,a duk sanda kaga wani bawa cikin wata ni’ima saika yiwa kanka sha’awarta kota birgeka,harma wani lokaci ka yiwa kanka sha’awarta ba tare da kasan irin qalubalen daya fuskanta ba kafin yakai ga wannan bigiren.
Suna zaune aka kawo furar a dame an jefa qanqara a ciki ta dauki sanyi,bude faifan dake kai tayi,kallon furar tayi tana tuna wani lokaci can baya,sai taji gaba daya ta fice mata a kai bata bata sha’awa ba,saboda haka ta turawa hanan gabanta
“Bismillah sis kisha” ja hanan tayi gabanta ta soma shan abinta,ta mata dadi sosai saboda sanyi da suger data sha
“Ke bakya sha indo?” Inna yelwa ta tambayeta,murmushi kawai aysha tayi,a dacan baya wani lokaci daya shude,lokacin da take da buqatarta,lokacin da take sha’awa da qulafucinta aka hanata,hakan ya sanya a yanzu ma sam bata sha’awarta,bata baiwa inna yelwa amsa ba murmushi kawai tayi mata,sai jikin inna yelwan yayi sanyi,kwalin da tasa aka shigo mata dashi ta bude ta fidda tsarabar kowa ta lissafawa inna yelwan,fuskarta washe da fara’a take jerowa ayshan addu’a da fatan alkhairi,sai tayi zugudi kawai tana kallon innan,lafuzan da tunda ta budi ido tasan me duniya ke ciki bata taba jin makamancinsa a kanta daga bakinta ba,saidai ta jiyo akasin hakan
“Allah ya baki miji indo dan albarka,mijin da ina jin kaf zuriyata babu yarinyar da zata samu kamarshi,hannun kyayta Allah yayi masa,ki duba yadda duk wanda ke cikin gidan nan sai daya dandani arziqinki indo,ba shakka kedin mai qashin arziqi ce,ki qara masa godiya bisa aikin da yayi mana,ki duba kaf fadin karkarar nan babu gida ya namu dana kakanki salihu” mamakin khaliphan ya kamata,yaushe duka yayi wannan aikin?,cikin shi ko anni ba wanda ya taba nuna mata anyi ko a fuska,ya Allah,wadan nan wanne irin mutane ne masu kyakkyawar zucuya har irin haka da Allah ya hadata dasu?,dame ita kuwa ayshatu zata sakawa rayuwarsu?,khalipha…khalipha sunan data ringa maimaitawa kenan a ranta har zuwa wani lokaci,bayan hanan ta kammala sha suka nufi gidan mero.
Ta samu mai jego lafiya ita da yaronta,nan ta zauna suka kacame da hira,hirar da suka jima basuyi irinta ba,itama kwali guda ne na tsarabarta,itadai dukka mamaki take,waita yaya khalipha yasan kowa yasan kuma siyayyar data dace da kowa?,waye ya gaya mishi?.
Godiya mero ta dinga yi sosai,kaya ne turamen atamfofi da rigunan jariri masu kyau da tsada,hira suka dinga wadda suka jima basuyi irinta ba,sun tuna baya sosai,sun tuna abubuwa kala kala,na dadi da akasin haka,hanan kam tana waje suna hira da saddiq dinta,basu bar gidan meron ba sai qarfe kusan goma na dare,gidan inna yelwa suka koma,a sannan tuni har an saka musu shimfida,qatuwar katifa ce mai kyau da taushi da bargunan rufa.
