Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 25

Sponsored Links

PAGE TWENTY-FIVE*

 

Juyowa sukayi a tare cikin mamaki dukkansu suke kallon Hajiyan da tayi kicin² ta riqe Umaimah gam tare da qara daka masa tsawa tace “ka saketa nace Hameed wlh kaji na rantse gdannan yau dagani sai ku Daddynku baya qasar nan saboda haka dole ka saki Umaimah bazaka kashe marainiyar Allah ba Hameed tsine maka zanyi idan kaqi yimin biyayya”

Related Articles

 

Cikin tsananin tashin hankali ya zube a gurin muryarsa na wata irin karkarwa yace “na roqeki Hajiya kiyimin rai ki ceci rayuwata wlh inason matata ita kadai ta saura me tausayina a duniya Hajiya kada ki rabamu wlh nayi miki alqawarin bazan qara kusantar Umaimah ba har abada amma ki barmu tare Hajiya tana sona inasonta….” daukeshi da mari Hajiya tayi tace “bawai tausayinka ne banaji ba amma kaima kasan zamanka da Umaimah cutawa ne a gareka da ita kanta saboda haka dole anan ka saketa” miqewa yayi yana layi kamar dan giya ya nufi qofa zai fice Umaimah tayi saurin riqoshi cikin kuka me ban tausayi tace.

 

“Kada ka fita cikin tsinuwar mahaifiyarka Uncle bawai saboda wannan dalilin ne kawai Hajiya takeson rabamu ba tanason rabamu ne saboda banida kowa banida gata don girman Allah Hameed kada ka sabawa umarnin Hajiya ka sakeni Hameed ka sakeni nace…” rufe mata baki yayi yana girgiza Mata kai Amma ya kasa cewa komai sai rawa da jikinsa yakeyi ya janyo Umaiman ya hadata da qirjinsa “Allah ya tsine….” da sauri Umaimah ta janye jikinta daga nasa ta cukumi wuyansa tace “wlh bazaka taba kasancewa cikin tsinuwar mahaifiyarka akaina ba dole ka sakeni Hameed” qara rufe mata baki yayi da sauri yana girgiza mata kai yana hawayen tausayin kansa cikin tashin hankali yace “Haj….” katseshi ta kuma yi tace “wlh saika saketa Hameed”

Cikin fitar hayyaci yace “shis.. shikenan na…na sakeki saki day….” bai ida qarasawa ba wani mugun jiri ya debeshi yayi baya kansa ya hadu da glass din qofar ya fadi tim tare da ballewar jini a kansa.

Nufarsa tayi da gudu tana sakin wata qarar tashin hankali tana cewa “shikenan kin kasheshi Hajiya mun shiga ukun mu…” riqo hanunta Hajiyan tayi cikin tashin hankali tace “kada ki tabashi babu aure tsakaninku” zubewa tayi a gurin tayi zaman tan bori kanta da kwakwalwar ta na juyawa jin abin take kamar a mafarki “Hameed ya sakeni” ta fada a fili tare da miqewa tana dafa bango ta nufi dakinta tana shiga ta zube a qasa sai yanzu kukanta ya dawo sabo zuciyarta nayi mata suya kanta na juyawa “ Innanillahi wa innah ilaihir raji’un Allahummah ajjirni fi musibati wa’akalifni khairin minha”

 

Su taketa maimaitawa batare da tunanin mafita tafi awa daya a zaune a gurin batasan lkc ya tafi ba saida wayarta tayi qara sannan ta iya rarrafawa ta daukota sunan Sa’ud tagani ta daga ta kara a kunnenta tare da fashewa da kuka tace “Sa’ud Hajiya ta rabani da farin cikina na shiga ukuna Sa’ud zuciyata zata fashe Ina tunanin mutawa tace ta iskeni a wannan lkcn” salati Sa’ud ta dauka tace “ta rabaku Umaimah yanzu Ina Hameed din?” bata iya bata amsa ba saboda wata hardewa da numfashinta yakeyi saurin kashe wayar tayi inda Sa’ud ta miqe cikin fitar hayyaci ta dauki motarta ta nufi gdan Umaiman amma tana zuwa get man din ya sanar da ita kusan sati batanan da mugun gudu ta juya ta nufi Sokoto road tana zuwa ta fara doka horn megadin yazo ya bude parking tayi cikin tsananin firgici ta bude ko kashe motar batayi ba ta shiga cikin gdan.

