Furar Danko Book 2Hausa Novels

Furar Danko Book 2 Page 19

Sponsored Links

 

‘…..!!

 

Related Articles

1️⃣9️⃣

 

……..Murmushi Daddy yay masa tare da sake damƙe hannayensu cikin na juna sannan ya fara da faɗin, “Tun ranar dana wayi gari da salwantar maƙudan kuɗaɗe a cikin Company hankalinna yay masifar tashi, nabi diddigi tako wane fanni amma ban fahimci komai ba akai. Na shiga ruɗani matuƙa da tunanin ta ina zan iya samun waɗan nan kuɗi haka, dan ko za’a saida duka ƙaddarar dana mallaka a wancan lokacin bazasu biya ko kaso biyu bisa goma na abinda ya salwanta ba. Ina cikin wannan ruɗani da ɗimuwar Alh. Sulaiman ya shigo rayuwata………” kaf ya kwashe labari ya sanarma Uncle Yousuf da jikinsa ke wata irin tsuma, ga hawaye shaɓe-shaɓe kaca-kaca da fuskarsa kamar wani ƙaramin yaro. Shima dai Daddy ɗin hawaye yake, ya jawo Uncle Yousuf jikinsa ya rungume yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Sai da yaji ya bar kukan sannan ya ɗagoshi. Zama Uncle Yousuf ya gyara cikin dasashiyyar muryarsa ya ce, “Yaya miyasa ka iya barin wannan babban al’amarin masu nauyi irin haka a ranka. Miyasa baka taɓa sanar damu ba dan ALLAH? Haba yaya har wanene Sulaiman da makircinsa da zai maka irin wannan ƙullin haka ka zauna kallonsa?”.
“Yousuf ka fahimceni hakan dolene a gareni saboda dalili masu yawa. Sannan ma lokacinne bai yiba shiyyasa, maybe UBANGIJI yay masa talalane da kuma hukuntani akan kuskurena nima. Na farko na yarda da shi da kallonsa da siffa irin ta mahaifinsa na mutumin kirki kasancewar a haka yazo min. Sannan bazan so maida sharri da alkairi ba a yanayin riƙon da mahaifin nasa yay min. Sannan dolene nayi komai domin kare ku a matsayinku na ahalina, dan shekarunka a lokacin sunyi ƙanƙantar da bazaka iya fahimtata ba yanda ya kamata. In da ban shanye komai ba za’a iya cutarmin da ku tako wace irin siga musamman ma kai, dan ko ita Kareema na hanata fita aikine daga baya bisa wannan dalilin, amma duk sai kuka fahimci cewar saboda Mawaddat ne. Eh saboda itane, dan ita ta ƙirƙiri hakan dan kuɓutar da Kareema daga sharrin Sulaiman batare da koni na fahimci hakan ba sai daga baya. Sai kuma lokaci da baiyi ba kamar yanda na faɗa, dan kasan komai na ALLAH ne sannan yanada lokacinsa.”
“Hakane Yaya na kuma yarda dakai. ALLAH sarki Maman Mawaddat munata zarginta akan abubuwa da yawa. Ciki harda tunanin ko asiri tai maka a farko, sai daga baya nima na fahimci ba haka bane saboda wasu dalilai. ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata.”
Cikin lunshe idanu Daddy yace, “Amin Yousuf, ai shiyyasa zargi bashi da amfani. Akoda yaushe da ace munama duk wanda ya shigo rayuwarmu uziri akan al’amuran rayuwa damun zauna lafiya da samun salama a zukatanmu”.
“Hakane Yaya. Amma duk da haka akwai abinda kayi da har yanzu basu wanke a zuciyata ba. Na farko akan Mawaddat daka nisantata da samun karatun Addini dama sakaci akan tarbiyyarta. Na biyu nuna mata goyon baya akan duk abinda tai dai-dai ne harda nuna ƙyamar talaka a matsayin mijinta. Why Yaya? Bayan nasa wannan ba ɗabi’un da iyayenmu suka horar da kai bane ba”.