Aysha na kwance rub da ciki tana danna wayarta yayin da hanan ke sakawa kanta hula suna shirin kwanciya
“Matar khalipha….baki gayamin ya akayi aka haihu a ragaya ba” murmushi tayi kafin ta kashe wayar ta aje,sannan ta dubi hanan sosai
“Muhammad khalipha mijina ne,munyi aure babu jimawa ya tafi qaro karatu nima nayo kust qaro nawa,yanzu haka aurenmu bai cika shekara ba,saidai mun kusa”
“Kai aysha,ashe duk solamu kawai kike,kuma ban taba ji kinyi maganarshi ba tunda muke dake” numfashi ta sauke tana kwanciya rigingine gami da lumshe idanunta kana ta bude
“Munyi aure ne ba tare da dukkanmu muna son junanmu,tausayi shine abu na farko daya jawo qulluwar aurenmu…..saidai bazan boye miki ba….” Aysha ta fada tana sake mirginawa ta koma rub da ciki saidai ta takore jikinta da gwiwar hannunta tana duban hanan
“Ina jin wani abu na daban akan khalipha wanda bansan meye shi ba,ina jin wata shaquwa aduk sanda muke tare,hakanan inajin wata kewa a duk lokacin da yayi nesa dani,ina jin tausayinsa a duk lokacin dana tuna gwagwarmayar rayuwarshi,akwai abubuwa da yawa da nakeji baqi a kanshi wanda bani da amsar meye su…” Murmushi sosai hanan ta saki wanda yafi kama da dariya
“Akwai ayar tambaya akanki aysha…saidai bazan gaya miki ba nima,kamar yadda kika jamin rai akan sanin kina da aure nima sainaja miki,saida safe” ta fada tana juyawa zata kwanta,dariya aysha tayi tana girgiza kai,bata ce da hanan din komai ba ta juya itama ta kwanta
Bata zata ba don har ta fidda rai taji muryar hanan din
“Aysha….koda baki soma son khalipha ba dab kike daki afka,dukkan abinda kike ji dangane da khaliphan ina kyautata zaton soyayya ce da qauna mai zafi” waiwayowa tayi gaba daya tana duban.hanan gabanta na dukan uku uku kamar taga khaliphan,gira hanan ta dage maya fuskarta qunshe da murmushi tana bata tabbacin abinda ta gaya mata
“Qwarai kuwa,shi so yakan iya farawa da tausayi,wani lokaci kuma daga faduwar gaba,tsoro,daduwar bugun zuciya a duk sanda taga abinda takeso din,yawan kallo,yawan shuru da nutsuwa a sanda kuka hada muhalli dashi,saboda haka nake miki albishir…..barka da zuwa duniyar soyayya” ta qarashe tana dariya,kai ayshan ta girgiza tana duban hanan fuskarta qunshe da murmushi
“Ban yarda da wannan sharhin naki ba malamar love” saita maida kanta ta kwantar
“Ki gama qi fadinki tsaf da kauce kaucenki,baki da wata makawa kan zancena,zaki ce kuma na gaya miki nan da wani qanqanin lokaci” itama hanan din ta fada tana gyara rufarta tare da gyara kwanciyarta,shuru aysha tayi tana sauraronta tana fidda boyayyen murmushi,
saidai can qasan ranta tana taraddadin rashin jin khalipha da bata yi ba har a sannan.
Washegari suna idar da sallar asuba ta zari slippers dinta tayi gidan suna koda akwai wani aikin da zasuyi a lokacin tabar hanan tana bacci,tasan yanayin yadda mutan qauye kesa asubanci,haka kuwa tayita cin karo da mata jefi jefi,tana tsayawa suna gaisawa,wanda hakan yana musu dadi sosai.
Sanda ta isa kuwa ana shirin yanka abun suna,ta gaisa da ‘yan uwan mero dake rumfarta ta tsallake uwar daka inda meron take tana shiryawa,mero na dariya tace
“Indo baki manta da al’ada ba,na zaci birni tabi jikinki ai ba zaki iya wannan asubancin ba” dariya tayi ta amshi yaron da tuni anyi masa wanka an shiryashi tsaf cikin daya daga cikin rigunan da khalipha ya sako masa,kyau yaron yayi sosai dama kuma kyakkyawa ne,ya debo babarshi xam,sai taji ya bata sha’awa
“Tushiya masomin dawa mero,ta yaya zan manta usulina”
“Wannan gaskiya ne,aike indo kam Allah ya baki,duk yadda akaso ayi da rayuwarki Allah bai nufa ba,gashi da yake ke din ‘yar qwarai ce irin halak daular da kika samu bata sanya kin manta da tushenki ba,bakya qyamatar kowa cikin ‘yan garinku,kowa sanbarka yake dake” cewar iyalle kishiyar babar mero wadda ke shigowa dakin ta tsinci zancan da sukeyi,murmushi mero tayi kaman yadda yasha itama shi tayi,tana zaunw suna hira da mero harta kammala shiryawa,tayi kyau cikin atamfa abinta,tanajin an shigo da abun sunan za’a soma gyarawa ta ajiye yaron tana cire hijabin jikinta ta rataye
“A’ah ina zaki kuma?” Maro ta tambayi aysha tana dubanta
“Aiki mana”
“Wanne aiki duk ga mutane nan,kiyi zamanki muyi hirarmu karki bata jikinki,inake ina bakin murhu ma” dariya aysha tayi,duk basusan irin uban aikin data tashi ta saba dashi bane,hakanan bata taba samun sararawa ko salamar aiki ba sai bayan data auri khalipha
“Mero kenan,aikin kuma ai da yana kisa da ban kawo iwar haka ba,bata jiki kuma mero idan a kanki ne ba kayana ba har fatata zan iya batawa,idan kin manta halaccinki a gareni ni bazan manta ba,ke kadaice wadda ta tsaya dani a sanda duniya ta juyamin baya,kin manta randa muka fara qawance,ranar da ‘yan uwana suka taddani bakin rafi zasumin duka kika qwaceni daga hannunsu?” Dariya mero kawai take tana girgixa kai,ba shakka alheri danqo ne baya faduwa qasa banza,ita ta mance yadda abun ya kasance amma har yau gashi ita indon bata manta ba
“Tunda sai kinyi jeki kiyi ki dawo muyi hirar” aysha na dariya ta fice,ko su sunso hanata amma ta karbe hanjin ta gyarashi fes ta kuma dorashi kan wuta,sai data gama suyar a sannan rana ta dan fito tacewa meron bari taje ta dawo ta duba baquwarta.