 

A durqushe ta sameta riqe da cikinta tana ta murqususu tare da cije lebe tana hawaye shiga tayi da sauri ta ruqota tana cewa “Subhanallahi Umaimah kada ki mutu don Allah tashi maza tashi mubar musu gdansu Umaimah na yarda maraya bashi da gata a wannan zamanin wannan dalilin yasa na ware kaina saboda kunci da baqin cikin rayuwa ya isheni” tana fadin haka tana hadawa Umaimah kayanta a cikin handbag dinta tare da jan akwatunan kayanta guda biyu dake jingine a jikin bango ta fita da gudu² sauri² ta zuba a motar ta dawo ta dauki wayar Umaiman tare da magungunan ta ta dagota da iyakar qarfinta tana juya kai tana kuka tana komai tasata a mota ta shiga taja tare da zuge baqin glass din saboda gudun kada get man din ya gansu suka fita unguwar Hotoro suka nufa cikin wata hadaddiyar Unguwa me suna Farawa layout suka shiga unguwar ganin yanda Sa’ud taga aminiyar tata tana riqe cikine yasata nufar wani babban asibiti da ake kiza Zeenat clernic and digonostic ta shiga tare da fita da sauri tayima likitocin bayani suka nufo motar aka kamata ranga² aka nufi cikin wani daki da ita suka duqufa aikinsu.

 

Bincike sukayi sosai akanta kafin su gano inda gizo yake saqar tashin hankalin da take cikine ya assasa mata hawan jini me tsanani wanda yayi tasiri wajan lalata cikin dake jikinta yakeson fita amma babu hali saboda haka suka fara qoqarin ceto rayuwarta ta hanya cire mata cikin sannan suka daura mata ruwa tare da neman jini kasancewar kafin zuwansu asibitin ta zubar da jini yafi leda biyu kallon likitan tayi tace “Dr indai akwai abamu mu siya sai nayi muku transfer bamu da kudi cash a hanun mu” bai wani damu ba yaje ya bincika yayi sa’a aka samu laida daya irin blood dinta ya maqala mata tare da rubuta mata magungunan qarin jini Sa’ud tayi musu transfer ta account dinta kamar yanda ta fada masa naira na gugan naira har 140,00 saida aka mayar da Umaimah dakin hutu sannan Sa’ud ta samu ganinta lkcn har tayi sallah take gida ta dawo tana kwance a gadon idanunta a lumshe tayi wani fari ta dashe saboda rashin Isasshen jinin da take fama dashi.

 

Kama hanunta Sa’ud tayi cikin hawaye tace “Sannu bloody kiyi hqr ki daina kukan nan kowanne bawa baya wucce qaddararsa kinji” bude idonta ta rinqayi a hankali harta saukesu tar a fuskar Sa’ud idanunta naci gaba da malalar da hawaye tace “ina Uncle Hameed Sa’ud wanne hali yake ciki ya mutu ko?” kada mata kai tayi tace “yananan Umaimah bazai mutu ba insha Allahu” lumshe idonta ta kumayi daidai shigowar likitan ya fara dubata yace “alhmdllh jiki yayi kyau sai fatan Allah ya mayar dana aika” bude idonta tayi da sauri da tsananin mamaki tace “kamar yafa ban gane ba?” shafa gashin goshinta Sa’ud tayi tace “damuwar da Hajiya ta jefaki a ciki ce tayi sanadin zubewar cikin jikinki Umaimah…” Miqewa tayi a tsorace tace “da gaske ya zube shima Innanillahi wa innah ilaihir raji’un shikenan farin cikin Uncle ya zube meyasa ya zube Dr inason cikina yanzu shikenan nayi biyu babu ba ubansa babushi”

Tausayinta ne ya cika zuciyar Sa’ud ta kamota ta miqe tace “insha Allahu komai zaizo qarshe Bloody nasan akwai ciwo a rabaka da mijinka batare da neman shawararka ba amma babu komai akwai Allah kuma Ina tabbatar miki Hameed bazai iya rabuwa dake ba saboda kece kadai zaki iya zama dashi ki biya masa buqata yanda yakeso kuma ya samu gamsuwa dake 💯 saboda haka karma ki wani damu tunda kinji qwari tashi mu qarasa gda kiyi wanka mu nemi abinda zamuci kinji” shidai likitan binsu kawai yakeyi da kallon mamaki “dama matan aurene ku?” Yakasa jurewa ya tambaya kallonsa sukayi a tare Sa’ud ce tayi qarfin halin cewa “eh Hussaina tace am don Allah Dr mace da aka saketa da ciki kuma cikin ya zube matsayin iddarta yake a musulumci?”