Ɗan jimm Daddy yay cikin tsantsar damuwa. Kafin ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya zubawa Uncle Yousuf. “Tabbas Yousuf wannan shine babban kuskuren da nai da cutar da rayuwar Mawaddat a rayuwata da bazan taɓa yafema kaina ba. Da farko halin Sulaiman ya rufemin ido da abinda naji dangin mahaifiyar Kareema na faɗa mata. Sai nake ganin nisantata da ƙasar kamar yanda mahaifiyarta ta roƙan tun farko kamar shine masalaha agareni da ita. Namanta shi UBANGIJI shine mai tsarewa a duk inda kake. Na tauye rayuwar Mawaddat akan rashin ilimin addini da kaita wata ƙasa da kafirci yafi ƙarfi a gaɓar da komai idan ta gani bazai zama abin ƙi ba a gare ta. Wannan itace jarabawata ni da ita. Maybe hakkin yarinya da Sulaiman yayma fyaɗe na ɓoye ne bayan nasan gaskiya UBANGIJI ya jarabceni da hakan, shaye-shaye kuwa a dalilin haɗa hannu da nai da su Sulaiman da bamu san iya adadin yaran da wannan safarar tamu ta gurɓatawa rayuwa ba duk da ban sani ba inaga shine nan UBANGIJI ya jarabceni akan ta. Sai kuma soyayyar da na dinga dana sani akan ƙin nuna ma mahaifiyarta har sai da ta roƙa gareta bayan ita ɗin jinina ce shima ya taka rawar gani. Sai tausayi da ya zama jagora Da silar zama komai. Ban taɓa ƙin Aliyu a zuciyata ba game da alaƙarsa da Mawaddat. Hasalima a kullum cikin tashin hankali nake kar adalilina su Sulaiman su cuta masa. Saboda har sacesa sun taɓa yi Sulaiman ya bashi aiki akanmu ni da ita. Amma yaron nan ko sau ɗaya bai taɓa gwada cutar damu ba. Yousuf baka san irin kalar ƙaunar da nakema yaron nan bane. Wlhy a duk sanda ya kawo Mawaddat gida nakan laɓe naita kallonsa da sanya masa albarka. Ko kuɗi da gida da mota dana bashi na bashine bada wata manufa ba sai don nima na ƙyautata rayuwarsa kamar yanda UBANGIJI NA ya ƙyautata tawa da silar Baba Garko, sai dai idan na fito da sigar da za’a kalla a masalaha komai zai iya faruwa da shi. Saboda yanda ya tsunduma kansa a al’amarin Mawaddat wanda na tabbatar zai iya cutuwa har sakawa nai ƴan sandan farin kaya na bin sa batare da ya sani ba. Inaga bayan aurenka ban taɓama wani aure kukan farin ciki ba sai na Mawaddat, dan a randa aka ɗaurashi na kwana yima ALLAH godiya, hakama randa ta tare na kwana roƙon ALLAH yasa gidan zamanta ne. Amma sai Kareema take ganin al’amarin nawa a juye. Ko nawa auren na farko dana biyu duk sunzo da dalilai ne, dan haka ban jisu a jinin jikina ba kamar wannan auren, ni kaɗai nasan irin addu’oi da nake maka a zuciyata. A randa na kirashi game da barinta ta fita aiki nayi hakane dan na tunzurashi da kai ku hanata fitar, dan hakan da zanyi ne kawai zai sake tabbatar min da yaron zai iya abinda nake fata akan Mawaddat. Sannan zai iya juyata a yanda kowane namiji ya kamata ya juya gidansa bawai ita a matsayin mace ta juya shi ba. Sosai na dinga dariya akan maganar da ya faɗa min, na yini raina fes, sai dai a fuska kowa ya gagara gane kaina har Kareema. Yousuf ina son Kareema sosai dan matar ƙwarai ce, sannan ita ɗin jinin jikina ce, zuciyata na mata uziri akan abubuwa da dama. Soyayyarku a gareni ta dabance Yousuf, ku nakema kallo tamkar iyayena, dan kuna iya gayamin gaskiya duk ɗacinta. Garama Khareema tana jin shakkata, wasu lokutan takan haƙura ta shanye”
Shiru kawai Uncle Yousuf yay yana kallon Yayan nasa da murmushi a fuskarsa mai ƙayatarwa, a zuciyarsa kam sai ayyana (Namijin duniya) yake. Tare da jin nadamar abubuwan da ya dinga yi game da ɗan uwan nasa musamman zargi. Cikin ƙarfin hali Daddy ya katseshi da tambayar ina Smart yake a yanzu?. Kai tsaye Uncle Yousuf ya sanar masa komai akan Smart daya sani da ga wajen Abdull-Hameed Coach. Sosai Daddy yaji tausayin yaron ya ratsa masa zuciya, tare da ƙaunarsa ta haƙiƙa na sake ratsashi…