Sanda ta koma ta tadda hanan a bararraje ita da inna yelwa suna kwasar hira kamar sun jima da sabawa,har tayi wanka abinta ta kuma karya da lafiyayyen kunun gyada daya sha madara da kuma qosai,idanun inna yelwar a kanta tunda ta shigo take kaffa kaffa da ita,kiran daya daga cikin surukanta ta kira ta hadawa ayshan ruwan wanka
“Jeki abinci inna karima,zan iya hadawa da kaina” ta fada tana zare hijabin jikinta
“Banda abinki indo da kin bari ta hada mikin,inake ina jan ruwa yanzu” dariya ma maganar ta inna yelwa ta bata,bata mantawa akwao sanda take wani azababben zazzabi haka ta tasota gaba kan sai taja ruwan,data gaya mata tana jin jiri ne tace ko zata fada cikin rijiyar sai taja,haka kuwa akayi wanda da qyar tayi guga uku,tana cikin na hudun jiri ya debeta gugan ya koma rijiyar,ita kuma Allah ya kawo mero a dai dai lokacin ita ta riqeta,bata tankawa inna yelwar ba ta daura zani da hijabi ta fice abinta ta debi ruwanta cikin babban dakin girkin da aka yi musu taja ruwa ta sirka ta shiga bandakin da aka yi cikin daya daga cikin dakunan dake falon inna yelwar,wanda ta shaida mata shine nasu da zasu dinga sauka a ciki.
Tana zaune tana karyawa jifa jifa tana duban inna yelwa,wadda ta taqarqare tana faman jansu da hira,ita a yanzu bata yadda ba qaunarta take?,haka aysha kewa kanta wannan tambayar cikin mamaki,data gama tare suka fice da hanan,wannan karon maimakon gidan mero gidan inna kulu suka nufa,shima dai gidan tun daga waje tasan tabbas aikin khalipha ya sauka ta kanshi,sanda ta gansu ita dinma da yake ba baya bace wajen son abun duniya kamar zata goya ayshan,itadai kallon kowa take
“Mamarki kuwa ina zaton yau zata shigo garin” cewar inna kulu,da mamaki take duban innan,tunda suke bata taba sako mata zancan innarta a tsakaninsu ba sai yanzu,bata ce komai ba wanda hakan yadan sanyayar da jikinta saita sauya hirar,awa biyu kawai sukayi mata suka wuce gidan sunan,a can hanan ta sake abinta,ta dinga yiwa mejego da ‘yan suna hoto,ita abun qayatar da ita yake,da yake su iyaye da kakanni ‘yan haifaffun cikin gari ne,kusan bata da wani qauye da zata nuna tace na kakanninta ne.
Duk hidimar nan da ake hankali da tunanin aysha na kan khalipha,tana shirin tada sallar la’asar taji shigowar saqo,cikin hanzari ta sanya hannu ta dauko wayar tana dubawa
_ina cikin aminci da kulawar ubangiji,na gode qwarai da kulawa_
Haka kawai taji amsar bata gamsheta ba,amma don kada ta takura shi saita haqura ta tada sallarta.
A ranar suka koma makaranta da yammaci lis,wanda motocin daukarta ma su sukayi jiranta,tana jin zuwan umminta garin a sanda suke shirin ficewa daga takai din,saidai ko kusa ko alama bata kwantanta dosarta ba bare taje wajenta.
Koda wani satin ya kewayo taje gida weekend kuma gida taje wajen daddy,tayi sa’ar samunshi a gida kuwa,sun jima suna hira dashi sosai,wanda hakan ya baqanta ran mummy,irin ci gaba da sauyin da take gani tattare da ayshan ya soma tabata,saita tuna asma’unta,wanda kusan rabin wahalarta ta dawo wuyansu,bata tabaji aysha tace ehmmm dazai nuna tana cikin wani hali ba bare takai ga furtawa har duniya ta sani.
????????????????