 

Shafa kansa yayi sannan ya zauna yace “ma’anar iddah tana nufin tsarkin mahaifa tsarkin mahaifa kuwa shine yin jini bayan rabuwar aure to wacce aka saketa da ciki kinga bazatayi jini ba harsai ta haihu shiyasa iddarta take da wahala bayan ta haihun da zarar ta haihu to iddarta ta cika ko ranar zaa iya daura mata aure kinga kenan a shari’ance matar da aka saketa da ciki tayi bari koda a ranar da aka saketa ne to ita ta tsarkaka wannan shine amsarki a taqaice wallahu wa rasulihi aalam” yana fadin haka ya miqe ya fita tare da basu sallama Sa’ud ta kama hanunta suka fita a sanyaye jikin Umaimah yake ji takeyi dama zata iya mayar da cikinta jikinta jikinta yanzu shikenan ta fita daga sahun matar auren Abdulhameed?

Wasu hawaye masu zafin gaske suka gangaro mata da haka suka shiga motar suka nufi cikin unguwar sunyi tafiya me dan tsayi sannan sukayi parking jikin wani dan matsakaicin flat house me kyau saida Sa’ud ta tabata sannan ta dawo hayyacinta ta bude mata qofar ta fito tana daga qafarta daqyar ta nufi qofar da taji Sa’ud din na budewa ta bude mata ta shiga tanabin gdan da kallo wata qofar taga tasa key ta bude nanma Umaimah tasa qafarta ciki wani sanyi da qamshi me dadi ya daki hancinta ta lumshe idonta duk da zuciyarta babu dadi amma taji dadin qamshin ta bude idonta tanabin parlourn da kalloh yayi kyau sosai sai qofofi guda uku da suke a kulle, zubewa tayi a saman kujera tana sauke ajiyar zuciya tanabin parlourn da kallo amma gaba daya hankalinta na wajen Uncle dinta “ko wanne hali yake a ciki?” Abinda ta tambayi kanta kenan.

Tana zaune Sa’ud din ta shigo ta cire hijjab dinta tana murmushi tace “tashina kenan daga bacci kika kirani kinga ko rigar baccin ban cire ba na zari hijjab na fita” kawar da kanta tayi gefe saboda batason hayani ko surutu itama bata qara yimata mgnba ta bude daya cikin qofofin ta shiga bata jima ba ta fito ta bude dayan dakin tace “bloody ki shiga ki kwanta kafin na sama mana abinda zamuci nasan zuciyarki tana cike da zargi na da tarin tambayoyi akaina da kuma tunanin meyene yasa na daukoki na kawoki nan to kiyi hqr zan baki amsa nan da yan mintuna”

 

Tana gama fada mata haka ta riqo hanunta suka shiga dakin data bude mata mamaki ne ya cika zuciyar Umaimah ganin dakin a shirye tsaf kamar na matar aure gado wadroop madubi da bedsat komai dai akwai sai wata qofa da take nuna alamun bathroom ne qarewa dakin kallo tayi kafin ta zauna a gefen gadon ita kuma Sa’ud ta fita ta shiga daya qofar ta fara hada musu abinci.

*************************

 