“ALLAH ya bashi nasara akan burinsa ya kuma yimasa albarka” Daddy ya faɗa yana miƙawa Uncle Yousuf wayarsa. Uncle Yousuf dake amsa addu’ar Daddyn ya amshi phone ɗin ya tsirama hoton ƙyaƙyƙyawan jaririn ido, tunani yake ina ma yasan wannan fuskar?. Kasa hasasowa ya sashi faɗin, “So cute Yaya, yaron wanene haka da nake jinsa a raina tamkar jininmu”. Murmushi Daddy yay mai haɗe da ƴar dariya, sai kuma ya dafa ƙafaɗar Uncle Yousuf ɗin da faɗin, “Jininka ne Yousufa. Dan ka zama Grand father yanzu”.
“Grand father? Ta yaya Yaya? Ni da bayan Mawaddat ɗina ban aurar da kowanne ɗa ba, duk da itama an sanar mana tana da ciki, sai dai rashin sanin ina take yasa bama musan yaushe ne haihuwarta ba”.
Sake faɗaɗa murmushin Daddy yay da tsare ƙanin nasa da ido dan san ganin irin reaction ɗin da zai nuna. A hankali ya furta, “Ai Mawaddat ɗin taka ce ta haihu jiya ɗin nan…”
“What!!!!”.
Uncle Yousuf ya faɗa da ƙarfi cikin wata irin zabura da ta saka jikinsa har yana karkarwa. Cikin rawar murya ya ce, “Yaya Please karka min wasa irin wannan dan ALLAH. Wlhy zan iya maka kuka”.
Dariya sosai Daddy keyi masa, kafin ya jinjina masa kansa alamar tabbatarwa. “Babu wasa a maganata Yousuf, bakaga ɗan na maka kama da ƙanin naka Aliyu ba.”
“Ya subahanalillah! Yaya dan ALLAH mafarki nake ko ido biyu? Idan a barci nake jin wannan zancen ka taimakeni karka bari na farka. Idan ko a zahiri ne ka faɗamin dama kasan inda Mawaddat take duk wannan kaiwa da komowar da nake yi”.
Daddy dake murmushi har yanzu ya kamo hannun Uncle Yousuf ya sake zaunarwa a kusa da shi. “Please relax sweet heart. Ai ina sane da duk wani shigi da ficinka, na Barka ne har zuwa irin wannan ranar ta yau sannan kasan gaskiyar al’amarin. Dan na sanka da rashin haƙuri farin ciki zai iya sakawa ka buɗe min aiki. Ai tun a randa Dada ta tabbatar min Mawaddat na’a wajenta na ƙara tsananta bibiyar Sulaiman. Saboda na tabbatar duk inda Dada zata kaita sai da gudumawarsa. Nace maka na tafi Hong Kong ne kawai dan na ɓatar da kowa a lissafi, da ga can na bibiyi Sulaiman ƙafa ya ƙafa har zuwa ƙasar Canada da ya nufa shi da ɗansa. Ban wani sha wahala na a bibiyar tashi ba na gano inda Mawaddat take. Sai dai ban zauna ba na kamo hanya na dawo, tare da jin ƙarfin gwiwar barinta cikin ƙudirar UBANGIJINA. Sai dai na saka wani yaro Usman ɗan Alhaji Bashir Sa’eed dake Canada cigaba da bibiyar min al’amarin su dama na gidan gaba ɗaya. A bakinsa naji Mawaddat na ɗauke da ciki, har ma da kaita asibiti da sukai domin yunƙurin zubar da shi, da ceto cikin da yay har zuwa yau……..” kaf ya kwashe komai da ya sanar masa. A abin mamaki sai ga hawaye share-share Uncle Yousuf na sake zubarwa. Daddy ya cigaba da faɗin, “Ina kan sani na barta can a wajen nasu duk da nasan Sulaiman zai iya cuta mata, sai dai kasancewar Usman na sanar min duk wani motsinsu ya sani sake samun ƙwarin gwiwa. Nasan hakan shine kawai zai sake koyama Mawaddat sabuwar rayuwa ta fahimci mi ake nufi da gundarin rayuwar ma kai tsaye. Ta kuma san wanene Sulaiman ta yanda duk sanda za taji komai game da shi abin bazai zo mata a bazata ba balle harta cutu. Sannan zata sake sanin muhimmancin mijin da darajarsa tare damu family nata gaba ɗaya. dan a yanzu haka Dada ta sanar mata mijinta ya saketa”………✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*

Zafafa

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*[ez-toc]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button