Qarfe biyar ne na yammacin ranar,suna zaune ita da mummyn ta a falon samanta,kayanta ne da suka zo daga lagos a bude suna lissafi ita da mummyn na kudaden kayan da sunan wadanda za’a rarrabawa.
Saman ya hawo yana amsa waya da alama shigowarsa gidan kenan,baiyi ko sallama ba ya ratso falon,suka hada idanu da mummyn,baiko nuna alamun ya santa ba ya samu daya daga cikin kujerun falon yayi zamanshi yana ci gaba da wayarshi,dif asma’u sukayi ita da mummyn ganin ya sanyasu gaba yana waya,sai daya kammala sannan yace
“Barka da yamma” yayi maganar yana latsa wayarshi ba tare daya nuna da mummyn yake ba,hakanan ta amsa saboda tasan da ita din yake,irin gaisuwar da ada idan yazo wajen asma’un yake maya kenan,banbancinta da waccar kawai yana kallonta yake gaidata,a sannan data danyi qorafi sai asma’un tace yanayinshi ne haka,haka mummyn ta qyale maganar ta biyewa son ran asma’un.
Mai aikinsu ya soma qwalawa kira,cikin mintina qalilan sai gata ta shigo,cikin girmamawa ta risina masa ya gaya mata abinda zata kawo mishi,dole mummy ta yiwa asma’u sallama,ganin abun na hamid ba girma ba arziqi.
Sanda mummyn ta fita mai aikin ta shigo ta shirya masa komai sannan ta fice,wata sabuwa kuma ya samo don tuni ya sallami wacar farkar tasa ya gaji da ita,idanunsa nakan kayan da salma ke lissafawa ba tare data ko dubeshi ba,lissafi yake cikin ranshi,so yake kawai ta kulashi suyi wani abu ta yadda zai samu damar cewa ta masa asarar wani abun ya debi lesunan gabanta ga kaiwa budurwarshi.
Tana sane taqi kulashi,don a yanzu ta gaji da hamid ta gaji da aurenshi,kamar ita asma’u tana ganin bai cancanci ta rayu da hamid cikin irin wannan uqubar ba,tana da kyau,tana da gata tana da usuli,ba shakka hamid bai cancanci ci gaba da zama da ita ba.
“Ke…wato saboda wuyanki yayi kauri kina ganin mutane baki iya musu sannu da zuwa ba ko?,kuma saboda rashin tarbiyya a gaban babarki amma bata tsawatar miki kota nuna miki rashin dacewar abinda kika aikata ba” abinda bai sani ba shine,ita kanta asma’un dama hanya take nema,saboda hama ta miqe a fusace cikin daga murya tace dashi
“Dakata hamid,karka sake kiran uwata saboda ita din ba sa’arka bace,sannan rashin tarbiyya aikao za’a tambaya wannan,tunda baka iya zama da matarka ba kaga kuwa daga wajen tsoho aka….” Bata kai aya ba ya wanketa da wani lafiyayyen mari
“Karki sake ki qarasa,wanda kike shirin zagi shi ya bada kudin da kika gani kika maqale min”
“Ni ka mara hamid?,….”
“An marekin ko kina da abinda zakiyi?”kai take kadawa kuka kamar zai qwace mata
“wallahi zakasan ka mareni,ka mari aurenka,yau saika sakeni,saika bani takardata” wata wawiyar dariya ya saki yana jan tsaki,komawa yayi ya zauna saman kujerar daya tashi a kai yana kwance agogon hannunsa mai tsada ya sanya hannunshi cikin abincinsa
“Aikin auru kenan har abada,idan ma kina mafarkin zan sakeki ne to kinyi kuskure,don ni ba shashasha bane,nasan ciwon kudina” daga haka yakai abincinsa baki ba tare daya sake bi ta kanta ba.
Dakinta ta shige cikin kuka ta dauko jakarta da mayafinta ta fito,ko kallonta baiyi ba,itama hakan yayi mata dadi,saidai bata gane manufar sharetan da yayi ba sai data je bude qofa taqi buduwa,sai daga bisani ta gane muqulli ya saka mata,dawowa tayi gabanshi cikin hargagi ta tsaya
“Ka tashi malam ka budemin qofa,don wallahi daga yau na gama aurenka na gaji”
“Ni kuma yanzu na fara aurenki wlh,don ba more komai cikin abinda na kashe miki ba” wani qululun baqinciki ne ya taso ya tokareta,me yake nufi kenan?,yana son yayi mata qwalelen rayuwar da ta shiryawa kanta samu a gaba?,yana nufin fa bazai saketa ba,wanda hakan dai dai yake da cewa haramiyarta rayuwar da takewa kanta hasashe.