Kusan awansu hudu da zuwa asibitin amma har yanzu bai farfado ba ko numfashi baya iyaye saida taimakon na’ura daga Hajiya har Aunty Zarah ba qaramin tashi hankalinsu yayi ba sun ma manta da baiwar Allah Umaimah da halin da zata iya shiga sai kaiwa da komowa sukeyi tare da likitocin a haka har dare yayi sai goma saura Zarah ta dubi Hajiya tace “Hajiya wai meye yayi coorsing din matsalar nan ne Ina matansa da banga kowacce a gurinnan ba?”
Gaban Hajiya ne ya fadi ta miqe da sauri tace “na shiga uku na Zarah amanar Allah wlh na manta da ita” tana fadin haka ta fita da sauri ta tari dan sahu ta nufi gdan tun daga parlourn ta fara ganin gdan a hargitse dakinta ta nufa tana qwala mata kira amma shiru tura kanta tayi a dakin ta fara dube² amma babu alamar mutum a gurin kunna light din dakin tayi idanunta ya sauka akan inda Umaiman ta zauna dazun taga yanda jini ya bushe a gurin da sauri ta shiga ta banka qofar bandakin amma babu wata alama ta an shiga toilet din sake fita tayi tana kalle² a parlourn sai yanzu idanunta ya kai kan Nihal da Maliha da suke kwance a qasa kan tiles suna bacci matsawa tayi da sauri gurinsu tana haskasu fuskarsu duk tayi jirwaye da alamun kuka sukaci har sukayi bacci hankalinta ya dada tashi ta nufi wajen gdan ta fara qwalawa me gadi kira ya iso da gudu ya rusuna tace “ina Umaimah?”

 

Da sauri ya kalleta yace “banganta ba nidai bayan ansa yallabai a mota kun tafi naga wata motar tazo amma banga wanda ya ke ciki ba kuma bata dade ba ta fita…”bata tsaya bata lkcn sauraron shirme ba ta juya gdan tana safa da marwa itakam taga ta kanta da yaran daga nema musu sauqi ta jangwalo fitina yanzu ina Umaimah ta tafi wata sani a garin wa take dashi a garin bayan su da zata wajenshi ta zauna? Tambaya ce mara amsa Hajiya take yiwa kanta har tana runtuma tuntube saboda tashin hankali.
Debe yaran tayi ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu ta kuma shiga dakin Umaiman itace leqe har qarqashin gado miqewa ta kumayi tana rarraba idanu ya shege a rabon gado sai yanzu ta lura ma duk wani abu da yake mallakin Umaimah babushi a dakin zubewa tayi a qasa tana karanto Innanillahi wa innah ilaihir raji’un kanta yana wata muguwar sarawa a fili tace.

 

“Na shiga uku ni Zulaiha yau naga bala’i me hakan yake nufi Baby ta gudu saboda na rabata da abinda zai cutar da ita? Allah ka sani bada wata muguwar manufa nayi hakan ba Allah naji tsoron kada yaron nan ya hallaka ta ne Allah ka fitar dani kunyar duniya ka jefa marainiyar ka hanu na qwarai” tana maganar tana kuka me ban tausayi wayewar garin yau tayi danasani tafi dari tilon danta yana kwance baisan inda kansa yake ba ga marainiyar Allah ta gudu “wallahi saboda ni bazaka rayu cikin tsinuwar mahaifiyar kaba Hameed ka sakeni saika sakeni Hameed ba wannan dalilin ne kadai yasa takeson ta rabamu ba akwai wani qulli a zuciyarta…” kalaman Umaiman ne suka rinqa dawo mata tare dana Hameed din lkcn da yake kuka yana cewa “ki barni na rayu da farin cikina Hajiya nayi miki alqawarin bazan qara kusantar Umaimah ba har abada Hajiya ita kadai ta ragemin wadda takejin tausayina Hajiya kada ki rabamu tana sona kuma kema shaida ce inasonta babu wanda ya isa ya raba tsakanin hanta da jini…..”

 

A matuqar sanyaye ta miqe ta fita zuwa dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran wayar Umaiman tun kiran farko aka fada Mata a kashe wayar take amma bata daina Kiran ba har saita charging wayar tata ya dauke ta koma ta kwanta zuciyarta tayi mata wani mugun nauyi daidai lkcn kiran Daddy ya shigo a tsorace Hajiya ta daga cikin rawar murya tace “hel…lo Daddy” bai iya amsawa ba yace “nakira wayar babana najita a kashe na kira ta Umaimatu itama a kashe nayi miki Miss call yafi ashirin baki daga ba Zarah ta kirani tacemin babana yana asibiti cikin mayuwacin halin da baisan wake a kansa ba meye yake faruwa ne”…….

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*

 

[1/15, 8:46 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/

*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_

 

*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

 

*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI’U UMAR*
*®FAUZAH*

 

[email protected]

 

Ki biya kafin ki karanta ta GTbank akan wannan account number: 0255526235; sai kiyi screenshot ki tura wannan number: 09013718241;
Ko katin waya MTN or Airtel ta wannan number:09031307566:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button